
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 25
.....lleta once but he didn't start walking until he came close to him. They walk slowly, in a situation that calms her heart. The air is beautiful....the light that illuminates the heart and the body.....you bring the people who are full of peace and worship, worshiping God in peace.....the peace of the soul and the body as a whole. Something caught her attention again during their illegal entry. The exclusive entrance that since she has been coming she has never entered the place, according to the guidance of the three men who are wearing the uniform of the workers who are in charge of the haram as a whole. From the moment they arrived there, the three of them arrived, "Welcome to the sheikh" They said respectfully. He smiled quietly, the smile that fills up his charm and perfection, brings out the secret of his beauty. Then he extended his hand to them and they shook hands. "Sheikh Yasir Addosary has signed the document of your residence...but he will not be leading the Isha'i prayer, Sheikh Abdurrahman Assudais....saidai is at the place, they will sit between them for a while, when it will be enough for you to complete your order and sit with them" He spoke in English which gav
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 25*
Da sauri ta sauke hannunta,ta kuma jefawa birra harara da jiqaqqun idanunta. Kafin tace komai birra tayi qasa da kanta.
"Don Allah kiyi haquri,ba laifina bane,yallabai ne ya tsara tafiyar kowa da masaukin ya zama daban daban.....muna qarqashin kulawar yaranshi"
"Yaranshi?" Ta furta tana duban birra. Kaman zata sake cewa wani abu da ita sai kuma tayi shuru tana dauke kanta miskilancin ya motsa,wannan ya bawa birra daman matsowa ta soma gyara mata gashin kamar yadda ta saba,wanda cikin minti biyu ta hade mata shi tsaf,ta kuma daureshi cikin madaidaicin ribbon,sannan ta miqa mata hijab din ta zura.
"Ina falaak?" Ta tsinci kanta da tambayar birra.
"Suna nasu hotel din a masaukinsu" Birran ta amsa mata. Mamaki kadan ya kama akhnan,wato ita hankalinta kwance?,yarinyar bata da hankali,haka kawai tabi wani namijin hankali kwance ba kuma wanda take nema?.
A qasa ta sameshi har ya sauka zuwa babban reception na hotel din. ya kalleta sau daya saidai bai soma tafiya ba har sai da tazo dab dashi.
A hankali suke takawa,cikin wani yanayi daya sanyawa zuciyarta nutsuwa. Iska me kyau....haske me haskaka zuciya dama gangar jiki.....kai kawo na mutane dake cike da nutsuwa da yanayi na ibada,bautar Allah cikin sakankancewa.....nutsuwar ruhi dama ta gangar jiki gaba daya.
Wani abu ya sake daukar hankalinta yayin shigarsu haram. Kebantacciyar mashigar da tunda take zuwa bata taba shiga ta gurin ba,bisa jagorancin mutum ukun da suke sanye da uniform na ma'aikatan dake kula da haram baki daya. Tun takowarsu gurin suka iso su uku
"Barka da zuwa sheikh" Suka fada cikin girmamawa. Murmushi ya saki a nutse,murmushin dake sake cika haibarsa da kamalarsa,yake sake fitar da sirrin kyansa. Sai ya miqa musu hannu sukayi musabaha.
"Sheikh yasir addosary ya sanya hannu kan takardar zamanku......amma ba shine zai jagoranci sallar isha'i ba,sheikh abdurrahman assudais ne....saidai yana gurin,zasu dan zauna a tsakaninsu,lokacin kamar zai isa ka kammala umararka ku zauna dasu" Yayi maganan cikin harshen turanci wanda hakan ya bawa akhnan damar jin dukkan abinda ya fadi din.
Maimaita maganan ta soma yi cikin kanta. Da waye zai gana?,da waye zaiyi meeting?. Imams na haram?......inde daidai taji imams na haram ne.......WAYESHI? Tambayar ta sake dokawa cikin kanta,saita daga kan nata da sauri tana ajewa a kansa,daidai sanda ya juya harshe yana bawa hadiman amsa da harshen larabci maimakon turancin da suka masa magana dashi.
"Kuma?.....an kuma?" Ta furta a hankali tana jin wani tsoro nasa da mamakinsa yana kamata.
"Anya bame had'ari bane?" Ta sake tambayar kanta tana jin tana rikicewa kadan. Yare nawa ya iya?,harshe nawa yake iya sarrafawa. Da farko yana hausa duk da bata zauna a bakinsa sosai ba ta yadda idan yanayi saika gane ba yarensa bace.....English.......france..... Tuareg kadan kadan.....ga kuma larabcin da bata jin komai a cikinsa......a iya haka ya tsaya?,ko da ragowar yaruka?.....WAYESHI.......tabbas akwai wani lullubi cikin rayuwarsa......akwai abinda dukkaninsu basu sani ba,ita da sultane dama dukkan wanda yake tare dasu. ME YAKE BOYEWA?,Mene manufofinsa?,ta samu kanta da fada tana jin yadda larabcin ke fita tartar daga bakinsa,bashi da maraba da Accent na larabawan da suke musu jagora.
Hanya kawai taga ana buda musu duk da yawan mutanen dake gurin,suna sake gaba.....suna kusantar inda duk zuwanta bata samun daman isa gurin.
"Ta wannan hanyar sheikh" Jami'in ya sake fadi yana musu nuni da wata kebantacciyar hanya.
Cikin mintuna qalilan suka iso wani guri,kebantaccen gurin da bata taba zata za'a sameshi a guri me cike da cunkoson al'umma haka ba. A tsare yake,ba cunkoson mutane,sai shimfidu bisa tsari da tarin tsaro.
"VIP zone sheikh zamu qarasa" Ya sake fadi cikin girmamawa ganin ya danyi slow kadan da tafiyarsa.
"Ki jira a nan.....kiyi sallarki a nan" Ya fada a nutse sannan ya juya yana takawa jami'an suna biye dashi ta wata hanyar da take dab da inda zai kaika bakin ka'aba matsayar da liman yake tsayawa a duk sanda za'ayi sallah.
A hankali ta taka zuwa saman shimfidun. Tana duban matan dake zaune cikin nutsuwa samansu. Dukkaninsu kusan qabilu ne daban daban daga qasashe daban daban,saikin lura da gaske zaki gane banbancin yanayinsu,alamu kadan tasa ta iya gane daga gidan mulki ko sarauta suka fito suma. Nutsuwarsu da shigarsu ta daban ce.
"Ga guri nan" Taji wata sassanyan murya tayi magana daga bayanta. Hausar da taji ya sanyata waiwayawa da sauri tana neman me maganar.
Kyakkyawar matashiya ce,wadda aqalla zasuyi sa'annin juna ita da ita a qiyasin shekaru nakai tsaye datayi mata. Murmushi ta sakar mata tana sake nuna mata muhallin dake kusa da ita wanda babu kowa. A hankali ta tsinci kanta da maida mata murmushin,sannan ta soma takawa zuwa inda tayi mata tayin,ta zare takalminta a nutse tana hawa saman carpet din.
Samun kanta tayi dayin bismillah kafin ta zauna,abinda ya tsaye mata cikin zuciya.
"Yaushe kika fara koya?" Ta tambayi kanta,bata da amsa bata sani ba,kawai ta samu kanta dayi ne.
"Halan ke dayace kema.....ba abokan tafiya?" Matashiyar ta sake fadi tana murmushi da alamun dake nuna yawan murmushi yana cikin dabi'arta. Kai akhnan ta daga mata a hankali tana qoqarin sake aza murmushi akan fuskarta.
"Ni ni dame gidana ne......yana bangaren maza.... Kefa?" Tambayar sai ta yiwa akhnan nauyi,ita dawa zatace mata?.
"Ni sunana ameenatu muhammad jadda.....amma ana kirana da iffa......kefa?" Sosai sunan ya yiwa akhnan dadi,sannan kuma sai takejin kamar akwai inda ta taba jin sunan.
"Khadeeja muhammad hammud" Ta amsata a taqaice. Kai iffa ta jinjina
"Sunanki yayimin dadi.....daga nigeria nake......kekam nasan ba 'yar can bane....." Kai ta gyada a hankali murmushi yana sake subuce mata kadan. Karon farko da hira da wani ya burgeta,wanin da ba shehnaz ko aisa ba.
"Nijer.....agadez" Idanu iffa ta fidda kadan.
"Daga agadez palace?" Kai akhnan ta gyada a nutse
"Yeah........haba,kaman nasan sunan......daughter of sultane muhammad hammud.....right?" Iffa ta furta tana dan fidda idanunta waje tana nuna akhnan da yatsa.
Wannan karon dole murmushin akhnan ya sake qaruwa,ta sake daga mata kai a hankali,saidai tayar da iqama da aka fara qoqarin yi shine abinda ya katse wannan hirar tsakaninsu.
Cikin sahu da matsayin da Allah ke bawa bayin da suka samu daman yin sallah a gurin suka gabatar da sallar isha'i ta wannan rana. Sallar da suna sallameta basu samu daman yin wata maganar da iffa ba me gidanta ya kirata
"Save my number please prince khadeeja" Iffa ta fada tana murmushi. A nutse ta fidda wayarta ta karantawa akhnan numbers dinta ta dora da fadin.
"A swissotel muka sauka....zamu qara kwana bakwai kafin mu wuce,ina fatan zamu sake haduwa?"
"In sha Allah" Akhnan ta amsa mata. Tana jin kamar ta samu wani madadi,wani madadi nasu shehnaz da aisa data baro a agadez din. (One of jadda's family......sabreen namesake).
Duk da yawan mutanen dake kaiwa da kawowa amma hakan bai hana idanunta ganinsa ba. Daga nesa sanda yake takowa sanye da wannan farin ihram din data kyawun daya masa ya kasa dusashewa a idanunta da zuciyarta. Daga nesa kadan take hangensa,hannunsa cikin na sheikh abdurrahman assudais,gefansa kuma sheikh yasir aldosary. Dukkansu suna murmushi ne,da alama akwai magana me muhimmanci da sukeyi. Hanya ce da idan zasu wuce ake cikata da security,suna kuma wucewa ne da dan sassarfa saboda mutane masu daukan hoto da kuma masu son tsaidasu.
Ta lumshe idanunta tana sauke ajiyar zuciya don ragewa zuciyartata nauyi. Tantama shakka da kuma kokwanto a kansa sake cikata yakeyi. Da gasken gaske takeson sanin shi waye,ta kuma fara aika bayani a kansa......amma tana jin kamar amsar ba zatazo mata a sanda takeso ba.
Ta sake daga idanunta,sai ta hangeshi yana takowa da wani irin nutsuwa,haske ihram din jikinsa yana sake haske fuskar nan tasa data rasa wanne irin sirri ne kwance a cikinta. Sirrin da idan ka kalleta kwarjini nutsuwa da kamala sune abinda kawai zaka iya gani.
Da alama bai ganta ba,wannan ya bata daman sake shigewa mutane kadan tana kallonsa,tanaso taga ta yadda zai iya zaqulota,duk da tare suke da daya daga cikin askar na gurin suna magana kadan kadan. Sallama sukayi ya koma bakin aikinsa,shi kuma ya tsaya cak da alamun yana wara idanunsa ne don zaqulota.
Idanunta zube fes a kansa,ya danyi qasa da kansa kamar me kallon wani abu,sai kuma ya juyo cikin second daya saiga idanunsa cikin nata. Zare idanun nata tayi,tana jin alamun takunsa a jikinta,tana jin sanda ya iso dab da ita,tana jin muryar nan tasa me zurfi da wani kwarjini yana fadin.
"Ina fata kin dauki niyya?" Kai ta daga a hankali,sai ya juya yana fadin.
"Bismillah"
Biye take dashi a hankali,qafafuwansu suna sake musu jagoranci zuwa gaban ka'aba. Idanunta akan dakin,daki mafi tsarki,muhallin da yafi kowanne martaba tsarki da daukaka a duniya. Tana sake kusantarta tana jin yadda zuciyarta ke sake sanyi.....tana qara duka taku guda tana jin yadda nauyin dake saman zuciyarta yana raguwa.
Sanda ta tsaya a saitin inda zasu fara dawafi,girman dakin ya bayyana a gabanta,sai taji wani karayar zuciya. Ta sauke idanunta akan tarin mutanen dake dawafi a sannan. Yau din kamar akwai cikowar jama'a sosai,abinda tafi tsoro kenan yafi kuma bata wahala duk cikin umara ko aikin hajji,wannan turmutsutsun,wannan cikowar.
Takawa ya fara yi,tana daga gefansa,a hankali take ajiye takunta duk inda ya ajiye nasa,suka fara zagayen farko. Dukkaninsu zuciyoyinsu sunyi nisa wajen addu'o'i da jin kusanci da mahaliccinsu. Ta lumshe idanunta,tana jin yadda cunkuso yake qara daduwa,amma hakan bai hanata jin daddadan sautinsa ba. Sautinsa shi kadai yana fita da wata irin nutsuwa,sautinsa shi kadai duk da tarin muryoyin bayi dake cike da roqo da kuma fata kala daban daban,saidai batasan dalilin daya sanya kunnuwanta ke tsame iya nasa sautin kawai ba.
Wani buri ne da takejin a yau ya ninka yadda ta saba jinsa cikin zuciyarta.....burin kaiwa gaban ginin dakin ka'aba,ta sanya hannunta ta tabashi,ta kifa fuskarta a jiki tayi kuka ta kuma gayawa Allah buqatunta. Tunda take zuwa bata taba damuwa da yin hakan ba,hasalima yawan cunkuson shike firgitata,tafi zabar yin dawafinta a sama tayi ta kammala,amma a yau din sai takejin shine abu guda dayan da take buri wato ta isa ga ginin dakin ka'aba. Tanajin kamar buqatunta masu nauyi ne a wannan karon......tana jin kamar buqatunta sun rinjayi na kowanne lokaci. Wannan qawa zucin ya sanyata ta fara neman hanyar kutsawa ta tsakanin wani rukunin 'yan qasar Malaysia da alamu ke nuna ahali daya ne,saidai yadda suka matseta a cikinsu ya sanya numfashinta ya soma sama sama.