Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 32
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 32: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 32. Abin dariya kuma sai ya kama buga ƙafa a ƙasa sai kace yaro, na…
4,495 words
Abin dariya kuma sai ya kama buga ƙafa a ƙasa sai kace yaro, na ware ido ina cewa,"Kayii". Sai kuwa ce yay,"Ai yaronki ne ni, nan gaba kaɗan ma breast feeding ɗina za ki ke yi". Ya faɗin hakan yana kashe min ido guda, nace,"Ban hanaka ba irin wannan maganan ba".
Tasowa yay ya zo gaba daf da ni ya tsaya, nayi saurin sunkwi da kaina ƙasa ina wasa da yatsun hannuna, idan na gansa gabana irin haka daf daf duk sai na nemi na ruɗe in kasa fassara irin yanda na ke ji a tare da ni. Ban ankara ba naji hannunsa cikin nawa, da sauri na nemi na zare ya hana hakan, nima kuma sai na tsinci kaina da hana ƙwacewar, sai dai murya can ƙasan maƙoshi nace da shi,"Kasan fa babu kyau, idan kayi haƙuri kwanaki kaɗan suka rage".
Bagarar da maganar tawa yayi da cewa,"Baby ina kika je aka sauya min ke haka? Kinga kyan da kika yi kuwa, ga rigar tayi fitting ɗinki, Baby faɗa min sirrin me kika samu da a kwana tara kika ƙara fidda shape".
Sai yay shiru yana cewa,"In faɗi wani abu?". Sai na masa wani kallo don idan yayi irin wannan muryan na tabbata zai min katoɓara ne, ile kuwa sai ce yay,"Naga twins ɗina ma sun ƙara cika, ko wani abu kika sa suka ɗago don ni dai ba a haka na tafi na bar su ba".
Dukan wasa na kai masa yay saurin ja da baya yana dariya, ya tsare ni da tambayan lallai alalla sai na faɗa masa me na sha na daɗa cika gaba da baya, ƙwayar idona ma har haske ta ƙara yi. Ban iya cewa da shi komai ba kamar yanda na kasa wani ƙwaƙwkwaran motsi dalilin yanda na ke jin yana kewaya babban yatsansa akan tafin hannuna, sai naji ina neman fita a hayyacina na haɗiye yawu ina rumtse ido.
Na ƙware wajen buɗe baki nace masa,"Salim ka bari".
Ai ban ida rufe baki ba ya sauke min mintsine a weast ɗina. "Ya sunana?". Dariya na ƙyalƙyale da ita dalilin cakulkulin da ya sakar min, na manne jikin bango ina cewa,"Salim sunanka". Ganin yana neman yi min rumfa na rumtse ido da kyau ina marairaice murya da cewa,"Kayi haƙuri ba sunanka haka ba, sunanka Lieutenant Onochie, kuma fa kaga kar wani ya zo wucewa".
"Ina ruwana ke za ki ji kunya ai, ni dama a ƙage na ke a bani abata na tafi, dama hotel ɗin da muka sauka idan za ki kwana kina ihu babu me kawo miki agaji". [2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR08FT5* Na aje wayar saman fuskata ina faman fitar da murmushi kamar sauna, sai daga bisani kuma naji raina ya ɓaci na kama jin haushin kaina, sai kace wata shashasha ma a soyayyar, ina neman zaƙewa daga ance ana sona sau ɗaya, to shi dama haka ma yake no text no call? Soyayyar ce bai iya ba ko kuma salon tasa kulawar kenan? Ko kuma ya gamata akan matarsa ta farko? Rashin nemana da bai yi ba fa tun zuwan farkonsa ya bani haushi sosai, don har ce nayi yana da girman kai, yana nufin kenan ma ba zan ja ajina ba tunda ni ba budurwa ba ce, sai yanzu da wani karkataccen bakinsa zai kira ni yana Baby, a'a Bebo.
To ni ina son miji me raha da zamu zama abokai bana son me ɗagawa, in ma zai sauke abinda ke kansa ya sauke, idan ba zai sauke ba yaje can ya nemi ƴar uwarsa ƙabila ko wadda zata iya da halinsa, Numbernsa na ƙara kalla da kyau don ko ya kira ba zan ƙara ɗagawa ba ehe, kar yaga ya kira ina ta wani zumuɗi ya zaci sonsa na ke yi. Ummani tace,"To ke ya kike ganin za'ai da waɗannan kuɗin? Dukka lefen miliyan ɗaya da rabi za'a haɗa miki? Ni fa kawai nayi shiru ne gudun faɗan Abbaanku, shi yana batun gwara ayi miki kaya na gani na faɗa kar su ce sun bada kuɗi masu yawa an riƙe. amma ai kuɗin ne sun yi yawa, a dai haɗa ko na miliyan guda ne, ke ni miliyan ɗin ma a wajena tayi yawa wanne sutturu za'a siya har na miliyan, ba gwara a raba biyu sauran a haɗa da wancan a bawa Sale kafinta yay miki kaya masu kyau".
"Kawai ma da zai dawo ya karɓi kuɗinsa da yafi". Na faɗa cikin muryar da ke shaida faɗa faɗa, ina ta gungunin masifa na ƙorafin yanda ma ya raina ni. Ta ce,"Uhmmm daga baya kenan, ni bana son gulma".
Sai na sami kaina da ɗagowa in kalleta, na buɗi ba ki nace,"To Ummani sai ka kama auren wanda bai san kulawa ba balle haƙƙinta, kuma ba zai ke nuna maka da gaske yana sonka ba saboda yana ji da kansa". Harar da ta galla min yasa na sauke kai ƙasa ina ci gaba da masifata ƙasa ƙasa. Lokacin Maman Yasmin ta shigo tana tsokana na da,"Amarsu".
Gaisheta kawai nayi ban ko ɗaga kai ba, Ummani tace,"Ƙyaleta". Suka shiga gaisawa Maman Yasmin ɗin na cewa,"Abban Yasmin yace min kina nema mana".
Ummani tace,"Ehh dama ce nayi ke da Nafisa ku zo ku shiga kasuwa ku haɗo kayan lefen nan, kunga wata guda kamar yau ne gwara ayi abu a tsanaki, gata nan ita ɗin kuma idan zata biku to".
Maman Yasmin tace da Ummani,"Tom shikenan, amma kinga ko za'a yiwa Mrs Arab magana a faɗa mata ga na iya adadin kuɗin da ake so ta haɗa, mu bar mata zaɓi nan da kwana uku za kiga ta haɗo su har akwatuna, kuma wallahi tayi masifar sanin makamar iya haɗa lefe, mayan bikin nan da ake duk ita ake bawa kwangila".
Ummani tace,"To idan kin san dai babu wata matsala ai sai ayi mata maganar ko".
"To shikenan bari a kirata ma yanzu, ke Sa'ida rubuta lambar wayata babu kuɗi, ai shegun kaya zata haɗa miki, da muka je bikin Surayya duk shegun less ɗin da kika ga tana sakawa ai ita ta haɗa lefen".
A ƙasan raina na ce ehh fa shigar Amaryar tayi kyau babu ƙarya. Na ɗau wayata ina,"Karanto lambar". "Oak, 07037599677". Ina gama dialling nayi saving da Mrs Arab Kano. Kiran lambar ya tafi na miƙa mata ina tashi na fita, ruwan wanka na ɗora kana na koma ɗaki na ɗakko wani ɗinki da zan ƙarasa haɗawa, masu shi na ta kirana na gagara ƙarasa musu.
Ƙarfe uku na fito a shirye don tafiya wurin aiki, tun uku saura na ke ta ganin kiran Salim na shigowa nayi biris naƙi ɗagawa, har aikowa yayi nayi saurin kora ɗan aiken kar ma Ummani taji. Na shiga ɗaki na yiwa Ummani sallama bayan ta min adu'a na fito, da zuwana soro kiran Maman Khairi ya shigo tana tambayana su siya min jugs ɗin tangaran yafi yawa ko kuwa? Nace ni na bar musu zaɓi kawai, tun ɗazu ta zo suka fita ita da Maman Yasmin yo siyayyan kayan kitchen lefen kuma kamar yadda ta faɗa ne sun gama magana da Mrs Arab zata haɗo komai ta kawo, ina jin Maman Yasmin na faɗin don Allah ta haɗa akwatu set uku, ni dai kam mun yi dacen sirikai don Matan Yayyuna kamar ciki guda muka fito, yanda Ummani ke yabon su haka suma suke yabonta ko ina suka shiga sai sun ce su kuwa babu abinda zasu ce da Allah sai godiya domin ya basu suruka ta ƙwarai wadda ta ɗauke su babu banbanci da abinda ta haifa, kuma babu takurawa sam a al'amuranta, to nima dai bana kukan rashin Yayyu mata don sun maye min gurbinsu, sai dai nayi kukan rashin ƙanne mata kawai.
Ina fita ƙofar gida nayi kiciɓis da mutum tsaye bakin mota shi da Yaya Al'amin, yadi ne jikinsa baƙi yay masifar masa kyau, duk yanda na so nayi masa kallo ɗaya hakan ya faskara sai da na ƙara kallonsa, Allah masanin ta inda farinciki ya samu damar lulluɓe ni, a ƙasan raina nace yay kyau kamar ba ƙabila ba, har wani kishinsa naji ya lulluɓe ni ganin ƴan matan layinmu na ta wucewa islamiya. Na kalla screen ɗin wayata da kiransa ke ƙara shigowa a karo na babu adadi, sai na ɗaga ido na kalle shi naga ni yake kallo yana jijjiga kai, hakan yaso ba ni dariya amma na fusge, hankalinsa ma ya dawo kaina gaba ɗaya ya bar Yaya Al'amin can yana ta faman zuba shi ɗaya.
Na sha murr na ɗauke kai kamar ban gansa ba, na ɗaga ƙafa zan tsallake na wuce a sumame kar Ya Al'amin ya ganni, aikuwa daidai nan naji yana cewa da ni,"Ke Sa'ida ba ki gan mu ba ne".
"Yaya kaina na ƙasa ban kula da ku ba". Na faɗi sa'ilin da na ke ɗaga ido na kalle shi zan harare shi, sai kuwa na kasa aiwatar da hakan dalilin ƙayattacen murmushin da ya sakar min wanda ya samu shiga har cikin ɓargon jikina, ga wani munafukan dariya da ya danne a saman leɓe. Ina ta ciccin magani haka na shiga motar, wai wai tunda uwata ta haifeni ban taɓa shiga mota me haɗuwa da tsada irin wannan ba, sai na zama kamar ƴar ƙauye har wani taɓa kujerun na ke yi da ko cire su a leda ba'ai ba, duk yanda aka yi sabuwa ce fil ma.
_"idan kika yi fushi da ni masoyiya hankali zaya tashi idanuwa su yi kuka, ki taimakawa soja kar ya zamo ragon namiji ai masa dariya"._
Haka ya shigo motan yana rera waƙar, da zummar in caccake shi da tsiwa amma ba shiri dariya ta ƙwace min har da sarƙewa, sai tari kwaf kwaf yay saurin miƙo min ruwa, na karɓa na sha idona har ya cika da ruwa tsabar dariya. Na miƙa masa goran ya galla min harara da cewan,"Kina wa me dariya?". Sauran dariyar na danne ina ɗauke idona a kansa idan ba haka ba tsaf zan ci gaba da dariya na zama kamar zararra.
Ganin bai da niyyan tashin motan na karkata ina dubansa na ce,"Please kar na makara".
Fuskansa a ɗaure yace,"Ba kina wa waƙana dariya ba".
Nace,"Ayya sorry ba waƙanka na ke ma dariya ba". Sai ya jijjiga kai yace,"Akwai ranar ƙin dillanci, tara ki kawai na ke za ki shigo hannuna, har ni za kike ganin kirana ki ƙi picking, kuma ma tsawon sati guda ba za ki iya kirana ki ce kin yi missing ɗina ba kina sona".
A hankali na ce,"Ai ba ni na fara zuwa nace ina sonka ba da zan ke bibiyanka". "Kika ce me?". "Ba komai". "Har na tausaya miki yarinya".
Sai na kalle shi leɓena na daɗa talewa da murmushi nace,"Wacece yarinyar?". Da yatsansa guda ya lakuce min hanci yana faɗin,"Ke me dimple ɗaya da rabi".
"Sa ido dai babu kyau, har ina kasan ɗaya dimple yafi ɗaya".
Kawai sai ya saki wani murmushi irin nasa na shi kaɗai me tsada da ya kusa sumar da ni, murmushin da ya tsaya min a rai wanda tuni ƙwayar idona tayi capturing nasa, Rufewar ido da buɗewarsa shi kawai na ke gani. Cikin sati uku muka yi wani shaƙuwa na ban mamaki da Salim, shaƙuwan da zaka rantse mun fi shekara guda, ga wani fahimtan juna da muka samu a tsakani, sosai ya fahimce ni haka nima sosai na fahimce shi, zuwa lokacin na gane ashe nayi masa bahaguwan fahimta ne a farko, amma mutum ne shi mai sauƙin kai, ya iya mu'amala bai da damuwa sam sam, sai na ce kusan halin su guda da gidan su Safiyya a ɓangaren kirki da mutunta ɗan Adam, ba ɗagawa ba nuna shi wani ne ko ɗan wani ne, ga kyauta da son yin taimako abin hannunsa sam bai rufe masa ido ba, ina ganin hakan ne duk sanda ya kaini aiki ko ya ɗakko ni, ko idan ya zo gidanmu ya gamu da wani nawa, ko a hanya haka idan yaci karo da masu neman taimako, duk da ni bai fiya sakar min kuɗi ko bani abu ba, kyautansa bai wuce idan ya zo naje raka shi ya miƙo min sauran turarensa, sai wataran da ya cire agogonsa yay alwala na ɗauka na gwada sai yace ya bar min.
Na saki jiki da shi sosai ya zama best friend ɗina, bamu fiya waya irin bini bini an yi kira ba, hakan bai dame shi ba sai aka yi dace nima kuma dama ba na son namiji me nacin kira, ko da yaushe a waya ko idan yazo cikin raha mu ke da farin ciki gami da annashuwa, har idan ina tare da shi na kan manta komai, bana jin asaran ɓata lokaci tare da shi domin kuma a duk wata hira tamu sai na ƙaru da shi ɓangaren ilimi ne ko ita kanta rayuwa. Yanzu ko da abu zan aiwatar shi na ke kira na nemi shawaransa, har Safiyya ke min ciwon bakin soyayya tasa na kware mata baya, nace ba za ki gane ba ne Beb, tace ni kuwa na gane tunda na san waye Yayana.
Ya haɗa ni da Mahaifiyarsa mun yi waya da ita, ranar ji nayi kamar na nutse a ƙasa don kunya, matan free take na fahimci tana da kirki sosai, tayi ta jana da hira tun ban amsawa har na saki jiki naji ma kamar tare da Ummani na ke, tana tambayan yaushe zan zo in ganta, ban iya cewa komai ba sai ita ke cewa to zata zo da kanta taga ƴarta, Kakarsa ma wadda ta haifi Babansa har da aike ta yo min na wani atamfa ankara me shegen kyau. Har matarsa da yaransa duk mun gaisa da su, matar ma ita ne ta takura masa kan sai ya haɗa mu a waya, ni kishi yasa na ke ta zillewa ranar kuwa muna tare sai gata ta kira, muka gaisa da ita cikin mutunci da girmama juna, da farko ina magana a daddaƙile daga baya da na fahimci ita with all her heart take waya da ni sai na sake kawai, tace min ga yarana ma kafin su zo su ganni, ina ji yaran na tambayanta Maama waye take ce musu New Mommy ɗin su ce wadda Papa zai kawo ta haifo musu Baby Boy, ni dai nayi ta mamaki na ce to Allah yasa dai yanda ake faɗan bata da matsala hakan take, don ni har ga Allah idan na tuna da ita na kan ɗan ji fargaba haka, to amma shi kansa yana yawan faɗa min kamar yanda Ummansu Safiyya ke faɗa min Kudrat bata da problem zan ji daɗin zama da ita sosai, idan kishina ya motsa min zan ta cewa ya tafi wurin matarsa ya ƙyale ni, sai ya nuna min shi ba ya son hakan, yana son matarsa kuma nima yana sona kowacce da matsayinta a zuciyarsa, zai kuma yi ƙoƙarin ganin ya fita hakkin kowaccenmu.
Haka Salim yay amfani da salon soyayyarsa yay raga raga da zuciyata a lokaci ƙanƙane, ashe ma ni ban san komai ba a soyayya, soyayya tana inda aka iya a wurin mutumin arziƙi, har tsokanata ake a gida da wurin aiki saboda nema na ke na zauce kamar farin shiga, alerm ɗin wayata duk sai da na cire, in ƙarfe biyu da rabi tayi shi zai tashe ni in yi sallar dare, haka idan asuba tayi, da safe kafin na farka yay min text da daɗaɗan kalamai da suke sawa naji ni a gajimare, har idan ban ji daga gare shi ba na ke takura, in koma kamar mara lafiya, Salim ya mantar da ni duk sauran guntun damuwan da na ke yi na famin ciwo, banda wata matsala ni kam na yarda Allah ya kashe ya ba ni, domin samun namiji kamarsa a wannan marrar sai dacen ubangiji kawai, wai kafin ma na shiga cikin gidan nasa kenan, shi kansa yana faɗa min Baby ba ki ga komai ba a soyayyan da na ke miki da kulawa sai kin shigo gidana tukunna, duk da wani sa'ilin ina cewa Allah yasa kar ya sauya daga baya, aurena na baya yasa na gasgata zancen Namiji bai da tabbas.
Ya rage saura kwana uku biki, ana ta shirye shirye, ƴan ƙauyenmu duk sun zazzo wasu daga cikinsu, ni sai mamaki ma na ke ko a aurena na farko irin hidima da zumuɗin da ake a yanzu ba'ai a wancan lokacin ba, na farko kamar wani taron mutuwa haka aka yisa, ni ba'a farin ciki ɗari bisa ɗari ba haka suma iyayen nawa, amma a wannan kam farin ciki da zaƙuwar da na ke ciki sun kai kaso fiye da dubu, farin cikin Ummani har ba ya barinta rufe baki, ta kira wancan ta aikawa wancan, haka Abbaa na ma shi kansa kamar yanzu ne karon farko da zai aurar da ni.
Kuma wannan auren sai ya zo da albarka, domin kuwa wani buɗi ubangiji ya kawowa Abbaa, yanzu haka babban teburi ya kama a kasuwa, cikin gida kuwa sai da ya aje botikan fenti huɗu aka shafe mana shi kamar za'a aurar da budurwa, na lura dai kowa yafi farin ciki da wannan auren hatta yayuna, idan nayi magana sai Ummani tace bazawarar ai me daraja ce, ni dai sai in murmushi kawai, idan na ɗauko kuɗi na bayar ayi amfani da su sai Abbaa yace a'a hakkinsa ne yay min komai, nauyinsa ne ba nauyina ne ba, in adana kuɗina za su min amfani nan gaba, amma yanzu na bari su zasu yi min komai, hatta kuɗin ɗunkuna duk shi ya bani yay min kashedin kar na sake na karɓi ko sisin Salim,
Abbaa yace shi ba zai ƙarya ba amma zai iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin ya fitar da ƴarsa kunya, haka ya yankewa Yayyuna kuɗi suka haɗa dubu ɗari biyu su huɗu, aka haɗa da kuɗin aurena dubu ɗari biyar, sai kuɗin kayan lefena da aka rage Ummani ta kaiwa Sale dubu ɗari uku tace don Allah yay min furnitures masu na miliyan ɗaya irin wanda ake yayi. To da yake ma aiki ya mayar da shi Delta state satin baya aka yi masa ƙarin girma, Kudrat ma da ta kira ni a waya tana zolayana wai ni ƴar sa'a ce, dama sun gaji da zaman Edo ɗin, ba yanda ba su yi ba a tashi a gidan yaƙi sai ga shi dole tasa an tashi babu shiri, ita da yarana suna min godiya. Salim ɗin na cewa ba sai anyi min kayan ɗaki ba, nayi karaf kuwa nace sam bai isa ba, na wani hasala kamar wanda ya zage ni, na dinka fifiƙa ina masa masifar ai ba'a gidan babu ya tarar da ni ba, Abbaa ma ba zai yarda da zance ba, mahaifina zai yi min kayan ɗakina idan ma ya san ya siya ya aje ya kwashe abinsa ya fitar da su idan kuwa ba haka sai dai idan ba zan zauna a gidan nasa ba, ni kuwa ai ban manta gorin da Nazifi yay min ba sanda zai ƙara aure na cewan iyayen matarsa har kayan ɗaki sun mata ba irin iyayena ba da suka bar miji da ɗawainiyan komai.
Saboda yanayin nisa zuwa can garin sai Sale yace zai ɗiba mutanensa suje Delta ɗin a haɗa kayan acan maimakon ace daga nan za'a a tafi, kuɗin mota ma kansa wani babban lamarin ne, hakan kuwa aka yi aka tafi da Yaya Al'amin da Abbayo, Salim ɗin yace akwai wurin zama a gidan nasa ba sai sun nemi hayan wajen kwana ba, Abbaa yace to gwara ayi tafiya ɗaya kawai tunda bikin ƴan kwanaki ya rage a tafi ayi jere gaba ɗaya, sanda ake fito da bahhunan kwanuka sai da nayi matuƙar mamaki, Ummani ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba har sai da na tambayeta ina ta samu kuɗi haka tace rufin asirin Allah ɗan abinda take tarawa ne, sai kuma gudumawar da ƙannenta da yayyunta suka aiko mata, kayan kitchen masu kyau da tsada ni har ce nayi ma ina zan kai su.
Kwanansu biyar a can, ranar da suka dawo kuwa suna bawa Ummani labarin gidan, sai santinsa suke yi su maza ma kenan, Anty Shafa da su Anty Lubna da Maman Khairi duk sai lokacin suka ji rashin jin daɗin da Abbaa bai bari sun je tare ba, shi kuma yace ne da akwai ƴan uwa acan ne sai a tafi da su, to ba za'ai rashin hankali ba kawai aje a tarewa mutum a gida, matarsa ma ba zata ji daɗi ba. Abbayo na faɗin wallahi Matar Salim ɗin tana da matuƙar kirki, haka ta karrama su kamar ƴan uwanta, motsi kaɗan sai ta aiko yaranta su tambaye su ko suna da buƙatar wani abun, abinci kuwa har ci suka yi suka ture, yace kuma idan suka yi aiki suka gaji da kanta take zuwa tace musu ga babban falo can ta buɗe musu ko za su yi kallo, iya kwanakin da su kai sun mata shaida me kyau.
Da daddare na samu Abbayo ina tambayansa ya fasalin gidan yake, yace min babban gida ne flat ba bene, ɓangarena bedroom uku ne kowanne da banɗaki a ciki, sai falo biyu da kitchen, amma fa kowanne ɗaki tafkeke ne, Yace babu laifi Sale yayi ƙoƙarin yin kaya masu kyau don duk zubin kayan turkey yayi sai kallon ƙurulla ne ma zai sai za a gane b kayan ƙasar waje ba ne, kuma bedroom biyu dukka an zuba kaya a ciki, dama yanda muka yi da su nace idan sunje sunga bedroom yafi ɗaya su kirani su faɗa min sai na tura kuɗi ayi min na ɗaya ɗakin ko ba mai tsada ba, hakan kuwa aka yi da ike ina dashi kuma ina adani na tura dubu ɗari biyar nace sai ɗakin ya zama shi ne nawa wancan kuma masu tsadar sai ya zama nasa. Abbayo har da tsokanata wai Kudrat ta fini kyau ita fara ce ƙal kamar ba ƴar ƙasar nan ba, mene mene ɗinsa dai, sai naji bala'in kishi da haushi ya kama ni har da guntuwar ƙwallana, ranar kuwa har fushi nayi da Salim yana ta kirana naƙi ɗagawa, yayo text nayi kamar ban gani ba. _________________________ _Kuyi haƙuri don Allah wallahi banji daɗin rashin post na jiya ba, tafiya nayi garin sakkowa a mota na faɗi na yi buguwan ƙashi a hannu, duk yanda na so na ƙoƙarta wallahi abin ya faskara, naga adu'oin ku na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi._
*B3ƘR10FT5* Fuska na tamke ina ce masa bana son irin wannan maganan kuma ya daina taɓa ni, ban aune ba kuwa kawai sai naji ya manna min kiss a saman goshi, nan fa na diririce nayi saurin ƙwace hannuna a nasa don a yanda na ke jinsa in ban wasa ba sai ya rungume ni.
Fuskarsa ya shafa tare da cewan,"Baby mu tafi, mu tafi kafin a samu matsala, wannan ƙamshin na ki zai iya sawa na aikata ba daidai ba". Na kalla ƙwayar idonsa duk nema ya ke ya rikiɗe, ya ɗan ban tsoro ganin har rumtse ido yake yana cije fuska da kyau, kuma kawai sai jin iskar bakinsa nayi a gefen bakina yana faɗin,"Baby ƙamshin nan fa ya tayar min da sha'awanki, ina neman gaza controlling kaina wajen turmushe ki akan katifan can".
Furucin nasa yasa duk jikina ɗaukan ɓari, na watsa masa harara ina ƙara cin magani, da sauri nayi ƙofa shima yay saurin fuzgoni har sai da na gogi da jikinsa, numfashi kawai yake saukewa kan ya kuma manna min kiss a kumatu, kana yace,"Ni Onochie ya zan yi da raina, yanzu haka ina ganin soft lips ɗin nan zan bar su, Baby please ko kaɗan ne".
Ƙwacewa nayi na fice da hanzari, sai daga baya ya fito yana dariya wai ni matsoraciya ce mene don an fara lissafi daga ɗakin Yaya Al'amin, na harare shi kawai ban ce masa komai ba. A hanya muna tafe muna hira abinmu ta masoya, yawanci duk yana magana akan kai ni, yana tunanin ko a fara kai ni can gidana daga can sai ya kai ni wurin iyayensa ko kuma a fara kai ni ta wajensu in ya so idan ya dawo sai mu wuce daga can, ni duk ma yasa na kasa sakewa da shi yau ɗin, fagge muka je wurin da zan amso ɗinkunana, ba yanda ban ba akan ya bar ni naje na karɓo da kaina yaƙi, wai ba ya so na fita wani me ɗaukarwa kan zunubi ya kalle masa halal ɗinsa, na ce ai ban riga na zama ba sai ya sha murr kawai ya fice ya bar ni a ciki, ya jima sosai a shagon ɗinkin kafin ya dawo yana ce min,"Kin sa duk an ɗauka yaronki ne".
Ina murmushi na ce,"To ai zan tura masa kuɗin ɗinkin".
"Na ara za ki biya ni kayana, kuma cash na ke so in doller ba Naira ba".
Murmushi nayi ina masa godiya, Calido ya biya da mu yace min yana jin yunwa, nima dama yunwar na ke ji, ai kuwa tunda muka shiga ido ya dawo kanmu, ɗaiku ne ba su tofa albarkacin bakinsu akanmu ba, har da masu satan ido su ɗauke mu vedio ƴan bani na iya a social media. Kuɗi ya kashe sosai a abincin da muka ci, ni da aka yi bill ma sai da na kallesa na ce kuɗin fa sun yi yawa Salim, sai ce yay zai zare a sadakina da za'a harhaɗa masa gudunmawa, wannan kuɗin ogansa ne yake ta bushasha da su.
A hanya ya tsaya yay siyayyan kayan dubiya masu yawa, ya bani yace sai na kaiwa mara lafiyan, naji daɗi ƙwarai yau yanda yake ta min sai naji na ƙara son abuna tare da fatan Allah ya barmu tare, Zuwanmu asibitin Murtala na kira jikar Baaba Mai Ƙosai, ita ta zo ta rakani can inda suke kwance, ban wani jima sosai ba a wajensu na fito saboda na bar Salim a mota yana jirana. lokacin da muka yi sallama da Baaba Mai Ƙosai wacca ta rakoni tana ta min godiya, ina tafe kawai naji an faɗo jikina an rungume ni, na kalla matashiyar budurwar da ke maƙale da ni ina sa hannu in jayeta a jikina, har ga Allah ban gane wacece ba sai da ta ga nayi mata kallon ƙurulla sannan tace,"Anty Sa'ida Rumana ce".
Ni da ta faɗi hakan ma sai ta saka ni a duhu, sai daga baya kuma na gane baki buɗe na ke kallonta kafin nace,"Rumana!". Sai ta ɗaga kai da sake cewan,"Ehh Anty Sa'ida, Rumanki fa".
Mamaki ya ƙara kamani, lallai girman ɗan mutum ba wuya. "Rumana ke ce kika zama ƴan mata haka, Ya akai kika gane ni?".
Kawai sai naji tausayin yarinyar ya tsarga min, na sake rungumeta kafin ta zame a jikina tana cewa,"Anty Sa'ida ko a mafarki naji muryanki sai na gane, balle kuma na ganki duk da kin sauya, farko ban ganeki ba sai da na tsaya dai naji muryan da kyau kuma matar da ta rako ki tana faɗin sunanki, Anty Sa'ida naga kin ƙara yin kyau sosai kamar ba ke ba".