Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete - Chapter 37
Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 37: Ƙayar ruwa book 2 and 3 complete Chapter 37. Bai kula da yanayina ba ya ƙaraso ya sunkuya gab da fuskata,…
4,439 words
Bai kula da yanayina ba ya ƙaraso ya sunkuya gab da fuskata, ƙamshin turarensa ya daki hancina wanda ya motsa ni, haka sautin murmushinsa har cikin zuciyata wanda kuma take naji fushin da na ke da shi ya gushe, cikin murya mai sanyi yace,"Myy muyi sallah ko?".
Sai a sannan na juyo na kalle shi muka haɗa ido, ya ɗaga min gira ya ja da baya, dole na miƙe ganin ya tsaya a kan ƙaramin carpet yana ƙoƙarin tada kabbarar harama, hijabina na ɗakko, na tsaya daga bayansa muka tada sallar. Bayan mun idar ya gabatar da duk abinda addini da al'ada ta tanadar sannan ya tashi yace,"Ina zuwa".
Yana fita na miƙe na isa closet na zuge, kayana ma duk ba'a shirya min ba, haka na janyo ƙaramar trolly na zuge na zaro doguwar rigar bacci mai haɗe da hula na saka, a sannan ya dawo shima jikinsa sanye da kayan bacci marasa nauyi riga da wando.
Waigowa yay yana kallona, ya wuce ya aje abu kan dressing mirrow, sannan ya ajiye ledan da ya shigo da shi ya zauna saman carpet yana faɗin,"Baby ina jin yunwa". Ban saurare shi ba na haye kan gado na zauna ina ɗakko ɗan ƙaramin ƙur'ani, ya kalle ni yace, "ki zo kici abinci, bana son wannan cin maganin da kike yi, miskilancin na menene? ban san daga inda ya samo asali ba haka kwatsam".
"Haka na ke dama, abincin kuma na ƙoshi". Na bashi amsa da muryan ɓacin rai ba tare da na kalle shi ba. Tasowa yayi ya dawo inda nake yace,"tunda nake jin yunwa kema kina ji dole kici". Ya faɗa yana karɓar qur'anin hannuna ya mayar da shi ya aje. Na kalle shi cikin jin haushinsa na ce,"Na ce maka bana jin yunwa ko". Nayi maganar da tsiwa.
Sai kawai ya sakeni daga ɗaukata da yake niyyar yi, ya ɓata rai yanayinsa na canjawa ya fito sak a sojansa yace,"Kina ji, tashi muje bana son musu, ke ba yarinya ba ce ai kin sa me ya kamata".
Shagwaɓe fuska nayi kamar zanyi kuka nace,"Nima bana son takura". Ai sai ya koma min zam Salim ɗin da bai taɓa wage haƙoransa ba. "Kar ki bari na ƙara mamaita kaina tashi na ce".
Ba yanda zanyi dole na tashi muka ƙarasa kan carpet, ledar da ya shigo da shi ya buɗe, packs na abinci guda uku ya buɗe yana kallona. Abincin na kalla duk da pack ɗaya ne na shinkafa sauran kaza ce gaba ɗaya, sai wani da ya buɗe shi kuma soyayyen dankalin turawa ne an zuba masa sauce a kai sai ƙamshi yake yi. "Bismillah".
Na sauke numfashi ba tare da nayi yunƙurin ci ba. Rai a haɗe ya kalle ni yace,"Allah zan miki ɗura, kuma ina ƙara maimaita miki bana son musu". Kallonsa nayi sai naga yana neman ya shareni, dama neman wuri ne irin nawa, ba niyya na kai hannu na soma ci, ina mita a ƙasan raina na dalilin da yasa ba zai ciyar da ni da kansa ba. Dankalin kawai na ci shima ban wani ci da yawa ba na zare hannu, sai ce yay,"ita kazar hararar ki tayi da za ki ƙi taɓa ta?".
Ina kumbura murya na ce,"Ni fa bana son cin abu mai nauyi in dare yayi, bana son ajjiye tumbi kamar kai". Na faɗa ba tare da na kalle shi ba. Dariya yayi, ya shafa shafaffen cikinsa, in banda sharri irin na Sa'ida ina shi ina tumbi, ko dan training ɗin da yake sha wajan aiki ai dole ma tumbi yaƙi zama a jikinsa.
"Ba fa yarinya ba ce ke da zan ta fama da ke, Allah sai kin ci kazar nan". Jin yace Allah ya saka na ɗauka na saka a baki, raina na daɗa sosuwa, da can bai san ni ba yarinya ba ce sai yanzu da ya kawo ni gidansa zai ta maimaita min ni ba yarinya ba ce, to ya rabu da ni mana ya ci gaba da zama da yarinyar, mtssww.
Ina jinsa yana cewa,"Kuma za ki nuna min a inda kika ga tumbi a jikina". Shareni yayi har ya gama nasa cimar, a cup ɗin da ya sha yogot ya zuba ya miƙo min gabana, ya miƙe ya fita ya barni na bi bayansa da kallo. Har ga Allah da kukan da na ke ji zai samu sakkowa da na rage raɗaɗin da ke raina, bayan kusan minti biyar lokacin agogo ya buga ƙarfe ɗaya saura sai ga shi ya dawo, ya ce na taso mu wuce ɗakinsa, ina ciccin magani na ce,"Me ya samu nan ɗin? Ko kayan ciki ne ba su maka ba".
Harara ya galla min, na ɗauka hijabina na saka na wuce, yana riƙe da hannuna muka fita a ɗakin bayan yasa key ya rufo ɗakin. Ta falo muka shiga wata ƙofa sai gamu a ɓangarensa mai ƙaramin falo mara kayan hayaniya, sai award da hotunansa duk yayi kyau sosai cikin kakin soja. hannuna ya saki yace,"Ki shiga zan kulle ƙofar".
A hankali na taka na shiga daga ɗakin da yake da girma sosai a gyare tsaf da shi, sai ƙamshi yake yi ga tiles ɗin ɗakin fari amma ko jurwaye babu a kansa har ɗaukar ido yake, ko anan a tabbatar da tsaftar matar gidan, idan wata ce yanda ba ya zama ai sai tiles ɗin sun rine, ba zata tashi gyara ba sai zai dawo, wannan kuwa da gani goge shi ake akan kari.
Ina tsaye ina raba idanu ya shigo, ya tako inda nake ya ɗaga hijabina ta baya ya cire shi ya faɗi ƙasa, ya saka hannayensa ya zagaye ƙuguna ya ɗora kansa a kafaɗata yana cewa,"Wannan fushin duk akan kishin Salim ne?".
Yanda yayi maganar a kunnena ya saka naji wani yarrr a jikina, na runtse idanuna sai naji yayi murmushi ya sake ni ya dawo gaba yana kallona yace,"Ashe haka kike sona da yawa ban sani ba?". Kai na sunkuyar, ya ɗago fuskata yana cewa,"Bana son wannan sunkuyar da kan da kike fa, ki kalle ni ki faɗi abinda yake ranki, ko ɗazun na yi maganar da bata yi miki daɗi ba?".
"Ni babu abinda yake raina". Na faɗa a hankali ba tare da na bari mun haɗa ido ba. "Akwai, ni nasan akwai wani abu a nan". ya faɗa yana ɗora hannunsa a ƙirjina yana kallon fuskata. "Ina jin bacci". Ya waro ido da faɗin,"Bacci? Baby bacci a wannan daren! Ko kin manta wanne dare muke ciki ne?".
Nayi shiru ina faman lumshe idanu kamar me jin baccin gaske, sam ganinsa da maganarsa ne bana so, muka isa bakin gado ya zaunar da ni saman cinyarsa, hular kaina ya zame ya shiga shafa wuyana, nan take na fara jin wani sabon yanayi, lokaci guda kuma na ruɗe jin yanda ya ƙanƙame ni yana aikin shinshinar jikina yana faɗin idan ina sa irin wannan humran kullum to zan janyo a sallame shi daga aiki ne, don zai koma aikin kan gado till down.
Maimakon naji daɗi ya ratsa ni da furucin nasa sai ɓacin rai ya ƙara wanzar min, ya zo ya gama min surutai yaje can itama wata me ƙatuwan murya ya karanta mata irinsu. Sai ga hawaye riii a saman kuncina, mamakin kaina kawai na ke yi, ban taɓa tsammanin ina da kishi haka ba, ba zancen son kai ba ne kana matuƙar kishin abinda ka ke so ne, na kasa dannewa kuma, ban san ta ya zan iya danne kishina ba tsakani da Allah, fatana ɗaya kar ta sanadina na haifar da zaman da ba zai yiwa kowa daɗi ba.
Sannu a hankali lamarin ya fara sauyawa, na san komai amma sai na ji kaman ban san komai ɗin ba, ba wai don ba a yi min irin salon a baya ba, a'a abubuwan da yake min ɗin ne cikin irin nasa salon na shi kaɗai daban da irin wanda na sani ne, jikina duk ya ɗauka rawa tun ba'a je ko'ina ba har ina neman shiɗewa. Shi kuwa tuni ya gama susucewa da ƙyar ma ya iya zuwa ya kashe fitilan ɗakin, haka ya koma min tamkar wani mayunwacin zaki, na miƙa ragaman jikina gaba ɗaya wa Salim da ya bi ya susutar da junanmu, tuni ya canja labarin da ya sha banban da wanda na ke tunanin zai afku, kuma babban al'amarin ya faru ne bayan shimfiɗuwar lamarin da ya tafiyu cikin natsuwa da gwanancewa, haƙiƙa jin kaina na ke tamkar a yau ne karon farko da na fara shiga duniyar da sanin irin daɗin da ke cikinta.
Ni ɗin ba sabuwa ba ce amma a yanda lamarin ya afku jina nayi tamkar yanzu ne aka ɓare ni, an tsumu, zuciyoyi da ruhi sun samu natsuwa, gangar jiki duk ta mace a cikin shauƙin daɗin da ta tsinci kanta, fitar numfashi da saukarsa kawai kake ji. Yana daga gefe nima ina daga gefe, ya tattaro ni ya janyo ni jikinsa ya ƙanƙame abarsa, ni kuwa sai faman sauke ajiyar zuciya na ke ina faman goga hanci da goshi a gashin ƙirjinsa.
"Myyy". Ya kirayi sunana cikin wata irin shaƙaƙƙan muryan da zan iya rantsewa ba nasa ba ne, yana ta aikin yawo da hannunsa a dukka ilahirin jikina. "Thank you Baby, thank you so much, God bless you".
Haka yake ta faman jera min kamar wanda ya samu sabuwa fil a leda, kamar wanda ya shekara aru aru bai samu ba tsaban gulma, sai bayan wani lokaci kafin mu tashi mu shiga toilet mu tsarkake jikinmu.
[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR15FT5* Tun bayan sallar asuba da na kwanta na ke bacci a jikinsa, ƙarar alerm ne ya tashemu inda muka buɗe ido a tare, hasken ranar da ya shigo ta siririn buɗawan labule ya haske min ido, ya kai hannunsa yana kare min, sannan ya miƙe ya isa gaban window ɗin ya gyara labulen. Dawowa yay ya kwanta yana mayar da kaina saman ƙirjinsa, muka haɗa ido da shi sai nayi saurin kulle idanu tare da kamo hannunsa na rufe fuskar tawa. dariya yayi da hakan yana cewa,"Baby gulma, mene ba ki sani ba to da zai saki jin kunyana".
Murmushi kawai nayi ba tare da na ce komai ba, sai ya miƙe zaune yana ɗaukar wayarsa, ganin tafiyar lokaci ya buɗe ido da cewan,"Subahanallah! Ashe haka lokaci ya tafi". Ina kallonsa na ce,"Har ƙarfe nawa dama?". "Sha ɗaya fa Myy, wanne irin bacci muka yi". Sai kuma yay murmushi yana shafo fuskana da cewan,"Ko da yake ai laifin ki ne".
Na ɗan juya idanu farr da cewa,"Laifina kuma?". Sai da yaja hancina tukunna yace,"Ehh mana, daɗin da aka jiyar da ni da kuma natsuwar da aka bani".
Idanuna buɗe ina kallon fuskarsa ba tare da na bari mun haɗa ido ba na ke shafa gashin gefen fuskarsa da cewa,"To kai ma ai ka bayar".
"Ummm na sani ai, shiyasa aka saki baki da hanci ana ta zuba munshari duk aka hana ni bacci".
"Kaiiii Salim ban da sharri dai". Leɓena ya ɗalle da cewa,"Ai ba sani za ki yi ba, lokacin ma da kika ƙanƙame ni kina kar na sakeki please continue its very sweet ai duk ba ki sani ba".
A jikinsa na tusa fuskata ina ta murmushi cike da jin daɗi. Shi kuma yaci gaba da duba wayansa, waya ya kira ina jin yana magana akan tafiyan da za su yi in the next 5days, za su tafi can America ne da shugaban ƙasa akan tattaunawan da aka yi na ƙasar zata taimakawa Najeriya kan harkan tsaro. Bayan gama wayar tasa attention nasa ya bani gaba ɗaya muna ta hiran mu cike da so da ƙaunar juna, a hiran namu kowanne ke bayyanawa ɗan uwansa irin abinda yake so da wanda ba ya so, yana ce min zai bani babban makamin mallakarsa gaba ɗaya, na buɗa dukka kunnuwa ina saurarensa cike da zaƙuwa kuwa.
Sai da ya fara manna min kiss a baki kana yace,"Idan kina so ki mallake ni totally na zamar miki raƙumi da akala to ki so Ƴaƴana, ki riƙe su tamkar ke kika haife su, ba na son ki nuna musu banbancin mahaifa, ko a bayan idona ban yarda ki hantare su ko muzguna musu ba...then".
Sai yay shiru, zuciyata dai na ta motsi cikin wani irin rauni da tayi, ina kallon ƙwayar idonsa na ce,"Then what?".
Sai da ya sauke numfashi, ya kamo kafaɗuna ya tayar da ni zaune muka fuskanci juna yace,"Ni mutum ne mara ɓoye ɓoye da barin abu a raina ina kallon mutum da shi. Ki sani ina darajta matata, ban ƙaro aure don bana sonta ba, ban ƙaro aure saboda tana da wata makusa a gare ni ba, ban mata kishiya domin ta gaza ba, ban mata kishiya don na wulaƙantata ba... Kuma ba ina faɗa miki hakan ba ne saboda ɓata miki rai ba ko kuma ke bana sonki ba, no! Bana so kiyi amfani da wata damar ne na ganin kamar kin fita a wurin miji ki samu hanyar cuzguna mata, duk ku biyun ina son ku, so da ƙauna ne yasa na aureku na ke fatan kuma har a aljanna mu kasance tare, dole son wata zai fi na wata amma wannan abu ne kawai da ke iyacin cikin zuciyata gudun haifar da fitina a gidana, ina sonki itama kuma ina sonta, Baby please ki controlling zuciyanki, ki iya sarrafa kishinki kamar yanda ƴar uwarki ta sarrafa nata. So'ida a ƙabilarmu idan ka ce zaka ƙara aure tashin hankali hakan ke zame maka tsakaninka da iyalinka, amma tunda na tunkari Kudrat da zancen aurenki zuwa kawoki da nayi ban fuskanci wata aba damuwa ba, hakan yasa ta ƙara samun girma a idanuna, ba wai bata kishina ba ne ta danne ne kawai, kema don Allah ki danne abinda na gani jiya a reaction ɗinki da ƙwayar idonki, if kika ce zamu tafi a haka to zamu samu matsala da ke sincerely speeking, fatana matana su haɗe kansu, ku zama abu ɗaya, ba faɗa ba gaba, sai kun fini jin daɗin zaman ma, duk kuwa wadda ta tayar min da fitina tabbas she will see the other side of me".
Zuciyana na zafi kamar zan saki kuka na ce,"To yanzu duk mi ɗaya ka faɗawa haka?".
"Yanda na karanta miki haka na karanta mata, shiyasa jiya na jima a wurinta har hakan yay sanadin da kika ƙullace ni a ranki, Baby kar ki bari zuciyarki ta rinjaye ki please, kike kaudar da duk wani abu da ba ki da tabbas akansa, kishi dole ne amma kiyi kishin wayayyu masu ilimi irinki".
Hawaye ne ya sakko min, ina wasa da yatsuna na ce,"Insha Allahu zan so yaranka, zan riƙe su kamar ni nayi tsugunon haihuwarsu, and zan zauna lafiya da matarka, ba zaka taɓa samun matsala ta ɓangarena ba nayi maka alƙawarin hakan mijina".
Sai ya kwanto ni jikinsa yana shafa kaina yace,"Na gode matata, na gode da kika fahimce ni, nayi miki alƙawarin zan samar miki da farin ciki da dukkan iyawata, zan kuma iya bakin ƙoƙarina wajen ganin ban haifar da ɓacin rai ko damuwa ba a tare da ke, alƙawarina ne kuma ba zan taɓa bari ki zubar da hawaye ta dalilina ba ko ta dalilin wani nawa".
Ya faɗi hakan yana manna min kiss a saman gashina, cikin soyayyarsa da yaƙinin samun kwanciyar hankali da dawwamemen farin ciki na kewaye shi da hannayena ina rugume shi na ce,"Ina sonka Mahbub".
Da wani sauri ya ɗago fuskana. "Mahbub?". Na jijjiga kai,"Beloved". Sai ya ƙara rungume ni yana faɗin,"Thank you for the name".
Muna haka ya duba wayansa. "Kinga kiran Kudrat har four times, Allah yasa lafiya". ya faɗa yana kiran wayar kafin ya tashi tsaye ya saka doguwar riga ya fita bayan yace min yana dawowa yanzu.
Fitarsa duk sai naji babu daɗi, zuciyata na harbawa, daga daren jiya zuwa safiyar yau adadin harbawan da zuciyata tayi yafi ƙarfin adadi, na ƙara nutsewa cikin kogon sonsa da kishinsa. Na bi ƙofa da kallo idona na ƙara haska min yanda ya fita da hanzarinsa saboda kiran Kudrat ɗin, duk yanda na so na danne na kawar amma na kasa, nan take naji raina ya ɓaci, gudun faɗawa cikin wani yanayi nayi saurin sakkowa akan gadon ina ambaton sunan Allah a cikin raina, wadrobe ɗinsa na buɗe na ɗakko jallabiyarsa na saka, sannan na shiga gyaran gadon, ban bar ɗakin ba sai da na gyara ko'ina tass, na je ɗakina na ɗakko turaren wuta na zo na saka, ai fa turaren Ummin Sauma ba na banza ba nan da nan ƙamshi ya gauraye gidan.
Bayan na kammala na koma ɓangarena, na shiga wanka haka ina wankan ina aikin ƙunci, turarukan wankan da nayi amfani da su kuwa idan ka shigo ɗakin zaka tsammacin kamfanin turare ka shiga. Ina zuge closet na yi katari da an gyara min ita, kayana an jera su jere me kyau, abayas ɗin duka a hanger suke, ansa wadrob balls sai ƙamshi cikinta yake. Amma ya aka yi haka? Naga ai sai da ya rufe ɗakin da key tukunna muka fita jiya da daddare, ko kuma da ina bacci aka zo aka karɓa, na san gyaran ba zai wuce na su Maman Khairi ba, murmushi nayi ina gode musu da ƙoƙarinsu, ɓangaren da aka jera atamfofi na kai hannu na ɗakko wata super me kyan gaske, ɗinkin riga da skirt ne simple ba me hayaniya ba, dama gani da hips masha Allah, na yi simple make up ena nayi kyau abun burgewa wanda na san dole mijina zai yaba.
Bakin gado na zauna tare da ɗakko wayata kafin na fita naje na gaida su Gwaggo, ina dubawa kuwa sai ga misscalls ɗin Safiyya har uku, Allah sarki ƙawar amana tuni fushin da na ke da ita akan kwana wurin kishiyata yabi iska, na bi bayan kiran tana ɗagawa kuwa da karaɗinta tace,"Su Beb an dirji soyayya wato sai ma yanzu naki garin ya waye, to ya amarcin da brother nah? I hope komai dai normal na san harka da sojojin nan ba wasa ba".
Samun kaina na yi da jan tsaki nace,"Daman abinda kika kira ki tambaya kenan gulmamma?".
Sai tayi shewa da faɗin,"Ahh lallai ne matar soja, kin sha madarar daɗi kin ƙoshi, bakinki a buɗe kike min tsaki ko".
"Nayi ɗin". Sai ta sassauta murya da cewa,"Na ji ki a fusace, lafiya dai?". Amon muryarta ya fito da kulawa.
Na rumtse ido sosai ina cewa,"Mayi magana idan kin shigo". Na faɗa ina yanke kiran".
Abbana na kira, mun jima muna magana da shi a wayar, yana gida yana faɗa min bai ma fita kasuwa ba saboda ana masa gyaran sabon teburin da ya siya, muka yi waya da Ummani ma har da Kaka, duk sunata tambayana ya baƙon waje, albarkar nan tasu da nasiharsu ta kullum ba su fasa sa min ita ba, Jin muryar iyayena sai naji komai da ke zuciyata na rashin daɗi yabi iskar ɗakin ya tafi. Mun gama waya da Yashaik a lokacin Salim ya shigo, yana aikin bina da kallo kamar sabon gani a idonsa, nima kuma kaina na san dole ya kalle ni saboda kyan da nayi.
Hannaye harɗe a ƙirji yake ce min,"Yaushe muka yi da ke ki taho nan?".
Nayi masa wani irin kallo me tafiyar da imanin masoya nace,"Naga ka ɗan jima ne, ni kuma ina so nayi wanka naje mu gaisa da su Hajjo".
Ƙarasowa yay ya zauna kusa da ni yana kama hannayena yace,"To na wa wankan kuma fa? Ni ban iya wanka da kaina ba, ga shi kinyi kwalliyan da ba zan so ya ɓaci ba". Sai ya marairaice min kaman yaro,"Shiyasa da kin ɗan yi haƙuri kin jirani na zo mun yi tare, ba ki san wankan miji da mata tare na ƙara danƙon soyayya ba, ko tsoro kike kar nayi maimaici?".
Murmushi nayi ina jan hancinsa da cewa,"Kai bakinka ko, yanzu to ai sai ka tashi muje na taimaka maka ɗin, amma saɓi ɗaya zan maka ka ƙarasa sauran da kanka".
Sai da ya ɗan matsa cikina kafin yace,"Ahaf ki yi min saɓi ɗaya saboda kina gudun kar labari yasha banban kenan, dama kema na san ai ba ki ƙoshi da ni ba".
Ƙaramin filo ɗin kusa da ni na ɗauka na ƙwala masa, sai ya miƙe yana dariya da cewa,"Tunda kin min wayo ba za ki min wankan ba yanzu bari naje na shirya, idan ban wanku ba ke ce kika ja kar ki zo shimfiɗa kina min ƙorafi. Sai kije wurin su Hajjo ɗin nima naje mun gaisa da su, kafin nan na gama sai muyi break fast ko ma nace lunch tun da dai har azahar ya kusa".
Na miƙe ina cewa,"Break fast ɗin ƴan boko ba, ka muje na maka wanka to ko da na ɓaci sai na sauya, kwalliyan ai dama na ka ne, kuma ka gani har ka yaba, so sai a ƙara yin wani ai ba za'a gajiya ba wajen yin abinda zai burgeka".
Janyo ni yay jikinsa yana shafa gefen fuskana, sai faman yabon kyan da nayi yake yi, a hankali hannayensa na shafa marata zuwa cikina yace. "Soon wannan shafaffen wajen zai ɗauki ajiya insha Allahu".
Maganar ta taɓa zuciyata, na ɗago ido na kalle shi da zummar yin magana, kamar yasan me nake shirin faɗa yayi saurin haɗe bakinmu waje guda, sai da yay me isarsa kana ya rabu da ni yana cewa,"Just sai Allahumma amin".
A sanyaye na ce,"To Allahumma amin". "Awwa ko ke fa Myy, adu'a na sauya ƙaddara so muyi adu'a kawai Allah ya bamu me albarka".
"Ko ban samu daga gare ni ba ma su Isioma sun ishe ni". Na faɗi hakan ina tunawa da baya, yanda duk sona da yaran Nazifi haka mahaifiyarsu tayi min katanga da su a ƙarshe har aka min ƙazafin kisa.
Haɓarsa bisa kafaɗana yace,"My muna da buƙatar ƙarin yara, Baby ina son yara, so na ke ku cika min gidan nan da ƴaƴa inta kallon ku ina jin daɗi".
Kunnena ya ɗan ciza tare da raɗa min magana, wai zan basa na rana yaji an fara tsikarinsa, sanyayyan murmushi nayi me faɗi wanda muka yi a tare da shi. Sai ce yay,"Na shiga na samu kuna magana da Safiyya a waya, saboda asaran kati irin na ku kuna cikin gida ɗaya, ko da yake na san gulmana aka yi".
Na waro ido waje ina cewa,"Gulmanka kuwa?".
"Ehh mana in ba haka ba Me kika ce mata to? Nasan dai ba za ki iya faɗa mata kin wahalar mata da ɗan uwa a daren jiya ba, sai dai zan so ki sanar mata ɗan uwanta ya rasa hankalinsa ta dalilin wannan halittar me kyawun sura, har yana tantamar akan da gaske ne kuwa matarsa ta taɓa wani auren a baya ba rufe shi kawai aka yi ba, Ki ce mata gaskiya ina da ja akan hakan, don ni hanyar da na shiga ba a taɓa taɓata ba".
Murmushi nayi kawai ina sunkuyar da kaina, ina jin farin ciki mara misaltuwa na ratsa ni, ni kaina a jiya nayi matuƙar mamaki, ko da yake ba ƙaramin gyara su Maman Yasmin suka min ba, ni kaina na rikice balle shi. Tare muka fita da shi a ɗakin, sai da na je na haɗa masa ruwan wanka da turarukan wankan da nayi amfani da su, na so nayi masa wankan sai dai yace no na bari nayi masa na anjima yanzu na je wajen su Hajjo kar na barsu da tunanin lafiya, su tsammaci ko yay musu kaca kaca da ƴarsu ne. Ina dariya na fito a toilet ɗin na ɗakko masa kayan sawa na ajiye masa, kana na fito na wuce wajen su Umman Batula, ina zuwa kuwa na faɗa jikin su Maman Yasmin cike da kunya har ina kasa ɗago ido na kalle su.
Hajjo tace,"Allah ya dawwamar da ke a wannan farin cikin da na ke gani a fuskarki".
Dukka aka amsa da amin. Wai sai naji suna min batun ai yanzu za su wuce, Abbaa ya kira ɗazu yana ta faɗa ba ko kunya sun zo sun yi zamansu a gidan siriki. Na ce,"Kwana biyun kawai? Ni fa nayi zaton ko sai zuwa jibi ma za su ku tafi".
Maman Yasmin tace,"To ni har zagina ma sai da yay, yace bai ga amfanin ace sai mun kwana a gidanki b, mene ma na zuwan to tunda mun bada amanar taki ai sai mu kamo hanya, gidan na ki ma zo daga baya".
"Kayiii Abbaa to shi da sai na zo gidana babu wani nawa, kenan ma ni na kawo kaina".
Mama A'i tace,"Ai kin dai san halin Babanki, shi da ya so ma ku taho da mijin kawai ba sai an miki rakiya ba".
"To kuma da gaske yau ɗin za ku tafi?". "Ƙwarai ma kuwa, ai yanda kika ganmu nan ke kawai muke jira dama muyi sallama, shima kansa Salim ɗin da ya zo yana ta mamaki yace ba zamu ƙara kwana ba, muka ce aa bar muku gida zamu yi ba a yi iyayen kawai ba".
Ni dai duk sai naji babu daɗi da zancen tafiyar tasu, jikina yay sanyi, Maman Khairi na tsokanata wai ni da naje na ƙule ma na barsu, idan suka ƙara kwana ai abinda yafi haka za su fara gani. Maman Khairi ke ce min,"Ai da safen na fito da ke ƙarfe shida fa Abbaa ya doka mana kira Allah yaso wayar Maman Yasmin ce". Ta faɗa tana dariya. "Da Safiyya ai naci karo a falon, dama ina cewa zamu je ɗakin naki a shirya miki sauran abubuwa sai tace ai ta gyara miki komai".
Sai naji raina yay min babu daɗi, na san fa tabbas Safiyya zata iya gyara min ɗakina amma saboda banzan kishi ban wani kawota cikin raina ba. Mama A'i na ta faɗa min kirkin Kudrat, suka ce ita ta zo ta tada su da asuba, da kanta ta shiga toilet ta saita musu ruwan zafi suka yi alwala da shi, kuma kafin bakwai ta kawo musu abin kari tana ta ce musu idan da akwai wani abu da suke buƙata suyi mata magana, sai faɗar kirkinta suke yi, Gwaggo na cewa ance dai baka saurin shaidar mutum amma ita wallahi har zuciyarta taji Kudrat ta kwanta mata, haka kuma ta shaidata shaidar da tana da tabbacin ba za su ji labari mara daɗi ba.
Nan suka sakani gaba suna ta min faɗa da nasiha gami da shawarwari, sai ma da Hajjo tasa aka kira Kudrat suka haɗe mu gaba ɗayanmu, hannuna cikin nata haka Mama A'i tasa muka yi musabaha tana cewa adu'anta da dukkan fatanta yasa hannayenmu ba zasu rabe ba. Kudrat ɗin har da hawayenta tana ce musu suyi tayi mana adu'a don Allah kar a samu shaiɗanin da zai raba kawunanmu.