Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 30

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 30

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 30: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 30. Cikin sanin makamar aikina da ƙwarewa na cire drip da ke jikinta…

4,472 words

Cikin sanin makamar aikina da ƙwarewa na cire drip da ke jikinta tare da mata alluran da za'a yi a lokacin, bayan duk na gama kana na ke tambayarta ya take jin yanayin jikin nata duk ta min bayani. Na dubi ɗaya daga cikin ƴan uwan nata wacca ke tsaye daga bakin gadon, ni dariya ma ta so bani don kamar a tsorace take, ganin cewa dukka ƴan boko ne cikin ƙwarewar harshen turanci idona cikin ƙwayar idonta na ce,"Kun bata drugs ɗin ta?".

Kamar bata gane me na ke nufi ba ne sai ta tsaya lakato kamar wadda ta samu kallo kallo, ta ɗan ban haushi na canja fuska ina mayar da dubana zuwa ga ɗayar wacca ta taso tana cewa,"Wallahi na sha'afa kin ce ƙarfe biyu za'a bata, kuma yau ɗin kawai aka yi kuskuren hakan".

Faɗa na kama musu akan sakacin da suka yi na rashin bada maganin akan lokaci, kafin daga bisani na nusar da su muhimmancin bayarwar akan kari. Muna haka Sister Badiyya ta shigo, ai fa sai ta amshe ganin ina magana a sanyaye wai da sunan faɗa na ke yi, tunda ta fara musu faɗan suka shiga bata haƙuri saɓanin ni da shiru kawai suka yi sai wata dattijuwa ce ma tace za'a kiyaye gaba. "Yanzu sai wani abu ya faru da ita ba fata ake ba ku janyo mana ace rashin iya aikinmu ne".

Dattijuwar ta taso daga inda take tana cewa,"Ayi haƙuri Nurses ba za'a kuma maimaita kuskuren ba".

Sai da na lallaɓata kana tayi shiru, domin idan aka kaiwa Dr gulma zai iya zamar mana matsala ace mun zo kan patient muna ɗaga murya kamar bamu san ya nurse ya kamata yayi ba idan irin hakan ta taso, balle su da suke ganin kuɗi suka biya maƙudai ba kamar asibitin gwamnati ba. Barinta nayi tana musu bayanin jinin da Dr yace za'a saka mata. Ni kuma office ɗin Dr na shiga na basa file ɗin mara lafiyar tare da masa bayanin yanda tace min tana ji a jikinta, yay rubuce rubucen da zai yi da sake rubuta magunguna a ciki yace ga drugs ɗin da za su ƙara siya, sannan ya faɗawa Badiyya ta sanar musu da batun ƙarin jini leda ɗaya da za'a yi mata.

Ina fitowa daga office ɗin sai ga Badiyya ta ƙaraso, ta dafa kafaɗana muka nufi recieption tana ce min. "Ke naji wata cikin ƴan uwan marasa lafiyar can na ƙusƙus akanki, saura kaɗan na daki bakinta to sai naji maganar da take yi kamar ta sanki, kar naje ko ƴar uwarku ce in abin kunya".

Murmushi nayi da sautinsa ya fita sosai, ba sai na tsaya tambayarta wacce a cikinsu ba balle ta tsaya min dogon bayani, tuni na rigada na san wadda take nufi, ni kaina nayi mamakin yacca nayi fuska na ɗauke kai, wanda na san kuma hakan dole yaywa wanda ya san ka sanshi ciwo, nuna tamkar ban ganta ba da nuna tamkar ban santa ba dole zai sanya ta magantu, ba kuma nuna ko in kulawar ganinta ba ne zai daketa illa yanda ta ganni, dole tayi mamaki kuma dole ta girgiza. Muka gama abinda zamu yi a phermacy don mun ɗan jima tsaye da su Manager muna magana, a hakan ma banda na zame Badiyya da surutu ba tahowa zata yi mu tafi ba. Can ɗakin mara lafiyar muka koma, ina kallonsu ɗaya bayan ɗaya na ce,"To cikin ku wa zanyi wa bayani?".

Suka yi min nuni da Dattijuwar ɗazu, nace,"Mama ga wannan total amount ɗin drugs ɗin da Dr ya sake rubutawa ne, ayi payment yanzu sai kuje can pharmacy already an haɗa magungunan karɓowa kawai zaku yi, amma don Allah Mama kar ayi wasa ƙarfe shida na yamma za'a dinga bata".

Ta amsa da to. Ni kuma na ƙarasa gaban gadon domin ƙara yi mata allurar da Dr ya sake bayarwa, ina cikin mata ne wadda tun ɗazu ƙwayar idonta tamkar zata faɗo ƙasa don kallona tace,"Ni kuwa kamar na san fuskar nan".

Nayi kamar ban jita ba har na gama aikina, har sai da zan fita ne ta sake maimaitawa tana tasowa da sauri ta dafa shoulder ɗina. Na waigo na mata kallon sama da ƙasa sai duk ta dabarbace, irin kallon da na watsa mata yasa ta ɗauke hannun nata da cewa,"Am so Sorry".

Na ce,"Lafiya?". Ta ce,"Ce nayi kamar na sanki, ko ba Sa'ida ba ce?".

Na kalleta kamar ba zanyi magana ba sai kuma nace,"Ehh sunana Nurse Sa'ida".

Ta kaɗa kai,"Haba nifa in ce, Sa'ida tsohuwar matar Nazifi ko?".

Na ɗaga gira da ke nuni na tooo ina kallonta tare da girgiza kai nace,"Anya kuwa? Ƙila na miki kama ne da wadda kike magana".

Baki ta saki da al'ajabin da ya bayyana muraran a fuskarta ta sake cewa,"Tsohuwar matar Nazifi fa me kalwa na ke magana, ke ba ki gane ni ba ne?".

Nayi saurin girgiza da cewa,"Ban gane ki ba, kuma ban san ma akan abinda kike magana". Ina faɗin haka nasa kai na fice ina murmushi. Maɗaukakin mamaki yasa Zahra'u kama ƙugu baki sake tana bin bayan Sa'ida da kallo, kafin tace,"Kutmar amma yarinyar nan ta mugun manna min hauka".

Ƙanwar Babansu tace,"To ke kin santa ne? Ƙila kamannin kika gani".

Ta juyo tana dubansu tace,"Wallahi ƙarya take yi ta san akan abinda na ke magana, rainin hankali ne kawai da son ci min fuska, amma ta sanni sarai, Kishiyata ce fa".

Wata cikinsu ta waro ido waje,"Kishiyarki kuma? Kishiyarki ta gaske?".

"Hmmm". Ta faɗa tana wucewa ta zauna kan kujera tana jijjiga kai. "Kun san Allah kishiyata ce ada, ba fa wulaƙancin da ta min ne ya damen ba, mamakina ɗaya matsayin da na ganta akai, yaushe Sa'ida tayi gogewar da har ta taka matakin zama ma'aikaciyar lafiya?".

Ta kusa da ita tace,"Wai kina nufin kishiyarki ɗin nan da tayi sanadin mutuwar yarinyarki?".

"Ita fa! Kin san ai tun lokacin shari'ar nan suka rabu bata dawo gidan ba, to yanzu ace cikin shekaru shidda ta zama haka? Ƴar talakawa ce fa ina taje tayi karatun da har ta zo babban asibiti irin wannan aiki? Ke fa lokacin da muke tare na rantse miki da huwallahu ko turancin kirki bata ji, yo ina ma ilimin bokon, batta dai akwai ilimin addini ni kaina ba ƙaramin burge ni take ba a ɓangaren nan, Samiha na rantse da Allah na girgiza, Samiha asibitin nan fa sai waɗanda suka yi karatu a ƙasar waje ko kuma a makarantun kuɗi na cikin ƙasar nan suma sai manya manyan makarantun, kuma ko hanya za'a maka sai ka biyo ta babbar hanya, Daddy kansa ba ya cin alfarmar asibitin nan kina kallo duk nacin Naja'atu haƙura tayi, Samiha ta ina ta shiga ta fita ta zo nan? Albashinta fa yaci uwar nawa Samiha".

Wadda take kira da Samiha tayi dariya da cewa,"Yo ba bazawara ba ce, ke har kya yi mamaki, kika san manyan mutanen da ta ke bi".

Zahra'u tasha mur tace,"Ban son iskanci wanna irin furuci ne wannan, ku babu dama mace taci gaba sai kuce ai bazawara ce ga yanda akayi ga yanda aka yi, lallai duka zaurawa ƴan iska ne?". Tayi maganar cike da jin haushi har da su tsaki.

Samiha ta dafa kafaɗarta tace,"Maida wuƙar mene abin ɗaukan zafi, kema kin san dai tsakani da Allah akwai zaurawan da ke siyar da mutuncinsu ke majority ɗin su ma haka suke, kuma ina da tabbacin yarinyar nan na ɗaya daga ciki don haka ɗaya dai ƴar talakawa ba zata zo aiki wannan asibitin ba. To ke mene na ki a ciki don na faɗi haka? Ke ko iskancin ma kika yi ai ba za'a ce kin yi ba tunda ansan ƴar waye kuma dama tuni kina da aikin yi, cikin kuɗi kika taso cikinsa kike, to wa ya isa kuwa yace kina sahun zaurawa masu siyar da mutunci, ni ita ɗin dai na ke maganar shiga hotel da fitarsa ce ta kawota nan".

Zahra'u ta sauke numfashi kafin ta tuntsire da dariya. Duk suka kama kallonta. "Wallahi Allah Nazifi na hango! Idan ba yaga Sa'ida sai ya yanke jiki ya faɗi ba, kun san yanda ya wulaƙanta yarinyar nan kuwa shi da ƴan uwansa, ranar farko da ya fara haɗuwa da ni cewa yake matarsa bagidajiya ce, bata da wayewa, babu boko kwata kwata, babu aikin yi, mummuna shi kawai yana zaman dole da ita ne". Sai ta ƙara sakin dariya da cewa,"Allah ka haɗa Nazifi da Sa'ida, shegen Ƙwallo yaga yanda rayuwarta ta sauya".

Ƙanwar Babanta tace,"Du Allah ke rabamu da zancen nan, kamar fa muna cin namansu ne dukka. Kema kuma ya kamata ki yiwa kan ki faɗa ki koma gidan mijinki".

Tuni tasha mur tana faɗin,"Allah ya kiyaye ya tsare, haba Anty Amina ko maƙiyina ai ba ya min fatan na koma gidan Nazifi ba, mutumin da bai da ko sisi ina zan iya zama da shi, me yaci me ya ban naci balle ƴaƴa?".

"Yo ba da kuɗinsa kika auresa ba, me yasa ba za ki tawakkali ki zauna da shi cikin jarabawar da ubangiji ya aiko masa ba, ko don ƴaƴanki ma ai kya koma".

Ta cuno baki ta ce,"Komawa to sai dai ko wata Zahra'un amma ba dai ni ba, ƴaƴa kuwa ai na rantse ba zan taɓa ba shi ba, alƙalin ma kansa ya rattaba hannu ba zan basa yara ba za suke zuwa dai su gansa jefi jefi shima don ba yanda na iya ne ubansu ne dole, amma ina yarana ina rayuwar karkara kuma cikin talauci Allah kiyaye".

Ƙanwar Baban na su ta sake cewa,"To aikuwa dai ba ki kyauta ba".

Zahra'u ta jingina kanta da bango abinda Sa'ida tayi mata na tsayawa a ranta, Idanuwanta suka rufe hoton shekaru biyu baya na haskawa cikin idonta bayan haihuwar Mardiyya da ta ƙara yi don lokacin da ta sha maganin zub da cikin nan Allah bai nufa ya zube ba. Kwayar idonta ta haska mata hoto tarrr lokacin da hukuma suka zo tafiya da Nazifi da sunan yaci bashin banki bai biya ba, tana tunawa haka ya tsuguna gabanta yana roƙonta Allah Annabi har da hawaye akan ta taimaka masa da takardun gida ya siyar ya rage wani abu, tayi mirsisi taƙi lamarin har kotu tsakaninta da shi aka je, tace ita babu wani abu nasa da ya mallakawa yara ƙarya yake mata, haka aka yi ta bincike aka duba aka ga kaf wasu kadarori da yake faɗa yana da su duk mallakin zahra'u ne ba nasa ba, dole haka aka tasa ƙeyarsa gidan ɗan kande sai da ya shafe watanni bakwai a prison kafin ya fito. Itama fitowar tasa ba don an biya kuɗin ba ne an dai rage wani abu a ciki, kuma tasirin adu'a ne ma yay ƙarfin da har aka bayar da shi, mahaifinsa ne ya siyar da gidan da suke zaune sai ya nema musu gidan ƙasa wanda gaba ɗaya bai wuce dubu ɗari ba, gidan ɗaki biyu ne jal amma haka duk suka ruguntsuma suka koma. Sannan itama Zahra'u tayi imani darajar Iman da kullum ke kuka tana kiran Daddy, shi ne ta yarda aka siyar da gidan da suke ciki miliyan tamanin da biyar ta bayar da miliyan hamsin, aka haɗa aka bayar da miliyan casa'in, da yarjejeniyar duk wata zai dinga ba da dubu hamsin.

Ranar da ya fito kuwa daga kurku ta maka ƙararsa a kotu kan cewar ba zata iya ci gaba da zama da wanda bai haihuwa ba, kuma ba zata zauna da wanda bai da muhallin zama ba, bai da akin yi sannan bai da abin da zai ci da su don haka ya zama dole ya saketa, ta gama zama da shi har abada, haka akai ta daburwa tsakaninta da shi, duk taurin kan Nazifi kan ba zai saketa ba sai da ya sallama yay mata saki ukun da suka nema, domin shari'a da me kuɗi wahala ce, ya sha wulaƙanci kuwa a gun mahaifinta, kuma ko wata guda ba'ai da sakin ba sai ga sabon sammaci sun kuma kawo masa, sun kai ƙararsa gaban alƙali wai ya ce lallai sai ta ba shi yara alhalin ƙarya suka masa, tunda ta bar gidan bai waiwayeta ba duk da yana so yaga yaransa kuma wulaƙanci yasa yake danne zuciyarsa bai neme su ba, ga halin masifar da yake ciki na kai kuɗi da aka saka masa duk wata shi kuma babu sana'ar yi ko da ta ihu ce, haka dole ya rattaba hannu kan takardar da alƙali ya ba shi kan cewa Yara wurin mahaifiyarsu za su zauna ba za'a ba shi ba ko guda ɗaya.

Ya damu amma damuwar da yake ciki tafi wannan, don lokacin yana tsaka da tashin hankali, fitowarsa a bursun da ya zo ya tarar da gidansu faɗuwa yay, matan Babansa uku ace ɗaki biyu jal a cikin gida? Ga uban yara? Wai sai da dare yayi yaga kawai Malam yayi shimfiɗa a tsakar gida da shi da yaran maza, ɗaki ɗaya ƴan matan ke kwana a ciki ɗayan kuma Iyam da Amarya, don ita Ummaa tuni ta tafi gidansu, manyan samarin kuwa duka a ƙofar gida suke kwana, a lokacin kawai sai ya kama hawaye ya rasa dalilin wannan masifar, a barsa ma da lalurar mahaifiyarsa na rashin ƙafa da na magani kaɗai ya isa yay hauka, amma sam Zahra'u bata tausaya masa ba haka tace lallai sai ya ke tura kuɗin abincin yara da kuɗin makarantar Iman rabi, to ita yanzu ma bata san a halin da yake ciki ba.

****Ƙarfe uku na tashi daga aiki, akan hanya na yanke shawaran wucewa gidan Safiyya, ban ma kirata na sanar mata da zuwan nawa ba, kwana biyu bamu yi ko chart ba balle waya, sai fushi take yi da ni shine yau zanje na lallashi abata mu shirya, duk da wanda ma take fushin da ni akansa na mance da shi da babinsa, rabona da shi tun zuwan da yay, ni kuma wannan rashin neman nawa ya tabbatar min da ba son gaskiya yake min ba dama yaudara ce tsantsa, to Allah yasa ban faɗawa tarkonsa ba, zaluncinsa ya ƙare masa.

Falon Safiyya idan zaka kwana kana kwaɗa sallama babu me jinka, kuma ni na saba duk sanda na zo kaina tsaye na ke hayewa samanta, dama kuma bana zuwa ranar da mijinta yake gari, ba mazauni ba ne shi zaman kwana uku yake yi a sati. Na zare mayafina nayi cilli da shi saman kujera tare da jakata, kaina kansa ji nayi yay min mugun nauyi saboda haka na cire hular itama na jefar, na cire after dress ɗin ma, ribon ɗin ma na cire gashi ya baje a kafaɗa, Allah ya gani nayi mugun gajiya ga uwar yunwa da ke ƙwaƙwalar cikina.

Kwanciya nayi akan kujerar sanyi Ac na dukana ta ko'ina, sai kuma na tashi, da yake akwai wani switch na ƙararrawa shi ake dannawa ya isar da zuwan baƙo, naje nayi ta dannawa don ba zai wuce tana can tana aikin baccin da bata gajiya da shi ba, ƴan aikin nata ma inaga basa nan. Sanin cewar mijinta bai gari na zaƙe kamar gidana, ban da shamaki da ko'ina a gidan Safiyya, kai tsaye na wuce kitchen ɗinta sai miƙa na ke, na duba babu abinci sai na buɗe firij na ɗauko maltina, sai da na kusa shanyewa na sauke robar, sannan ne na ɗanji dama dama na fito ina faɗin Allah ka rabamu da ƙishiryawa da yunwa.

Da yake gaskiya abinci ba ya yankewa a gidan, in babu a kitchen to akwai a dining, saboda haka na nufi rumfar da dining table yake. Ina zuwa naja kujera zan zauna, a wani mugun tsorace naja da baya ganin mutum zaune kamar aljani, ina aikin zare idanu na ke kallon ko'ina musamman ma shi ɗin da na ke ganin kamar gizau, ƙaramar riga ce ta kaki a jikinsa kansa babu hula. Ko motsi bai yi ba abincinsa kawai yake ci hankali kwance kamar ma bai ji alamun mutum ba, duk sai na rikice naji kamar na saka ihu.

Haka na daskare a tsaye kamar wata soja, na kasa gaba na kasa baya, idona a rumtse ina jin kamar nayi kuka, takaicina ɗaya yanda na ke, kai babu ɗankwali na saki gashi, ga rigar jikina ta kamani daga sama, dogon wuya duk a waje. Bugun zuciyata ya ƙaru, mintinan da ba su fi biyu ba suka wuce, na buɗe ido a tsammanina ya tashi ya bar wajen sai naga har yanzu yana nan, ya gama cin abinci ya ture plate ɗin gefe, ya kwantar da bayansa jikin kujerar yana shafa waya, na saci kallonsa naga taunar cingom ɗinsa kawai yake alamun bai da wata matsala, babu ko tunanin ya kamata ya tashi ya bar wajen.

Nayi guntun tsaki a ƙasan raina ina cewa ƙabila ma dai sam ba su da kunya, ni na kasa barin wajen saboda yacca na ke amma shi bai da hankalin ya tashi ya bar min wajen tunda ya san ni ba muharramarsa ba ce, na ƙara jan tsaki wanda na san yaji don sai da naji saukar ido akaina. Na ɗaga ƙafa a hankali cikin jin kunyar kaina sai naji muryan Safiyya na cewa,"Me ya kawo aljana gidana? Me aka zo yi min? Saukar ƙur'ani ake min duk sati don haka aniya bil aniya tub tub, azo ayi waje bana neman ku".

Kamar in je in hamɓareta saboda takaici, na ɗaga ido ina kallon inda take tsaye na ce,"Dilla Malama ni miƙo min hulana da rigana".

Maimakon ta ɗauko tukunna ta taho wai sai da ta zo ta gama ƙare min kallo tana cewa ta ina na ke jiyo maganar jinnu, muka haɗa ido ta wani yatsine fuska irin nata na wulaƙanci kana ta dube shi tana masa magana cikin yare. Bai bata amsa ba ko da ido ya amsa mata oho ni ba kallon inda yake na ke ba, sai ta juya ta koma, sai da ta shafe kyawawan mintuna kana ta jefo min hular tana faɗin,"Kuma ban girka da mutum ba".

Na sunkuya na ɗauka hulan na saka, kamar zan bar wajen sai naji har ga Allah ba zan iya ba, ko bai kallona ji zan yi kamar ni ɗin yake kallo, yanzu sai in tafi na juya masa baya mazaunai na rawa? Inaa ba zan iya ba, kawai sai na dake naja kujerar nayi zamana, na kai hannu na janyo flask na zuba abincin, da ƙyar na ke iya kai spoon ɗin baki ina tauna kamar ba zan ba saboda duk na tsargu, gani na ke kawai kallona yake yi.

Dalilin haka sai na haɗe girar sama da ƙasa ina harare harare da murguɗa baki, karaf idona ya kai kan hannunsa ya fito da shi daga cikin aljihu ya aje bindiga a gabansa, gabana ya yanke ya faɗi, tuni na jefar da spoon ɗin ƙirjina sai bugawa yake yi, lokaci ɗaya zufa ta wanke min fuska, na kasa ɗauke ƙwayar idona akan bindigar, ba komai na ke haskowa ba sai lokacin da ƴan sanda suka ɗora min ita a goshi suna cewa na faɗa musu me na bawa Noor tasha ta mutu.

Hawaye ya sakko min zirrr, na ɗago kai na sauke kallona akansa, sai naga shima ni ɗin yake kallo kuma haɗa idon da muka yi sai kawai ya ɗauke nasa ya basar irin ma bai san da ni a wajen ba. [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR08FT5* Na aje wayar saman fuskata ina faman fitar da murmushi kamar sauna, sai daga bisani kuma naji raina ya ɓaci na kama jin haushin kaina, sai kace wata shashasha ma a soyayyar, ina neman zaƙewa daga ance ana sona sau ɗaya, to shi dama haka ma yake no text no call? Soyayyar ce bai iya ba ko kuma salon tasa kulawar kenan? Ko kuma ya gamata akan matarsa ta farko? Rashin nemana da bai yi ba fa tun zuwan farkonsa ya bani haushi sosai, don har ce nayi yana da girman kai, yana nufin kenan ma ba zan ja ajina ba tunda ni ba budurwa ba ce, sai yanzu da wani karkataccen bakinsa zai kira ni yana Baby, a'a Bebo.

To ni ina son miji me raha da zamu zama abokai bana son me ɗagawa, in ma zai sauke abinda ke kansa ya sauke, idan ba zai sauke ba yaje can ya nemi ƴar uwarsa ƙabila ko wadda zata iya da halinsa, Numbernsa na ƙara kalla da kyau don ko ya kira ba zan ƙara ɗagawa ba ehe, kar yaga ya kira ina ta wani zumuɗi ya zaci sonsa na ke yi. Ummani tace,"To ke ya kike ganin za'ai da waɗannan kuɗin? Dukka lefen miliyan ɗaya da rabi za'a haɗa miki? Ni fa kawai nayi shiru ne gudun faɗan Abbaanku, shi yana batun gwara ayi miki kaya na gani na faɗa kar su ce sun bada kuɗi masu yawa an riƙe. amma ai kuɗin ne sun yi yawa, a dai haɗa ko na miliyan guda ne, ke ni miliyan ɗin ma a wajena tayi yawa wanne sutturu za'a siya har na miliyan, ba gwara a raba biyu sauran a haɗa da wancan a bawa Sale kafinta yay miki kaya masu kyau".

"Kawai ma da zai dawo ya karɓi kuɗinsa da yafi". Na faɗa cikin muryar da ke shaida faɗa faɗa, ina ta gungunin masifa na ƙorafin yanda ma ya raina ni. Ta ce,"Uhmmm daga baya kenan, ni bana son gulma".

Sai na sami kaina da ɗagowa in kalleta, na buɗi ba ki nace,"To Ummani sai ka kama auren wanda bai san kulawa ba balle haƙƙinta, kuma ba zai ke nuna maka da gaske yana sonka ba saboda yana ji da kansa". Harar da ta galla min yasa na sauke kai ƙasa ina ci gaba da masifata ƙasa ƙasa. Lokacin Maman Yasmin ta shigo tana tsokana na da,"Amarsu".

Gaisheta kawai nayi ban ko ɗaga kai ba, Ummani tace,"Ƙyaleta". Suka shiga gaisawa Maman Yasmin ɗin na cewa,"Abban Yasmin yace min kina nema mana".

Ummani tace,"Ehh dama ce nayi ke da Nafisa ku zo ku shiga kasuwa ku haɗo kayan lefen nan, kunga wata guda kamar yau ne gwara ayi abu a tsanaki, gata nan ita ɗin kuma idan zata biku to".

Maman Yasmin tace da Ummani,"Tom shikenan, amma kinga ko za'a yiwa Mrs Arab magana a faɗa mata ga na iya adadin kuɗin da ake so ta haɗa, mu bar mata zaɓi nan da kwana uku za kiga ta haɗo su har akwatuna, kuma wallahi tayi masifar sanin makamar iya haɗa lefe, mayan bikin nan da ake duk ita ake bawa kwangila".

Ummani tace,"To idan kin san dai babu wata matsala ai sai ayi mata maganar ko".

"To shikenan bari a kirata ma yanzu, ke Sa'ida rubuta lambar wayata babu kuɗi, ai shegun kaya zata haɗa miki, da muka je bikin Surayya duk shegun less ɗin da kika ga tana sakawa ai ita ta haɗa lefen".

A ƙasan raina na ce ehh fa shigar Amaryar tayi kyau babu ƙarya. Na ɗau wayata ina,"Karanto lambar". "Oak, 07037599677". Ina gama dialling nayi saving da Mrs Arab Kano. Kiran lambar ya tafi na miƙa mata ina tashi na fita, ruwan wanka na ɗora kana na koma ɗaki na ɗakko wani ɗinki da zan ƙarasa haɗawa, masu shi na ta kirana na gagara ƙarasa musu.

Ƙarfe uku na fito a shirye don tafiya wurin aiki, tun uku saura na ke ta ganin kiran Salim na shigowa nayi biris naƙi ɗagawa, har aikowa yayi nayi saurin kora ɗan aiken kar ma Ummani taji. Na shiga ɗaki na yiwa Ummani sallama bayan ta min adu'a na fito, da zuwana soro kiran Maman Khairi ya shigo tana tambayana su siya min jugs ɗin tangaran yafi yawa ko kuwa? Nace ni na bar musu zaɓi kawai, tun ɗazu ta zo suka fita ita da Maman Yasmin yo siyayyan kayan kitchen lefen kuma kamar yadda ta faɗa ne sun gama magana da Mrs Arab zata haɗo komai ta kawo, ina jin Maman Yasmin na faɗin don Allah ta haɗa akwatu set uku, ni dai kam mun yi dacen sirikai don Matan Yayyuna kamar ciki guda muka fito, yanda Ummani ke yabon su haka suma suke yabonta ko ina suka shiga sai sun ce su kuwa babu abinda zasu ce da Allah sai godiya domin ya basu suruka ta ƙwarai wadda ta ɗauke su babu banbanci da abinda ta haifa, kuma babu takurawa sam a al'amuranta, to nima dai bana kukan rashin Yayyu mata don sun maye min gurbinsu, sai dai nayi kukan rashin ƙanne mata kawai.

Ina fita ƙofar gida nayi kiciɓis da mutum tsaye bakin mota shi da Yaya Al'amin, yadi ne jikinsa baƙi yay masifar masa kyau, duk yanda na so nayi masa kallo ɗaya hakan ya faskara sai da na ƙara kallonsa, Allah masanin ta inda farinciki ya samu damar lulluɓe ni, a ƙasan raina nace yay kyau kamar ba ƙabila ba, har wani kishinsa naji ya lulluɓe ni ganin ƴan matan layinmu na ta wucewa islamiya. Na kalla screen ɗin wayata da kiransa ke ƙara shigowa a karo na babu adadi, sai na ɗaga ido na kalle shi naga ni yake kallo yana jijjiga kai, hakan yaso ba ni dariya amma na fusge, hankalinsa ma ya dawo kaina gaba ɗaya ya bar Yaya Al'amin can yana ta faman zuba shi ɗaya.

Na sha murr na ɗauke kai kamar ban gansa ba, na ɗaga ƙafa zan tsallake na wuce a sumame kar Ya Al'amin ya ganni, aikuwa daidai nan naji yana cewa da ni,"Ke Sa'ida ba ki gan mu ba ne".

"Yaya kaina na ƙasa ban kula da ku ba". Na faɗi sa'ilin da na ke ɗaga ido na kalle shi zan harare shi, sai kuwa na kasa aiwatar da hakan dalilin ƙayattacen murmushin da ya sakar min wanda ya samu shiga har cikin ɓargon jikina, ga wani munafukan dariya da ya danne a saman leɓe. Ina ta ciccin magani haka na shiga motar, wai wai tunda uwata ta haifeni ban taɓa shiga mota me haɗuwa da tsada irin wannan ba, sai na zama kamar ƴar ƙauye har wani taɓa kujerun na ke yi da ko cire su a leda ba'ai ba, duk yanda aka yi sabuwa ce fil ma.

_"idan kika yi fushi da ni masoyiya hankali zaya tashi idanuwa su yi kuka, ki taimakawa soja kar ya zamo ragon namiji ai masa dariya"._

Haka ya shigo motan yana rera waƙar, da zummar in caccake shi da tsiwa amma ba shiri dariya ta ƙwace min har da sarƙewa, sai tari kwaf kwaf yay saurin miƙo min ruwa, na karɓa na sha idona har ya cika da ruwa tsabar dariya. Na miƙa masa goran ya galla min harara da cewan,"Kina wa me dariya?". Sauran dariyar na danne ina ɗauke idona a kansa idan ba haka ba tsaf zan ci gaba da dariya na zama kamar zararra.

Ganin bai da niyyan tashin motan na karkata ina dubansa na ce,"Please kar na makara".

Fuskansa a ɗaure yace,"Ba kina wa waƙana dariya ba".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull