
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 26
.....why was she pressed so much, he knew that at this moment she did not have the strength to limit herself in front of the Kaaba. She quickly lowered her eyes from his head to the ground, and her heart began to move. "Oh God..." She said as she felt a sudden fall. What should she pray for first? What prayer should she pray?. As if he knew the question that was in her mind, this voice of his entered her ears again with some prayers that made her heart feel like she was sprinkled with cold water, she just kept repeating what he was saying. Every time she repeated each letter that came out of his mouth, she felt her heart calm down again. Every time she repeated the stick, she felt a kind of calmness and peace. One thing is given to the situation, change her part which does not matter how many times. From his left shoulder to his right, and from his right shoulder to his left. She felt a kind of protection when she walked there..... a kind of safety and security that she had never felt since she was going to Umrah, even with how many servants she was going to have. She didn't feel pressured again since the first pressure, she didn't repeat every prayer except the prayers that came o
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 26*
"H.....ha.....haisammmm" Ta fada da sauri tana qoqarin qwato numfashinta. Har tsakiyar kansa yaji saukar sunan cikin kunnuwashi da wani kebantaccen yanahi,wani baqon sauti da a yau ya fara jin fitar sunan a gurbin. Da wani irin Zafin nama ya miqa hannunsa ya damqe nata,sannan ya jawota daidai kafadarsa yana manne tafin hannunsa cikin nata da wannan yanayin dake zare mata kowacce laka ta jikinta ya maye gurbinsa da kasala.
Sosai ya mata gurbi kusa dashi,ya hade dukka tazarar dake tsakaninsu ta yadda ko zare bazai iya ratsawa ba. Idanunta ta daga tana qoqarin kallon fuskarsa. Zafin naman daya gwada mata kadai ya isa ya gaya mata qarfi da kuzarin daya mallaka. Ba ita yake kalla ba,idanunsa suna gabansa da yana lissafa yadda zasu samu isa gaban ka'aba cikin sauqi. Sai sautin sunansa daya fita a bakinta da yaketa maimaituwa cikin kanshi.
"Ki zauna kusa dani" Ya furta cikin wani salo na umarni kai tsaye. Ya fahimci abinda yasa aka matseta har haka,ya sani kuma a daidai wannan lokacin bata da qarfin da zata iyakai kanta gaban ka'aba din.
Da sauri ta sauke idanunta daga kansa zuwa qasa,zuciyarta ta soma motsawa.
"Ya Allah......" Ta fada tana jin wani faduwar gaba tana samunta. Me ya kamata ta fara roqa?wacce addu'a zatayi?. Kamar yasan tambayar dake ranta kenan,wannan muryar tasa ta sake shiga kunnuwanta da wasu addu'o'i da taji zuciyarta na kwanciya kaman an yayyafa mata ruwan sanyi,sai kawai ta dinga maimaita abinda yake fadi.
A duk sanda ta maimaita fadin kowanne harafi dake fita a bakinsa sai taji zuciyarta ta sake nutsuwa. Duk sanda ta maimaita sai taji wani irin nutsuwa da kwanciyar hankali. Abu daya data ga yanayi,sauya mata bangare wanda batasan adadin sau nawa yayi ba. Daga kafadar hagunsa zuwa ta dama,daga kuma kafadar damansa zuwa hagu.
Wani irin kariya takeji tako ina.....wani irin aminci da tsaro irin wanda bata taba jinsa ba tunda take zuwa umara,koda kuwa da hadimai guda nawa zatazo. Bata sake jin an matseta ba tun matsewar farko,bata sake maimaita kowacce addu'a ba sai addu'o'in da suke fita daga bakinsa cike da wata irin nutsuwa,addu'o'in da koda batasan ma'anarsu ba......amma tana jin wani gamsuwa da aminci a cikin maimaitasu.
Zagaye bakwai me cike da wani irin yanayi.....zagaye bakwai me cike da wani sirrin aminci da nutsuwa da bata taba sanin akwai irinsa ba.
Suka tsaya cak,tsill hannunsa cikin nata. Akwai rangwamen cunkos zuwa sannan,saidai hakan bai hana cunkuson masu son zuwa gaban ka'aba. Hannunta ya saki a hankali,sai ya riqe tsintsiyar hannunta yana zagayo da ita gabansa.
Qugunta ya riqe da hannunsa guda daya,a hankali ya sanya idanunsa cikin nata,sai itama ta daga blue eyes dinta tana ajesu a nasa. Wani irin abu ya sauka saman zuciyar kowannensu,wani abu me nauyi taji yana taba zuciyarta da wani irin yanayi data gaza fassarashi. Kallon ido cikin ido da qaramar tazara irin wannan.....tazarar da hatta da numfashin junansu musayarsa sukeyi,tazarar da take iyajin yadda jikinsa yake gogar nata,tazarar da ta fara gaban babban daki.....babban gurin da babu irinsa,tazarar da ta sanya wata nutsuwa a ruhinta....wannan tazarar da taji a karo na farko ba wata tazara mai qaranci da muhimmanci irinta.
"Es-tu prête?(kin shirya?)" Ya furta yana motsa labbansa da suka janye hankalin Akhnan sosai,sannan cikakkiyar girarsa guda daya tana dagewa sama. Sai data lumshe idanunta a hankali,tana jin wani yanayi na daban yana ratsata. Tayi qoqarin motsa labbanta amma ta gaza cewa komai,sai kai ta daga masa a hankali.
Shima da idanu ya amsa mata,kallon daya sanya taji wani abu yana narkewa tun daga zuciyarta yana kwaranya a gangar jikinta gaba daya.
Ba zato taji yasa hannuwansa biyu ya rabata da qasa. Tadan tsorata har batasan sanda ta riqe faffadar kafadarsa ba. Hannunta ya sauka saman lallausar fatar kafadarsa......laushinta ya hadu da taushin nata tafin hannun. Saman qafafunsa taji ya dora tafukan qafafunta bayan ya juyata,bayanta yana cikin qirjinsa,ya saka hannuwansa ya zagayesu saman cikinta,ya mata kyakkyawar garkuwa da dukkan jikinsa. Ta yadda ba wani abu da ya isa ya tabata.......a yanayin da ba wani abu da zai kusanceta muddin ba gangar jikinsa ba. Habarsa ya dora saman kafadarta,da wani kusanci sosai cikin muryarsa a tausashe yake fadin.
"Zaki tafiya saman qafafuna....zamu qarasa gaban ka'aba kiyi addu'a.....gurine me muhimmanci sosai.....gurine na amsa addu'a da dukkan buqatu.......zakiyi alqawari?". Sauka kowacce kalma take daga bakinsa kai tsaye zuwa kowane sashe na jikinta,saqon da dukka maganar suna ratsata. Alqawari daya fada ya sanyata bude idanunta dake lumshe tunda ya fara maganan,bata motsa ba,amma yaga alamun bude idanun nata.
"Zaki sakani cikin addu'arki?" Ya fadi maganan yana kaiwa qarshenta da wani irin numfashi me nauyi. Shuru kawai tayi.....tana jin sautin bugun zuciyarta ta cikin kunnuwanta. Zata sashi a addu'o'inta kamar yaya?,bata fahimta ba,ba kuma zata iya tambaya ba. Abu daya ta sani.....zai mata wani abu da zai shiga sahun tarihinta.
"Kinyi alqawari?" Ya fada yana dan matsa qashin qugunta kadan ba tare da yasan yayi hakan ba. Kai ta daga a hankali ba tare data shiryawa hakan ba.
Qafarsa ta farko ya cira,wani tsoro ya kamata taji kaman zata fadi,saita manne bayanta sosai da jikinsa tana riqe hannuwansa dake qugunta.
"Ki tsaya" Ya sake fadi kaman me rada a hankali muryarsa na sauka da wani irin sanyi.
"You're safe.......kina tare dani" Ya sake maimaitawa. Sai taji ta aminta dashi din.....ta aminta da maganarsa,sai taji ta saki jikinta hankali kwance. Yana takawa a hankali da ita,mutane na wucewa ta gefansu amma tana jin kamar komai ya tsaya. Da dukka jikinsa ya bata kariya,yana kutsawa da ita da wani irin qarfi na zuciya da hikima ba tare da cutar da kowa ba har suka isa gaban ka'abar.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Sauketa yayi a hankali daga saman qafafunsa,ta sake takawa ta matsa zuwa gaba,bai matsa daga bayanta ba,sai ya sanya hannuwansa ta gefe da gefan kafadunta yana dafe bangon ka'aba dashi,yayi mata wata ingarman rumfa da gangar jikinsa,ya lullube bayanta da kyau da jikinsa,ya kuma samar mata da space din da zai wadaceta tayi addu'a.
Hannunta ta dora itama saitin nasa tana dafe ka'aban. A karon farko kenan,duk da shekarun data dauka tana zuwa. A karom farko ta sanadinsa,da dukka wata kariya da zai iya bata ya sadata da dakin. Sai taji wani hawaye me dumi yana saukar mata,ta masa a hankali ta sumbaci hajarul aswad,ya sake matsawa da ita gefe kadan,ta saka bakinta fa sumbaci ka'aban,kafin ta dauke kanta ya sake manneta cikin jikinsa,ya kuma zuro kansa ta kafadarta,abinda ya hanata iya dagowa kenan,sai tabar fuskarta a jikin dakin tana sauraren fitar numfashinsa,dumin jikinsa,da sautin addu'o'in da ba zata iya tantance abinda yake roqa ba.
Wani yanayi ta jita a ciki,irin yanayin da yafi kowanne yanayi yi mata dadi cikin duniya. Ya zareta a hankali ya riqe qyam cikin jikinsa yana sake zareta daga turmutsitsin.
Sallah sukayi raka'a biyu daga nesa kadan da ka'aba din. Saita samu kanta da cikar hawaye a idanunta. Ta daga hannuwanta ta rasa me zata roqa?. Bayan addu'a data sakewa sultane,a yau saita samu kanta da yiwa mamarta addu'a.
"Ya Allah,kayi mata rahama.....ka shafe kurakuranta......ka yafe mata zunubanta Allah" Saita dakata,tana tuna me zata roqawa kanta.
"Allah......ka......" Kasa qarasawa tayi,tana juya abinda zuciyarta ta raya mata ta roqa din,ya cancanta?,ya kamata ta roqi wannan kuwa?. Wannw tabbaci take dashi?,wanne yaqini take dashi?. Bata da dukkan wata makama......bata da dukkan wani qwarin gwiwa nayin addu'a akan wannan.
Daga inda take zaune tana iya ganinsa. Tsaiwarsa a sallah......ruku'unsa dama sujjadarsa. Komai nasa sai take ganin yana da wani irin banbanci da wanda ta sani da kuma wanda ta saba gani.
Yadda ya zauna saman qafafunsa,cikin wani tawali'u da qanqan dakai,ya hade dukka tafukan hannayensa,ba wani sauran izza a tare dashi.....ba wata qasaita....sai zallar nuna miqa wuya ga ubangiji,sai taji itama tata zuciyar tana karyewa. Kuka kawai taji tana son tayi,ba tare da tasan dalili ba,sai kawai ta cure guri daya,ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana bawa hawayenta daman sauka yadda sukeso.
Ta dauki mintuna aqalla ashirin a haka......a hankali taji kaman qamshinsa a kusa da ita.....a hankali takejin kamar akwai wani kusanci na daban a tare da ita,sai ta soma qoqarin daidaita kanta da sassauta kukan,kafin a hankali ta soma qoqarin daga kanta.
Shine a zaune a gabanta,da wani irin coolness ya zuba mata manyan idanun nan nasa. Kallon ya mata nauyin da ba zata iya jura ba.
"Kiyi addu'a......guri ne na bayyana dukkan damuwa da samun waraka". Sai ya miqe a hankali ba tare da yace komai ba. Maganar ta tsaya mata a rai,tayi qasa da kanta a hankali tana bawa zuciyarta daman ambatar dukkan abinda take buri da muradi.
Karo na biyu ta sake ganin an miqa mata cup,ta daga idanunta a hankali. Shine ya dawo,yana tsugunne saman qafafunsa da cups guda biyu masu cike da zamzam mai sanyi.
Batayi musu ba ta miqa masa hannun,yatsunsu suka hadu da juna,sai ya zare hannunsa a hankali. Kauda kanta tayi tana juya yadda zata sha ruwa a gabansa,yana zaune dab da ita,idanunsa ta tabbatar kuma suna cikin nasa. Kamar yasan me take tunani,kamar yasan abinda yake ranta,sai ya matsa gefe kadan yana zama sosai saman tiles din masallacin.
A nutse ta shanye gaba daya,sai taji wata nutsuwa tana saukar mata a hankali. Ta sake satar kallonsa,baya komai don ya nuna kansa.....amma komai qoqari yake ya nuna wayeshi. A yanzun tana jin kawai kamar binne kansa yakeyi......tana jin wani binnnan mutum ne kawai suke rayuwa dashi,ba ainihin haqiqanin sheikh haisam na agadez ba.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽