Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 36
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 36: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 36. Sai kuma ta damƙi kafaɗata da iya ƙarfinta tana jijjigata cikin…
4,459 words
Sai kuma ta damƙi kafaɗata da iya ƙarfinta tana jijjigata cikin ɓacin rai take faɗin,"Tun yaushe na gaya miki ki nisanci taɓa mata yara tun da bata so, sau nawa na faɗa miki kar ki ƙara kallon ko da inuwar ƴaƴanta ne, ke me yasa ba kya jin maganata ne, me yasa idan na ba ki shawara ba kya ɗauka? Yanzu ai ga irinta nan, garin nunawa ƴartata ƙauna suna miki ƙazafin yin kisa".
Sai ta juya tana kallon ɗan sandan tana cewa,"Cire mata wannan abar da ku ka saka mata". Tayi maganar cikin ƙarajin murya tana neman ta warci maƙullin. Ganin ta ruɗe tana neman itama sanya kanta cikin matsala sai Abbaa yace da Maman Yasmin ta kamota, Maman Yasmin da Anty Naim suka ruƙota tana fiffizgewa tana faɗin,"Abbaa wallahi sharri suke mata, ɗan sanda ƙarya ne kar ku ci mutuncinta, na rantse da Allah ƙarya suke mata sharri ne ba zata aikata ba, Abbaa dama akwai abin da baka sani ba gama da zaman Sa'ida a gidan nan, zan maka bayanin komai Abbaa a wannan karan ka tsaya ka saurareta".
Maganar take yi tana kuka sosai tamkar ita aka ce tayi kisan, ta faɗa jikin Ummani ta ƙanƙameta tana cewa,"Nazifi sai Allah ya kamaka, haƙƙinta ba zai barka ba sai Allah ya saka mata da gaggawa, wallahi sai rayuwa ta wulaƙantaka akan baiwar cutarwa da ka yiwa Sa'ida, ka jira yi lokaci talala ne yanzu duniya take ma".
Muryar Malam na fidda ɓacin rai tsantsa yace,"To wai ni matsalar cikin gidanka ma me ya kawo hukuma cikinta? Su waye shaidun gani da idon cewar tayi kisan har akai gaggawar gayyato hukuma? Yarinya dai gata nan a hannunka babu ƙwarzanen komai, to da me tayi amfani ta kashe maka ƴa? Ko haka ɗaya ku ke neman ɗora mata laifin da bata ji ba bata gani ba".
Muryan Nazifin ta fito tarr a cikin shirun da ya ratsa saboda ɗagawar muryar Malam. "Ban da masaniyar zuwan hukumar. Amma Malam yacca Sa'ida ta tsani yaran nan yanda ka san Annabi da kafiri, wallahi ban da ina da haƙuri babu namijin da zai zauna da macen da bata ƙaunar jininsa irinta, ba na son ace ina kai kararta shiyasa na ke barin takaicinta iya ni, kuma Malam ba ta ɗaukar yaran nan kwata kwata, ko nace ta ɗauke su sai taƙi, amma yau ta ɗauki yarinyar har ma da goyata ta fita da ita yin aiki"...
Sai Malam ya katse shi da cewa,"Da ta fita da ita aikin sai ta dafata ko ta soka mata wuƙa ko?". Yay maganar yana jifan Nazifin da mugun kallo.
Abbaana ya sauke nauyayyan numfashi yace,"Matsalar ka fito ka nuna ƙiyayyarka ƙarara kenan, ko kayi mummunan furuci, ita ƙiyayya ɓoyeta ake, magana kuma zarar bunu ce, ba komai duk ake gudu ba sai irin wannan ranar".
Malam ya dubi Yayan Zahra'un yace,"Kaga kuje zamu san yanda zamu yi da lamarin nan da kanmu, kuje kawai bama da buƙatar hukuma a ciki".
Ya kaɗa masa kai yace,"Ai ba zai yiwu ba ranka ya daɗe, lamarin kisa fa ya wuce duk inda tunaninka yake, idan ace ba'a gayyacemu tun farko mun sani ba shikenan, amma yanzu ba zai yiwu mu ƙyaleta ba duk da cewa suspect ce a wurinmu, idan muka barta ko da bata aikata ba zafin zuciya zai iya sawa ta zo ta aikata abun da ba daidai ba, ko kuma ta aikata ɗin an tafi an barta to gaba ma zata ƙara yi, so dole ne sai mun tafi da can wajenmu an shigar da bayanai duba da yanda ita uwar yarinyar ta shigar da ƙorafinta, sannan kaga su da suke ƙarar suna shaidu ita kuma babu wata shaidar nuni da cewa bata aikata ɗin ba, if ace ma da akwai zamu iya duba case ɗin iya nan mu gani idan na ƙyalewa ne mu ƙyale, to amma yanzu zamu tafi da ita ta bayar da nata bayanan suma su ƙara ba da nasu duk mu shigar a rubuce, anan zamu duba muga me ya dace ayi, a'a lamarin zai tsaya iyaka station ne ko kuwa da yiwuwar mu tura shi gaban alƙali".
Durƙushewa nayi na fashe da kuka sosai mai tsuma zuciyar duk wani mai imani. "Wallahi ba ni na kasheta ba, wallahi wallahil azim ban taɓa yunƙurin cutar da su ba, ban taɓa ba...".
"Kinga ki adana duk wasu kalamanki idan muka je can kya mana bayani, anan babu wani amfaninsu gareki...Amm ku sata a gaba muje".
Abbaana yace,"Yallaɓai a yanzu ne zamu iya shigar da tamu ƙarar na cewa bamu yarda da abin da ake tuhumarta ba ko kuwa sai kun gama shigar da rahoto?".
"Ehh da zarar mun gama jin bayanansu idan munga da yiwuwar zuwa gaban alƙalin to kuna iya neman lauyan da zai tsaya muku, koma dai me kenan zaku ji daga garemu acan station ɗin".
Yashaik yace,"Yallaɓai mu ta ɓangarenmu zamu iya shigo da likita cikin case ɗin don bincike kafin ayi jana'izar yarinyar?".
Ɗan jimmm yay kafin ya ɗaga kai yace,"Ehh zaku iya hakan ma dabara ce ta nemarwa kai mafita, da kuma sauƙaƙawa shi lauyan na ku idan har maganar ta kai gaban alƙali kenan".
"Bari a saka mata hijabinta". Maman Yasmin ta faɗa yayin da take dakatar da tafiyarmu, hijab ɗin ta saka min sannan muka wuce, ɗan sanda ɗaya gabana ɗaya bayana. Zan shiga motar ƴan sandan Abbaa ya ce,"Babu bawan da ubangiji ba ya jarabrtarsa, taki kalar jarabawar kenan, me cikakken imani shi ke karɓar ƙaddara a duk yanda ta zo masa. Ki yi ta kiran Allah cikin zuciyarki da bakinki, sannan ki nutsu wajen yi musu bayani wanda ba za'a samu matsala ba ki ƙara dulmiya kanki a ciki, ba na so tsoro yasa kiyi musu ƙarya kin ji Sa'ida, ki faɗi dukkan gaskiyar da kike da ita, kar barazana ko tsawa ko duka su sa ki canja daga abin da kika faɗa da farko, babu abin da zai ƙwace ki face gaskiya. Zamu biyo bayanku yanzu, Allah yayi miki albarka ya kuma shiga lamarin".
Tun da Abbaa ya fara maganar kallonsa kawai nake yi ta cikin ruwan hawayen da ya cika a idona. To ban san ya zan fassara yanayinsa ba amma daga amon muryarsa zuwa yanayin da ban taɓa ganinsa a ciki ba, zan iya cewa wani al'amarin daban da ban tsammata ba zai iya faruwa. Na fashe da kuka sosai, ƴan uwana ne kawai suka fito ganin tafiyata banda Yaya Imam da ya tsaya daga ciki, ina jin mahaifiyata na gunjin kuka, Safiyya ma na yin nata tana neman zabura ta shigo motar. Sai ga inspector ɗin sun fito shi da Yaya Imam da kuma Nazifi wanda har wa lokacin yake riƙe da gawar a hannu. Lokacin da motar zata ta shi Yaya Imam yace,"Ki bar kuka, daga nan zuwa bangon duniya su shigar da ƙara, kina da Allah kuma kina da mu Sa'ida, zamu tsaya miki ko da silar hakan zamu ƙare, nayi miki alkawarin bayan kukan mutuwar rashi da za ki iya yi anan gaba, to kin bar yin kowanne kalar kuka na ƙunci muddin ina raye".
Wani sabon kukan ya zo min, garin na kalli Yaya Imam ƙwayar idona ta shiga cikin ta Nazifi, nayi saurin rufe idona tare da kifa kaina a saman cinyoyina. Haka aka tafi da ni mutane sai kallona suke yi, nayi ƙoƙarin rufe fuskata kamar yanda Anty Naim tace min.
Muna zuwa can station ɗin na roƙe su akan su da su taimaka min nayi sallah, aka haɗa ni da ɗan sanda ya rakani zuwa banɗaki nayi alwala sannan ya dawo da ni ofishin insifecta, nayi sallolina na azahar da la'asar, na nemi taimakon a bani ƙur'ani duk ba a hanani ba, na ɗan yi karatu na mintuna uku sannan na ɗaga hannu sama ina faɗawa Allah, kuma lokaci ɗaya sai naji natsuwa tana wanzar min, dukkan wani tsoro na korewa daga zuciyata.
Sai da aka yi sallar magriba nan ma aka barni nayi sallah, sannan suka zo shigar da rahotona, aka yi min tambayoyi na faɗin dukkan abin da yake nan, suka kammala rubuce rubucensu bayan ɗan wani lokaci ina nan dai wurin zaune aka shigo da ita Zahra'un da Nazifi. Ita da ta shigar da ƙara ta bayar da nata bayanan sannan aka yi mata tambayoyi, bayan sun gama da ita shima ya bada nasa kana ɗan sandan yace suna iya tafiya zasu neme su daga baya.
Ni kuma aka shaidawa su Abbaa za'a tsare ni nan da zuwa gobe su gama bincika bayanai. Iyayena da ƴan uwana suka kasa tafiya, Ummani har lokacin kuka take yi, Safiyya ma haka wacca ke ta kirayen waya, haka Malam ma shi da Yayan Shago, har aka shigar da ni cikin sel duk suna tsaitsaye, bayan an rufe kuma suka juya suka tafi kowa jiki a mace.
Ina zaune cikin bayan shafe tsayin wasu lokuta, nayi nisa cikin tunani sai naji an ƙwanƙwasa ƙarfen sel ɗin. Na buɗe ido sai naga Abbaa tare da ɗan sanda, na taso da sauri na zo na tsaya bakin wajen. Ɗan sandan yace da Abbaa,"Minti goma muka baku".
Abbaana ya zauna ƙofar sel ɗin ya buɗe kwanon abinci yace na zauna nima, daga bakin ƙofar na zauna shi kuma yana saka hannu cikin kwanon abincin.
"Daure ko babu yawa ki ci abinci kin ji. Ba na so ki kwana da yunwa".
Ba na jin bakina zai ji ɗanɗanon wani abinci, haka babu buƙatar abincin a cikina. Amma saboda Abbaana haka na buɗe baki yana zuro hannunsa ta ƙarfen yana saka min ina ci, ban daina amsa ba har sai da ya barni da kansa. "Bari a siyo miki lemu ki sha ko". Ya faɗa yana lalubar aljihunsa wanda na san babu ko naira biyar a ciki, na riƙe hannunsa ina girgiza masa kai na ce,"Abbaa na ƙoshi ai".
Ya miƙe yana faɗin,"Bara to na ɗauko ruwan kinga na manta shi can kan kanta".
Yana tafiya ya dawo jikinsa sai rawa yake yi, kamar yanda sai da ya fara cin abincin a ɗazu haka yanzu ma sai da ɗan sandan yace ya fara shan ruwan duk kuwa da pure water ne. Lokaci na cika ɗan sandan ya cewa Abbaa lokacinsa ya ƙare, Abbaa yace min,"Kar ki hana kanki bacci, kuma ki yi min alƙawarin ba za ki kwana kina kuka ba, sauran pure water ɗin guda biyu kiyi alwala cikin dare kiyi sallah. Sai mun dawo zuwa goben idan Allah ya kaimu".
ka ina ji ina gani Abbaa ya tafi ya barni, duk da tun ɗazu yana ta ɓoye min hawayensa amma a yanzu ina ganin yacca yake sa hannu ya share su, gefe ɗaya kuma bayan ruɗani da tashin hankalin wannan case ɗin, na kassa tantance wani yanayi na daban da ke tare da shi wanda tun a gida naga hakan, sai dai zance ɗan iya cewa kamar me shirya wani abun.
*B3ƘR14FT5* Na sauke numfashi bayan fitar Safiyya, ɗakin na bi da kallo, masha Allah ya haɗu sosai ga shi ƙatoto, kuma funitures ɗin sai suka yi tamkar daga waje aka kawo su ba haɗi na gida ba, wadrobe ɗin ma irin me zugewa ce gaskiya Sale yay min matuƙar ƙoƙari, ana siyan wadrobe da gado ma kawai na miliyan guda amma shi kaf set ya haɗa min na alfarma, duk da banga kujerun ba amma na san suma sun haɗu. Ina zaune shiru shiru Salim bai shigo ba, zuciyata ta cika fal da kishi da ɓacin rai, ban da tabbacin yana wurin matarsa, to amma in ba can ɗin ba ina ya zauna bayan ya san an kawo masa ni ɗaki, rumtse ido nayi ina jin ciwo a ƙasan raina, nayi ƙwafa na tashi a raina ina ƙudurtar in har na idda sallah bai shigo ba to zai zo ya tarar da ƙofa a rufe ne, sai yay zaman nasa can wajan makiran matansa ɗin da ni ban wani yarda da ita ba.
Alwala nayi na fito ina tunanin ina ne gabas ɗin, na ɗauki waya na kira Safiyya ta faɗa min, itama har tana tambayana har yanzu Salim ɗin bai shigo ba, na kashe wayana ba tare da na bata amsa ba don itama haushinta na ke ji, ina cikin gidan zata je ta wani tare wurin kishiyata. Ina raka'an ƙarshe naji sallamarsa da kuma takun shigowarsa, ya ƙaraso ta ɓarin da na ke ya zauna a gefen gadon yana kallona. Duk da sallah na ke yi haka na haɗe rai daidai da lokacin da nayi zaman tahya, har na sallame ina jin kallonsa a kaina.
Bai min magana ba har sai da na gama tazbihi, da murmushinsa yana shafa tasa fuskar cikin zallar farin ciki da kuma annushuwa. Ni dai ban dube shi ba irin ban damu da zuwan nasa ba, sai dai fa ina kallonsa ta ƙasan ido, ya sauya daga kayan ɗazu ina ga ko da zamu taho ne ya canja, manyan kaya ne yanzu a jikinsa shadda dakakka irin kalar swizz less ɗin jikina blue, ya saka hula kalar aikin yayi kyau sosai dan kayan sun amshi jikinsa, shi kam kowanne shiga yayi yana yin kyau a ciki.
A tsammaninsa duk kunya ce ta hanani ɗagowa, nan kuwa bai san fushi na ke da shi ba da kishinsa, don me zai barni ni ɗaya, ita matan nasa ba jiddan walahairan suna tare ba. ya duƙo kai yana ce min,"Idan amarya ta idar ko zata iya bani aron kanta zuwa falo wajen ƴar uwarta?".
Yanda yayi maganar sai da gabana ya faɗi, haka na taushi kaina na daure ban nuna ba, sai naga ya tashi ya riƙe kafaɗuna ya miƙar da ni tsaye, kaina yana ƙasa still ban kalle shi ba, shi ya tallafo haɓata ya ɗago da fuskata, na sake kulle idanu don ji na ke kamar bana son ganinsa, bai kawo komai a ransa ba game da yanayin nawa yayi siririyar dariya yace,"Ko yaushe aka ɗauko wannan sabon salon ban sani ba, amma za'a yi min bayani ne muje mu dawo".
Ya faɗa yana riƙe da hannuna muka fita daga ɗakin yana gaba ina bayansa, zuciyata na ta ce min in koma in canjo mayafi maimakon hijab ɗin sallar da ban cire ba, don gani na ke na je a haka Kudrat zata raina ni, ko fa da nayi sallah yanzu sai da na roƙi ubangiji ya sassauta min zafin kishin da na ke ji, ya kuma hane ni biyewa ingiza uwar me kantu da zuciyata ke karanta min a cikin kai.
A falon muka tsaya ya saki hannuna ya wuce ya nemi waje ya zauna, Kudrat ma na zaune a kujeran da ke fuskantar shi da ƙaton hijab ɗinta ta duƙunƙune alamar sanyin daren na ratsata, kuma da gani ma daga bacci ya taso ta. Salim ya shafo fuskarsa yana cewa da ita,"Sorry fa na barki da jira, na tadda tana sallah ne, hope babu laifi ko?".
Tana murmushinta na bata da matsala da yanayinta da ke nuna gajiya tace,"Ni na isa nace kayi laifi? To koma ba sallah take ba dan ka jima ai ba zaka yi laifi ba balle sallah guda".
Sai ta dube ni daga inda na ke tsaye, da zolaya tace min,"Sisi Nah idan nayi bacci anan to ki tabbata ke za ki ɗauke ni ki kai ni ɗaki".
Tun kallon farko da na mata na ɗauke sai yanzu da ta ƙara magana tukunna na kalleta a yatsine, kamar wata sauna wawiya sai murmushi take yi hankalinta kwance, lamarin dai ba daraja sam, an miki kishiya kina ta faman sakin baki da tusa kai. Sai da ya dube ni yace,"Wai sarauta kike ji da ita ne? Please have a seat my dear".
A fakaice na harare shi tukunna na taka sannu a hankali, zan zauna kusa da shi sai ya girgiza min kai da cewan,"Koma kusa da ƴar uwarki". Haka na koma na zauna kamar yanda yace ba don rai ya so ba, sai don kar na yarfa kaina gaban kishiya. Na sunkuyar da kai zuciyata na zillo cikin yanayin da ban taɓa tsintar kanta a cikinsa ba, ko lokacin da Nazifi ya taramu kamar haka ni da Zahra'u ban tsinci kaina a yanayi na jin ciwon zuciya irin haka ba, ko kuma duk amarya tafi uwar gida kishi ne ban sani ba dai, don kishin da na ke ji a yanzu yafi wanda naji a sanda Nazifi ya ƙara aure.
To su wai su Ƙabilar haka suke babu zuciya a ƙirjinsu ne? In ba haka ba miji ne ya haɗamu ta kuma san maƙasudin zaman wai amma sai ta dafa ni tana cewa,"So'ida ki saki jikin ki, indai ta ɓangarena ne insha Allah baza ki samu wata matsala ba, ni matsayin ƴar uwa na ɗauke ki, kuma ƙanwata kuma ƙawata, Sofiyya ta shaida min duk irin kyawun halinki, ta faɗa min ba ki da wata matsala. Na miki alƙawarin zan zauna da ke da zuciya ɗaya kaman wacce muka fito ciki ɗaya, ina fatan kema haka daga gareki, sai dai kuma ɗan sabani na yau da kullum wanda yau da gobe ta gaji haka, kin san ɗan adam ajizi ne ni dai na san ko da zan ɓata miki sai dai bisa kuskure, amma bayan wannan insha Allah za ki ji daɗin zama da ni, ba yabon kai ba ne amma ni na san wacece kuma duk wanda ya zauna tare da ni zai san ni ba mutunce me matsala ko sonta ba".
Murmushin yaƙe na mata ina knodding mata kaina, ba ma zan iya ce mata komai ba, ita da taga zata iya dogon bayanin kanta, ƙarƙari dai ba zan yarda da kalaman yaudarar kai ba, kishiyar zan yarda da ita? Ni zata rainawa wayo, wato na saki jiki da ita sai na gama sakankancewa ta shiga ta fita ta raba ni da miji ta raba ni da gida, to ai ba yau ne farau ba, na zauna da ita a baya na gani, kuma na saki jiki da ita ban ji daɗi ba daga ƙarshe, saboda haka ba zan ƙara maimaita kuskuren da ya gabata ba, ta ciki na ciki na sani, idan tana ganin ta iya taku ne to nima yanzu na yi gogewar da sai dai na ɗorata a layi.
Idon Salim akanta yace,"Zabiya tun ban yi nawa magana ba har kin ida na ki jawabin ko". Nima dai a raina na ce ƙila ko tana da matsala a kanta ne, idan ba me almatsutsan ka ba kawai ki fara sakin baki da magana wa kishiya, ai kya bari miji yay nasa tukunna. Kudrat ta rumtse ido tace,"Allah ya baka haƙuri".
Gyaran murya yayi wacce ta dawo da ni daga duniyar ɓacin ran da na tafi, na ɗago na kalle shi muka haɗa ido ma sake ɗauke idanuna, lokaci ɗaya na ke jin zuciya ta tana harbawa sosai. "Muyi salati ga Annabin mu". Ya faɗa a kamilan ce, dukka muka yi salatin kafin ya sake cewa,"Alhamdulillah, Cikin hukuncin Allah gashi ya nuna mana wannan rana wacce dukkanmu ba muyi zaton zata zo ba, komai muaƙaddari ne na jalla wa azza. Ku sani ban yi auren nan domin na cutar da wani ɓangare a tsakaninku ba, dukkanku matana ne, kuma soyayya ce tasa na aure ku, kyawun hali da ɗabi'a yasa na zaɓi na shimfiɗa rayuwa ta dindin tare da ku, kowacce da irin matsayin da take da shi a zuciyata, kuma kowacce ina ganinta da girma a idanuna, ina fatan kuma yanda Allah ya haɗamu rayuwa anan duniya, haka ma ya haɗamu a aljanna. Kudrat ke ce babba a cikin gidan nan, akwai karin maganar da ke cewa idan babba yaja girmansa yaro komai ƙanƙantarsa bai isa ya tsinka shi ba, Amma idan babba ya zubar da girmansa yaron duk ƙanƙantarsa zai bi ta kansa ne ya wuce. Kin san shi girma ko na ce mutunci tamkar madara ne, indai ta zube babu yadda za'a yi mata dole sai dai a haƙura da ita. Abinda na ke nuna miki a nan shine da kija girmanki matsayinki na babba a wannan gida, don Allah ki riƙe So'ida tamkar ƴar uwarki, in kinga tayi wani abu ba daidai ba ki sanar da ita ko da zata ji haushinki. Abinda taga kinyi shi zata yi, in taga kin gyara kin ɗauke ta kamar ƴar uwa itama haka zata ɗauke ki. In kuma taga kin ɗauketa akasin haka itama haka zata ɗauke ki. Don Allah ba na son tashin hankali da ƙananun maganganu a cikin gidana, yau ko da ni ne nayi ba daidai ba azo a same ni a faɗa min kar a riƙe ni a zuciya, ko ace dan nayi wata yanzu na canja babu wanda ya wuce kuskure a rayuwarsa. Babban abinda na ke so a gareku shine haɗin kanku, hakan shine kawai zai saka kuji daɗin zaman gidan, nima kuma naji daɗi nayi farin ciki, ba fata nake ba a wayi gari iyalina sun zama shashashai, dukkan ku masu ilimi ne, kuma daga gidan tarbiyya ko wacce take a cikinku, gidan mutane masu dattako. A kori shaiɗan a kuma kori zugar mutane da ta zuciya don Allah, ku toshe kunnenku kar ku bari wata zuga tayi tasiri a zuciyarku musamman ta ɓangarenki Kudrat, ke ake ganin anwa kishiya ke abokai za su yi tururuwan ganin sun zugaki sun wargaza miki rayuwan aurenki, don haka ki kula ki kuma kiyaye, na san banda matsala da ke in har ba ke kika canja ba".
Ina kallonta ta gefen ido, kai take girgizawa cikin gamsuwa da maganarsa, kafin ya maido da batunsa kaina. "So'ida ke ce ƙarama, ke ce baƙuwa a wannan gidan, gidana gidan zaman lafiya ne da kwanciyar hankali da farinciki, ki kula ki kuma kiyaye, kar naji kar na gani, ba zan lamunta da zuwar min abinda zai tarwatsa farin cikin gidana ba. iyalina ba me fitina ba ce, don Allah ki bata girman da take da shi, kar ki kalle ta matsayin kishiya ki kalle ta matsayin ƴar uwar ki kuma yayarki. Bana son jin ko wanne tashin hankali ta ɓangarenki ba zan ɗauka ba ina daɗa maimaita muku gaba ɗaya".
Nima na jijjiga kai cike da gamsuwa da shi, duk da irin abinda nake ji a zuciyata sai dai ban nuna ba domin haka kawai kalaman nasa na ji suna sanyaya jikina, duk da a ɗaya ɓangaren ina jin kamar a nasihar tasa yayi son kai. Ya sake cewa,"Allah ya bamu zaman lafiya, yasa mu sake maimaita wannan zaman a aljanna, Ya kawar da dukkan abun ƙi a cikin zamantakewar mu, ya kau da sharri ya shigo mana da dukkan alkhairi, zan iyakar yina wajen zama adalin miji a gare ku, please duk wacca ta ga na kauce hanya tayi ƙoƙarin ankarar da ni da wuri".
Ni da ita muka haɗa ba ki wajen ba shi tabbacin da yardan Allah ba zamu ba shi matsala ba. Ya amsa da good yana sake faɗin,"Kowaccenku tana aikinta, Sa'ida Kudrat ma'aikaciyar banki ce, tana fita aiki 7-4, Kudrat Sa'ida ma'aikaciyar lafiya ce, aikinta zai kasance morning and evening, so a ɓangaren girki ina shawartan kowacce da ta dinga girkinta, in yaso in kayi niyya kuna iya bawa junanku, alkhairi yana da daɗi komai ƙarancinsa. Dalilina na yin hakan shi ne; kar yanayin fita aiki yasa a zo a fara samun saɓani, ga yara a gida azo ana complain".
Kudrat ta ce,"Hakan yayi sosai". Ya sake cewa,"Sai maganar raba kwana zance ko?". ya cigaba da faɗin,"Al'ada ta tanadar da kwana uku ga Sa'ida bayan wannan kuma ya ku ke ganin za'ayi? Bana son ayi abinda wani zai cutu a cikinku, kar a yanke hukunci wata tazo tana ce min ai ita bata so ba wancece tace haka ba ita ba. Dalilina na maimaita muku bana son ƙananun magana ne Allah ya sani shiyasa gwara ayi komai a gaban kowa. Ku yanke da kanku in ma waje ne zan baku kuyi shawara kwana nawa kuke ganin za'a raba a tsakaninku wanda babu wacce zata cutu a cikin ku?".
Kudrat na murmushi tace,"Wai sai ka bamu waje, to in ka bamun ma ai zaka dawo". Yayi murmushi shima yace,"Ai wai kar kuji nauyina ko kunyata".
"Ba wata kunya, ni dai ta ɓangarena sai na ke ganin kamar kwana biyu yayi. Amma Sisi ke ya kika gani?".
Shiru nayi ban iya cewa komai ba, sai guntun murmushi me ciwo da ya sauka akan leɓena tunawa da ranar da aka zo min da batun in siyar da kwanana. Ta sake ce min,"Sisi abu ne da ya shafe mu gaba ɗaya, ki faɗi abinda yake ranki, lamari ne na fahimta ke kin fi kowa sanin kanki ko ba haka ba". To ni in ba yanzu zan canja ba ai ina iya riƙe kaina ko za'a shekara, wanne horuwa ne ban yi ba a sanda na ke da mijin, na sauke numfashi na kalle shi kafin na kalleta na ce,"Ni bani da matsala ai, abinda kika yanke yayi min".
"A'a dai ki faɗi na ki ra'ayin zai fi". "Na amince da naki tsarin". "Kin tabbatar?". Kai na ɗaga alamun eh. Kudrat ta kalle shi tace,"To kaji, kwana biyu yayi mana".
"To Masha Allah. Allah ya bani ikon yin adalci a tsakaninku. Kamar yanda na faɗa ɗazu kar aga nayi ba daidai ba a zagaya ana gulmana, dan Allah a faɗa min ko da zanyi faɗa na tabbatar in na nutsu zan gano gaskiya aka faɗa min. Sannan ba zan dinga yawon bin ɗakunan ku ba gaskiya, duk wacce ta san girki a hannunta yake zata zo inda na ke ne bani zanje inda take ba".
Kudrat ta amsa da insha Allah. Ya gyaɗa kansa da cewan,"Madallah, shikenan iyaka abinda zan ce kenan". Miƙewa tayi ta ɗauki Rofi'at da take kujerar kusa da shi wacca ma ni ban lura da ita ba. "Tom Amarya da ango sai da safen ku Allah ya tashe mu lafiya".
Tashi yayi shima ya karɓi yarinyar yace,"Muje na kai miki ita, Myy ina zuwa". Ya faɗi sunan Myy kansa tsaye, sai na ɗago ina kallonsa, hakan ba zai taɓa zuciyar Kudrat ɗin ba? tunanin da na ke ya yanke sa'ilin da yake ce mata. "Derling gobe a samar da break fast da wuri saboda baƙi".
Ya faɗi hakan suna jerawa, ohh shi bai da wani shayi kenan? A gabana yake kiranta da sunan soyayya, duk sai naji na raina nawa sunan da yake faɗa min, mene wani My? Ita fa Derling yake ce mata. Nan take raina ya sake ɓaci kishi ya mamaye min zuciyata, a fusace na miƙe na koma ɗaki zuciyata na bugawa da sauri, idanuna sun ciko da ƙwalla. A fili na furta,"Mene ma amfanin auren mijin wata?".
Jin shiru bai dawo ba ya sake ɓata min rai zuciyata nayi min hasashe mara kyau akan jimawarsa, ji nake kamar na fashe da kuka sai kuma naji ya shigo da sallama, nayi saurin kawar da kaina ina faman cin magani.