Kenza eBookz

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 34

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 34

Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 34: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 34. Na musamman tayi parking tana faɗin,"Ai yanda kika ga wannan…

4,363 words

Na musamman tayi parking tana faɗin,"Ai yanda kika ga wannan shegiyar Yayar tasa kamata yay ki fakaici idon jama'a kisa ƙafa ki kwarfe asararriya a ƙasa, ki bi ta kan ƙafarta ki wuce, akwai uban da ya isa ya biyoki ne a yanda kike? Sai dai ma ta ɗaure kanta idan ta nemi ta ɗora miki, kai Allah nah ka bawa banzar nan ta kusa da ni hankali, doluwar banza da wofi kawai, a haka kamar ba shashasha ba, ina ji kamar na buɗe motar nan na tankaɗa ki waje ne".

"To aikata mana Yayanki kika yiwa asara ai".

Sai kuma taci gaba da jarabata, yi take yi bata ko numfasawa. "Idan da ina nan na rantse miki da Allah sai na fita na yiwa Nazifi ihun kwarto, kashh, yanda za'a rugurguza shege a ƙofar gidan nan ai ko ni sai na shiga na ɗakko murhu".

A hankali na ce,"A ke dai manta baya".

Harara ta watsa min, kuma har muka isa beejay bata ƙara yi min magana ba, ni ɗaya na dinƙa maganata ina wa Ilham wasa. An mana ƙunshi me kyan gaske, ni bana son wani na salatep na zane aka min, duk wanda ya shigo shagon kuwa sai ya tofa wow amma dai ke amarya ce, ƙawar arziƙin nawa ce dai bata ce ƙala ba, da ana kwancewa ma na nuna mata kauda kai tayi, kuma ita ce me nanatawa mai lallen ta ƙure basirarta akaina ko nawa ne zata biya. Gaskiya wajen sun iya aiki babu ƙarya, hatta gashina da aka wanke aka gyara sai da nace anya kuwa nawa ne, sai lokacin Safiyya ta samu damar magana tace ayi min ƙanan kitso nace a'a ba zan iya zaman ba, yanzu kafin a gama ma sai mu wuce bayan isha'i, ina gudun faɗan Abbaa, nan kuwa ba kitson ne ban so ba, Salim ne yace kar nayi kitso yafi son gashina a haka.

Bamu koma gida ba sai daf da isha'i, har ƙwalla nayi wajen yiwa Safiyya godiya, ita ta biya kuɗin kitso da ƙunshi har spa da ta dage sai anyi min, kuɗi ba kaɗan ba kuɗi masu yawa. A daren bayan dawowata Hindatu ta raka ni na shiga wasu gidaje da suke mutunci da Ummani sosai aka zama kamar ƴan uwa, kowanne gida na shiga kaji adu'a me daɗi ana yi min, muka dawo nan ma aka saka ni gaba da ƙarasa shanye wasu magunguna da wanda har wanka nayi da shi, ni da kayan sawata duk sai da aka yi mana turaren ƙaiƙayi koma kan masheƙiya. Ban samu zama ba sai ƙarfe goma tukunna, lokacin kuma kewar Salim duk ta cika ni, yau na kira wayarsa yafi ƙarfin a ƙirga bata ko tafiya, na masa text har sau uku sai dai na san da ace ya gani zai min reply wajib ne, amma ban san ba ko jiya yayi fushi ne shi ne zai rama shima, na kasa daurewa sai da na tura masa text na ban haƙuri ina faɗa masa yau nayi kewansa musamman golden voice ɗinsa.

Duk sai nayi wani sukuku bana jin daɗin raina, yana ta ɗokin nayi lalle na tura masa ya gani, to a online ɗin ma ba ya kai, rabonsa da hawa tun safiyan jiya, na rasa meke min daɗi, na rasa natsuwata ina ta saƙe saƙe cikin raina, har Safiyya sai da na kira tace min in kwantar da hankalina inda suke ne babu network ɗazu ma da ta biya gida taji Baba na faɗin yana ta neman wayarsa bai samu, amma Sir yace masa sun yi magana da shi ta oba oba irin wannan abar da sojoji ke magana da ita. Yau kam ba batun kwanan ɗakina don anan aka jibge miyar abinci gobe, da kayan abinci da kayan gara. Na fito da zummar tafiya gidan Maman Yasmin na ji inaa yau a kusa da uwata zan kwana, dolen dai haka na wuce na tafi don tun da baƙin nan suka zo ta bar musu ɗakinta ta koma ɗakin Abbaa, to ina ni ina batun shiga cikin su na kwana.

Washe gari tunda wuri kafin ɗaurin auren ma sai ga mutanena ƴan amana sun zazzo, Hassana Tijjani ce farkon zuwa don ita ƙarfe tara ma anan tayi mata ita da yaranta, can sai ga Maimuna itama, ƙawayena dai tun na secondry school waɗanda ake tare har yanzu, Safiyya sarkin kishi tuni ta haɗe rai tana aikin ciccin magani, faɗa take wai akan mene Hassana Tijjani zata rigata zuwa, haka ta dinƙi mitarta har sai da suka taɓa da Hassanar don dama sun saba indai akaina ne, suyi ta rigima da juna kamar yara, ni da Maimuna muka zama ƴan kallo don idan suna yi ni bana saka musu baki.

Lokacin da na ke fitowa daga wanka lokacin ƴan asibitinmu suka zo su Maman Nana da su Sister Khady, su dai shidda haka suka yo zuga suka taho, suma sun yi min kara da na su gudunmawar na frame da aka sa hotona da na Salim, ni da uniform na asibiti shima da uniform na sojoji, wanda na rasa ma ai na suka samu nasa hoton, merging aka yi wanda yay editing ɗin ya iya sosai ba zaka taɓa cewa haɗa hotunan aka yi ba, da 25k ɗin su da aka haɗa aka ce a bani, nayi ta musu godiya kuwa, sosai naji daɗin kyautar tasu, ban ma shirya ba na fara kai su gidanmu suka gaisa da Ummani, dama Abbaa na ƙofar gida da shi suka fara gaisawa, sai ce min suke sun ji daɗin adu'an da aka musu.

Muka baro gidanmu muka shiga nan maƙotanmu gidan wata Umman Habu, nan muka yi zaman mu da mutanena, don ko gidan Maman Yasmin ma ba wajen zama, gidanmu cike itama gidanta a cike, Hassana Tijjani ta kwaso duk abubuwan buƙatana daga gidan Maman Yasmin ɗin ta kawon nan, Safiyya kuma ta tafi ɗakko me min kwalliya duk da nace mata ni bana so, abun da ba dinner ko party ba tace wallahi sai anyi. Ƙarfe sha ɗaya na ranar lahadi, cikin watan ƙarshe na shekarar dubu biyu da ashirin da uku, dubban mutane suka Shaida ɗaurin auran Lieutenant Salim Sadiq Oluwa da Amaryarsa RN Sa'ida Salman Madobi akan sadaki dubu ɗari biyu lakadan. Masha Allahu ɗaurin auren ya tara dubban mutane, don gaba ɗaya kan titin layin kashe shi aka yi sai zagaye aka koma yi, duk wanda ya zo kuwa sai ya tambayi ɗaurin auren wa ake yi haka. Abbaa har sai da yayi mamakin irin jama'ar da wasu ma zai ce bai san daga ina ba, taro kamar da aljanu, kowa kuma ya zo sai ya miƙo masa hannu an gaisa, tawagar mahaifin Salim kuwa ba zai iya cewa ga adadin su ba, motar sojoji kamar tayi magana jiniya kawai kake ji na tashi a faɗin unguwar.

Ni dai tunda aka shigo ana ce min an ɗaura aure naji jikina ya mutu, ban san sanda hawaye ya sakko min ba. An gama min kwalliya a sa'ilin sai ga kiran Salim wanda rabona da shi tun shekaran jiya, sai sannan hankalina ya kwanta da naji muryarsa, duk da fushi na ke tayi da shi, fushin nawa ya gushe dalilin jinsa da nayi cikin farin ciki mara misaltuwa, tunda na ke da shi ban taɓa jinsa a irin yanayin murna da annushuwa ba irin haka, yana ta ce min nima in godewa Allah da ya nuna mana wannan rana. Yace ga shi ya yakice da ƙyar ya shiga mota in kunna data muyi vedio call ya ganni, nima ɗin kuma son ganinsa na ke nace ya kira a ta Safiyya nawa babu data.

Wani kallo da ya kafe ni da shi ta cikin vedio call ɗin kamar zai fizgo ni, yana ta faɗin nayi kyau ina ma yanzu zai tafi da ni, shi duk ya ƙosa akai masa ni, na ce bayan kana bakin aiki, yace ai sai mu kwana a otel ɗin da suke, na ce a'a ni na fi so mu raya darenmu a cikin gidanmu kan gadonmu na sunnah ba na otel ba. Shima ina ta faɗa masa yayi kyau sosai a babban rigan da yasa, ya cire hulan yana nuna min askin su na sojaji da bana sonsa, ba ranar da bana ƙorafi akai, yace ya so yayi irin wanda na ke so to ba yanda zai yi da Emeka ne. mutane anata kiransa, Sir ma yana nemansa za'ai hotuna, da abokansa haka dole ya yanke kiran, bayan ya sanar min cewa ya bawa Khalid Yayan Safiyya Ticket ɗinmu, can garinsu za'a fara kai ni Anambra wajen iyayensa, zan kwana acan washe gari akwai igbo day da Kakarsa ta haɗa za'a yi, da daddare kuma sai a wuce da ni can Delta gidana, abokansa kuma sun haɗa masa dinner na sojoji da za'ayi ranar da aka kai ni.

Cikin gidanmu kuwa sai guɗa ake yi anata taya ni murna, na so ace Salim ya samu shigowa an mana hoto tare da mahaifana to sai bai samu dama ba suna ta sauri za su koma can Abuja fadar shugaban ƙasa. Taron da aka yi a gidanmu sai wanda ya gani, Alhamdulillahi taro yayi masha Allah, ni kaina na fi farin ciki a wannan ranar sama da wancan lokacin, kowa ya shigo adu'a da fatan alkhairi yake min, abinci kuwa shiga da fita da shi kawai ake yi, ba wanda zai ce bai ci ya ƙoshi ba.

Bayan dawowar ƴan ɗaurin aure Abbaa yace na shirya nan da awa guda za'a zo a tafi da ni, yace da Ummani kuma a samu mutum biyar da zamu tafi tare da su. Yaya Al'amin ya shigo yake cewa Salim ɗin ya kira shi idan da kayan da za'a tafi da su akwai mota da zata tafi can garin na su yanzu. Aka shiga aka fito da akwatunan lefe na da kayayyakina dukka wadanda zan tafi da su, sai kayan gudunmawa da aka bar bani da na wajen Ummani dukka aka haɗa aka tafi da su, kayan gara kuma Ummani tace a bari sai zamu tafi sai a tafi da su.

Ƙarfe Ɗaya na gama shiryawa cikin wani swizz less maroon colour me tsadar gaske, ga shi Habibu yay min ɗinki na garari, Anty Saim ta ɗaura min lafaya milk colour akai, aka fito da ni daga gidan Maman Yasmin zuwa gidanmu, ƙamshi ne kawai ke tashi duk ta inda na gimla, muna shiga muka wuce ɗakin Abbaa ni da Safiyya, yana zaune bisa dardumar sallah a sa'ilin, da rediyonsa a kunne sabuwa wadda na siya masa babu jimawa, na zauna gabansa Safiyya ma na zaune a kusa da ni, muka gaida shi lokacin itama Ummani ke shigowa.

Yanda na ke jina tamkar yau ne karon farko da nayi aure a rayuwata, musamman jin irin nasihar da Abbaa ya shiga yi min kamar a auren farko. Duk yanda naso riƙe kukana kasa riƙe shi nayi, hawaye kamar an kunna fanfo sai sauka yake a kuncina, gaba ɗaya yanayina ya canja jikina yayi sanyi kamar sabuwar amaryar da bata taɓa zuwa gidan miji ba. Ummani ta amshe maganar Abbaa tana kallona tace,"Nasan duk kinji abinda mahaifinki ya faɗa, mun amince da hankalinki da nutsuwarki, auren farko ma da kike da ƙarancin shekaru da wayo da kuma ƙarancin ilimi kinyi ƙoƙari wajan riƙe sirrin ki da na mijinki duk da wahalar da kika sha, balle kuma yanzu da kika daɗa hankali, kika ƙara gogewa da ilimi da sanin rayuwa, To ba ma yi miki fatan sake maimaita kwatankwacin abinda ya gabata Sa'ida, amma kamar yanda kika sa ni dole sai an saɓa yau da gobe ta gaji haka, ita zamantakewa haka take, ba sai a aure kawai ba duk da wanda zaka zauna yau da gobe wataran sai an saɓa. Abokiyar zamanki kuma dan girman Allah Sa'ida ki zauna da ita da zuciya ɗaya, kar ki zama cikin matan da burinsu in sun shiga gidan mai mata su kori wacce suka je suka tarar ko su muzguna mata, mijinta kika aura in ma kishin ne ita zata fiki jinsa domin tana zaman zamanta ita da ƴaƴanta kika shiga rayuwarsu. Dan Allah Sa'ida ki riƙe ta kamar ƴar uwarki, kinga mun samu labarin halayenta na gari dan Allah karki lalata tarbiyar da muka yi miki wajan ganin kin ɓata zamanku".

Ni dai hawaye nake a hankali wani iri nake ji a jikina, wai yau ni ce nayi aure a karo na biyu wanda ban taɓa hasaso hakan a rayuwata ba, kullum tunanina Nazifi shi ne mijina na farko kuma na ƙarshe har na bar duniya ina tare da shi, ko da na rabu da shi kuwa ban taɓa tsammanin zan sauka akan bakana na cewa ba zan ƙara yin aure ba, ashe ba haka Allah ya tsarawa rayuwar tawa ba.

Abbaa ya numfasa kafin ya daɗa cewa,"Ko bayan raina Sa'ida kar ki watsi ki sauka daga kan nasiharmu gare ki, ruƙo da ita shi zai sa kiji daɗin rayuwarki a duk inda kika tsinci kan ki, a wannan karan ba zan ta maimaita miki kalmar haƙuri don kije kiyi ta cutar kanki ba, ba fata na ke ba kuma bana so ranar da zata zo ki kawo ƙorafin mijinki, amma kar kiyi zurfin cikin da za ki zauna ana cutar da ke, kina da mu kina da ƴan uwanki, ki kira mu duk lokacin da kike da wata matsala, wataran zamu zo ni da mahaifiyarki insha Allahu. Ku tashi kuje mota tana jiran ku, Allah ya bada zaman lafiya, yasa kin shiga kenan sai mutuwa ce zata raba ku, idan akwai rabo ina roƙon Allah ya ba ki zuriyya ɗayyiba, Allah yay muku albarka gaba ɗayanku".

Safiyya ta miƙe, ta kamo ni na tashi da ƙyar saboda yacca ƙafafuna suka yi bala'in sanyi, Ummani ta miƙe na faɗa jikinta, tana shafa bayana take lallashina, ita ta kama hannuna muka fita, ina jin Abbaa na tambayar Safiyya tare zamu tafi tace masa ehh sai ta kai ni har gidana ma, Abbaa yay aduan Allah ya bar mana zumuncinmu ya ƙara haɗa kawunanmu.

Ummani ta kai ni ɗakin Kaka, shima yay min nasa nasihan, Baba Tijjani da Baba Sabi'u dama su tun dawowa daga ɗaurin aure suka kira ni suka min nasu nasiha da faɗan. Yayyuna ma haka duk mun yi sallama da su tun dawowan ɗaurin aure. Ba'a yi wasu motoci da yawa ba, duk da Salim ɗin yace babu matsala ko mutum nawa suke son zuwa za'a tafi da su, tunda ba motan haya ba ne motoci ne na gida kuma duk za'a dawo da su, ni ba da shi ma muka yi maganan ba da Yashaik suka yi, Abbaa dai ya hana yace da mutum biyar za'a tafi, Hajjo, Umman su Batula, Mama A'i, Mama ta kurna, sai Anty Ziyada, sai da ƙyar Ummani ta lallame shi ya yarda za'a tafi da Maman Khairi, Maman Yasmin, Hindatu, Bibalo da Juwairiyya wa'anda duk suke sa'anni na ne.

Da kuka sosai aka fito da ni daga cikin gida, kowa adu'a yake min Allah sa na shiga kenan sai mutuwa zata raba, Allah yasa sa'a ce ta kiraye ni, Allah ya kaɗe tsautsayin dare da rana da yini, tarin adu'oin da suke ta fitowa daga bakin ƴan uwa da abokan arziƙi kenan, sai lokacin na buɗe fuskata na yiwa Maimuna da Hassana sallama, da ma su ƴan asibitinmu tun ɗazu suka wuce. Muna tsaye ƙofar gidan kamar ba zan tafi ba Abbaa ya fito Ummani na biye a bayansa, shi ya karɓi hannuna daga hannun Gwaggo Abula ya kamani ya kai ni bakin tsadaddiyar motar da za'a ɗauke ni, ina ta faman sharan ƙwalla ya shigar da ni ciki, ya kama hannuna muka yi musabaha yana daɗa saka min albarka da tarin adu'a, Ummani ma ta miƙo nata muka yi musabaha, zuciyata naji ta tsinke ganin mahaifiyata na goge hawaye, shima Abbaan kansa dauriya kawai yake amma naji a muryarsa, ya rufe ƙofa yana cewa da Abbayo su kori yara daga bakin motar ana daɗa ɓata lokaci, haka muka bar ƙofar gidanmu, Allah sarki Rayuwa kenan, aure babu inda ba ya kai mutum, ni yanzu ina na taɓa hangowa kaina ma garin da za'a kai ni.

Ina ta kuka Maman Khairi da Maman Yasmin na ta lallashina, Safiyya na gaba tana ce musu su ƙyale ni kukan munafurci ne. Zuwanmu airpot Salim ya kira wayan Safiyya ta bani, yana ta ban haƙuri na rashin samun space muyi waya, nace masa babu komai, yace na kula masa da kaina kuma idan akwai wani abu na kira shi, da haka muka yi sallama ina ce masa zamu shiga jirgi, yay mana adu'an a sauka lafiya.

A cikin jirgin na sake muna ta hira, muna ta shan dariyar Maman Khairi da ke buga mana ƙauyanci, awanmu uku da minti talatin da uku muka sauka a filin jirgi na Anambra International Cargo Airport, lokacin da muka sauka muka tarar da har anzo ɗaukarmu da wasu tsala tsalan motoci na gani na faɗa, dama ina sakkowa a jirgin na yiwa Salim text na shaida masa mun sauka, muka shiga mota ɗaya, ɗaya kuma ƙannensa ne mata da maza a ciki waɗanda suka zo tararmu, gabanmu da bayanmu duk motar sojoji ce, yau ni Sa'ida da ban iya turanci ba ya zan yi, to duk daga yare sai english a bakinsu, Maman Khairi da Maman Yasmin aka yi tsilli tsilli da idanu sai aikin yaƙe baki da suke ta faman yi, har dariya na so yi amma haka na cije, Sisters ɗinsa kamar za su cinye ni saboda murna, da ƴar ƙaramar ƴarsa Rofi'at yarinyar kamar ƴar turawa, bama ta kama da shi gaba ɗaya sai dogon hancinsa da ta ɗakko, naji kishi ya kama ni kar da da gaske Abbayo yake Kudrat ta fini kyau, to idan kuwa haka ne me Salim ya gani a tare da ni?. wata cikin Sisters ɗinsa me suna Apunanwu har sai da ta lotsa yatsanta cikin dimple ɗina tana faɗin zan sammata.

*B3ƘR12FT5* Mun yi tafiya me nisa kafin mu kai ga ƙauyen Aguata, kaf ɗinmu ba wanda bai gaji ba duk da a mota muke, Safiyya kuwa da ke ta saba ce mana take babu nisa ga shi ma har an zo. Masha Allah a arean gidajen da suke duk gidan su Salim yafi girma, kyau da kuma tsari. Kusan gari guda sai da muka fito a mota Safiyya ke ce mana ai family house ne, shima Salim ɗin banda yanayin aikinsa da anan zai tare, don ƴaƴa da jikoki kaf anan suke zama idan aka yi aure sai in mata, to da ke ma a matan Ummansu ce kawai tayi aure a wajen ƙabilar su amma sauran duk auren ƙabila ne.

Ba wai don zuwanmu ba haka gidan yake baibaye da sojojin da ke tsaron gidan a ko da yaushe, kun san an ce masu abu da abunsu, ga uba ga ɗa dukka masu babban rank ai dole. Tun fakawar motarmu a haraban gidan wasu suka zazzo taranmu, Safiyya tuni ta falle ina gani ta kwasa a guje tayi jikin wata mata, ni kuwa ina tsaye kaina a ƙasa, ƴan uwa duk sun yo kaina ana ga bride ɗin Onochie, abinda na ke iya fahimta kenan daga abinda suke cewa don duk da yare suke magana.

Wata dattijuwa ce ta kama hannuna, muna gaba su Maman Khairi na bayanmu, sai kuma wasu daban da ke ƴan waƙoƙinsu daga gefenmu suna rawa irin tasu. A wani tafkeken falo muka yada zango, ban da kar nayi ƙarya sai na ce falon yay girman gidan gaba ɗaya, ashe nan ne main falo na kowa da kowa, falon ya ƙawatu da kujeru na alfarma ga adon mafitai irin na su da aka ƙara ƙawata haɗuwan falon da shi, arziƙi dai yana inda yake, amma kai da ka shigo gidan ka san an aje doller.

A ƙasa na so na zauna sai dattijuwan da ta ruƙo ni tace a'a bisa kujera zan zauna, ai fa lokaci guda sai na zama wata abar kallo ko kuma in ce na zama ƴar gata, shigowa kawai ake ana ganina ana yaba irin kyan da nayi, sai ce suke shi dai Onochie ya iya zaɓo mata masu kyau. Ni fa in har za'a dinƙa faɗin kyan Kudrat to lallai sai zuciyata ta motsa da wani bala'in kishi da haushi, har ji na ke kaman dan cin mutunci ne ma Salim ya aure ni, in ba haka ba yana da matarsa me kyan da kowa ke faɗa mene na zuwa ya auro ni, wannan ma ai wulaƙanci ne, ji nayi ma na daina missing ɗinsa na sa sai haushinsa.

Salima ƙanwarsa wadda suke cewa Chiagozie, dama ita mun taɓa magana ta waya da ita ranar ta kira shi tana roƙonsa ya sauya mata new phone kuma pocket money ɗinta na makaranta sun ƙare, ta ƙaraso riƙe da dukka yaransa ukun, Ƴar ƙaramar ta ɗazu da suka je ɗakko mu ita ta fallo da gudunta ta haye saman cinyata tana cewa Yayyunta,"Here is our new Mommy".

Ni dai murmushi kawai na ke yi mai cike da burgewa, lokaci ɗaya naji yaran sun shiga raina, masha Allah kyawawa da su dukka kai baka ce haihuwar ƙasata najeriya ba, dama ya taɓa faɗa min Foridat miskila ce ko a yanzu ma ita ta noƙe daga baya, su kuwa biyun duk sun maƙale a jikina, Isioma ma kuwa dama yace akwai surutu faɗa suke da shi ma akan yawan maganarta, na ke ce masa ai nafi son yara irin haka muma muna da Walida, yace ba zan gane surutunta ba sai na shigo gidan, ile kuwa tun yanzu ga shi na gani, ta sake da ni tana ta bani labari Paapa yay musu sabbin kaya na biki, shima yayi sabo iri ɗaya shi da Maama, kuma Maama tace musu idan sun ganni suyi hugging ena suyi min peck a kumatu, ina son su da yawa, kuma sai ta faɗawa Maama Big Sis ta ganni bata gaishe ni ba. Dukka haka muka sa dariya, ta maƙale wuyana tana ce min,"New Mommy i love you so much, you are so beautifull".

Na kama kumatunta ina ce mata nima ina sonta kuma ai ta fini kyau ma, zata sammin nata kyan, tace ai Paapa ne itama ya sammata. Haka ne kuma duk cikin yaran ita tayo kamansa, biyun dai sai kama ta jini ina ga su kamannin mahaifiyarsu suka yi, Salima ce ta kwashe su tana su bar ni na huta, Rofi'at har da kukanta sai an barta a wurina, ita kuma Isioma na cewa sai ta faɗawa Paapa an ɗauketa a wurin New Mommy, zai sa bindigansa yay shooting ɗin mutum, ina kallo Salima ta talle mata ƙeya ni dai nayi dariya, ina ƙara jin sha'awan yaran.

Nan aka barmu kowa ya watse, ina ta baza ido ma na ga shigowan Safiyya ba ita ba dalilinta, Maman Yasmin ta zunguro ni na dubeta, yanda take da fuska abin ya bani dariya, a hankali tace,"Ke mun kawo kan mu, yanzu mu ta ina zamu fara musu bayani baki babu turanci balle yaren da suka fi ji, wannan shi ake kira da kasassaɓa ina zaman zamana na ɗebo ki na kawo ki zanji kunya".

Maman Khairi tace,"Kin san ni da tsarguwa ni ta ɗazu ma da taje ta rungumeta sai naji kamar zaginmu tayi, ko yaren ne me yanayin zagi oho".

Dariya nayi da ce musu,"To ai Safiyya tana nan, kuma Umma ma na nan". Suka ce,"Ohh tou da sauƙi". Maman Khairi na faman kalle kalle take cewa,"Ohh wuri kamar ba'a ƙasar nan ba, mu dai yi shiru kar wannan abar CCTV ta naɗe ƙauyenci mu ta nuna". Nima sai na ɗaga ido ina ƙarewa falon kallo, ta bakin nata ba za'a rasa CCTV ba kam, musamman a gida irin wannan, Maman Khairi da mugunta ta bushe da dariya tana cewa ita wallahi zuwan su Gwaggo ta hango za'a buga diramar ƙauyanci.

Natsuwa muka yi jiyo takun tafiya. Kaina na ƙasa na ke jiyo muryan Safiyya na ta kwara bayani da harshen da ba na ɗaukar komai a cikinsa, ni duk tsayin lokacin da muka ɗauka da ita ma ban taɓa tsammanin ta iya wani harshen ba bayan Hausa, kawai dai na yi mamaki sosai lokacin da muke makaranta yanda kaf makaranta babu wanda ya kaita iya turanci, balle ga shi ta gwamnati muke yi, lokacin har ga Allah ba ƙaramin kishi na ke ba, ashe da dalilin dalilai ba bahaushiya ba ce zuryan, da take ce min suna zuwa hutu Anambra ce na ke ko dai irin ƴan uwa na kalen dangin nne da su, gene ɗin Baba yafi yawa a jikinta shiyasa ba zaka taɓa cewa ita ɗin ruwa biyu ba ce.

Cikin aji da takun nustuwa mahaifiyarsa da Kakarsa suka shigo falon, fara'ar da ke saman fuskar Maa kaɗai zai tabbatar maka da ita ɗin macece mai ilimi da iya zamantakewa, haƙoranta duk a waje, ashe itama me kyau ce, na ganta a hoto don ita ce akan wayarsa amma sai naga a fili ma tafi kyau nesa ba kusa ba, tun daga nesa Safiyya ke ce min gulmamman ga surukar ki nan, har da Umma don na jiyo muryarta itama, dama ita tun jiya ta taho. Nayi saurin zamowa na duƙe a ƙasa, Maa ta kama ni zata maida ni kan kujerar sai na kasa zama don gaskiya ba zan iya zama gani gata ba, da nauyi kam. Ta dubi Umma tana ce mata ta faɗa min ita uwata ce, Umman su Safiyya ke cewa ai halinmu ɗaya da Kudrat. Maa tana ta saka min albarka da nuna jin daɗinta, itama har da adu'anta na Allah yasa na shigo family ɗin na su da ƙafan dama.

Kakarsa wadda suke kira da Mommi itama muka gaisa da ita tana ta saka min albarka, wata cikin ƙannensa wadda suke cousin ta zago ta bayana tana haɗa gefen fuskarta da tawa tana cewa,"Aunt Dimple you are highly welcome to Chibuzo family". A hankali cike da kunya na ce mata,"thank you". fuskata na fitar da murmushi. Gaskiya family ɗin su Salim mutane ne masu karama, sun karɓemu hannu bibbiyu cikin girmamawa da mutuntawa, babu nuna wani ƙabilanci, kowa haba haba yake da mu, Mommi sai faɗa take yi me yasa sauran matafiyan suma ba su biyo mu a jirgin ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull