Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 35
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 35: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 35. Aka ce za'a kai ni can ɓangaren Maa na zauna sai Mommi tace a'a a…
4,447 words
Aka ce za'a kai ni can ɓangaren Maa na zauna sai Mommi tace a'a a kaini wajenta, can muka tafi muna zuwa duk muka yi alwala muka yi sallah, su Maman Yasmin suka rarrashe domin hutawa sai ga shi ana shigo da flask flask na abinci da lemuka iri daban daban, wani wawaken tray kuwa me zurfi cikinsa aka zubo wasu daƙwala danƙwalan kaji kamar sayi magana, kana kallo yawunka zai tsinke, Mommi ce take muci mu ƙoshi namu ne dukka kar mu rage ko saura. Muna nan zaune tasa aka kira direbobin da suka taho da su Umman Batula, ta ke tambayarsu suna dai tafe lafiya ko. Mun yi waya da su Ummani na faɗa musu mun sauka lafiya, Abbaa yana ta ce min na yi haƙuri a inda na tsinci kaina, za su zo wataran insha Allahu, sai duk jikina ya ƙara yin sanyi kewarsu ta ƙara kama ni. Bayan mun yi sallar magriba ne Mommi tayi min rakiya falon Kakan su Salim, Allah sarki shima ya tsufa tukuf kamar Kaka, yana daga kishingiɗe akan wata kujera, Ƴaƴansa na kewaye da shi ciki har da baban su Salim wanda sai yau shima na taɓa ganinsa, shi ko a hoto ban gansa ba kuma da shi ne dama bamu gaisa ba, ina ganinsa na gane shi saboda zubin ingarman jikinsu ɗaya da Salim hatta sautin muryarsu.
Ai ko da fara'arsa shi ma kamar Maa ya karɓe ni, na lura dai family ɗin na su dukka haka suke, babu wani me damuwa a cikinsu Allah ya ba su kyakykyawan zuciya, yana kan kujera a zaune Mommi ta kai ni har gabansa ƙasa gaban ƙafafunsa, sai gani nayi ya miƙo min hannu mun gaisa, naji na kasa sai Mommi ɗin ce ta kama hannuna ta sanya cikin nasa, "Allah yay miki albarka kin ji daughter nah, kuma ina miki barka da shigowa cikin mu, ki ɗauke ni tamkar mahaifinki kin ji, idan kina son wani abu ko kina da damuwa am here for you dont feel shy, babu kunya tsakanin uba da ɗiyansa, kina son ko menene ki neme ni, idan Salim ya miki ba daidai ba ki sanar da ni, amma kema kar ki yi masa ba daidai becouse he is ahead of you, shi mijinki ne aljannarki na ƙasan kafafunsa".
Haka Mommi ta dinƙa zagawa da ni ina shiga ina gaida iyayen gidan, muna tafe tana bani labarinta itama freely babu ruwanta, har tana bani labarin asalinta ba musulma ba ce kaman yanda dai Salim ya bani labari. Ashe haka tafiyar garin take da nisa, mu da su Maman Yasmin muna ta zuba idon ganin su Umman Batula sun sauka zuwa bayan isha'i sai ji muka yi Safiyya na faɗin ai tafiya da saura, su da isowa sai cikin dare wajen ƙarfe biyu da rabi zuwa uku, tafiyar tafiyayya ce awa sha uku da mintina, na jinjina kai dole Salim yace ba zai bari a taho masa da ni a mota ba, ashe haka aka kwaso ni gari me uban nisa, ni ƴasu idan zuwa mutum zai yi nawa zai kashe kuɗin mota? Ai kuwa duk tsada insha Allahu ma kuɗin jirgi zan biyawa mahaifana su zo su ga gidana, da inda na faɗa sabuwar rayuwa, Allah dai ya bamu aron rai da lafiya.
[2/2, 07:48] Hlm: *B2ƘR13FT5* Zahra'u ce ta taso cikin gigitar yanayi, duk da halin da na ke ciki na tashin hankali sai da nayi matuƙar tsorata da yanda tayo kaina, nayi gefe don bata hanya a tunanina ko zata bi bayansa ne sai ji nayi ta shaƙi wuyana da dukkan ƙarfinta, ta maƙure ni jikin bango tana faɗin,"Wallahi sai na kashe ki kema, tun da kika kashe min yarinya ba zan barki ba, saboda kina baƙin cikin ke ba ki haihuwa shine kika kashe min yarinya".
Kiciniyar ƙwatar kaina na shiga yi, Innarta ta taso don ƙwace ni saboda yanda take yi ɗin kamar ba ita ba, amma ina Innar ta kasa taimakona haka nima saboda jikina da ke a mace bani da wani ƙarfi. Ganin zata illata ni muka koma dambe, ni dai ƙwace kaina kawai na ke so nayi, amma ita burinta tayi min rauni, wani ƙarfe da ke jikin bangon ɗakin nata ta ciro zata soka min, har na saddaƙar sai Allah yasa Inna da su Marawiyya suka rufar mata, nima na tattaro kuzarina na fizge su kuma suka riƙeta zuwa ciki.
A sannan Iyam ta iso wajen da salati tana cewa,"Wai me yake faruwa ne, menene na ke ta jin hayaniya, ba dai fitina kika tayar ba".
Ta faɗa tana kallona kafin ta buɗe ƙofa ta shiga ɗakin, na waiga ina kallonta idona na sauka kan ƴar da ke kwance kan gado tamkar mai bacci. Kasa yarda nayi da cewar ta mutu don haka na faɗa ɗakin na isa gadon na kai hannu zan ɗauketa, aikuwa sai ji nayi an kwashe ni da zazzafan mari, marin da yasani ganin ƙyallin wuta a idona wanda tunda uwata ta haife ni ba'a taɓa min irinsa ba, cikin gigita da ɗimauta na dubi Iyam da bama na iya ganinta da kyau.
Nuna ni take yi da yatsa tana so tayi magana, ban san me ya hanata ba sai ta fashe da kuka tana zama wuri ɗaya. "Wannan yarinya Allah ya isa tsakaninmu da ke, Allah ya isa ba zamu taɓa yafe miki ba wallahi, ke annoba ce aurenki musiba ne, aurenki jaraba ne, ban san mummunar ƙaddarar da ta haskawa Nazifi ke a rayuwa ba, tun da kika shigo rayuwarsa yake ta ganin jarrabawa iri daban daban, kin hana shi sakat kina so ki toshe masa duk arziƙin da zai kusance shi, na tabbata dukiyar da Allah ya ba shi ma da kina da iko sai kin ga bayanta, yanzu shine saboda mutuwar zuciya da tsantsar zalunci irin naki na mahassadiya ki ka kashe masa ƴa, ke kin san irin wuyar naƙudar da baiwar Allahn nan ta sha kafin haihuwarta kuwa, amma kika rabata da abin da ta haifa saboda ba ki san zafin haihuwa da daɗinta ba. To da yardar Allah abin da kika yiwa Shalele kema sai ya faru da ke".
Inna tana dubanta ta ce,"Don Allah wannan maganar bata kamata ba Hajiya, idan kun duba dama yarinyar nan ai bata da lafiya...".
Iyam ta ce,"Kinga Zulai kiyi shiru babu ruwanki a wannan lamarin, ki bari ni da ya shafe ni nayi magana, ba ki san wacece Sa'ida ba ne, ta hana kanta haihuwa da shi, kuma ya auro an haifa masa amma ta raba shi da ƴarsa, dama ni ta tsane ni shiyasa ta kashe me sunan nawa. To wallahi lamari nan sai mun danganta shi ga hukuma, sai Alƙali ya karɓa mana hakkinmu don ba zan yafe kashe min jika da tayi ba, yanda ta kashe itama sai an kasheta".
Ƙafafu na rawa nayi gaggawar fita a ɗakin, ɗakinsa na shiga sai na tarar da shi zaune a kan kujera, yana riƙe da Iman a hannu ya kafe yarinyar da idanu, kai kana ganinsa ka san a fusace yake Allah ne da ikonsa kawai yake riƙe da shi a zaunen. na rasa me zanyi, hawaye kawai na san da yana sakko min masu zafin gaske, sai kuma hoton tsautsayin ɗaukar Noor da ke ta haska min a idanu, abin kamar almara! Na ɗauki yarinya lafiya ƙalau kuma ace ta mutu a hannuna, tabbas tsautsayi ba ya wuce ranarsa, sai mai tsantsar imani me zai karɓi wannan mummunar ƙaddarar.
Sama na kalla a fili na furta,"Ya ubangijina ka yafe min zunubin da na aikata a gareka da na ke fuskantar hukunci".
Duk ashe bai san da shigowata ba sai yanzu, ya ɗago rinannun idanuwansa yana kallona, na zube a gabansa zan buɗi baki nayi magana ya ɗaga min hannu alamun ba ya son jin komai. "Ba na son ganinki, bana son ganin ko da inuwarki, na tsane ki Sa'ida, ki tashi ki fice min a ɗaki, ki bar gabana Sa'ida".
"Don girman Allah ka tsaya ka fahimce ni Hub...".
Uwar tsawar da ya doka min yana tasowa kaina ita tasa nayi shiru na kare kaina da hannayena. Cikin ɗaga murya yace,"Fita a in da na ke, kar ki ƙara zuwar min ɗaki, kije ki kira ubanki da ya saba yiwa gawa sallah ya zo ya sallaci ƴar da kika kashe...Har yanzu cikin kaina na rasa mummunan matakin da zan ɗauka akanki Sa'ida, kar kiyi tunanin saki a wurina domin ba za ki kashe min ƴa na barki ki tafi kiji daɗin rayuwa ba".
"Ban kasheta ba, wallahi ba ni na kasheta ba". Abin da na faɗa kenan na fita a ɗakin kamar zararriya, kamar mahaukaciya haka na koma, ina shiga ɗakina na zube a ƙasa na cire ɗan kwalina nayi wurgi da shi don wani zafi na ke ji ta ko'ina a jikina, kai na ke girgizawa ina ta maganganu ni ɗaya. Duk da sanyin gari amma haka zufa ke tsatstsafo min kamar an watsa min ruwa, da Allah na dogara kuma shi kaɗai zai fidda ni daga taskon da na faɗa. Rumana ta zo ta rungumo ni jikinta tana kuka itama, sai tasa ɗan ƙaramin hannunta tana share min hawaye tace,"Antyna ki daina kuka, ba na so inga kina kuka".
Kalamanta sai naji tamkar ɗan cikina ne ke faɗa min, bani da wata kafaɗa da zan kwantar da kaina nayi kuka a cikin gidan nan, ita ɗin kawai na ke da, sai na kama hannunta itama ina faɗa mata ta tayani gaya musu bani na kashe musu ƴa ba. Allah sarki uwa kamar ta san halin da ƴarta ke ciki sai ga kiranta ya shigo wayata, ban iya ɗaukar wayar ba sai Rumana ce ta ɗaga tasa min a kunne. "Sa'ida ya naji kamar kina kuka".
"Ummani, Ummani ki zo don Allah, ku zo ku cire ni daga wannan bala'in". "Hasbunallahu wani'imal wakil, me ya faru haka, me ke faruwa Sa'ida? Ke da wa?".
Wani irin numfashi na ke yi me wahalarwa na kasa maganar gaba ɗaya, tana ta tambayata sai Rumana ce tace,"Ummani Anty Amarya ce". Sai naji Ummanin na faɗin,"Sa'ida kishiya kike yiwa kuka?". Kaina ya lanƙwashe ina jin numfashina na neman ɗaukewa, muryar Abbaana da naji ita ta saka na buɗe ido. "Sa'ida! Sa'ida! Ba ki da lafiya ne? Menene?".
A hankali muryata kamar ba tawa ba nace,"Abbaa ba ni ba ce wallahi, ban yiwa ƴarsu komai ba Abbaa, Allah ne shaidata bani na kasheta ba amma sun ɗora alhakin mutuwarta akaina, Abbaa ku zo ku taimaka min ban san me za su yi min ba".
Muryan Abbaan a zabure naji ya furta,"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Sai ƙit naji an kashe wayar. Kaina dai na lanƙwashe a kafaɗar Rumana wacce ke riƙe da hannuna tana ta aikin goge min hawaye, ƙwayar idona ƙafe take a wuri ɗaya. Hawayen ma sun daina zubo min sun ƙafe, na zama dai gani nan kamar me rai kamar mara rai, ai na san zamana da Nazifi kuma ya ƙare, to amma ta ya zai barni haka nan? Sakina kawai ai ba zai sa ya huce baƙin cikin da yake ganin na haifar masa ba, to me zai yi min wanda yake ganin ta nan zai ɗauka fansa?
Bani da wani abu da na ke matuƙar so sama da mutuwa a wannan lokacin, ina raye bana raye Allah zai wanke ni na sani. To amma rayuwar na gaji da ita, bana so na ƙara kwana a duniyar nan, da ace nayi haƙuri ban zaɓi Nazifi sama da burin Abbaana ba da ban tsinci kaina a bala'in rayuwa haka ba, danasani ban fifita farin cikin Nazifi akan na iyayena ba, ina nadamar fifita soyayyar Nazifi sama da samarwa kaina rayuwa me inganci. Kusan kamar bayan minti goma haka aka turo ƙofar ɗakin, sama sama na ke jin komai, idan ka ganni zaka tsammaci nayi dogon suma ne.
"Bata nan ne?". Naji maganar a tsakiyar kaina amma ban iya motsawa ba, ban kuma shaida muryar ba, sai dai ko wace ma bata gane ni ba ce tunda na bata baya. "Gata nan". Rumana tace da ita, duk wani taku nata da nake ji ina jinsa tamkar ana gutsirar naman jikina. Rumana ta gaida ita tana amsawa lokacin da take zagowa gabana, ta duƙa tana tambayar,"Lafiya dai ko?".
Ni dai kallonta kawai na ke yi da ƙwalalan idanuwana irin wacca aka sassaƙa aka dasa, Anty Naim ce maƙociyata, gaba ɗaya layinmu da ita muka fi mu'amala, Farfesa ce a ABU take lakcarin, tana da kirki sosai don ta kan shigo musha hirarmu da ita, ni ce ma ban fiya shiga gidanta ba, farko farkon zuwana ma har yaranta take turo min. Da aka yi haihuwar nan ne na shiga gidanta na faɗa mata sai yaranta suka ce min ai ta jima bata gari.
Hannu ta kai ta taɓani, naga tayi saurin janye hannunta, ko bata faɗa ba na san ji tayi tamkar ta saka hannun nata ne a garwashi, don ni kaina zafin jikin nawa ƙona ni yake yi. " Subhanallahi Sa'ida ba ki da lafiya ne haka?".
A hankali na ce,"Anty Naim ina wuni".
Tace,"Aa ina batun gaisuwa ina ganinki a haka, me yake damunki. Kuma babu kowa a gidan ne naga sai ƙaramar yarinya tare da ke, me zata iya yi miki wannan, tashi muje asibiti".
Tayi maganar cike da kulawa da nuna damuwarta, Wahaltaccen yawu na haɗiye na ce,"Ai lafiyata ƙalau, nima ban san me yake faruwa ba Anty Naim, ban san me yasa ƙaddara ke ta ƙwallo da ni ba".
Kallona ta tsaya yi kafin tace,"Wata matsala ce Sa'ida?".
Kamar wata susutacciya na kaɗa mata kai nace,"A'a babu komai, kawai dai Anty Naim, Ki zauna mana akan gadon".
Yunƙurawa tayi ta zauna bakin gadon tana ta dubana da nazari. Na daɗa cewa,"Kin zo ba zan iya kawo miki komai ba, idan na tashi ƙirjina ne zai faɗo zuciyata ta fito kiyi haƙuri".
Sai ce tayi,"Kai akwai matsala, kira me gidan naki a waya a shaida masa zan kai ki asibiti, zafin zazzaɓi har ya kai ki ga yin surutai". Ta fada tana cicciɓata ta matsar da ni bakin gado na jingina a jikin gadon, don ce mata nayi ban san ta yanda zan tashi ba, ban san yanda ma ake tashin ba.
Rumana ta kawo mata ruwa ta ajiye. Bata bi ta kan ruwan ba tace,"Na dawo tun wancan satin Yara ke faɗa min Amaryar gidan nan ta haihu, har ma kin shiga ki faɗa min kika samu bana nan, to fa ina ta cewa zan shigo kinga sai yau Allah yayi".
Idona a gefe ɗaya na ce,"Ehh Anty Naim, wata ɗaya ma kenan. Amma na kashe ɗayar yanzu, na kashe musu Ƴa Anty Naim". Ai kana jin yanda nayi maganar ma kasan ba'a hayyacina na ke ba.
Ita kuwa da sauri ta furta,"Auzubillahi kisa! kin san me kike faɗa kuwa, Sa'ida ba ki cikin hankalinki duk yanda akai, akwai matsala ni ba wacca za ki ɓoyewa ba ce, mene yake faruwa?".
Sai na kama cewa da ita,"Ai bani da hankali Anty Naim, bani da shi, ya ƙare. Na kasheta na kasheta, amma ban san ta yanda ta mutu ba".
Jin ina maganar zararru sai ta toshe min baki tana cewa da Rumana ta dubo lambar mijina ta faɗa masa. Ni kuma sai ce mata na ke yi,"Anty Naim ki taimaka min zuciyata na ke so ki cire min, idan aka gama soyata a waje sai ki mayar min kinji, wayyo jikina ma ki watsa min ruwa me sanyi kinga duk na babbake, kuma don Allah ki taimaka ki kaini inda za'a ciro hotunan da ke cikin idona a nunawa Nazifi ya gani, so na ke ya gani idona ai ya ɗauki hoton komai".
Ido na rumtse ina dafe saitin zuciyata, kafin lokaci ɗaya kuma saƙuwa ta sarƙe ni.
"Ruwa! Ruwa Anty Naim, zan sha ruwa Anty Naim, ki ban magani ƙirjina zafi yake min".
"Anty ga ruwan". Rumana ta faɗa tana kafa min kofin a baki, tun da na kafa baki sai da na shanye, tana saukewa nace ta ƙara min, nan ma na kuma shanyewa na ce su ƙara min, Anty Naim tace ya isa haka. Roƙonta na kama yi akan ta taimaka ta kira min Ummani da Abbaa su zo, su zo yanzun nan, su zo da likitan da zata tashi Noor da ga baccin da tayi, Noor suma tayi amma taƙi tashi, kuma a zo da wanda zai ciro idona a nunawa Nazifi hoton komai.
Ruwa ta watso min a fuska na firgita ina ƙanƙameta jikina sai rawa yake yi. [2/2, 07:48] Hlm: *B2ƘR14FT5* Cikin tsananin tausayina Anty Naim ta kewaye ni jikinta. Idona akan Rumana na ce,"Rumana kirawo min Abbaa".
Anty Naim tace,"Sa'ida za ki ɗaga musu hankali, barsu tukunna. Duk da ban gama gane kan Al'amarin ba amma kamar kina magana ne akan yarinya ta mutu an ce kece ko?".
Kai na ɗaga mata ban iya cewa komai ba. Sai naji ta sauke gwauron numfashi. Nace mata,"Anty Naim da an kirawo min Abbaan nawa don Allah, shi zai faɗa min maganar da zan ɗan samu sauƙin ciwon da na ke ji a ƙirjina".
Wayar ta karɓa a hannun Rumana tana faɗin,"Yanzu shi ina me gidan na ki?".
"Yana ɗakinsa ban san wanne mataki zuciyarsa zata yanke akaina ba".
"To wai ƴar mutuwa tayi ne ko me? ki nutsu ki min bayani".
Ido na rufe na ce,"Eyy Anty Naim mutuwa tayi kuma ni na kasheta haka Babanta yace, Babarta ma tace na kashe mata ƴa, Kakarta ma tace na kashe mata jika".
Ni dai tun da na faɗi hakan kuma sai naji numfashina na karkatsewa. Waya naji an ɗora min a kunne wadda ko ƙararta banji ba, muryar Safiyya naji tana cewa,"Beb wayar Ummani na kira zanwa Abbaa ya jiki sai naji muryar kamar babu lafiya, na ƙara kiranta kuma bata ɗaga ba na dai ji tana mota".
Shirun da taji ta ƙara cewa,"hello Beb, Beb, Sa'ida bacci kike yi ne naji numfashinki na fita da ƙyar, ko ba ki da lafiya ne?".
Cikin wata murya da tayi daban da tawa na ce,"Safiyya ba ni ɗaya ce babu lafiya ba komai ma babu lafiya". Sai na fashe da kuka wanda ya katse maganar da take son ƙara yi, na ce,"Safiyya ɗayan yarinyar Nazifi ce ta mutu kuma sun ce ni na kasheta".
"Kutumar bura'uba kika kasheta kamar ya? Nazifi da matarsa suna shaye shaye ne? Me ma ya kawo zancen kin kashe musu ƴa, sun bugu ne, taɓa ƴar kika yi ko me?".
"Safiyya kuka take na goyata ya ɗaukota, bacci tayi a bayana Safiyya kafin ta farka kuma daga nan...". Kukan da yaci ƙarfina ya hana ni ƙarasa me na ke son cewa. Ita kuma tana cewa,"Daga goyo sai mutuwa, ya za'ai haka abu kamar shiri. Kinga gani nan zuwa gidan". Ƙit ta kashe wayar ina jinta kafin kashwewar tana faɗin,"Anty ba ni aron maƙullin motarki".
Anty Naim tace,"Amma abun da matuƙar ɗaure kai, to dama yarinyar bata da lafiya ne ko me?".
"Wallahi ban sani ba, ni dai na goyata kuma na sakkota babu rai".
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, lallai kin shiga tsaka mai wuya, tabbas kina cikin garari me fitar da ke sai Allah. Amma kwantar da hankali bi'izinillahi Allah zai yayyafawa bala'in sanyi. A hankali nace,"Amin".
Rufe bakina kenan sai jin muryar Yaya nayi ta shigo ɗakin tana zage zage, na buɗe ido a wahalce da duk suka ƙanƙance, gayyarsu da na gani ita ta tsorata ni yawu me azaba ya wuce a maƙoshina. "Ai yanda kika kashe mana ƴa muma sai mun ga bayanki". Maganar da suke yi kenan suna ɗure ɗuren ashar suna neman rufe ni da duka, Anty Naim tayi saurin tashi ta kareni. Yayan ta fallawa Rumana mari tace da ita,"Don ubanki fice kafin kema ta kashe ki". Yarinyar na kuka ta fita tana waigowa ta kalle ni.
Kun san ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, duk yanda Anty Naim ta so ɓoye ni sai da suka tureta suka fizgo ni. Ba zata iya da su ba haka ta fita da sauri wai tana ƙwalla kiran neman taimako, To waye zai taimake ni a cikin gidan nan? Ban da muryar da zan ɗaga na ce ta dawo ta ƙyalesu suyi yanda zasu yi da ni. Anty Fati ta fizgoni na miƙe Fati ta kawo hannunta zata mare ni nayi saurin kawar da fuskata. Kan na farga kuma Zahra'un ta shiga dukan cikina tana wallahi sai dai idan ta kasheni itama a kasheta. Ana haka sai muryar Nazifi naji yana cewa,"Yaya ku zo, Ke Fati kamo Zahra'un ku fita".
"Ai Nazifi ka bari mu raunata shegiya". "Malam ne ya zo".
Jin hakan sai ɗakin ya zama kamar anyi ruwa an ɗauke yay tsit, shi ya zo ya fizge Zahra'un wacca ke ta abubuwa kamar me iska, ficewa duk suka yi. Anty Naim ta dube shi tana gaida shi, ni kuma tuni na rikice da ganin nasa tsaye kaina yana jifana da wani irin kallo na me zan miki na huce. har yanzu Iman na hannunsa, hawayen da suka ƙafe tun ɗazu suka gangaro, ban iya ɗago kaina a jikin bangon ba nake ce masa,"Kar ka yanke hukunci cikin fushi, don Allah kar yarda da zancen zuciyarka".
A ƙalla ya kai cikakken minti ɗaya kafin ya buɗe baki yace da ni,"Ki sakko ƙasa, jiranki ake kar ki ɓata min lokaci". Yay maganar da wata irin murya yana juyawa.
Ni kuma na dubi Anty Naim nace,"Kiyi haƙuri kin zo gidan namu babu yanda yake".
Ta kamani tana zaunar da ni tace,"Sa'ida ai ni lamarin duk na rasa ta cewa".
Miƙewa nayi a dabarbarce zan fita, sai ta dakatar da ni wajen ruƙo hannuna, ɗankwalina da ke ƙasa ta durƙusa ta ɗauko ta ɗaura min wanda ni ban ma san babu ɗankwalin akaina ba. Rumana na kuka sosai ta riƙe Anty Naim tana ce mata,"Don Allah kar ki kai musu Antyna, kar ki kaita don Allah, Ƴan sanda ne suka zo, kuma Iyam tace tafiya za'ayi da ita".
Nima ta kamoni tana cewa,"Anty kar kije, kar ki je Anty". Fita kawai nayi fuuu tamkar iska ce ke hankaɗa ni, wanda bai sani ba kuwa zai iya cewa ga mahaukaciya nan, Anty Naim ta biyo ni da sauri tana riƙe ni saboda nema na ke na faɗi a matattakalar na gangara wajen sauka.
A falon na tarar da mamaki da akasin sa, nayi matuƙar kaɗuwa da police ɗin da na ke gani, sai dai fa yanda na gansa da sauran mutanen da ke a falon ba ƙaramin amsawa zuciyata tayi ba wanda ta kai ga har sai da na kai hannu na dafe ƙirjina. Shine tsaye a tsakiya rungume da yarinyar da ta mutu, sai ita Zahraun na kan kujera Inna da Marawiyya a kusa da ita sun riƙeta alamu ife ife take faman yi, su kuma tawagar Iyam duk suna tsaye ƙofar ɗakinta. Daga gefe Malam ne a tsaye hannayensa harɗe ta baya kansa sunkuye a ƙasa, sai Abbaana shima a kusa da Malam ɗin ƙwayar idonsa cak a kaina. Na girgiza sosai da ganinsa don ban san da zuwan nasu ba, can kujerar bayansa Ummani ce zaune ta rufe fuska da mayafi da gani ka san kuka take yi, har da su Yashaik da Yaya Imam.
Daga bakin ƙofa kuma ƴan sanda ne guda biyu tsaye masu baƙin kaya, sai ta ɓarin da su Abbaa suke wani ɗan sandan ne amma shi wandonsa ne baƙi rigarsa kuma sky blue. Iyam tayo kaina ta cakumo ni daga hannun Anty Naim ta hankaɗa ni gaban ɗan sandan wanda naji ta kira da Usman. Kafin ta fara kora bayanin,"Don Allah kuyi mata hukunci daidai da abin da ta aikata, wanda ya kashe a kashe shi ne. Ta kashe jaririyar da bata ji ba bata gani ba".
Malam ne ya doka mata tsawa da cewa,"Jummai ya isa! Kar na ƙara jin bakinki a wurin nan idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci".
Kana ya kalli ƙofar ɗakinta yace da yaran,"Ku kuma kafin na ƙifta ido ku fita ku bar gidan nan, kar wacca tayi gangancin da minti ɗaya zata cika mata a gaban idona, kun sanni sarai zan saɓa muku".
Sum sum dukkansu suka yi hanyar fita cikin sauri. Idona ya kai kan Zahra'u da ke kuka tana faɗin,"Yaya itace ta kasheta, Yaya ka ƙwatarwa ƴata hakkinta". Tayi maganar da ɗan sandan kusa da su Abbaa.
"Saka mata ankwa". Furucin da Yayan nata yayi kenan, nima kuma yana kallona cikin ɗaga murya wanda har sai da naji tsoro ya ce,"Ke bada hannunki". sai ɗaya daga cikin ƴan sandan da ke tsaye bakin ƙofa ya tako ya zo gareni, ya buɗe ankwar yana cewa na ɗago hannayena. Muryar kukan Ummani ta cika falon da faɗin,"Don Allah a fara bincike tukunna, ku fara bincike amma tabbas Sa'ida ba zata kashe rai ba, ba zata kashe jaririya ba, ajalin yarinyar ne yazo ta hannunta amma ba ita ta kasheta ba".
Yanda take maganar a ruɗe take. Ta taso da hanzari zata zo wajena Abbaana ya riƙeta. Sai ta sake fashewa da kuka tana faɗin,"Abbaa kar ka bari su tafi da ita, yarinyar nan sharri aka yi mata wallahi".
Muryan Abbaa da Allah ɗaya ya san me yake cikinta yace,"Na sani Sa'adatu, Na sani Sa'ida ba ta aikata abin da suke tuhumatarta da shi ba, sai dai lamarin a zargeka da kisan kai babba ne wanda a halin yanzu ba zamu iya yi mata komai ba. tun da har shi mijinta ya yarda ta aikata to babu me yarda da ba ta aikata ɗin ba, mu bar hukuma tayi nata aikin, mu kuma zamu kwana muna gayawa Allah da shi ne shaidarta, Allahnta shi kawai zai kawo mata mafita".
Idona a kansu dukka, a raunane suke maganar, sai naji na bar tausayin kaina na koma tausayinsu. Kallon ɗan sanda nayi babu musu na ɗaga hannayena biyu a haɗe na miƙa masa. Sai Anty Naim tace,"Ku tsaya! Ankwa! Asaka mata ankwa kamar ya? Ina shaidar cewa tayi kisan kan da kuke tuhumarta?".
Yayan Zahra'un ya ɗaga mata murya da faɗin,"Wacece ke da za ki hana hukuma yin aikinta, ba ki da hurumi a wannan lamarin saboda haka ki koma gefe".
Ta dube shi tace,"Idan da hadasi akanka zaka san cewar ina da hurumi akan lamarin da ya shafi maƙociyata. Ba zan yarda da wannan cin zarafin da ake neman yi ba. Zargi ne kuke yi, baku da tabbacin ta aikata".
Ya nunata da bindigar hannunsa yace,"Malama ki iya bakinki, hukuma ba sa'arki ba ce".
Safiyya ce ta faɗo falon tamkar an jefota, turus tayi daga nesa tana bin hannayena da ke cikin ankwa da kallo, haka har ta ƙaraso gabana cikin girgizar al'amarin. "Ankwa suka saka miki Sa'ida? Tafiya za su yi da ke? Mene hujjarsu na kin kashe mu yarinya?".