
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 20
.....the gray sofa, she was squinting her eyes in relaxation. She quickly picked up her iPhone 15 Pro Max, checking whether her husband called or answered her messages. But still silent. She sent him many messages in WhatsApp, but there were no signs that he read them. She felt a kind of anger rising up, but she held firm, keeping her mind calm. As'ad, her husband, a rich man who owns a large construction and investment company in Dubai and Nigeria and is the fourth in line to the King of the City, has never been this silent. He always answers her calls or messages. But now? Another heart took her until she pressed a heavy breath. The plane took off quietly, she held the cup of cold Zuma water that was kept for her by the attendant in the plane, and she kept checking the phone. Until she landed at Charles de Gaulle International Airport in Paris, there was no call from Asad. Her driver greeted her and said: "Madam Ayshatu, the car reserved for you is waiting for you." Without a word, she got into the Rolls-Royce Phantom, which had been waiting for her. Then they went to the big hotel where they were prepared for her, the Ritz Paris, one of the hotels.....
SHAFI NA ASHIRIN.
DUBAI INTERNATIONAL AIRPORT...
Wata katafaren motar alfarma ce ta tsaya a bakin ?ofar VIP na filin jirgin sama na Dubai International Airport, inda ake ganin yanayin tsare-tsaren masu ku?i kawai. Daga cikin motar ta fito, sanye cikin shiga mai tsada - farar foguwar riga ta Valentino, wadda ta yi rolling da kanta cikin salo. Gilashin ido na Gucci mai launin toka ya ?ara bayyana kyanta, tana tafiya cikin nutsuwa da kima, kamar wacce aka shirya don kasaitaccen liyafa.
Kafin ta shiga cikin jirgin, direbanta ya bu?e ?ofar cikin ladabi, yana mai cewa "Madam Ayshatu, jirginku na jiran ku."
Ta ?an gya?a kai da murmushi mai taushi, sannan ta taka cikin sau?i zuwa cikin jirgin. Jirgin kuwa ba ?aramin Na alfarma ba ne wata katafaren Gulfstream G700 Private Jet, mai ?auke da cikakken ?akin kwana, falo na alfarma, da kuma ofishin sirri. An tsarashi da kujeru na fata masu she?i, launin fari da ja a ko'ina, yayin da ?akin ya cika da ?amshin turaren Tom Ford Oud Wood.
Ta zauna kan babban kujera mai launin toka, tana lumshe idanu cikin annashuwa. Da sauri ta ?auki wayarta iPhone 15 Pro Max, tana duba ko mijinta ya kira ko ya amsa sa?onninta. Amma har yanzu shiru. Ta aika masa da sa?onni masu yawa a cikin WhatsApp, amma babu alamun cewa ya karanta.
Tana jin wani irin tsananin fushi yana tasowa, amma ta daure, tana kwantar da hankalinta. As'ad, mijinta, attajirin da ya mallaki katafaren kamfanin gine-gine da harkokin ku?i a Dubai da Nigeria kuma ?a na hudu ga sarkin Garin, bai ta?a yin wannan irin shiru ba. A koyaushe yana amsa kiran ta ko sa?on ta. Amma yanzu? Wata zuciya ta ?auke ta har sai da ta danna numfashi mai nauyi.
Jirgin ya tashi cikin nutsuwa, ta rike kofin ruwan Zuma mai sanyi da aka ajiye mata daga mai yi mata hidima a cikin jirgin, tana ci gaba da duba wayar. Har ta sauka a filin jirgin saman Charles de Gaulle International Airport a Paris, babu wani kira daga As'ad.
Direbanta ya yi mata gaisuwa tare da cewa: "Madam Ayshatu, motar da aka tanada don ku na jiranku."
Ba tare da magana ba, ta shiga cikin motar Rolls-Royce Phantom, wacce ta kasance tana jiranta. Sannan suka nufi katafaren otal ?in da aka shirya mata Ritz Paris, daya daga cikin otal-otal mafi tsada a duniya.
Ta kara gwada lambar mijinta sau uku, amma har yanzu ba'a daga ba. Da takaici, ta yi tsaki mai tsawo tana kwanciya a kan gadon otal din, cike da damuwa.
"Da Ayshatu kake magana, As'ad!" Ta furta a hankali, tana jin wani irin nauyi a zuciyarta.
PARIS, FRANCE...
Tana cikin ?akin otal na Ritz Paris, Ayshatu ta kalli agogon zinariya na Rolex Daytona dake hannunta. Wata murya mai laushi daga cikin wayarta ta sanar da ita cewar tana da saura awanni biyar kacal kafin ta bar Paris ta nufi Najeriya. Wannan lokaci ka?an ne, don haka sai ta fara sauri wajen kammala duk wasu ayyuka da suka kawo ta garin.
Bayan ta gama wasu muhimman ganawa da wakilan kamfanin da As'ad, ta koma ?akinta don yin wanka. Bayan haka, ta zabi wani ha?a??en kaya wanda ya dace da yanayin hutawa da tafiya riga da wando palazo na Balmain, mai launin toka mai duhu, wanda ta yi rolling da zane mai kyau a kanta. Fuskar ta a ma?ure da gilashin ido mai duhu na Dior, sai ?amshin turaren Creed Aventus for Her ya mamaye ?akin. Duk wanda ya ganta, ba sai an gaya masa cewa matar mai kudi ba ce ba.
Ta sauka daga ?akin otal cikin nutsuwa, direbanta yana jiran ta a waje tare da motar alfarma Bentley Mulsanne. Bayan sun isa filin jirgin sama, ta hau cikin jirgin sirrin ta cikin girmama.
LAGOS, NIGERIA...
Bayan awanni da ba su wuce uku ba, jirgin ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport, maimakon a filin jirgin sama na birnin tarayya Abuja kamar yadda aka tsara farko. Wani sabon tsari da aka yi ya sa dole ta sauka a Lagos saboda wasu muhimman ayyuka data tsara a can.
Daga nan aka yi mata iso zuwa daya daga cikin manyan otal-otal na garin Eko Hotel and Suites wanda aka tanada don hutawar ta. Tana shiga, wani mutum mai kula da ba?i ya ?auke mata jakar ta cikin ladabi, yana mai cewa "Barka da zuwa, Madam Ayshatu. An tanadi daki mai alfarma a gare ki."
Ta yi murmushi ka?an, tana tsayar da shi da hannunta. Bayan ta shiga dakin, ta ajiye wayarta a kan gadon alfarma, sannan ta zauna tana yin la'akari da duk abubuwan da suka faru cikin kwanaki kadan. Tana jin nauyin gajiya, amma ta san cewa a nan ne zata samu damar hutawa kafin ta tafi birnin tarayya.
Bayan ta ci abinci mai sau?i na girke-girken Continental, ta sake shigewa cikin wanka mai sanyi. Bayan haka, ta canza kayan ta zuwa Atampha mai launin shudi da zinariya, wanda ya bayyana kyanta na Hausa Fulani sosai. Ta yafa likaf mai haske a saman kanta, har ba wanda zai gane cewa itace matar attajirin nan da duniya ke magana akai.
Tana barin otal din cikin salo mai cike da wayewa da kamewa, ta samu damar fita ba tare da wani ya gane ta ba. A wannan lokaci, tana da wani tsari mai matukar muhimmanci a Lagos kafin ta zarce zuwa Abuja.
Tafiyarta ba ta yi sau?i ba, saboda motar ta nufi wasu unguwannin da ke cikin garin Lagos. Bayan tafiya mai nisa da kusan sa'a guda, ta ji kamar an sauke nauyi daga zuciyarta, yayin da ta iso wani yanki da ke kusa da kasuwa. Tana ganin yanayin kasuwar nan, sai ta fahimci cewa wannan ba sabon wuri ba ne a gare ta. Duk da sauye-sauyen da aka samu, akwai alamun cewa ta saba zuwa wannan wuri a can baya.
Ta taka cikin kasuwar, tana tafiya cikin natsuwa. A cikin kasuwar, ta tsaya a wajen da ake sayar da kyalle, inda wani babban fili ke cike da jan kyalle masu kyau da kalar alfarma. Ta zabi guda biyu cikin hikima, tana tambayar farashi cikin yaren Yarbanci da nutsuwa. Mai sayar da kayan ya yi murmushi, yana yabawa yadda ta iya harshen, sannan ya bata farashi mai sauki.
Bayan ta gama sayayyarta, ta koma motar, amma zuciyarta tana sanar da ita cewa akwai wata hanya mai tsawo da dole ta bi. Daga nan ta yanke shawarar ci gaba da tafiya ta hanyar da ta saba a da. Tana cikin tafiya, sai ta tsaya a wani wuri da ake tsayawa domin shiga Bus.
Sannan ta samu bus mai dauke da mutane na ciki da waje. Tana shiga, ta zabi zama a cikin dan kyakkyawan wuri, tana lumshe idanuwa kamar mai tunani mai zurfi. Wannan tafiyar mai nisan gaske ta kai su kusan awanni hudu kafin su isa wani gari a gefen birni, cike da gajiya.
Tana sauka daga bus din, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Ta bude jakar ta, ta dauko snacks da drinks da ta hada tun daga otal din. Bayan ta dan ci, sai ta duba agogonta, ganin cewa lokaci na wucewa sosai. A wannan gefen gari, babu motocin alfarma kamar yadda ta saba gani, sai mashina kawai ake amfani da su.
Wani matashi mai mashin ya karaso gare ta, yana tambaya cikin yaren mutanen garin "Madam, ina zaki?"
Ta tsaya tana tunani, sannan ta bayyana masa garin da take son zuwa. Sai kuwa ya ?an kalle ta da mamaki, yana cewa "Madam, garin da zakije, wanda ake sallah ko wanda ba'a sallah?"
Ta ?an yi shiru kafin ta amsa cikin sirri "Wanda ba'a sallah."
Matashin ya gyara mashin dinsa sannan ya ce "Toh, farashin shi dubu goma ne."
Ba tare da wata gardama ba, ta amince da farashin, Ta hau kan mashin, suna tafiya a cikin duhun dare mai ?an kauri, iska tana kadawa a fuskar ta.
Bayan tafiya mai nisan gaske a kan mashin cikin duhu da iska mai sanyi tana busawa, sun iso wani wuri da ya fara nuna alamun bambanci daga sauran garuruwan da suka ratsa. Garin yana da wata irin yanayi mai ban tsoro titunan ?asa ne, cike da laka da ?azanta. Gidaje masu fasali na gargajiya suna kewaye da dutse da ciyawa mai tsawo, kuma akwai hayaki mai ?amshi mai nauyi yana tashi daga wani yanki na tsakiyar garin.
Kafin su shiga cikin garin sosai, mai mashin din ya tsaya, yana kallon Ayshatu da idanun da ke nuna rashin jin da?i. "Madam, ki kula sosai da wannan wuri. Babu wani imani a cikin wannan gari. Matsafa ne ke nan."
Ayshatu ta ja numfashi mai nauyi, tana jin wani irin bugun zuciya ya sauya. Amma ta ?ara rike kanta da kima. Ta ciro wani ?an ku?i daga cikin jakar ta, ta mi?a masa tare da cewa "Nagode. Zan ci gaba daga nan."
Mai mashin din ya yi mata kallon tausayi, sannan ya juya mashin dinsa da sauri ya bar wajen. Bayan tafiyarsa, sai ta tsayar da numfashi tare da kame kanta, tana kara tabbatarwa cewa dole ne ta yi wannan tafiya domin amfanin rayuwarta.
Garin ya kasance cikin tsananin shiru, sai fitar hayaki daga tsakar unguwa da wasu ?ananan yara su biyu suna wucewa suna jera wakar da ke ?auke da kalmomi masu tsoro "Ba mai rai, ba mai gaskiya, cikin duhu muke, mu bauta wa jini."
Ayshatu ta ?an tsayar da tafiyarta, zuciyarta na bugawa da sauri. Lokacin da ta isa tsakiyar garin, ta hangi wata tsohuwa tana zuba wasu irin ganyayyaki a kan wata ?aramar wuta, tana zazzaga wasu kalamai a yaren da ba a fahimta. Kallo guda da ta yi mata, sai ta ga idanunta na zaro kamar na maciji.
Wani mutum mai kyan jiki ya matso kusa da ita, yana magana da murya mai taushi amma mai ban tsoro "Me kike nema a wannan gari, matar mai kudi?"
Ta ?an tsaya tana tunanin yadda ya gane ta. Tana iya jin fitar turaren Creed daga jikinta, wanda ya yi tsami da ?an gumi saboda gajiyar tafiya. Ta kame kanta, tana cewa "Ina neman Baba Asabe."
Mutumin ya yi murmushi mai cike da mugunta, yana nuna mata wani gida a gefen kasuwar duhu, yana cewa "A can ne."
Ta ?an runtse idanu, tana jin zuciyarta na tsananta bugawa. Amma duk da haka, ta ?ara ?arfin hali, tana tafiya a hankali zuwa gidan. Gidan yana da tsohuwar kofa mai ?arfe, akwai hotunan tsafe-tsafe a jikin bango, da wasu alamu na dodanni da aka zana da jini.
Ta ?aga hannunta, tana neman bugawa, amma kafin ta kai ga dukan ?ofar, sai ta ji murya daga ciki "Shigo, Ayshatu. Tuni na san kin iso."
Zuciyarta ta buga da karfi, amma ta tura ?ofar ta shiga cikin gidan mai duhu. Wata irin murya mai ?arfi ta karade dakin "Yau shekara biyar kenan, Ayshatu. Me ya dawo da ke garin nan?"
Cikin jin zafi a zuciyarta, ta ce: "Burukana sun cika, kuma ina son na daidaita abin da ya dusashe tun lokacin da na baro nan."
Tsohuwar da ke zaune cikin duhun ?aki ta fito, tana da jajayen idanun da suka bayyana cikin duhun. Ta yi murmushi mai cike da mugunta, tana cewa "Ai nasan za ki dawo. Kuma na san dalilin dawowarki kin zo neman ?arfin da aka sake miki. Amma fa, wannan karon akwai sharadi."
Ayshatu ta yi shiru, tana jin yadda maganar ke ratsa zuciyarta. Tsohuwar ta yi dariya mai sauti mai cike da tsoro: "Kin san sharadin kenan sai kin sadaukar da wani abu na kusa dake kafin a dawo miki da wannan ?arfin Mulkin mijinki."
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH