Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 19

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 19

.....drink, I persist in trying to complete the work. After I finished washing, I went into the kitchen and started cooking. I know that if Mumy comes back and sees everything clearly, she will stop bothering us. I chopped onions and tomatoes and fried them in a pot of soup. As it was almost lunch time, I cut yams and put them on the gas. That's when Mumy came back into the kitchen, looking at me with a look of humiliation. "Hey, didn't I tell you to fix the house? Or are you doing something new here?" "Mummy, I finished cleaning the room and washing, now I'm cooking," I said in a trembling voice. She shook her head in dismay. "Now when you do your housework, will you be clean? You are just undisciplined! By God, you are ruined. After she finished her ordeal, she turned and left, continuing to curse. I stood staring at the kitchen door, my heart was pounding. I don't know when I picked up my phone. I opened TikTok, my heart was looking for entertainment to ease the pain caused by Mumy's words. I danced that I felt good about, I danced in moving dances, at that time, I felt like.....

Standalone post2,126 words

SHAFI NA GOMA SHA TARA

Bayan Mumy ta gama yi mun masifa tare da marin da ya girgiza dukkan zuciyata, na zauna a kan katifa ina kuka mai tsanani. Amma ba jimawa ba, sai na ji zuciyata ta fara tsorata da abin da zai biyo baya. Na san cewa idan har na ci gaba da zama haka, zai iya zama wani sabon laifi a idanun Mumy.

Cikin tsananin fargaba, na share hawayena da sauri, na mike tsaye. Dakin ya yi shiru, sai karar zuciyata da nake ji tana bugawa tamkar gangar rawa. Na duba gefen dakin, na hango kayan da suka watse saboda cunkoson da aka yi a lokacin Mumy tana masifa.

A hankali na fara gyara dakin, na tattara duk wasu kaya, na wanke kwanonin da suka taru a gefe. Idanuwana sun kumbura saboda kuka, amma ban damu ba. Na san cewa gyaran gidan zai rage min zargi a idanun Mumy.

Bayan na kammala gyaran dakin, na fito falo cikin tsananin tsoro, na fara tattara kayan wanki. Na kai su waje, na zuba ruwa a cikin kwandon wanki sannan na fara wankewa cikin sauri. Duk da jikina yana ciwo saboda marin da na sha, na dage ina kokarin kammala aikin.

Bayan na gama wanki, na shiga cikin kitchen na fara dora girki. Na san cewa idan Mumy ta dawo ta ga komai a tsaf, zata rage mun tsangwama. Na jajjaga albasa da tumatir, na soya cikin tukunyar miya. Da yake an kusa lokacin cin abincin rana, na yanka doya sannan na dora ta a kan gas.

Dai-dai lokacin ne Mumy ta sake shigo cikin kitchen din, tana kallona da wani irin kallo na wulakanci.

"Ke, ban ce ki gyara gidan ba? Ko kuwa kinzo kina yin wani sabon iskanci a nan ma?"

"Mumy, na gama gyara dakin da wanki, yanzu kuma girki nake yi," na fada cikin rawar murya.

Ta girgiza kai cikin rashin jin dadi. "Yanzu ke idan kina yin aikin gida, zaki samu tsarki ne? Mara tarbiyya kawai! Wallahi kin lalace.

Bayan ta gama masifar ta, ta juya ta fita, tana ci gaba da zuba zagi. Na tsaya na kurawa kofar kitchen din ido, zuciyata tana tafarfasa. Ban san lokacin da na dauko wayata ba. Na bude TikTok, zuciyata tana neman nishadi don rage radadin ciwon da kalaman Mumy suka haifar.

Na kunna waka mai sa rawa, na fara taka rawa cikin kunci da takaici. Na zabi wasu dabaru na rawa da nake jin dadi a kai, na hau yi cikin raye-raye masu motsa jiki. A lokacin, na rika jin kamar nishadin da nake nema ya fara zuwa.

Na danna "post" a TikTok, na dora bidiyon ba tare da tunanin me zai biyo baya ba.

Bayan na gama rawa, na sake zaunawa a kan kujera cikin falo, zuciyata tana cike da damuwa da mamakin yadda rayuwa ta sauya a kaina cikin kankanin lokaci.

*************

Bayan kwana biyu, na samu sauki sosai daga damuwar da ta addabe ni. Na shirya cikin kayan makaranta, na fesa turare mai dadi, sannan na dauki littafaina na fita. A yau na kuduri aniyar cewa zan mayar da hankali sosai a karatu. An kusa fara jarabawar WAEC, kuma Abba yana da burin mu ci gaba da ilimi yadda ya kamata.

Tun da Abba ya bayyana cewa yana so mu tafi Dubai ko London don karin ilimi idan muka kammala, Mumy ta fara nuna rashin goyon baya. Ta dage tana fadin cewa ita ba za ta bar diyarta ta tafi nesa ba, kamar yadda ya faru da Yaya Billy, wacce take ganin ta sha wahala sosai daga nesa.

A makaranta, lokacin break ya yi. Na zauna tare da Fatima a gefen bishiyar mangwaro da ke bayan ajin mu. Muna hira cikin nishadi, sai Fatima ta dauko wayarta tana dube-dube.

"Ramlah! Kin san kuwa cewa yanzu kin zama fitacciya a TikTok? Ki duba, kin kai dubu dari (100k) a followers!"

Na kura mata ido cikin mamaki. "Fatima, wannan ai ba komai bane. Abun da ya dame ni shine yadda maza suka cika comment. Wallahi akwai wanda har ya ce zan yi dadin kwanciya."

Fatima ta ja numfashi, ta harare ni cikin wasa. "Ke kuwa Ramlah, kina nufin kina tsoron haka? Ai wannan damar ce! Kina iya amfani da wannan farin jini ki tara kudi."

Na yi murmushi mai ciwo. "Wallahi Fatima, bani da ra'ayin hakan. Ni kawai ina son inyi nishadi ne, ba don wani abu ba."

Ta yi dariya, tana cewa "To fa, amma ke dinma kinyi shahara. Kuma akwai wadanda suke ganin cewa kin fi kowace yarinya kyau da iya rawa."

Bayan an tashi daga makaranta, na nufi gida cikin natsuwa. Na shiga daki na, na canza kaya don in tafi Islamiyya. Bayan na dawo da yamma, na shiga kitchen don dora girki. Ina cikin shirya kayan miya, sai ga sakonnin Khalil kala-kala a wayata.

"Ramlah, ki yi hakuri. Ba ni da laifi. Wallahi ban so abin ya kai haka ba."

Na harari wayar, na watsar. Ban da lokaci na kula da shi.

**** Dare ya yi, ina cikin falo ina kallon wani shirin talabijin, Abba ya shigo tare da Yaya Usman. Na yi saurin tashi na yi masa sannu da zuwa.

"Yauwa, Ramlah. Yau na gaji sosai. Na gode da girki," Abba ya fada yana murmushi.

Daga nan, sai muka zauna muna hira har zuwa lokacin da Mumy ta shigo cikin palon da fuskar da ta canza. Abba ya lura da yanayin fuskarta, ya dan juyo yana tambaya:

"Lafiya dai ko?"

Mumy ta durkusa a gabansa, tana rik'e wayarta. "Abban Ramlah, akwai matsala fa. Ka ga abinda 'yar ka take yi a TikTok? Wallahi na rasa me yasa yarinyar nan take neman lalacewa!"

Abba ya kalli Mumy da mamaki. "Me take yi a TikTok?"

Mumy ta mika masa wayarta. "Ga bidiyonta nan, tana rawa cikin rashin kamun kai. Mutane sun fara magana a gari. Har maza sun fara yi mata tsokaci mara kyau."

Abba ya karbi wayar yana duba bidiyon. A take fuskar sa ta canza.

"Me yasa zaki dora irin wannan bidiyo? Ba na son rashin nutsuwa a cikin gidan nan!"

Na zaro idanuwa cikin tsoro. "Abba, wallahi... wallahi kawai nayi nishadi ne..."

Kafin in kai ga rufe baki, sai na ji saukar marin da ya girgiza dukkan jikina. Abba ya mike tsaye cikin fushi, yana nuna ni da yatsa.

"Ni na gaya muku bana son rashin kamun kai! Kina neman daukaka ta hanyar Rawa? Ramlah, wannan ba tarbiyya bace!"

Mumy ta fashe da kuka. "Ka ga abinda na fada maka! Mutane suna cewa yarinyar mu tana neman lalacewa. Abba, sai mu dauki mataki kafin ya wuce hankali."

Abba ya juya gare ni, yana fadin

"Tashi ki bace mun daga gani! Wallahi ki tara kayanki ki fita daga gidan nan idan haka kike so. Iskanci kika zaba? To sai ki bar mun gida!"

Kukan da nake yi ya gagara tsayawa. Na yi ta rokon Abba da Mumy, amma suna nuna rashin jin dadi da damuwa. Abba ya sake marin fuska ta, yana daka tsawa

"Idan haka kike so, ki shirya ki tafi gidan Khalil tunda shi kike so! Wallahi ban haifi marar kamun kai ba!"

Na kasa magana, zuciyata tana kuna tamkar wuta. Na durkushe a kasa, ina rike kuncina da hannu biyu. Ban taba ganin Abba cikin irin wannan fushi ba. Bayan wannan masifar da ta faru a gida, na kwana cikin kuka da damuwa. Na kasa samun natsuwa duk tsawon dare, zuciyata na tafarfasa da ciwon da marin Abba ya haifar. Na rike kuncina da hannu daya yayin da dayan hannun na ke rike da mayafi, na kwanta a gefen katifa kamar wadda aka azabtar.

Da safe na mike da kyar, jikina duk ciwo saboda dukar da Abba yayi mun. Na yi wanka da kyar, na sa sabuwar uniform, na daura gyale a hankali. Na dubi fuskata a cikin madubi, na ga idanuna sun kumbura saboda kukan da nayi daren jiya.

Na fito daga daki, na shiga kitchen don dora girki na safe. Mumy tana falon tana duba wayarta, tana yiwa Yaya Zainab magana da sassanyar murya. Na dan yi shiru a bakin kofa, ina jin yadda take korafin cewa "yarinyar nan tana neman ta bata mana suna a gari."

Cikin jin haushi, na daure na cigaba da aikin girki, amma zuciyata na tsananta bugu. Na san cewa ina cikin tsaka mai wuya.

Da na dawo daga makaranta, jikina duk a sanyaye saboda tunanin abin da ya faru da ni kwana biyu da suka wuce. Na dade ina tunanin yadda zan gyara kuskuren da nayi, har na yanke shawarar gogewa duk wasu bidiyona daga TikTok. Na san cewa hakan ne kawai zai rage damuwa a gida.

Da na shigo gidan, na same su a falo, Abba yana zaune cikin tsananin fushi, Mumy kuma tana gefe tana cigaba da korafi kamar yadda ta saba. Na tsaya daga bakin kofar falon, zuciyata tana tsananta bugu. Abba ya dago kai yana kallona da idanunsa wadanda suka nuna karara cewa ransa a bace yake.

"Ramlah!" Ya kira sunana cikin karfi.

Na durkushe a wajen, hawaye na zubo daga idanuna. "Abba, na dawo daga makaranta."

"Ke! Ki tattara ki fice mun daga gida! Bazan iya zama da marar kamun kai kamar ke ba!"

Cikina ya murda tamkar an doka ni da guduma. Na kalli Abba cikin tsoro da tsananin damuwa. "Abba, don Allah kayi hakuri! Wallahi na goge dukkan bidiyona daga TikTok. Bazan sake ba. Idan na fita, ina zan tafi? Abba, nifa bantaba aikata iskanci ba, don Allah kayi hakuri."

Abba ya girgiza kai cikin takaici. "Ramlah, kin cutar da ni! Kin bata mun suna a gari. Mutane suna tambaya akan ki tamkar ba ni da tarbiyya. Wallahi, idan ba ki fita daga gidan nan ba, zan yi abin da na rantse!"

Mumy ta daga murya tana cewa, "Wallahi ka daina tausaya mata! Wannan yarinya ba zata natsu ba. Ka koreta kawai! Kalli yadda aka koma magana a gida, mutane sun fara tambayar mene ne ya samu 'yar gidan Malam Ibrahim!"

Na zube a kasa ina kuka, zuciyata na kuna kamar wuta. "Abba, don Allah, nayi kuskure ne. Wallahi bazan kara ba. Na goge komai! Na canza, kuma na gane cewa nayi kuskure. Don Allah kada ka kore ni."

Dai-dai lokacin, sai ga Yaya Abbas ya shigo cikin falon. Yana ganina a kasa ina kuka, ya yi saurin karasowa, yana duban Abba cikin mamaki.

"Abba, lafiya? Me ke faruwa ne?"

Abba ya nuna ni da hannu, yana fadin, "Wallahi, Abbas, idan wannan yarinyar bata bar mun gida ba, zan yi abin da na rantse!"

Yaya Abbas ya kalle ni cikin damuwa, sannan ya kalli Abba cikin natsuwa. "Abba, don Allah kayi hakuri. Ramlah bata da inda zata je. Ta goge bidiyonta, kuma ta gane kuskurenta. Bamu ba ta wata dama ba?"

Mumy ta harari Abbas cikin takaici. "Yaya Abbas, ka daina sa baki! Ita dai lalacewa tayi, kuma bazata gyaru ba!"

Yaya Abbas ya dauki tsaki, ya kalli Mumy. "Mumy, ki daina zugawa! Wannan ba maganin matsala bane. Ai abin da ya wuce ya wuce. Duk wani abu da aka yi, Allah zai gyara ai abun mugodewa Allah ne dayasanya har aka gani yanzu."

Abba ya sauke numfashi, ya kalli Abbas cikin fushi amma a hankali fushin nasa ya fara raguwa. "Kai ma ka san cewa wannan abin da tayi ya kai makura.

Yaya Abbas ya zauna kusa da Abba, yana fadin, "Abba, ka tuna fa cewa ita din yarinyarka ce. Idan muka koreta, ta ina zata fita? Kuma menene ma zai faru da ita a waje? Kayi hakuri, wallahi tayi nadama."

Abba ya ja numfashi mai karfi, ya kalli ni da idanu masu tsananin tsawa. "Ramlah, wannan shine na karshe! Idan kika sake aikata irin wannan abu ko wani abu da zai jawo mana magana, wallahi sai kin bar gidan nan har abada! Baki da sauran uzuri!"

Na daga kai a hankali, ina kuka, na goge hawayena. "Nagode Abba. Wallahi bazan sake ba. Na yi alkawari zan gyara halina."

Yaya Abbas ya kama hannuna yana rarrashi. "Kin ji ko Ramlah? Ki natsu, ki daina abubuwan da zasu sa kowa ya zarge ki."

Abba ya mike daga kujera yana girgiza kai. "Ba zan kara dauka ba idan wani abu makamancin wannan ya faru. Kuma ki daina amfani da TikTok gaba daya. Baki da wani abu da zai rufe ki sai karatu. Na gama magana."

Na gyada kai cikin jin kunya, na share hawayena. Mumy ta yi tsaki, ta juya ta fita daga falon, tana cigaba da mita. Yaya Abbas ya dube ni, ya yi murmushi mai sanyaya zuciya.

"Ki daina kuka, kin ji? Na san kina cikin tsaka mai wuya, amma ki natsu. Abba ya yafe miki amma kada ki sake abinda zai sa ya fita daga hayyacinsa."

Na yi masa godiya cikin sanyin murya.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH