Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 33
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 33: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 33. Wato har ga Allah ban tsammaci zan ƙara ganin iri iri Nazifi ba a…
4,470 words
Wato har ga Allah ban tsammaci zan ƙara ganin iri iri Nazifi ba a duniyata har kuwa na koma ga Allah, ko fatan haɗuwa da wani na nasa bana yi, Murmushi nayi ina shafa kumatunta nace,"Me kike yi anan?".
Da yanayin tausayi tace,"Ai mun daɗe anan asibitin, an kwantar da Iyam bata da lafiya".
Nace, "Subhanallahi, Allah ya sawwaƙe".
"Anty Sa'ida ban san gidanku ba ina ta cewa zan zo, watarana ma na biyo hanya sai ban gane ba".
Na ɗan murmusa na ce,"Ayyah, ya school to". "Alhamdulillahi, yanzu ina jss 2 amma ba wancan makarantan da kika san muna zuwa ba, Jakara special primary school na ke zuwa yanzu, mun bar gidan Baba Ƙarami tunda jimawa".
Haba ni dai nayi mamakin yanda na ganta yarkace yarkace, a raina sai da nace kamar ba yaran Alhaji Nazifi ba, ashe sun koma gaban iyayensu, Allah masanin dalili. Muna hakan sai ga Atika ma ta iso, itama ta girma yaran duk sun zama ƴan mata ƙirji ya fara fitowa, itama muka gaisa da ita, sai dai ita ɗin ta kasa sakewa da ni sai satar kallona da take yi, Rumana kuwa ta maƙale min a jiki tana ta min surutu. Maganan Rumanan ta katse min gajeran tunanina,"Anty yaushe za ki dawo gidan Baba Ƙarami, naji ance za ki iya dawowa".
Lallai yaro yaro ne, Rumana kuma na daga cikin mahaukatan yara, ni kuwa idan ba gawata ba me zai mayar da ni gidan Nazifi, ko da ike ƙarshen hauka na wurin me mafarkin zan koma gidan Nazifi. Mun gama magana da su ina cewa su yiwa Iyam ɗin sannu, zan wuce sai naji suna ga Mama nan, na ɗaga kai na hango Yaya na tahowa, yanda take tafiya bugujin bugujin kamar wadda aka tarewa duk matsaltsalun duniya akanta ita ɗaya, kuma har ga Allah ban shaidata ba saboda yanda ta zaftare ta rame, duk ta fita a hayyacinta, tun kafin ta ƙaraso na ɗauke kai nayi kaman ban ganta ba, ita kuwa baki buɗe ta iso gabanmu tana dubana sama da ƙasa, mamaki bayyane ƙarara a saman fuskarta tana tafa hannu tace,"Wa idanuna ke gane min, Sa'ida!". Ta faɗa da muryan da ya fito da sautin murna.
Wani yatsinen kallo nayi mata, fuskarta a sake ta gaida ni,"Sa'ida Ina yini". Na amsa mata babu yabo babu fallasa, sai naga jikinta duk yay sanyi, kamin ƙifta ido sai ga saukar hawaye saman kuncinta tana ce min,"Sa'ida na jima ina cewa zan zo gidanku sai dai abubuwan da ke ta faruwa yau da gobe na kasa samun dama, ashe da rabon anan zamu gana, kin ji labarin muna nan ɗin ne?".
Furucin nata sai ya bani dariya, wai naji labarin suna nan, to ko naji na zo nayi musu me? Kaman ta gane zancen zucin da na ke yi ta sake cewa,"Wallahi ni dai sai naji nauyin ganinki, amma ina nan tafe gidan na ku".
Nace,"To Maijidda me ma zai kawo ki gidanmu kuma". Tayi murmushi me ciwo da kuma jin amsawar sunan da na kirata da shi kai tsaye, tace,"To ai Sa'ida ya zama dole a zo gareki, to yanayin yanda rayuwar ke ta ƙwallo da mu ne kowa babu sukuni, wallahi muna cikin tsaka me wuya sai dai adu'a kawai, Ni dai Sa'ida ba sai nayi dogon jawabi ba ina me bada haƙuri akan abubuwan da suka faru a baya tare da neman yafiyarki, ni da mahaifiyata da ma dukka ƴan uwana".
Nayi murmushin da ni ɗaya na san ma'anarsa nace,"Ah haba ni ai babu komai, yanzu ma banda Allah ya ƙadarta haɗuwarmu ai tuni na mance da ku balle batun mun taɓa rayuwa tare har wasu abubuwa marasa daɗi sun faru, ki manta kawai Allah ya kawo sauƙi cikin lamuran na ku, ni yanzu ai sai godiyar lillahi bana cikin wata matsala da damuwa".
A sanyaye tace,"Haka ne wallahi duk wanda ya ganki zai shaida, banda nayi miki farin sani ma ai ba zan saurin shaidaki ba, wallahi kin ƙara kyau kamar sake halittarki aka yi".
"Uhum". Ina faɗa ina ƙoƙarin barin wajen, ta dakatar da ni da faɗin,"To Sa'ida ni ina nema mana yafiya, haƙiƙa mun zalunce ki a rayuwa". Na ce,"Na yafe Allah ya yafe mu gaba ɗaya".
Sai naga taji daɗi sosai. Nan take bani labarin yanzu ma ta dawo ne daga police station Fati ce suka samu matsala da kishiyarta abin dai babu daɗi tana can tsare wurin ƴan sanda, to kuma ma tana kan hanya aka kirata Barira ƴarta auren ya mutu, Uwar mijin ta sakota gaba akan rashin haihuwa to yanzu can zata tafi taje ta taho da ita wai duk sun watso mata kayanta waje, bayan cin mutuncinta da zarafinta da suke yi ko da yaushe yanzu har suna cewa ma za su yi ƙararta saboda ƴar ƙanin mijinta da aka bata ruƙo ta ƙala mata sharri.
Nace,"Allah sarki". A kunyace ta sake cewa,"Don Allah Sa'ida kifa yi haƙuri ko yawun bakinmu zai ƙare wajen baki haƙuri bamu yi komai ba".
"Hmmm ni fa Maijidda kin ganni a rayuwar nan tawa da na ke cikin jin daɗi da walwala na mance da ku da abinda ku ka min, yanzu ma ban da kun shaida ni zancen gaskiya daga ke har yaranki babu wanda na gane".
Sai ta shiga roƙona akan in daure in ƙarasa na duba Iyam, na ce mata ai bani ɗaya ba ce tare da mijina na ke, furucin da yasata zabura amma haka ta dake ta shiga taya ni murna har da cewa amma har nayi aure ba su da labari, a raina nace uhmm ana nan dai har yanzu da ƙarancin tunani, taron girma ai mutanen arziƙi ake gayyata ba na tsiya ba. Tare da ita muka je wurin Salim, yana daga cikin motar ya buɗe ya zuro ƙafa ɗaya waje yana ce min,"Baby yanzu na ke shirin biyo ki ai, kin barni ni ɗaya babu daɗi?".
Na ce,"Sorry Sojana, ga wasu bayin Allah ku gaisa".
Yayan ta duƙa ita da yaran su ka gaida shi, yanda take faman gaisuwar ka rantse irin almajiran nan masu baran kan hanya. Ina ta kallonta ni dai a raina sai mamaki na ke yi, mace ƴar gayu da ƙwalisa amma kalleta fuskar hijabi ma a karkace, na kasa yiwa Salim bayanin wacece, ban san me zai iya faruwa ba idan nayi hakan don har ga Allah yana nuna min tsananin kishinsa akan tsohon mijina, sai Allah yasa ma bai tsaya tambayana ba ya zaro kuɗi masu yawa wanda a ƙalla na san zasu wuce dubu goma yace na basu.
Ai kuwa kamar anyi mata bushara da aljanna sai gata ta koma ƙasa ta duƙe a gabanmu tana zuba godiya da adu'a, to ina ruwan zuciyan da bata da tsatsan komai a cikinta, sai duk naji mugun tausayinta ya kama ni, idona ya cika da ruwan ƙwalla ganin tana hawaye, kana dai ganinta ka san ba'a jin daɗin rayuwar ana tsaka me wuya. Sai da ta tafi ina kame kame nace da shi zan je na duba Mamarta ce aka kwantar, yace muje tare sai naji ƴaƴan cikina sun kaɗa, ina tunanin abin ce masa aka kira shi a waya yace daga wurin aiki ne naje kawai amma kar na jima, ya koma cikin motar ni kuma na kama hannun Rumana muka wuce.
Muna tafe tana bani labarin makarantar islamiyarsu, littafan da ake musu bata jin wuyarsu ta riƙe karatun da nayi mata, jarabawarta ma duk ta biyu take zuwa, ni dai jinta kawai nake yi, dukkan tunanina ya tafi akan ina Nazifi da ya bar Iyam take kwance a asibitin Murtala bai kai ta babban asibiti na kuɗi ba, shi kuwa yana me? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, da naga yanda Iyam ta koma wallahi sai da na nemi ƙarfen gado na dafe har na zube ma ban sani ba. Jikina ya kama rawa tsoron duniya ya shige ni, Lubabatu ta taso da sauri ta riƙo ni, abinka da me ruwan ido tuni hawaye suka wanke min fuska, murya na rawa nace,"Lubabatu me yake damun Iyam?".
Sai itama hawaye suka sakko mata tace,"Wallahi ciwon kansa ne na hanta, kinga duk yanda ta ƙare ko".
Na rufe ido ina girgiza kai, sosai ta bani tausayi, ko gane wanda yake kanta ba tayi, lamarin ya matuƙar taɓa ni Allah dai yasa mu gama da duniya lafiya. Kusan mintina goma wajensu kafin nayi musu sallama, ban taho ba sai da na kira Sister Khadija ta haɗa ni da Yayarta da ke aiki anan asibitin, nace mata don Allah ga wa'annan bayin Allah'n take taimaka musu, Lubabatun taji daɗi sosai har ta kira Malam ta shaida masa, yay ta mini godiya yana cewa ya so ace yana nan ya ganni yaji daɗi, na karɓi account number ɗin Lubabtu na tura mata 20k na ce don Allah ta bawa Malam 10k, sauran kuma sayi wani butaƙan da shi, godiya ta dinƙa min kaman yawun bakinta zai ƙare.
Ta rakoni a hanya take faɗa min ibtila'in da Nazifi ya gamu da shi, wai Zahra'u ta yashe shi ta gudu ta barsa, ƴaƴansa biyu dukka ta hana shi, yanzu ma dai yana nan shima bai da cikakken lafiya, jininsa ne yay mugun hawa, hannunsa guda ya samu matsala dalilin faɗuwan da sanda aka ce ƙaramar ƴarsa ta ƙone, ana dai ta so ayi masa hoto a gano me ya samu wajen to ba'ayi ba har yanzu saboda matsalar rashin kuɗi, dama ga banki na binsa maƙudan kuɗaɗe, ga shi shagon da yake gadi an haura anyi sata an ce da sa hannunsa lamarin dai babban lamari ne, yanzu haka anata cuku cukun gano gaskiya saboda sun ce ba zasu yarda ba sai ya biya su duk ɓarnar da aka yi, take cewa wallahi ta tabbata har da hakkina, tana ta roƙona akan na yafe musu, na ce,"ai ni Lubabatu ba ki min komai ba wallahi, zaman da muka yi ba zan taɓa manta alkhairinki gare ni ba". Tace,"To don Allah na yafewa Iyam da Yaya Ƙarami".nayi murmushi me ciwo da takaici na ce,"Iyam ma ai na yafe mata". Tace,"To Yaya Ƙarami fa? Wallahi Sa'ida ba kiga ba duk yana cikin damuwa, ko ranar nan ina jinsa yana faɗin yayi nadamar abubuwan da ya aikata miki". Wani murmushin kawai nayi nace,"uhumm".
Har bakin mota ta rakoni, suka gaisa da Salim itama sai da ya bata kuɗi, haka tayi ta masa godiya itama cikin jin daɗi tana gaya min haɗuwarmu tayi musu rana saboda yanzu haka tun shekaranjiya ake neman kuɗin da za'a siya alluran Iyam da scanning ɗin da za'a mata, bayan nan tana faɗin ta taya ni murna sosai da ci gaban da na samu. Ni dai tunda na shiga mota hawaye na ke ta yi, matuƙa na tausayawa Iyam, haka na tausaya musu dukkansu, Nazifi ne kawai banji komai ba a kansa. Salim kuwa na ta complain akan da ya san da haka bama zamu je asibitin ba, ban iya masa magana ba har muka ƙaraso gida, yay lallashin duniyar nan amma ina ni dai na rasa ta yanda zan dakatar da hawayena zuba, haka ya haƙura muka yi sallama zuƙatanmu duk babu daɗi ni da shi.
Ko da na shiga gida ma duk sai suka yo kaina da tambayar me ya faru, na dai ce musu rasuwa aka yi a asibitinmu na shige ɗaki kawai na rufo ƙofa. Wayata na ɗauka na kira Lubabatun don sai da muka yi exchanging number wanda Malam ne yace ta karɓa masa lambata, tana ɗagawa nace ta lissafa min kuɗin bill ɗin na su sai ta tura min account number, haka na tura mata dubu asharin a madadin dubu arba'in da ake nema, to nima babu kuɗin ne da dukka zan tura mata. Ba jimawa sai ga kiran Yayan Shago wanda yake ta min godiya, shima yana bani haƙurin abubuwan da suka faru, ya haɗa ni da Malam wanda yace yana matuƙar godiya da abun arziƙin da na yi musu haka yay ta shi min albarka, yace ai a kasuwarsu ma an faɗa masa Abbaa yaje nemansa bai nan amma yaga ya bar masa invitation, nan yay ta min adu'a tare da fatan alkhairi, nayi godiya kafin nan muka yi sallama.
Da magriba na fito zan yi alwala, sanyin magriba duk yasa an shishshige ɗaki, na aje buta zan tsuguna sai ga yaro ya shigo, yace wai an aiko shi wurin Sa'ida, na ce masa menene ya miƙo min baƙar leda an nannaɗeta kamar laya yace wani ne a waje yace a bani. Karɓa kawai nayi, wa zai min aike idan ba Salim ba, ni kuma a yanayin da na ke ciki ban jin zan iya fita na sameshi.
Na idar da alwalar na shiga ɗakin Ummani na sauya kayan jikina, take nuna min buhun kayan miyan da ƴan ƙauye suka ƙara kawowa, nace an gode, bata lura da yanayina ba nayi saurin fita gudun kar ta tsare ni da tambaya. Sai da na idar da sallah tukunna na kunce ledar, takarda ce a ciki ƙarama, na warwareta ina duban gajeran rubutun da ke jikinta.
_"Amincin Allah da yardarsa su tabbata a gare ki, ina mai wannan rubutu ne gareki yayin da idaniya ke zubar hawaye haka kuma zuciya ke cike da nadama da tarin danasani, haƙiƙa tunda kika bar rayuwata na ke ta ganin ibtila'i daban daban, cikin shekaru shidda har yanzu na kasa samun natsuwa da kwanciyar hankali, babu jin daɗi babu farin ciki, sai daga baya na ankare da dukkan laifukan da na aikata miki sune ke dawowa gare ni, tabbas hakkinki kaɗai ba zai bar ni sukunin rayuwa ba, ni na sani na zalunce ki, zaluncin da sai dai Allah yay miki sakayyya kawai, na so ace na samu wata dama da zan maido da ke cikin rayuwata domin na gyara kuskurena sai dai lokaci ya ƙure min, bakin alƙalami ya riga ya bushe...na samu labarin kin je kin duba mahaifiyata, na gode Allah ya saka miki da aljannah, kuma naji an ce kin yi aure da irin mijin da kika aura, tabbas har zuciyata naji miki daɗi na kuma tayaki murna, Allah yasa albarka ya tabbatar da alkhairi a rayuwan aurenki, ina me yi miki adu'a tare da fatan samun rayuwa ingantacciya a gidan aurenki, ya dawwamar da ke a farin ciki da kwanciyar hankali, kazalika ba zan ƙi sanar da ke cewa rashinki a rayuwata wani babban giɓi ne da ba zai taɓa cikuwa ba sai da ke, na soki, ban kuma san ranar da zan daina sonki ba, don Allah ki yafe min, ki yafe min ko na samu sassaucin bala'in da na ke fuskanta a rayuwar da babu ke a cikinta, ki yafe min ko na samu salama a lahirata, na rasa da idon da zan iya fuskantarki, ina jin kunyar ganinki, ina kunyar haɗa idanuwa da ke...tsohon mijinki Nazifi Bala Mai Kalwa"._
Tun farkon fara karatun naji zuciyata tayi rauni, kafin na gama karantawar tuni hawaye ya jiƙa rabin takardar, na shiga rera kuka a hankali hanci na ta zubda majina, hawayen da ban san dalilinsa ba, kaina jingine da bango idona a rufe hoton Nazifi kawai ke haska min, hoton da na ke ganin laɓɓansa suna karanto min wannan rubutun. A gefe ɗaya kuwa zuciyata ta matse da tausayinsa da wani abu da ke harbawa a cikinta wanda ban san menene shi ba, kuma kamar an tsikare ni haka na miƙe na ɗauka mayafi, ina fitowa nayi kiciɓis da Ummani wadda ke ce min,"Ke lafiyarki kuwa? Naji ma kaman kukan ki shi ne na taso".
"Ina zuwa Ummani". Na faɗa da karyewan harshe, nayi saurin fita, haka na gama leƙena a ƙofar gida, har ɗaya ɓangaren na tsallaka amma banga ko da inuwar Nazifi ba, me yasa zai yi min haka? Me yasa zai zo ɗauke da wannan kalaman a cikin takardar da ke ɗauke da rubutunsa kuma ya kasa jirana? Ban san me zan ce ina ji a tare da ni ba, kamar yanda ban san yanda zan kwatanta yanayin da na tsinci kaina a ciki ba, Ummani na tsaye inda na barta, ta ruƙoni ganin irin yacca na ke zubar da hawaye.
"Ke menene wai, wani abu ya faru ne?".
Kaina na kifa saman kafaɗarta ina cewa,"Ummani Nazifi ne, Ummani yana cikin wani hali, kuma ya zo ƙofar gidan nan ya tafi bai bari mun yi magana ba".
Ƙumm naji kaina ya ƙwalu da bangon tagar ɗakina, haka murfin tagar ta doko min fuska. Sautin tsakin Ummani ya shiga dodon kunnena ta wuce ta barni tana faɗin,"Allah ya shigo da ubanki ki yi masa wannan zancen, saboda wulaƙanci saura kwana biyu ɗaurin aurenki ki tayar da maganar tsohon mijinki, shi algungumin da can bai san da zuwa neman yafiyar taki ba sai yanzu? Ke kuma da babu cikakken tunani da hankali shi ne har da iya barin kalaman ƙaryansa suyi tasirin da za su ɗarsa tausayinsa a zuciyarki, mtsswww".
Bayanta na bi da kallo kawai har ta wuce ɓangaren Baba Sabi'u, yanzu kenan laifi ne don halin da Nazifi ke ciki ya taɓa ni? Ɗaki na shige na silale na zauna daɓas kan katifa, na kalla wayata da ke ƙaran shigowan text, ina dubawa naga sunan Salim kawai sai nayi cilli da wayan, na zuƙa wani irin numfashi, na rufe fuskana da dukka tafukana biyu, daki daki rayuwar baya na dawo min hotonta na haska min, haka daki daki kalaman rubutunsa ke maimaituwa cikin kaina, haka kuma labarin da Lubabatu ta bani na halin da yake ciki na haska min a ƙoƙon ka, duk garin ƙaƙa ya tsinci kansa a cikin mawuyacin hali haka? Halin da na magani ma ya gagare shi? halin da har ta kai shi ga cin bashin banki, halin da har ta kai shi ga gadin shago, duk ina tarin dukiyarsa? Ina tarin dukiyar da har muka rabu ban san adadinta ba? sai naji zuciyata ta ƙara tsinkewa.
"Na manta da komai, na goge komai da ga raina, na yafe maka, na yafe maka, baka da sauran hakkina".
Haka na zama sukuku kamar wacca aka yiwa mutuwa ko take rashin lafiyan da yaci ƙarfinta, Abbaa ma da ya dawo sai da ƙyar na iya miƙewa na fita yi masa sannu da zuwa saboda jikina da na ke jinsa ya mutu, ga ƙirjina bugawa kawai yake yi, ban san meke damuna ba, ban san dalilin sauyar yanayin farin cikin da na ke a ciki ba, Salim ya kira ni ya kuma kira amma ban ɗaga ba, bana jin kuma ina da buƙatar jin muryarsa...
*B3ƘR11FT5* Washe gari kiran Safiyya ne ya farkar da ni, na manta ma da batun zamu je ƙunshi da gyaran kai, jin ina bacci ta kama masifan dama ta san halina, sai mun je kuma mun daɗe acan ita na cikata da mita, na bata haƙuri na ce sai ta ƙaraso kafin ta zo ma na gama shiryawa. Zaune na miƙe ina murza idanuna da ke cike da bacci, on period na ke ko da asuba ban farka ba, nayi azkar ɗina na tofe jikina, sai a lokacin abinda ya faru jiya ya shiga dawo min, na kalla gefen filona ina kallon takardar da Nazifi ya yo min aike, wani mugun haushi da takaicin kaina ya kamani, lallai akaina na yarda mutum na haukan gaske na ɗan wani lokacin, ban da hauka da na fita neman Nazifi uban me zan masa? Kukan da nayi kuma na uwar menene? gwara da Allah yasa ma bamu haɗu da shi ba don ina ga da sai na kusa kashe kaina saboda baƙin ciki, takardar na ɗauka na yayyaga nayi gutsi gutsi da ita, akanta dai na huce takaicin rashin tunanin da nayi jiya.
Wayata na duba na ga uban misscalls ɗin Salim, tunda na ke da shi bai taɓa bari min miscalls irin haka da yawa ba, kuma na san duk ya damu ne da yanayin da ya tafi ya barni a ciki, lokacin ma da yana da dama ba zai tafi ɗin ba, sai naji ya bani tausayi, haushin kaina ya ƙara kama ni, ban kyauta masa da abinda na masa ba, kawai dai na san duk wanda yaga halin da Yaya suke in har kana da zuciyar imani sai zuciyarka ta karye, lokacin da zaka taimaka musu ɗin ma ba sani zaka yi ba, amma abin takaicin da akan tausayin Nazifi na ƙi picking call ɗinsa, hannu nasa na mari fuskata. Ina shiga message ma naga messages ɗinsa har biyu, ɗaya na lallashina ne da kwantar da hankali, yana faɗin in bar yawan saka damuwa a raina, marasa lafiya ne kamata yay nayi musu adu'a, ɗayan kuma yana faɗa min ya koma tun a daren jiyan sai ranar ɗaurin aure zai biyu jirgi da safe ya taho kafin lokacin ɗaurin aure, kuma za su shiga daji ne ba lallai in sameshi a waya ba ko da na kira shi, raina ya ƙara ɓaci da rashin kyautawar da nayi, na tura masa text ɗin adu'a ina aje wayar na tashi, ban basa haƙuri ba tun da dai ba laifi nayi ba.
Yau ɗin sai na ke jina na tashi da wani ƙwarin jiki, lokacin da na fito tsakargida rana ta ƙwalle nayi mamakin irin baccin da nayi, na yiwa su Anty Lami sannu da aiki, gaba ɗaya tsakar gidan ya zama babu masaka tsinke sai ka tabi kana zaka wuce ana baka hanya, gaskiya mu ɗin ƴan dangi ne, Ummani na da tarin ƴan uwa masu karamci da haɗin kai.
Ummani bata ɗaki muka gaggaisa da mutanen cikin waɗanda ke ta tsokanata Amarya ƴar hutu. Na wuce ɓangaren Baba Sabi'u can na samu Ummani suna aiki ita da Umman su Hindatu, muna cikin gaisawa da su sai ga Hindatu ta fito a guje ta faɗo jikina tana murna, nima murnar na kama yi ina tambayarta zuwan yaushe tace min ai ƙarfe takwas ma anan tayi mata, ta zo tana ta buga ɗakina ina can ina baccin mutuwa.
Jin ta ambaci ƙarfe takwas na waro ido ina faɗin,"Wai har takwas ta wuce kenan". Don ni ko da na ɗau wayata hankalina bai kai kan lokaci ba. "Ummani bara naje na shirya zamu wuce wurin Lalle, Safiyya zata biyo ta ɗauke ni tana kan hanya, tsammanina duk bai wuci takwas ɗin ba yanzu wallahi".
"To Allah ya tsare, kin dai gama haɗa kayanki kin kwashe ko?".
Goshi na dafe don gaba ɗaya na mance ma da sauran aiki a gabana, shashancin da na buga daren jiya yasa ni baccin da ban shirya ba, don wani zazzafan ciwon kai na kamu da shi, Abbaa ma da ya dawo ban samu damar fita nayi masa sannu da zuwa ba, kuma a lokacin ma na ɗan ji tsoro ne kar Ummani ko ta yi masa wancan batun, in je yaci mutuncina Abbaa ne bai ƙi ya buge ni ba ma.
"Zan ƙarasa haɗa su Yanzu kafin Safiyya ta ƙaraso".
"To ni dai ki tabbata kin gama duk abinda za ki yi da wuri Sa'ida, kinga jiya Abbanki sai da ya jaddada min ya zamana kin gama komai, goben ana ɗaurawa za su wuce da ke, ƙunshin nan ba lallai ne ku dawo da wuri ba kuma shi ma sai da ya bar min sallahun in sanar miki kar kije ƙunshi ki dawo masa da daddare".
Kalaman nata suka sanya jikina yin sanyi. "To an aje min abin karyawa?".
"Sai dai ki leƙa gidan Yusra idan kin samu to, in ba ki samu ba kuma ki siyo indomie ki dafa, kunun ma da aka yi babu inda yaje, kinga sai Umman Hindatu ce ta kawo awara aka ƙara da ita".
"Bari kawai idan mun je can na siya wani abun".
Umman su Hindatun na cewa ko zan shiga kicin na dafa wani abun nace mata a'a bara naje gidan Maman Yasmin ɗin ba za'a rasa a can ba, muka wuce ni da Hindatu, naji daɗi sosai itama ta kawo min gudunmawar zannuwan gado guda biyu da jug ɗin roba. Ita na bari tana kimtsa min wasu kayana da zan ƙarasa haɗawa, lokacin da na fito a wanka ma har ta kammala, sai ga ɗakin yay fayau, jikina ya ƙara yin sanyi ganin da gaske dai barin gidan zan yi, ina son ɗan ƙaramin ɗakin nan nawa fa, na gama shiryawa na fito na tafi gidan Maman Yasmin ni da Hindatu. Ai tun a ƙofan gida yara suka tsare ni Anty Sa'ida kuɗin party, sai arar kuɗin nayi hannun Hindatu na ba su don ko sisi bana magani, sauran kuɗin da na ke tattalawa na rabarwa dangin Nazifi jiya, na nemi suna hankalina ya kwanta, ko da yake ba faɗuwa ba ne taimako nayi har zuciyata saboda Allah, kuma Allah zai ninka min ya kuma bani lada.
Ban samu abincin ba sai wata guntuwar taliya na dafa naci da mai da yaji, ina gama ci kuwa sai ga Safiyya, faka faka na wanke hannu na fita muka tafi. Kasa ɓoye mata abinda ya faru jiya nayi ina bata labari, da ta lailayo wata ashariya me zafi ta yarfa min sai da na kusa buɗe motar na faɗa waje, har Ilham sai da ta tsorata nayi saurin cafo yarinyar da ta saki. "Safiyya za ki yarda da yarinya taji ciwo".
A fusace ta bige hannuna a jikinta,"Dilla Malama banza shashasha yi min shiru, Sa'ida ba ki da hankali ba ki da shi sam, ji na ke kamar na shaƙe miki wuya ki daina moruwa a duniyar nan, ke yanzu har wani kiga irin Nazifi ne kima tsaya ki saurare shi, wai har kina faɗa min kin je kin duba Uwarsa yen yen yen, Allah da ina wurin sai na ƙwaci bindigar Brother na harbeki gwara na rasa ki in huta da takaici da baƙin ciki, idan ma ba ki mutu ba ƙilan ƙarar bindigan yasa ki razana ki dawo hankalinki don naga alamar ƙwaƙwalar ki babu komai a ciki sai dusarar asara, shegiya ƴar bura'uba da ma da kika fito neman Nazifi kin zame a ƙasa kin yi targaɗe kinga sa dawo su taimaka miki ai".
Tagumi na zabga kawai ina dubanta, wannan masifar yanda take ɗaga murya tana faman huci da tada jijiyoyi idan a adaidaita muke ai sai me motar ya sauke mu, a hakan ma bata huce ba sai da ta figo wuyan rigana ta dudduke ni nayi saurin ƙwacewa kar tasa mu buga accident. "Haba Beb sorry mana, ba dai ya wuce ba, kuma nima sai letter na ke ta jin haushin kaina wallahi, don ina ga da na samu ganinsa ma kukan baƙin cikin da zan yi sai na iya haɗiyar zuciya".
"Dilla can rufe min bakinki me warin tsiya kafin in ragargazo miki haƙoran gaba, kuma sorry for your self don ni da kika ganni ban sallama kaina wa wasu asararru ajina da darajata sun zube ba, shegiya gwarama a kwasheki a kai can garin inyamuran ai don idan kika zauna nan satan hanya za ki ke yi kina zuwa wajensu tunda karen su ya cinye miki zuciya".