Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 31
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 31: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 31. Nace,"Ayya sorry ba waƙanka na ke ma dariya ba". Sai ya jijjiga…
4,478 words
Nace,"Ayya sorry ba waƙanka na ke ma dariya ba". Sai ya jijjiga kai yace,"Akwai ranar ƙin dillanci, tara ki kawai na ke za ki shigo hannuna, har ni za kike ganin kirana ki ƙi picking, kuma ma tsawon sati guda ba za ki iya kirana ki ce kin yi missing ɗina ba kina sona".
A hankali na ce,"Ai ba ni na fara zuwa nace ina sonka ba da zan ke bibiyanka". "Kika ce me?". "Ba komai". "Har na tausaya miki yarinya".
Sai na kalle shi leɓena na daɗa talewa da murmushi nace,"Wacece yarinyar?". Da yatsansa guda ya lakuce min hanci yana faɗin,"Ke me dimple ɗaya da rabi".
"Sa ido dai babu kyau, har ina kasan ɗaya dimple yafi ɗaya".
Kawai sai ya saki wani murmushi irin nasa na shi kaɗai me tsada da ya kusa sumar da ni, murmushin da ya tsaya min a rai wanda tuni ƙwayar idona tayi capturing nasa, Rufewar ido da buɗewarsa shi kawai na ke gani. Cikin sati uku muka yi wani shaƙuwa na ban mamaki da Salim, shaƙuwan da zaka rantse mun fi shekara guda, ga wani fahimtan juna da muka samu a tsakani, sosai ya fahimce ni haka nima sosai na fahimce shi, zuwa lokacin na gane ashe nayi masa bahaguwan fahimta ne a farko, amma mutum ne shi mai sauƙin kai, ya iya mu'amala bai da damuwa sam sam, sai na ce kusan halin su guda da gidan su Safiyya a ɓangaren kirki da mutunta ɗan Adam, ba ɗagawa ba nuna shi wani ne ko ɗan wani ne, ga kyauta da son yin taimako abin hannunsa sam bai rufe masa ido ba, ina ganin hakan ne duk sanda ya kaini aiki ko ya ɗakko ni, ko idan ya zo gidanmu ya gamu da wani nawa, ko a hanya haka idan yaci karo da masu neman taimako, duk da ni bai fiya sakar min kuɗi ko bani abu ba, kyautansa bai wuce idan ya zo naje raka shi ya miƙo min sauran turarensa, sai wataran da ya cire agogonsa yay alwala na ɗauka na gwada sai yace ya bar min.
Na saki jiki da shi sosai ya zama best friend ɗina, bamu fiya waya irin bini bini an yi kira ba, hakan bai dame shi ba sai aka yi dace nima kuma dama ba na son namiji me nacin kira, ko da yaushe a waya ko idan yazo cikin raha mu ke da farin ciki gami da annashuwa, har idan ina tare da shi na kan manta komai, bana jin asaran ɓata lokaci tare da shi domin kuma a duk wata hira tamu sai na ƙaru da shi ɓangaren ilimi ne ko ita kanta rayuwa. Yanzu ko da abu zan aiwatar shi na ke kira na nemi shawaransa, har Safiyya ke min ciwon bakin soyayya tasa na kware mata baya, nace ba za ki gane ba ne Beb, tace ni kuwa na gane tunda na san waye Yayana.
Ya haɗa ni da Mahaifiyarsa mun yi waya da ita, ranar ji nayi kamar na nutse a ƙasa don kunya, matan free take na fahimci tana da kirki sosai, tayi ta jana da hira tun ban amsawa har na saki jiki naji ma kamar tare da Ummani na ke, tana tambayan yaushe zan zo in ganta, ban iya cewa komai ba sai ita ke cewa to zata zo da kanta taga ƴarta, Kakarsa ma wadda ta haifi Babansa har da aike ta yo min na wani atamfa ankara me shegen kyau. Har matarsa da yaransa duk mun gaisa da su, matar ma ita ne ta takura masa kan sai ya haɗa mu a waya, ni kishi yasa na ke ta zillewa ranar kuwa muna tare sai gata ta kira, muka gaisa da ita cikin mutunci da girmama juna, da farko ina magana a daddaƙile daga baya da na fahimci ita with all her heart take waya da ni sai na sake kawai, tace min ga yarana ma kafin su zo su ganni, ina ji yaran na tambayanta Maama waye take ce musu New Mommy ɗin su ce wadda Papa zai kawo ta haifo musu Baby Boy, ni dai nayi ta mamaki na ce to Allah yasa dai yanda ake faɗan bata da matsala hakan take, don ni har ga Allah idan na tuna da ita na kan ɗan ji fargaba haka, to amma shi kansa yana yawan faɗa min kamar yanda Ummansu Safiyya ke faɗa min Kudrat bata da problem zan ji daɗin zama da ita sosai, idan kishina ya motsa min zan ta cewa ya tafi wurin matarsa ya ƙyale ni, sai ya nuna min shi ba ya son hakan, yana son matarsa kuma nima yana sona kowacce da matsayinta a zuciyarsa, zai kuma yi ƙoƙarin ganin ya fita hakkin kowaccenmu.
Haka Salim yay amfani da salon soyayyarsa yay raga raga da zuciyata a lokaci ƙanƙane, ashe ma ni ban san komai ba a soyayya, soyayya tana inda aka iya a wurin mutumin arziƙi, har tsokanata ake a gida da wurin aiki saboda nema na ke na zauce kamar farin shiga, alerm ɗin wayata duk sai da na cire, in ƙarfe biyu da rabi tayi shi zai tashe ni in yi sallar dare, haka idan asuba tayi, da safe kafin na farka yay min text da daɗaɗan kalamai da suke sawa naji ni a gajimare, har idan ban ji daga gare shi ba na ke takura, in koma kamar mara lafiya, Salim ya mantar da ni duk sauran guntun damuwan da na ke yi na famin ciwo, banda wata matsala ni kam na yarda Allah ya kashe ya ba ni, domin samun namiji kamarsa a wannan marrar sai dacen ubangiji kawai, wai kafin ma na shiga cikin gidan nasa kenan, shi kansa yana faɗa min Baby ba ki ga komai ba a soyayyan da na ke miki da kulawa sai kin shigo gidana tukunna, duk da wani sa'ilin ina cewa Allah yasa kar ya sauya daga baya, aurena na baya yasa na gasgata zancen Namiji bai da tabbas.
Ya rage saura kwana uku biki, ana ta shirye shirye, ƴan ƙauyenmu duk sun zazzo wasu daga cikinsu, ni sai mamaki ma na ke ko a aurena na farko irin hidima da zumuɗin da ake a yanzu ba'ai a wancan lokacin ba, na farko kamar wani taron mutuwa haka aka yisa, ni ba'a farin ciki ɗari bisa ɗari ba haka suma iyayen nawa, amma a wannan kam farin ciki da zaƙuwar da na ke ciki sun kai kaso fiye da dubu, farin cikin Ummani har ba ya barinta rufe baki, ta kira wancan ta aikawa wancan, haka Abbaa na ma shi kansa kamar yanzu ne karon farko da zai aurar da ni.
Kuma wannan auren sai ya zo da albarka, domin kuwa wani buɗi ubangiji ya kawowa Abbaa, yanzu haka babban teburi ya kama a kasuwa, cikin gida kuwa sai da ya aje botikan fenti huɗu aka shafe mana shi kamar za'a aurar da budurwa, na lura dai kowa yafi farin ciki da wannan auren hatta yayuna, idan nayi magana sai Ummani tace bazawarar ai me daraja ce, ni dai sai in murmushi kawai, idan na ɗauko kuɗi na bayar ayi amfani da su sai Abbaa yace a'a hakkinsa ne yay min komai, nauyinsa ne ba nauyina ne ba, in adana kuɗina za su min amfani nan gaba, amma yanzu na bari su zasu yi min komai, hatta kuɗin ɗunkuna duk shi ya bani yay min kashedin kar na sake na karɓi ko sisin Salim,
Abbaa yace shi ba zai ƙarya ba amma zai iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin ya fitar da ƴarsa kunya, haka ya yankewa Yayyuna kuɗi suka haɗa dubu ɗari biyu su huɗu, aka haɗa da kuɗin aurena dubu ɗari biyar, sai kuɗin kayan lefena da aka rage Ummani ta kaiwa Sale dubu ɗari uku tace don Allah yay min furnitures masu na miliyan ɗaya irin wanda ake yayi. To da yake ma aiki ya mayar da shi Delta state satin baya aka yi masa ƙarin girma, Kudrat ma da ta kira ni a waya tana zolayana wai ni ƴar sa'a ce, dama sun gaji da zaman Edo ɗin, ba yanda ba su yi ba a tashi a gidan yaƙi sai ga shi dole tasa an tashi babu shiri, ita da yarana suna min godiya. Salim ɗin na cewa ba sai anyi min kayan ɗaki ba, nayi karaf kuwa nace sam bai isa ba, na wani hasala kamar wanda ya zage ni, na dinka fifiƙa ina masa masifar ai ba'a gidan babu ya tarar da ni ba, Abbaa ma ba zai yarda da zance ba, mahaifina zai yi min kayan ɗakina idan ma ya san ya siya ya aje ya kwashe abinsa ya fitar da su idan kuwa ba haka sai dai idan ba zan zauna a gidan nasa ba, ni kuwa ai ban manta gorin da Nazifi yay min ba sanda zai ƙara aure na cewan iyayen matarsa har kayan ɗaki sun mata ba irin iyayena ba da suka bar miji da ɗawainiyan komai.
Saboda yanayin nisa zuwa can garin sai Sale yace zai ɗiba mutanensa suje Delta ɗin a haɗa kayan acan maimakon ace daga nan za'a a tafi, kuɗin mota ma kansa wani babban lamarin ne, hakan kuwa aka yi aka tafi da Yaya Al'amin da Abbayo, Salim ɗin yace akwai wurin zama a gidan nasa ba sai sun nemi hayan wajen kwana ba, Abbaa yace to gwara ayi tafiya ɗaya kawai tunda bikin ƴan kwanaki ya rage a tafi ayi jere gaba ɗaya, sanda ake fito da bahhunan kwanuka sai da nayi matuƙar mamaki, Ummani ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba har sai da na tambayeta ina ta samu kuɗi haka tace rufin asirin Allah ɗan abinda take tarawa ne, sai kuma gudumawar da ƙannenta da yayyunta suka aiko mata, kayan kitchen masu kyau da tsada ni har ce nayi ma ina zan kai su.
Kwanansu biyar a can, ranar da suka dawo kuwa suna bawa Ummani labarin gidan, sai santinsa suke yi su maza ma kenan, Anty Shafa da su Anty Lubna da Maman Khairi duk sai lokacin suka ji rashin jin daɗin da Abbaa bai bari sun je tare ba, shi kuma yace ne da akwai ƴan uwa acan ne sai a tafi da su, to ba za'ai rashin hankali ba kawai aje a tarewa mutum a gida, matarsa ma ba zata ji daɗi ba. Abbayo na faɗin wallahi Matar Salim ɗin tana da matuƙar kirki, haka ta karrama su kamar ƴan uwanta, motsi kaɗan sai ta aiko yaranta su tambaye su ko suna da buƙatar wani abun, abinci kuwa har ci suka yi suka ture, yace kuma idan suka yi aiki suka gaji da kanta take zuwa tace musu ga babban falo can ta buɗe musu ko za su yi kallo, iya kwanakin da su kai sun mata shaida me kyau.
Da daddare na samu Abbayo ina tambayansa ya fasalin gidan yake, yace min babban gida ne flat ba bene, ɓangarena bedroom uku ne kowanne da banɗaki a ciki, sai falo biyu da kitchen, amma fa kowanne ɗaki tafkeke ne, Yace babu laifi Sale yayi ƙoƙarin yin kaya masu kyau don duk zubin kayan turkey yayi sai kallon ƙurulla ne ma zai sai za a gane b kayan ƙasar waje ba ne, kuma bedroom biyu dukka an zuba kaya a ciki, dama yanda muka yi da su nace idan sunje sunga bedroom yafi ɗaya su kirani su faɗa min sai na tura kuɗi ayi min na ɗaya ɗakin ko ba mai tsada ba, hakan kuwa aka yi da ike ina dashi kuma ina adani na tura dubu ɗari biyar nace sai ɗakin ya zama shi ne nawa wancan kuma masu tsadar sai ya zama nasa. Abbayo har da tsokanata wai Kudrat ta fini kyau ita fara ce ƙal kamar ba ƴar ƙasar nan ba, mene mene ɗinsa dai, sai naji bala'in kishi da haushi ya kama ni har da guntuwar ƙwallana, ranar kuwa har fushi nayi da Salim yana ta kirana naƙi ɗagawa, yayo text nayi kamar ban gani ba. _________________________ _Kuyi haƙuri don Allah wallahi banji daɗin rashin post na jiya ba, tafiya nayi garin sakkowa a mota na faɗi na yi buguwan ƙashi a hannu, duk yanda na so na ƙoƙarta wallahi abin ya faskara, naga adu'oin ku na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi._
[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR09FT5* Maman Khairi da Maman Yasmin haka suka miƙe tsaye wajen gyara ni ciki da waje, kayan mata kamar hauka Maman Yasmin tasa na tura uban kuɗi aka yo aike tun daga niger, ga Safiyya ma da nata tasa aka kawo min daga sokoto, sam ba'a son raina na ke amfani da magungunan ba, haka na ke shansu a dole wani da daɗi wani ba daɗi, wani ma sai na kusa amai ma na ke iya sha, haka zan ta yiwa Safiyya ƙorafi Maman Yasmin ma na yita mata nurƙufanci, don ni a nawa ganin wannan abubuwan duk ba su da amfani duba da irin rayuwan da nayi a baya, amfanin da na dinƙi yi da su a banza.
Safiyya ce ma me cewa ai yanzu zan san amfaninsu tunda sai yanzu ne zan yi auren, in daina lissafin wancan buhun a sahun maza, in bari in zan maganar ƴan iska mahaukata sai na ke sako shi a ciki, amma na bar tuna na taɓa aure a baya tunda dai ban haifa na baro ba.
Da Safiyya muke ta shige da ficen abubuwan da na ke siya ta ɓangarena, itama haka ta tura min 100k ta account a matsayin gudunmawa, naji daɗi sosai da kuɗin na bawa Yaya Imam nace ya siyo buhun shinkafa da fulawa sai ya bawa Abbaa. Shima yay ta min godiya har da ƙwallata don ce masa nayi sirri ne tsakanina da shi. Na siya shadda nayi mana anko iri ɗaya ni da Ummani da Abbaa, sannan na siya wani kalan daban na ɗinkawa yayyuna da matansu da ƴanƴansu har da budurwan Yaya Al'amin ma, shigar da na ke so muyi ranar ɗaurin aure kenan, Uwata kuwa kayanta sunan sai ana gobe ɗaurin aure zan ɗakko in bata, don so na ke farin cikin saman fuskarta ya ninku sau dubun dubata, danƙararen less ne na siya mata guda biyu mai shegen tsada kuma nasa aka yi mata ɗinki na zamani, atamfofi biyu kowanne da shigar takalmi da mayafinsa, Abbaa nah ba da kala ɗaya na barsa ba bayan shaddar ɗaurin aure har da set biyu na yi masa na boyel.
Salim ya tura min dubu hamsin na kuɗin gyaran jiki da lalle da kitso, ranar kuwa Safiyya ta dinƙa masifa wai yaushe Brother ya koyi tsumulmula basu sani ba, zata kira shi na hanata sai ta kira Ummansu ta faɗa mata, Umman nasu ma ta kama faɗa wai ko bai da shi ai ba ya bani 50k a matsayin kuɗin gyaran jiki ba balle kuma yana da shi, itama tace zata kira shi taci mutuncinsa nayi ta roƙonta da ƙyar ta haƙura ta ƙyale, ko kusa bana sawa Salim ido musamman akan kuɗinsa, ni yanda yake nuna min bai da wani kuɗi, ko hira muke yi zai ce in koyi haƙurin zama da shi a yanda yake, shi ba mai kuɗi ba ne amma insha Allahu zai yi ƙoƙarin ganin ban nemi wani abu daga gare shi na rasa ba, ba zan yi kukan babu ba in Allah ya yarda, saɓanin yacca na san labarin kuɗinsa a wurin Safiyya, to nima dai a haka na ke binsa dama ni abun hannun namiji ba damuna yay ba, har ce yay min motan da yake zuwa da shi ma na ogansa ne, wannan dai na jisa ne kawai ban wani yarda ba, kawai dai na san kyauta a soyayya da daɗi musamman ma a wurin wanda zaka aura, to ni zan iya cewa bai taɓa kawo min wani abu da sunan kyauta ba, kuma ko da na faɗawa Ummani ma ce tayi kar in sa hakan a raina, ƙila tsarinsa ne a haka sai na shiga cikin gidansa tukunna zai buɗe min aljihunsa, kuma gwara ma hakan akan ya buɗa min a waje sai na shiga daga ciki kuma ya matse kayansa, idan kuwa na nuna masa ban damu ba babu ƙorafi babu tambaye tambamye balle sa ido sai nafi kima a idonsa, shi kansa sai yafi jin daɗin yi min, balle ma mene na damun kai tunda ina aikina ina samu sosai kuma ga kasuwancin da na ke na kawo min kuɗi.
Yau dai ƴan uwa sun ƙara cika gidanmu, Hajiya Ummani an kasa zaune an kasa tsaye, ayi can ayi nan, gidan ya kacame da hayaniya, ni da ban son hayaniya duk sai kaina ya ɗauka yay nauyi, na ƙagu ma ayi a gama taron a watse, du da ina ta faman mita akan me ma za'a tsaya yin wani taro aure ba auren budurwa ba, Maman Yasmin ta danno min zagi tace in ci gaba da maida kaina baya hakan yana da kyau ai. Yau tun asuba da na tashi kasa komawa bacci nayi, Maman Khairi ma da ta ganni da duku dukun Safiya a gidan Maman Yasmin sai ta kama tsokanata wai ta lura na zaƙu dai a ɗaura auren nan, yau ni ce babu baccin asuba. Nayi dariya kawai na shige ciki ni bata san me nake wa ba, ai kuwa na sha tsiya a wurin su Adama da duk mutanenmu dai na ƙauye da suke kwana gidan Maman Yasmin, ni da naje na ƙarasa haɗa kayayyakina takurawarsu ta hana ni sai baro gidan nayi na dawo gidanmu.
Ɗakin Kaka na shiga inda anan aka ajiye akwatunan lefena da aka haɗa guda sha biyu, ɗauke da kaya masu tsada da kaya na alfarma, da aka kawo su ni dai sai dana tofe abuna da adu'oi saboda baki, kaya kamar ɗiyan wata ƙusar, ko shi da na ɗauka hoto na tura masa sai da yace mun fitar da shi kunya, da shi aka ce ya haɗa ba zai haɗa masu kyan haka ba, har da ce min yanzu da su Granny ba su yi karo karo an haɗa masa ya kawo wannan kuɗin ba ya zai yi? Ni kuwa na ce ummm shine yay ƙwafa wai in koka da ranar haɗuwarmu.
Akwatun da ke ɗauke da abayoyi na buɗa na ɗauko guda ɗaya, pink colour tasha ado, na ɗakko agogo da yari ma har da sabon takalmi. Umman Batula ta ƙwala min kira na fita da sauri ina ɓoye kayana cikin hijabina kar a gani a ishe ni da mita, ni kuwa yau ban ga me hanani cakarewa da kwalliya ba.
"Kije ga ruwan can na kai miki banɗaki, akwai wani daban cikin koriyar robar nan ki zauna a ciki sai ya huce sai ki fito". To kawai nace mata na wuce ina ƙunƙuni, wai ba za'a kiraka gefe a faɗa maka abu a sirrance ba sai an gama yayataka a bainar nasi kowa yaji me zaka yi. Shiyasa tunda ta zo da naji kiranta ina fitowa na ke faɗawa banɗaki, sai ta ƙara wani ince gani ciki.
Kamar dai wata zautacciya haka nayi wankan nan na fito sai aikin imagination na ke ina ta murmushi, yau ɗin dai kana ganina kasan cikin farin ciki na ke sosai, kamar ma ranar ɗaurin auren, annurin fuskata sam yaƙi ɗaukewa duk murnar zuwan Salim ne, kwanana tara kenan ban gansa ba, na riga na saba duk kwana uku yake zuwa, waya ma bama samun damar yi sosai, idan ya tasheni da safe sai zan kwanta zai ƙara kira, nan ma ba zamu jima ba 2-3mints ne zai ce naje na kwanta yana cikin aiki ne.
Sun je taro ne can garin Ekiti, suna tare da shugaban ƙasa sun masa rakiya, kuma a can ɗin suna tattaunawa ne akan matsalar tsaro na ƙasar nan, to duk basu da wani isashshen lokaci, a hakan ma yau ɗin sato hanya zai yi ya taho, yace shima ya gaji da missing ɗina, ƙwayar idonsa kullum zafin rashin ganina take yi, kuma idan yay kuka duk bai da me lallashinsa. Ina zancen zuci sai ga kiransa ya shigo, naji ƙirjina yay duka, wani sanyayyan abu ya ratsa jikina, da azarɓaɓina kuwa na ɗaga.
"Myyyy". Ya kira sunan da wani irin salo da ya saukar min da kasala. Na lumshe ido kana na amsa,"Na'am Salim". Sautin murmushinsa ya fito, yayi yayi na canja masa suna nace ni haka zan ke faɗi, da haka kuma sai ya koma cewa nafi kowa iya faɗin sunan, kamar ni na raɗa yafi daɗi a bakina.
"My mun dawo fa, gani a ƙofar gida". Basarwa nayi irin ban damun nan ba na ce,"Ah dama yau zaku dawo, amma kun yi sauri, ai ce na ke sai kun yi good one month".
Na tabbata sai da ya tsotsi leɓensa kafin yace da ni,"My abu ɗaya yasa na ke ɗaga miki ƙafa, ni za ki munafurta ki nuna min ba kiji daɗin dawowana ba, to fito da sauri kafin na kasa jurewa na shigo gidan da kaina".
Idona a waje na ce,"Kuma sai ka iya?". "Kina mamaki? Ki ƙara five minutes kika ga ni sai dai ki tsince ni ina tsallake mutane, kuma a gaban kowa zan kamo hannunki na fito da ke".
Dariya nayi sosai nace,"Yi haƙuri Sojansu kar ka bani kunya".
Aje wayan nayi na leƙa na ƙwalawa Yasmin kira na ce taje ta buɗe masa ɗakin Yaya Al'amin. Na dawo daga ciki na shiga shiryawa, kamar wanda zata je gasar kyau, ba fa wani makeup na tsaya yi ba, powder kawai da kwalli sai lip bam shikenan amma kamar a sace ni a gudu, ni kaina ba ƙaramin kyau na yiwa kaina ba. Na fito ina wani takun ɗaiɗai, na leƙa ɗakin Ummani bata nan na bita ɓangaren Ummansu Hindatu, wanda bai sonka dai har a bada ba zai so ka ba, tunda aka fara hidiman bikin nan ƙala Umma bata ce da mu ba, kamar ma bata san da za'ai biki a gidan ba, ranar da aka buɗe lefe ma Sha'awanatu ƴarta ce kawai ta zo taga kayan, amma har yau Allah sanya alkhairi bata ce da Ummani ba, ni kuwa idan taga gimlawata sai da ta harare ni, nima kuwa na koyi shareta ko gaida ita bana yi, me zaka yi da mutumin da bai gamin mahaifiyarka da mutunci.
"Ummani zan tafi". Suna awon masarar da za'a kai niƙa ayi tuwon dare na yau saboda baƙi, ta ɗago tana kallona tace,"Kika ce kin ɗau hutu".
Umman su Hindatu tace,"A'a ƴata irin wannan kyau haka, ko dai sirikin nawa ne ya zo".
Nayi murmushi ina cewa da Ummani,"Bana faɗa miki zan je karɓo sauran ɗinkuna ba".
"Ohh haka ne, to ke da wa zaku tafi? Ko ta gidan Safiyya za ki biya".
Na ɗan yi ƙasa da kaina ina sosa gira cike da kunya na ce,"Salim ya zo shi zai kai ni".
Ta ɗan shiru kafin tace,"To sai kun dawo Allah ya kiyaye ya tsare hanya, kinga idan ki samu dama ki biya asibitin ki duba ƴar gidan Baaba mai ƙosai".
"Ai kuwa gwara da kika tuna mini, wallahi na manta kuma fa ko jiya sai da ta kira ni tace ko da nurse ɗin da zan taimaka na haɗa su".
"To inda hali sai ki ƙoƙarta musu, yarinyar naji ance sai an ƙara yi mata wankin ƙunar".
Ina jinjina kai da tausayawa nace,"Allah sarki, Allah ya bata lafiya. Bari na tafi".
"To sai kun dawo Allah ya tsare, a kula don Allah Sa'ida". Ni wai sai kace wata ƙaramar yarinya, indai zan je wurin Salim ko zance zai ne Ummani ta dinƙa a kula a kula, balle kuma idan na ce zamu fita tare ai sai an ja kusan rabin awa ana min wa'azi da nasiha, yau ɗin ma don tana cikin hidiman aiki ne da tana nan tana min nasihar yau da kullum, ni duk idan tana haka sai nayi ta tsarguwa ina cewa ko bata yarda da ni ba ne.
Umman su Hindatu tace,"Ƴar uwar taki dai sai gobe zata samu shigowa".
"Ai ki rabu da ni da ita Umma, duk rashin mutuncin da zan mata kar kusa baki".
Suna dariya duk ɗin su na wuce Umma na faɗin mun fi kusa, a tsakar gidanmu su Gwaggo Talatu na ta faman yabon kyan da nayi, wata Kakarmu ta ɓangaren su Ummani na zolayata da cewa ko dai gasar kyau zan tafi, wata ƙawar Ummani kuwa na faɗin gaskiya wadda tayi min gyaran jiki tayi mugun iyawa, fatata sai sheƙi take yi na zama kamar ƙwanduwar ƙwai, ko da madara da kankana ake wanke ni kullum ai sai haka, ga ƙamshi na tashin hankali tun daga nesa, su Juwairiyya gulmammu na tsokanata wai ai nan dai da jibi ne in kwantar da hankalina sunga ina ta rawan ƙafa, dama tunda suka ga mota a waje suka san shine ya zo, Mubaraka na bada labari wai ya zo da kakin soja ya fito duk ya tsorata ƴan unguwa, yara har da masu gudu.
Zuwana soro ƙamshin turarensa ya dakeni na lumshe ido, har ga Allah ƙamshin nan shi ne ke rikitani na kasa sarrafa kaina a duk sanda na ke tare da shi. Ina tsaye Maman Khairi ta zo wucewa zasu kai buhun fulawa gidan da za'ai kayan gara, ta mintsine ni da cewa kar dai in kai kaina in yi haƙuri in bari su kaini, kunya ta rufe ni nayi saurin rufe fuska ina saurin shigewa ɗakin Yaya Al'amin. Yana zaune gefen katifar Yaya Al'amin, dama ya saba duk sanda ya zo anan yake zama, na ce me yasa bai son zama kan kujeran, sai ce yay gwara ya ke zama kan abu me taushi da ɗumi kar sanyi ya shige shi in zo ina cika shi da mita a shimfiɗa, haka ya saki baki yana ta zuba maganganun da suka sa har ya tafi ban ƙara kallonsa ba saboda mugun kunya, mamaki ya bani sosai sam ban san haka yake ba, hmmm dama namiji ka gansa kawai sai in bai samu wuri ba, duk da na san komai amma haka yasa naji kalaman suna neman su fi ƙarfin kaina.
Ni dai ko da na shiga sai na kasa motsi, na maƙale a wuri ɗaya shauƙin ganinsa duk ya game min ilahirin tsoka da jinin jikina, har wani abu na ke ji yana tsikarina a yatsan ƙafa, ƙafafuwana suka yi bala'in sanyi saboda kallon da ya kafe ni da shi wanda ke neman kassara gaɓɓaina gaba ɗaya, ya lumshe ido yana sauke wani wawiyan ajiyan zuciya da yasa na ɗago babu shiri na ƙura masa ido.
Yau ne ranar farko da na gansa cikin shigar uniform complete, ashe haka kayan suke masa bala'in kyau, har ga Allah sai da naji ina ma ya zama halalina in ƙarasa gare shi da sauri in rungume shi cikin shauƙin soyayyarsa da ƙaunarsa, ai ko kamar ya san me ke raina sai gani nayi ya buɗen hannaye wai in zo in hugging nasa, ina murmushi na maƙe kafaɗa ina a'a.