
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 18
.....pick me up from school, wondering if it was Yaya Abbas. This news shocked Abba very much. Abba shook his head nervously, speaking slowly as if he was not serious. "Who took her from school? Who is this?" At the same time, Yaya Abbas came in quickly. "Abba, what happened?" he asked worriedly. Abba looked at him angrily and said, "Someone took Auta from school. No one knows where she is now." Momy held her heart and looked at Abbas, "Abbas, my mind is up. Don't let those useless friends of hers drag her into something that is not right. Today I entered three!" Yaya Abbas shook his head, trying to calm them down. "Mommy, Auta is not like that. She doesn't follow her friends like that." Then Billy came out of the room in fear. "Abba, I called her friend Fatima. She said that someone named Khalil came to take her." Abba's heart was so upset, that he reached to pick up his phone quickly. He called Khalil's mother that night, arguing with her about why her son would take a girl without knowing her parents. Khalil's mother regretfully asked for forgiveness, saying that he had nowhere to take her. She also fought him on this day.....
SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS
Bayan sallar Magariba ne hankalin Momy ya fara tashi. Na san hakan saboda duk lokacin da aka fara kunna fitilar dare har ya kai ga shudewa, ni dai ban dawo gida ba. Duk yunkurin da Momy ta yi na kiran lambar Malam Idi ya ci tura lambar ba ta shiga ko ?aya.
A lokacin da Abba ya dawo daga aiki, hankalin kowa ya yi mummunan tashi. Na san cewa Abba yana cikin gajiya daga aikin sa, amma lokacin da ya shigo falon, sai na ji muryarsa cikin damuwa yana tambayar Momy
"Lafiya? Me ya faru?"
Momy ta kalle shi cikin damuwa, tana girgiza kai. "Wallahi har yanzu Auta ba ta dawo gida ba tun da safe da ta tafi makaranta. Na kira lambar Malam Idi sau da dama amma ba ya shiga."
Abba ya runtse idanu cikin damuwa, ya nufi inda yake ajiye wayarsa. Na san cewa yanzu Abba zai yi duk abin da zai iya don gano inda nake. Nan take ya umarci wani daga cikin mutane su je gidan Malam Idi don jin inda nake. Kafin lokaci ya ja, an dawo da amsa daga gidan Malam Idi cewa wani mutum ne ya zo ya ?auke ni daga makaranta, yana tunanin ko Yaya Abbas ne. Wannan labari ya girgiza Abba sosai.
Abba ya dafa kansa cikin tashin hankali, yana magana a hankali kamar ba da gaske yake ba "Wani ne ya ?auke ta daga makaranta? Waye wannan?"
A daidai lokacin ne kuma Yaya Abbas ya shigo cikin gaggawa. "Abba, me ya faru ne?" ya tambaya cikin damuwa.
Abba ya kalle shi cikin fusata, ya ce "Wani ya ?auki Auta daga makaranta. Ba wanda ya san inda take yanzu haka."
Momy kuwa ta rike zuciyarta tana kallon Abbas "Abbas, nifa hankalina ya tashi. Kada dai wadancan kawayen banza nata su ja ta cikin abin da bai dace ba. Yau fa na shiga uku!"
Yaya Abbas ya girgiza kai, yana kokarin kwantar musu da hankali. "Momy, Auta ba irin wannan bace. Ba ta da halin bin kawaye haka kawai."
Sai ga Billy ta fito daga daki cikin tsoro. "Abba, na kira kawarta Fatima. Tace wai wani mai suna Khalil ne ya zo ya ?auke ta."
Ran Abba ya baci sosai, har ya kai ga ?aukar wayarsa cikin hanzari. Ya kira mahaifiyar Khalil a daren, yana yi mata fada kan dalilin da yasa danta zai ?auki yarinya ba tare da sanin iyayenta ba.
Mahaifiyar Khalil ta nemi gafara cikin nadama, tana cewa babu inda zai kai ta. Ta kuma yi masa fada kan wannan rashin tunani. Sai dai wannan ba ya rage fushin Momy ba, wadda ta fara zazzaga zagi. "Wallahi, dama na san Khalil ne ke zuganta! Daman shi ne ya sa ta fara fitsara da rashin kunya. Wannan dai sai an lallata tarbiyar yarinyarta saboda irin wannan hali!" Momy ta fada cikin bacin rai.
Abba ya rasa abin cewa saboda tashin hankali ya yi masa yawa. Ya yi shiru yana tunanin abin yi. Yaya Abbas kuwa ya cigaba da kokarin kiran lambar Khalil, amma har yanzu ba ya dauka.
Da suka ga zaman gida ba zai amfana ba, Abbas ya ce "Abba, bari mu ja mota mu fita. Zai fi idan muka bincika da kanmu."
Abba ya amince, suka fita cikin hanzari. Har lokacin Momy tana cikin fargaba tana cewa "Wallahi idan aka sake ganina tare da wannan yaron, zan hukunta ta da kaina!"
Ko da su Abba suka fita, babu inda ba su je ba amma babu ni babu labarina. Har wasu abokan Khalil din ne aka tambaya amma kowa sai yace ai ba su gan shi ba. Da kansa Abba ya je gidan su Khalil, ya samu mahaifinsa yana tambayar inda ?ansa yake. Mahaifin Khalil ya ce ba shi da labarin inda ?ansa yake, amma ya tabbatar wa Abba cewa za su yi bincike domin gano inda suke. Saboda tsananin damuwa da tashin hankali, Abba ya fara kuka. Yaya Abbas ya shiga bashi baki akan babu abin da zai same ni.
***
Su Momy dake gida kuwa, dariya ta sa bayan fitar Abba, tana barin falon cike da murna. "Alhamdulillah! Wannan shine abin da nake fata. Insha Allahu sai na tabbatar da cewa ta yi ciki ta kawowa abba cikin gidan nan."
***
A bangaren Yaya Billy kuwa, daki na ta shiga ta bincika ko'ina amma ba ta samu komai ba. Hakan yasa ta saka dariya itama, sannan ta fita. Na lura cewa tana jin dadin wannan hali, kamar wani abu ne aka yi yadda take so.
*******
Na rasa gane me ya same ni. Zuciyata kamar ta faso ?irji. Hankalina ya gama tashi, ban san abin yi ba. Ina kallon khalil idona ci?in nasa yacire wandonsa yana kokarin hawa ji?ina gaba daya jikina rawa yakeyi Narasa da yaren da zan yi masa bayani..Cikin wata murya mai rauni da ba ta fita da kyau ba, na dubi Khalil, wanda ke tsaye yana kokarin ta?oni, yana kallona da idanu masu cike da fitina. Cikin hawaye da zazzafan kuka nace masa
"Wannan ce soyayyarka gare ni? Khalil, So kakeyi ka batamin rayuwa, ka rusa duk wani abin da na dogara da shi. Wannan ita ce ?aunarka gareni? Khalil, wannan ce kaunar da kake ikirarin kana yi min? Shikenan... ka rusamun rayuwata kayimun Abunda kake gani mafita ce gareka ba rusa rayuwata ba.
Na fashe da kuka, wani irin kuka mai cin rai, wanda ya kunshi duka matsananciyar radadin da zuciyata take ciki. Na san cewa a wannan lokacin banda mai taimakona sai Allah banda ikon yin komai.. Na ji kamar komai ya ru?e, tamkar duniya ta gama rugujewa a kaina.
Khalil kuwa ya rasa abin cewa. Cikin hanzari ya fara jan baya yana ?adamun ?ai yana fa?in kiyi hakuri bazan aikata ba kiyi hakuri ya tattara kayansa yana kuka kamar ?aramin yaro. Muryarsa na rawa yana cewa "Ki yi ha?uri Ramlah, ki gafarta min... wallahi ba haka na yi niyya ba bazan aikata ba bazan aikata ba."
Ban tsaya sauraronsa ba. Na kwashi wasu kayan da suka rage a dakin cikin gaggawa. Na yi saurin saka siket dina, amma rigar ta yage. Cikin rashin zabi, na dauki hijabin makaranta na, na rufe jikina sannan na fice daga dakin da hawaye suka gama ji?a fuskata..
Na fito waje, na same shi yana tsaye bakin mota yana jiran ni. Ba tare da ya ce komai ba, ya bude min kofa, na shiga. Motar ya ja cikin shiru, babu wanda ya iya cewa komai. Na ci gaba da kuka kamar zan rasa numfashi. Ya kalleni yashiga lallashina akan nayafe masa sharrin shaidan ne da soyayyata..
A hanya sai ga Khalil ya tsaya a wani wurin siyar da kaya. Na ga ya sayo wata sabuwar abaya ya miko min. "Ramlah, ki saka wannan... don Allah," ya ce cikin sanyi.
Na karbi abayar ba tare da kallonsa ba, na saka, sannan na koma cikin shiru. Har lokacin kukan nawa bai tsaya ba. Na rasa yadda zan bayyana bakin cikin da ke cike da zuciyata. Khalil bai ce uffan ba har muka iso kofar gidanmu.
Na fita daga motar da kyar, saboda jikina babu ?arfi. Khalil ya tsaya daga nesa yana kallona har na shiga gida. Na san cewa zuciyata na iya bugawa ko yaushe, saboda tsananin nauyin da take ji, yanzu da yayimun fyade Fa? Shikenan rayuwata ta lallace?? Shikenan Narasa farin cikin? Wayooo Allah na Nagode daga sanya yafasa..
Ina shiga cikin gidan, na ji duniya ta fara juyawa. Sai gani a kasa, na sulale a bakin kofa. Masu aikin gidanmu ne suka hango ni, suka yi gaggawar kawo dauki. Abba da kansa ya fito cikin hanzari ya dagani.
"Subhanallah! Ramlah, lafiya?!" ya tambaya cikin rudani.
Na rike hannunsa ina kuka kamar zan mutu. "Abba... Abba... na shiga uku! Khalil ne ya saceni abba.."
Ya dubi masu aikin gidan da suka yi tsuru suna kallona. "Ku kawo ruwa, da sauri!" Abba ya umurce su.
Bayan sun kawo ruwa, ya yayyafa min a fuska, sannan na bude idanu cikin tsananin rauni. Momy ta fito tana tambayar abin da ya faru. Abba ya ce "Ina da zaton cewa an yi mata wani abu. Wannan ba halinta bane."
Momy ta kalle ni cikin tsananin fushi da damuwa. "Ramlah, me ya faru? Don Allah ki fada min."
Na ci gaba da kuka, na kasa magana. Hankalin kowa ya tashi. Abba ya kalli Yaya Abbas da ya shigo cikin gaggawa. "Abbas, ka kira 'yan sanda yanzu-yanzu."
Sai dai Yaya Abbas ya ce "Abba, a bari na fara kira Khalil mu ji daga gareshi. Wannan lamari yana bukatar sanin gaskiya daga dukkan bangarori."
Abba ya amince, amma har lokacin zuciyarsa na bugawa da karfi. Yaya Abbas ya yi kokarin kiran Khalil, amma lambarsa bata shiga.
Na jingina a kan gwiwar Abba, ina jin tamkar rai zai fita. Cikin zuciyata naji wani nauyi mai girma. Na ji muryar Momy tana cewa "Wallahi yau zan ga iyakar wannan abin. Khalil sai na hukunta shi. Wannan rashin kunya da rashin tarbiyya yana son ya lalata min yarinya!"
Abba ya tsayar da ita da hannu. "Ki yi hakuri Momy. Mu ji yadda lamarin yake da farko."
Amma Momy bata iya boye fushinta ba. "Toh, idan wannan yaron ya lalata min rayuwar 'ya, wallahi sai ya yi nadama!"
Yaya Abbas ya dawo da rashin nasara wajen kiran Khalil. "Abba, lambarsa bata shiga.
*******
Na bude idanuna a hankali, ganin hasken safiya na shigowa daga tagar dakin ya sa na motsa kadan. Kai na ya yi nauyi kamar an loda kaya a ciki, idanuna kuwa suna luhu-luhu tamkar ban samu bacci ba duk dare. Na runtse idanuna na sake bude su, sai kawai na ji muryar Abba daga kusa da gadon.
"Ramlah, tashi ki yi sallah. Kada ki bari lokaci ya wuce."
Na juyo daga kwanciyata da kyar, zuciyata tana bugawa cikin kasala. Na ce, "To, Abba." Na mike da kyar, ina jin yadda jiki na ke yi mini nauyi. Abba ya tsaya har sai da na mike tsaye sannan ya fice daga dakin.
Da na kammala sallah, na koma na zauna a kan gado ina tunanin yadda dare ya kasance mini. Ban ma san lokacin da na yi barci ba saboda yanayin ciwon kai da na ji jiya. Kafin na gama tunani, sai ga Abba ya dawo da kofin shayi a hannunsa.
"Ki sha shayi kafin ki huta," ya ce, yana ajiye kofin a gefen gado. Na kalli fuskar sa da kulawa, duk da cewa na san yadda Momy take ganin wannan kulawar a matsayin wani abu da ba ta yi tsammani ba.
"Nagode Abba," na fada a hankali, ina jin wani sanyi a zuciyata. Wannan al'amarin ya ban mamaki sosai, musamman ganin yadda Momy take nuna bambanci tsakanina da Billy. Amma Abba bai damu da hakan ba.
Na karba kofin shayin cikin nutsuwa, na kurba kadan yayin da na ji sanyin zafin na shiga zuciyata. Na kalli Abba yana murmushi, sai ya ce, "Ki koma ki huta bayan kin sha."
Na kada kai, na san cewa idan Momy ta ga hakan, ba lallai ne ta ji dadi ba. Da zarar Abba ya fita, na ji motsi a tsakar gida. Na hango Momy tana yawo a cikin kicin kamar tana cikin tashin hankali. A wani lokaci, sai ta tsaya tana zuba tagumi.
"Me yasa Abba yake nuna wa Ramlah soyayya haka? Me ya faru?" na ji ta furta cikin sanyin murya. Sai na sake mayar da hankalina ga shayin da ke gabana, amma zuciyata ta cika da tambayoyi.
Ina cikin wannan tunani, sai ga Abba ya sake dawowa falo. Ya tsayar da ido kan Billy da take zaune tana latsa waya.
"Ke Bilkisu," Abba ya kira ta cikin natsuwa. "Ki dafa wa Ramlah abinci kafin ta farka."
Billy ta dan tabe baki, tana kallon Abba cikin rashin jin dadi. Kafin ta yi magana, sai Momy ta yi saurin cewa, "Abban Auta, bari ni na dafa mata. Babu damuwa."
Abba ya kalle ta da mamaki, yana fadin, "Zainab, ni nasan cewa Bilkisu bata aiki a gidan nan, amma kullum Ramlah ce ke fama. Yanzu haka ba ta jin dadi, amma kalli gidan nan? Aikin gida fa wajibi ne ga kowa."
Momy ta saki fuska kamar tana so ta ce wani abu amma bakinta ya mutu. Sai ta kalli Billy da idanu kamar tana fada da su. Billy kuwa ta kau da kai, tana cigaba da latsa wayarta.
Na ji zuciyata tana tafasa amma na danne. Lokacin da Abba ya fita, Momy ta nufi dakin Billy tana fadin, "Wallahi babu abinda zan yi. Idan yana so, sai shi ya yi." Na kalli yadda Momy ta shiga dakin da karfi ta rufe kofa. Na jinjina kai, zuciyata tana cike da mamaki.
"Me ya sa Momy ke yi min haka? Me yasa soyayyar da Abba ya nuna min take tada mata hankali?" Na tambayi kaina cikin sanyin murya, zuciyata na jin ra?a?i.
Abba na fita daga Gidan yatafi offices, yana gayawa mumy ta kula dani fa sosai kar kuma nayi aikin komai agidan nan makaranta ma yace bazanje ba. Cikin zuciyata, na ji kamar an yaye mun wani nauyi, amma kafin na samu natsuwa, sai ga Mumy ta banko kofar dakin nawa cikin tsananin fushi. Fuskar ta cike da masifa, idanunta sun kada ja, alamar ranta ya gama baci.
"Wato ke?!" Ta fara magana cikin karaji, tana daga hannayenta kamar wadda zata kai mun duka. "Kin je kin gama yawon iskancinki, kun gama zinace-zinacenkku da Khalil, shine zaki dawo kina hadani da mijina? Shegiyar yarinya!"
Na zuba mata idanuwa cikin mamaki, jikina yana rawa. Kalaman ta suna shiga zuciyata kamar kibiya. Baki na yaki buduwa, na kasa cewa uffan.
"Zaki tashi ki shiga ki gyara mun gida ko kuwa sai na ci ubanki a cikin gidan nan? Ko an gaya miki ni baiwar uwarki ce? Shegiya, munafuka! Mara tarbiyya mai yawon bin maza!"
Kalaman sun sake harbawa zuciyata, suna tashi mun wani ciwo na daban. Na ji wani irin ra?a?i a cikin zuciyata da ya hana ni natsuwa. Cikin tsananin damuwa, kukan ma ya ki zuwa. Ban iya cewa komai ba, sai dai kawai na zuba mata idanuwa, hawaye suna yawo a gefen idanuna.
Na rasa yadda zan yi, jikin nawa yana rawa kamar wanda aka doki zuciyarsa. Tunanina yana komawa baya, inda rayuwata ta kasance cikin kwanciyar hankali da soyayya. Me yasa rayuwa ta zama haka? Me yasa zargin da bata da asali ya zamo min karfen da ya tsaya mun a wuya?
Kafin na gama tunani, sai kawai na ji saukar marin ta a fuskata, wani gigitaccen mari wanda ya sanya na rike kunci cikin tsananin azaba. Na mike tsaye da sauri, na zaro idanuwa, zuciyata na bugawa kamar tana neman tsagewa.
"Ina zaki je?" Mumy ta sake kwalla mun ihu. "Wallahi zaki zauna nan har sai na yanke hukunci. Wallahi, sai kin gane kurenki a yau."
Na fashe da kuka, kuka mai cike da tsananin takaici da ciwon zuciya. Har yanzu bakina a rufe yake, na kasa cewa uffan. Wani murdaddan zafi ne ya mamaye jikina, numfashi na yana fita da kyar.
Na juya a hankali, na zauna a kan katifa, jikina yana karkarwa. Kalaman Mumy sun cika kunnuwana, har wani irin ciwon kai ya fara kamani. A cikin zuciyata, ina rokon Allah ya bani karfin guiwa da ikon jure wannan jarabawa.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH