
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 27
.....who has arranged a message only right other than calling until they complete the order. _Muhammad is worried.....he wants to see his sister since he lost his mother_ is the only message. He felt a heavy weight on his soul, he felt compassion for the boy, and he gave the boy a short answer. _give him patience, they will meet in Ethiopia_ From there, she was looking at them in a different part, he was lying on her lap with the Qur'an in his hand, and she pushed her fingers into his hair, stirring it gently and following the sound of his reading. His sound is higher than hers, but all their sounds are mixed together to give a beautiful color. I don't know why he put a smile on her face......then he turned her attention to looking at him through the window, did he see it too? Still his eyes were on the phone, she felt something uncomfortable when he stood up to her, she turned her gaze on him and turned back to him, and he slowly turned around and looked at her in a way that would make it difficult for you to understand what he was looking at. For the first time, he looked at her with a different look..... her compassion for the first time began to penetrate his heart with real st
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 27*
Ba a nan kawai ba.....sanda suke takawa a hankali ita dashi,tana daga gefansa.....iskar dare me tarin nutsuwa da wani irin sanyi tana kadasu. Kusan dukka inda sukebi kamar abun shiri,ma'aurata ne guri guri cikin yanayi na soyayya da zai dauki hankalin duk wanda ya gansu.
Wasu a kwance daya yayi pillow da cinyar daya......wasu a zaune suna hira......wasu karatun qur'ani.....wasu kuma dukkansu bacci suke kusa da kusa da juna,yayin da wasunsu kuma suke maqale da hannun juna suna tafiya zuwa gurarensu.
Idanunta yawo kawai yakeyi a kansu,haka kawai takejin komai yana burgeta,haka kawai takejin yanayin duk da take kalla yana burgeta.
Ba soyayya sam cikin tsarinta.....saboda ba kalan namijin da takejin yakai ya mallaketa......amma a yanzun batasan me yasa couples din suke burgeta ba.
Qarar da yaji wayarsa tayi ta Bluetooth din dake kunnensa shi ya sanyashi cirota daga qaramin wallet din hannunsa.
Beeno ne ya ajiye masa saqo,wanda ya tsara saqo kawai dama banda kira har sai sun kammala umara.
_muhammad ya damu.....yanason yaga 'yaruwarshi tunda ya rasa mamarsa_ shine kawai saqon. Wani nauyi yaji ya sauka a ransa,tausayin yaron ya kamashi,sai ya maidawa beeno din amsa a taqaice.
_ka bashi haquri,zasu hadu a Ethiopia_
Daga can wani sashe na daban take kallonsu,yana kwance saman cinyarta da alqur'ani a hannunsa,ita kuma ta tura yatsunta cikin sumarsa tana hargitsata a hankali tana kuma biye da sautin karatun nasa. Sautinsa ne sama da natan,amma dukka sound dinsu ya cakude ya bada wani launin qira'a me dadi.
Batasan me ya saukar da murmushi saman fuskarta ba......sannan ya fusgi hankalinta zuwa ga kallonsa don taga ko shima ya gani?. Still idonsa nakan waya,wani abu taji mara dadi ya tsaye mata,saita janye dubanta a kansa ta maida kansu,daidai sanda shi kuma ya juya a hankali yana dubanta da wani yanayi da zai wahala ka gane ita yake kalla.
Karon farko ya zuba mata ido da wani kallo na daban.....tausayinta a karon farko ya soma ratsa zuciyarsa da qarfin gaske. Yaji zuciyarsa tana nauyi,yana rayawa a ransa,idan shine ya rasa nanay dinsa yaya zaiyi?. Inda ya rayu ba noorah......ba hussam.....ba rumaisa.....ba khansaa.....ba Aareef yaya rayuwa zata kasance masa?.
Tausayinta yakeji da gasken gaske.....dukka batasan dadin wadannan ba?. Batasan dadin uwa ba.....batasan dadin 'yan uwa ba. Ta rasa da yawa cikin rayuwarta ba tare data sani ba.....ta rasa wasu bangarori masu matuqar Muhimmanci bata gane ba. An kange mata rayuwa an tsaidata a wani muhalli guda daya,ta dauka iya haka ta morewa rayuwarta.
A yadda ta motsa ya fuskanci dauke idanu tayi daga kallon wani abu,kallon wani abu da ya tabbatar shine. Yaji a jikinsa a dazun,amma kuma yanason kamata a yansu da kansa......yanason kamata yadda ba zata iya musa masa ba,don haka yayi kaman ya dauke kai.....yayi kaman ba yaci gaba da abinda yake gabansa ne.
Karo na biyu ta sake waigowa,tana jin wannan haushin can qasan ranta. Me yasa yakeson maidata mayyar kallonsa?,me yake dashi me janye hankali har haka?. Ba haka take ba.....ta sani ba haka dabi'arta take ba. Komai kyau....komai isar d'a namiji baya da wannan muhimmancin a gareta.....me yake shirin canzata?.
Da wani irin zafin nama ya waiwayo,ya kuma kamata kaman yadda yayi timing. Ta dan razana don haka tayi saurin kauda kanta.
Murmushi ya saki....wani kalan murmushi me sanyi.
"Me yasa ba zaki bar wuyanki ya huta ba akhnan?" Har tsakiyar tafin qafarta taji yadda ya kira sunanta. Wani irin accent yayi amfani dashi daya sanya sunan ya sauya kamar ba sunanta ba....kamar ba sunan data saba ji daga bakunan mutane ba. Izzarta ta motsa kadan,saita hade ranta sosai,tana ji a ranta bai kamata haka taci gaba da kasancewa ba,bai kamata ya ganta tana kallonsa ba har haka.
"Da akayi me?". Wannan karon murmushin nasa sai daya bada sauti kadan,murmushin daya masa kyau ainun,har ya dauki hankalin wasu 'yammata dake zaune daf da inda zasu wuce,kuma akan idanunta,tana ganin yadda dayar ta tabo 'yar uwarta a dabarance,tabar danna wayar da takeyi ta xuba masa idanu kuwa. Idanunta ta dauke a kansu tana jin wani abu ya matse a qirjinta.
"Me yasa duka wannan?" Ta tambayi kanta,me yasa takejin kanta kamar ba ita ba?,kamar ba ita akhnan ba?,me yasa?.
Ya shirya shayar da ita mamaki,don haka ya miqa yatsunsa ya kama habarta ya juyo da fuskarta zuwa saitin tasa cikin ba zata. Tazarar dake tsakaninsu ya hade yana duban tsakiyar qwayar idanunta,a hankali ya motsa labbansa,tafiyar tasu dukka su biyun tana komawa very slow kamar wadanda qafafunsu sukayi sanyi.
"I'm your halal.....ki kalleni kai tsaye kaman zaifi your highness.....kina yawan kauda kai,kaman bakisan kina kallona bane"
Kasa cire idanunta tayi daga nasa,kaman yadda shima ya zabi ci gaba da karantarta ta cikin qwayar idanunta masu kalan blue da haske qwayayen haram ke sake haske masa su. Wani unique qwayan idanu da suka banbanta da irin wanda kowa yake dashi.
"Sun narke dukkansu......amma inda zakace wani abu yanzu kowannensu saiya qaryataka" Maleek dake tsaye daga nesa kadan dasu ya fada yana riqe da falaak sosai cikin jikinsa kamar wani zai qwace masa ita,saidai kuma akhnan da haisam din dukkansu sun dauki hankulansu fiye da yanayin da suke ciki.
Duk da yanayin kunyar da maleek keta saka falaak adan tsukin......amma a yanzu....a daidai lokacin saita hango wani boyayyen abu....wani boyayyen abu da yafi qarfin kansu ita da maleek din gaba daya. Wani abu da yasa taji kamar zata narke.....kamar bata taba ganin abun burgewa a rayuwarta ba irin tsaiwar akhnan da haisam a gurin......duk da basajin maganan me suke.....amma ko daga nesa duk wanda zai wuce sai ya kallesu,sai kuma ya sake waiwayowa ya sake kallonsu,saboda wani irin perfect match da aka tasa a gurin.
A hankali ya sake mata habarta,taja baya da sauri tana sunkuyar da kanta qasa. Me yasa ta tsaya?,me yasa taci gaba da kallonsa?.
"Yaaa akhnan" Muyar falaak ta fusgi kunnuwanta,falaak din data kasa jurewa sai data kira akhnan din,duk da yadda maleek yaso ta bari su mamayesu kawai.
Tunda yaji muyar falaak ya tabbatar tare suke da maleek. Sauke hannuwansa yayi ya soma laluben nata hannayen cikin nasa ba tare daya waiwaya ya kalli inda suke ba.
Sosai ya matsesu cikin nata,dumin dake jikin tafin hannun kowannensu yana zagayawa sassan jikin kowannensu. Idan yace bayason tafukan hannayen ta yayi qarya......idan yace dumin da yakeji a ciki basa burgeshi yayi qarya......idan yace siraran dogayen yatsansa da suke shigewa cikin nasa basa burgeshi yayi qaerya. Karon farko a rayuwarsa daya tsaya karantar yanayin hannun wata diya mace.....kaman yadda ta zama mutum ta farko daya fara saka hannuwanta cikin nasa irin haka.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Banaso ki kalli kowa......shi yasa nace ni ki kalleni kai tsaye a duk sanda hakan yayi miki" Ya qarashe maganan yana duban idanunta,can qasan ransa kuma yana jin kamar maganar tayi nauyi.....kaman bai furta maganan daidai ba.
"Maleek na tahoha......boundaries please" Ya fada muryarsa can qasa kamar wanda kejin bacci,abinda ya tayar da duk wata tsiga kenan ta jikinta,saboda sai daya kawo bakinsa saitin kunnenta sannna ya qarashe maganan.
Ta rasa wannan boundaries da yake saka mata na meye......ta rasa me yasa yake yawan nanata mata kalmar a duk sanda zasuyi wata hulda data hada da maza a gurin.
Sakin hannunta qwaya daya yayi,sannan ya maidata a gefan kafadarsa daya suka fara takawa a hankali suna tunkarar su maleek dake tsaye a gurbinsu.
Idanunsa akan fuskar maleek kawai suka tsaya,yana kallon yadda maleek din ya sunkuya a hankali yayi magana da falaak. Bai kalleta ba.....amma in blurry vision yake ganin kamar ta saka tafin hannunta ta lullube fuskarta. Baisan me yace da ita ba.....amma yayi imanin gulmarsu sukayi.
Sakin hannunta yayi a hankali ya miqawa maleek sukayi musabaha,yana jin falaak na gaidashi.
"Barka da warhaka Aman-nin"
"Barkanki kina lafiya?"
"Alhamdulillah".
"Aman-nin......me kenan habibty?" Duka sai falaak din taji ya aza mata nauyi. Tun daga saukarsu zuwa yanzu a yau din ita kadai tasan nauyin da maleek yake sakawa takeji.
"Yaren Tuareg ne.....yana nufin yaaya"
"Zaa koyamin?" Ya tambayeta yana narke murya idanunsa dukka a kanta kamar ya cinyeta. Kai ta daga a hankali.
"Kun kammala umrar?". Haisam ya katse tattaunawar tasu,saboda lura da yadda maleek yake neman sauka daga layi.
Maido dubansa maleek yayi ga haisam din,dama kuma abinda yakeso kenan,sai haisam din ya watsa masa harara. Dariyarsa ya danne,ya sani muddin idanun haisam suna kanka baka isa kayi abun arziqi ba.
"Habibty ta gaji......gobe zamu qarasa sa'ayi" Kafada haisam ya daga dukka biyun.
Kallon akhnan falaak tayi,wannan qaunar.....wannan 'yan uwantakar,sai taji ta kasa jurewa duk da dariyar da take boyewa. Ta taka da sauri yana rungume akhnan din don ta sani ba lallai ta fara samun hakan daga akhnan din ba.
"Yaa biftu.....Essaghlegh-kem(nayi kewarki).Temegded temhust(kinyi kyau)". A karon farko taji wani 'yan uwantaka na ainihi yana ratsata sanda falaak ta rungumeta,sai ta samu kanta itama da zagaya hannu ta rungume falaak din cikin jikinta,sannan ta amsa mata itama cikin yaren Tuareg din,don suna ganin shine kadai safest yare da zasuyi maganansu cikin sirri.
"Kice wani abu daban mana falaak?,ta ina kikayi kewata?,ina kuka bace?". Baya kadan falaak taja tana dariya a kunyace,amma kafin tace komai taga haisam din riqe da hannun maleek suka qara taku kadan gaba dasu suka basu tazara.
" Ya biftu......man dinki....man dinki shine ya koremu,yace bazai hada masauki da habeeb ba.....ina jins......"
"Habeeb?" Akhnan ta samu kanta da maimaitawa tana zubawa falaak ido. Kunya ta saukarwa falaak,tasa tafin hannunta tana toshe bakinta gami da sakin dariya.
"Afwan ya biftu......amma shine ya koremu seriously fa........basan wanne irin hot love zaa baza ba haka da ba'a gayyatarmu" Ta qarasa fada qasa qasa tana raba idanu.
Fuska akhnan din tadan hade tana hararan falaak
"Baki da kunya sosai ashe falaak ?.kin manta?Nekk a weltma-kem tameqqart.(ni yayarki ce?" Ta fada tana komawa ainihin akhnan dinta.
Murmushi ta sake saki a kunyace,sai suka taka suna zama saman tiles din gurin. Idanu kawai akhnan ta zubawa falaak,yadda take magana yake bata mamaki. Me maleek ya bata haka kaman ta zauce a kanshi?.
"Ya isa" Akhnan ta fada a hankali tana dagawa falaak hannu. Wani irin soyayya ne me zafi take gani a idanun falaak din,koda suna tare amma idanunta yana tare da maleek din,kamar yadda ta karanci kaman shike tsokanota daga inda yake.
"Zamu wuce yaa biftu" Falaak ta fadi bayan ta miqe.
"Byee" Akhnan ta fada tana daga mata yatsu,itama saita maida mata ta soma takawa tana nufar inda maleek din yake.
Qasa ta danyi da kanta tana murza yatsunta. So take ta fayyace.....laifi falaak tayi?,ko kuma akan daidai take?. Wanne irin so ne wannan?,baiyi zurfi da yawa ba?. Tadan yi taku biyu baya don daidaita tsaiwarta,sai taji kaman ta dunguri wani abu,ta juya da sauri.....saurin daya bawa fuskarta daman shiga cikin nasa,sukayi musayar numfashi sannan tataka baya da sauri,saidai tuni ya saka hannunsa ya riqo qugunta. Da sauri ta daga ido ta kalleshi sanda take riqe cikin hannunsa,sai ya mata nuni da bayanta da idanu.
Takalmi ne a gurin na mutane,wanda tabbas data taka koda bata fadi ba saita kusa faduwa,saita maida dubanta kansa,a hankali ya zame hannunsa yana sakinta amma still idanunsa cikin nata.
Kallon nan yana mata nauyi da yawa,ko a yanzun sai taji idanunsa suna neman sanyata ta diririce,saita soma gyara zaman hijab dinta ko zata samu chance na lalubo nutsuwarta.
"Coffee?" Ya motsa labbansa ya fadi a hankali idanunsa suna kan kwantaccen gashin gefan fuskarta daya fito.
Manyan blue eyes dinta ta daga tadan kalleshi,haka kawai wannan karon yaji kamar an qarawa qwayar idanun nata haske,sai kuma ta zame a hankali ta motsa bakinta tana fadin.
"Okay".
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽