Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 28

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 28

..... her hand gently until one notices it. "Can you drink after he calms down?" He asked her, taking his eyes off her. She was silent before slowly taking the cup to her mouth. She calmly sipped and lowered the cup, enjoying the coffee as it passed through her. She put her eyes in the cup and looked at the contents of the cup. There was nothing wrong with it, so she raised her eyes again and looked at it. He raised his eyebrows at both of them as he set his cup down. "Oromian coffee" He said briefly, she pressed his lips and looked at the one who put his warm coffee back into a red color. Thirty minutes later, they went back and forth to the raffles so that they could rest again. Birra came to her room, took off her clothes, took a shower, came out and put on the same nightgown and took it for her. "What's wrong with you, Birra?....What are you doing and you're greedy?" She bowed down to herself in reverence "I am repenting.....the sheikh said everything about the house should be left here....that is the order I accept". She kept silent and looked at Birra, and she wanted to find out the reason why he gave this order. She doesn't understand.....

Standalone post1,904 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 28*

A nutse take qarewa gurin kallo,shima ko ba'a gaya mata ba vip ne......ta sani vip ne gurin,don komai nasa a tsare yake. Hatta da butoci da cups da tray na tea din daban suke.

Daya daga cikin ma'aikatan gurinne ya qaraso cikin girmamawa ya gaida haisam. Sai yayi magana dashi da yaren da bata fahimceshi ba. Juyawa yayi ba dadewa ya dawo da kalolin tea da coffee din ya ajiye musu ya juya.

Kallonta yayi kadan sannan ya kalli tray din,ya dauki buta daya ya tsiyaya mata cikin madaidaicin cup din ya tura mata zuwa gabanta.

"Akwai wani abu daban da kike da buqata?" Ya tambayeta yana kai nasa cup din bakinsa. Original oromo coffee......tea din daya jima dayin missing dinsa tun bayan shigarsa agadez. Kai ta girgiza a hankali,ta miqa hannu ta dauki cup din,amma kuma ta kasa kaiwa bakinta. Wani irin rashin sakewa da rashin sabo takeji,cin abinci a gabansa wani sabo kuma baqon abune a gurinta. Saita dinga juya cup din kawai cikin hannunta a hankali har sai daya lura da hakan.

"Kina iya sha bayan ya huce?" Ya tambayeta yana sauke idanunsa daga kanta. Shuru ta danyi kafin a hankali ta dauki cup din takai bakinta.

A yangance da nutsuwar izzarta tayi sipping sannan ta sauke cup din tana jin dadin coffee din yana ratsata. Idanunta ta maida cikin cup din tana kallon abinda yake ciki sosai abinda batayi ba a dazu,sai ta sake daga idonta tana dubansa.

Girarsa ya daga mata dukka biyun yana aje cup dinsa.

"Oromian coffee" Ya furta a taqaice,ta danbi lips dinsa da kallon wanda dumin coffee dinsa ya sake sanyawa yayi wani irin jaja jaja me kyau,saita dauke idonta a hakali zuciyarta na raya mata wani abu.

Minti talatin kawai sukayi koma koma raffles don su sake hutawa sosai. Birra ta shigo har dakinta ta tayata rage kayan jikinta,tayi wanka ta fito ta sake shiryawa cikin kayan baccin guda daya data dauko mata.

"Me yake damunki ne birra?....me kike sanda kika hadamin kaya ne?" Qasa tayi da kanta cikin Girmamawa

"Tuba nake.....sheikh yace komai daya danganci gida a barshi a nan....umarnin dana karba kenan". Shuru akhnan din tayi tana kallon birra,tana kuma son gano dalilin daya sanyashi ya bada wannan umarnin. Bata gane komai ba,don haka kawai tace da ita.

"Jeki"

"Ki huta lafiya" Ta fada tana juyawa sannan ta fita.

Duk da duhu daya mamaye dakin,amma hakan bai hana shigowar haske daga gurare daban daban na waje ba. Wani irin sukuni takeji a duk sanda ta bude lumsassun idanunta ta hangi hasken harami daga nan inda take kwance da kuma ginin ka'aba.

"Astgafirullahal azeem" Ta samu kanta da maimaitawa tana tuna wannan kalmar.....wannan kalmar ita ta dinga ji haisam din yana yawan maimaitawa,wannan kalmar a yau batasan adadin sau nawa ta jita a bakinsa ba.

Ta sake lumshe idanunta komai yana dawo mata sabo. Tun daga tasowarsu daga agadez,Niamey,jidda zuwa cikin haram.

Dawafinsu da komai daya gudana a tsakaninsu yau din. Gyara kwanciyarta tayi zuwa rigingine tana zurfafa tunaninta.

"Wayeshi......wannan rayuwar batayi kama da wanda aka yiwa alfarma ba" Ta motsa labbanta a hankali tana fadi. Tuna komai take in details,tuna yadda yake gudanar da komai da yanayin sabo na mu'amala da komai da komai ma. Akwai yanayi sosai daya bayyana sabo da rayuwa me tsada a tattare dashi.....akwai yanayi daya bayyana gogewa da iya mu'amala da mutane.....akwai yanayin da yake haska wani abu a tare da dukka motsinsa......yanayin dake bayyanawa idanu kaman ya saba hulda da manyan mutane.

Ta yaya zai iya ganin manyan malaman harami haka idan har shi din ba wani bane?. Tambayar data sanyata miqewa sosai ta zauna tana rungume da pillow a qirjinta. Idanunta suna juyawa tsakanin dan haske da duhun dake gauraye a dakin.

Wani irin shuru taji cikin kanta,ta juya qwayar idanunta tana jin sautin muryarsa yana dawowa cikin kunnenta.

Ta lumshe idanun tana sake bibiyar kowanne sauti.... Kowacce magana da yayi mata a yau din.

Yana da wata irin murya me taushi.... Mai sanyi sannan kuma me zurfin gaske da idan ya maka magana kakejin saukarta kai tsaye saman zuciyarka. Wata irin murya da idan ta jita koda da kalma daya take ne sai taji zuciyarta ta buga. A hankali ta sake lumshe idanunta tana wassafa fuskarsa cikin gizanniyar idanunta.

Giant ne.....ta dade da lura da wannan....wani irin giant da tsaiwarsa kawai tana iya daukan hankalin diya mace,saboda murjajjen jikin da yake dashi,wanda ta dade tana kyautata zaton ma'abocin motsa jiki ne da daga qarfe daga yanayin structure din jikinsa duk da bata taba ganinta a sarari ba.

Tana iya tunawa da dogayen hannayensa masu dogon yatsu da suka sha tareta daga shan kayi daga dawakinta. Wani irin dogayen yatsu da suke mata kama dana mutumin daya saba da iko. Motsinsa bame sauri bane......amma kuma yana da wani irin control da zafin nama idan yaso.

Idanunsa sune mafi daukan hankali,manya ne ita kanta shaida ne akan wannan,amma ta lura wani lokacin daga shine?,ko halittarsu ce a haka?,sukan rage girma su lumshe sosai,har sai kayi zaton bacci yakeji,akwai wani irin calm intensity a tattare dasu me yawa. Sau tari idan ya kalleta,sai taji kaman yana ganin fiye da abinda ke saman fuskarta,har cikin jininta da jikinta tana jin yana da wani kebantaccen baiwa na iya karantar yanayin mutum ta cikin idanunsa,wannan yana daga cikin dalilin daya sanya take kaucewa dogon kallo daga gareshi.

Eyebrows dinsa da suka kusa hadewa da juna......hancinsa daya zauna sosai saman fuskarsa.....shi ba siriri ba kuma shi bame fadi ba,ya hade duka siffofin guri guda.

Ta lura dashi.....baya da yawan murmushi,amma aduk sanda yayin sai fuskarsa ta sauya da wani sirrin boyeyyen kyau da a iya lokacin murmushin kawai yake bayyana. Kawai komai nasa yana sake fadi da wani irin murya me nauyi da qarfi cewa he's not an ordinary man........amma me yasa ta gaza gane komai a kansa?,ta gaza gane ainihin wayeshi?.

Lips dinsa data tuna saida dukka tsigar jikinta ta tashi,wani abu ya motsa mata sosai cikin jikinta wanda batasan dashi ba,saita samu kanta da curewa guri daya,ta matse pillow din cikin qirjinta sosai tana tuna yadda dumin hannunsa ke bibiyar kowacce jijiya ta jikinta da wani irin sauri ya sauke mata kasala da gajiya.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Wani irin mirginawa tayi tana girgiza kanta.

"Why akhnan?.....me yasa?....me yasa?" Ta tambayi kanta tana girgiza kai.

Ko sau daya a farke ko a sarari bata taba zama irin haka tana wassafa wani d'a namiji ba tunda take. Ba wani d'a namiji data taba zama tama tuna da cikakken sunansa bama nasabarsa ballanta siffofinsa. Ba wanda yayi wannan isar.....ba wanda matsayinsa yakai...me yasa saishi?.

Wannan malamin?,wannan mutumin daya fara karya kusancinta da sultane,ya canja mata table na rayuwarta ya mallaketa da dukkan mugunta?.

Ada idan ta tuna hakan ciwo takeji.....baqinsa take gani,amma a yanzun duk da zuciyarta ta maimaita mata sai taji bataji komai ba,bataji komai ba sai wani irin yanayi dake mamayarta.....bataji komai ba sai wani abu me kama da kewar idanunsa.....kewar muryarsa da wannan miskilancin nasa.

Ta tabbatar a yanzun dare ya soma nisa,yadda kuma suka kwaso gajiya dole shima ya kwanta ya huta. Wani bushewa maqogoronta taji yayi,ruwa taji tana da buqatar sha,wani yanayi ya saukar mata da wata irin matsananciyar kasala a jikinta,saita zare pillow din,ta jawo jiki ta sauko daga saman gadon,ta saka hannunta tana tattare gashinta ta daure cikin scarf mahadin kayan baccin,sannan ta fara takawa zuwa living room din.

A nutse ta bude qofan ta soma fitowa tana mamakin labulen fuskar ka'aba dake a bude,wannan yasa living room din baiyi duhu sosai ba,don haka bata buqaci kunna haske ko daya ba taci gaba da takawa tana duban sashen da yake tarwai da fitilun haram da basa dusashewa ko daukewa.

Sai a sannan ta lura dashi,shine a zaune saman daddumar dake shimfide gaban gurin wadda ke dauke da tambarin hotel din. Cikin sujjada yake,wata doguwar sujjada da har ta dauko ruwan ta dawo tazo ta wuce bai dago ba. Haka ta dinga satar kallonsa har ta koma cikin dakin.

Zama tayi gefan gadon,ta bude ruwan ta riqe a hannunta. Baya gajiya?,shikam baya gajiya ne?. Haka kawai takejin kamar ya mata wayo,tana nan zata kwanta tayi bacci amma shi ya gagara baccin.

"To amma.....na gaji" Ta fada can qasan ranta.

"Kisha ruwan ki kwanta,saiki tashi da wuri kafin asuba tayi" Zuciyarta ta bata shawara. Saidai koda tasha ruwan ta koma ta kwanta baccin kasa zuwa yayi. Tsintar kanta tayi da tashi a hankali,ta jawo qofar baya ta soma leqensa ta tsakanin space din.

A yanzun a zaune yake,qur'ani ne kuma a hannunsa sautin karatunsa yana fita can qasa da wannan sautin nasa dake kusan narkar da zuciya. A hankali ta maida qofar ta rufe sanda yakai qarshen surar da yake karantawa,ta koma da baya a hankali har zuwa saman gadonta.

Pillow ta sake riqewa sosai tana sauke ajiyar zuciya,kafin ta tashi a hankali ta bude jakarta. Littafinta na tarihi ta dauko,tarihin fiyayyen halitta,littafin data kammala na farko ta dauko wallafar ibn taimiyya,sai kawai ta kunna fitilar gefan gadonta ta matsa rub da ciki ta bude ta dora karatu.

Batasan adadin awannin data kwashe ba a zaune,don ko bacci cikakke bata ji,tasan dai ta fada wata duniya daban da wadda take ciki. Zata iya cewa karatun a yau ya mata amfani fiye da kullum,saboda gata a gurin,gata a kusa da inda komai ya wakana na tarihin rayuwarsa. Taga abubuwa masu yawa,taga gurare masu muhimmanci gurin amsa addu'a,ta sake fahimtar abinda ya sanya haisam din bai yarda ya kwanta yayi cikakken barci ba. Sai taji gaba daya ta sake daura tata damarar,sai taji kaman duk zuwan da takeyi umra a baya kaman wasa ne,wannan zuwan.....wannan lokacin shine sahihin lokacin zuwa na gasken gaske.

*_W A S H E G A R I_*

Duka washegarin basu hadu dashi ba,tun daga asuba har zuwa dare,don ita dimma washegarin saita zamar mata kamar an mata allura an kuma sake qara mata qaimi akan ibada.

Sam bata huta ba,kusan yini tayi cikin haram tana addu'o'i. Har addu'ar da bata dauka cewa zata iya ba. Addu'o'in da bata taba kawowa a ranta wataran zata roqa ba. Shi take kalla a sanda yake zaune yake kuma dadewa saman abun sallah hannuwansa a sama. Wannan ya mata tasiri qwarai,ya kuma cire mata qyuya da ganda na dogon zama tana addu'a. Tayi zaman addu'ar da tunda take a rayuwarta bata taba irinsa ba. A hankali sai takejin wani tarin nutsuwa suna shigarta.

Bayan sallar la'asar ne birra ta iskota,tana zaune a lokacin tana hutawa kawai bayan ta shanye ruwan zam zam cup har biyu.

"Yallabai yace.....bayan sallar isha'i zaku qarasa sa'ayinku" Kadan ta daga kai ta kalleta,kaman ta tambayeta inda ta ganshi sai kuma ta fasa ta daga mata kai kawai.

Sai datayi sallar isha'i sannan ta wuce masaukinsu. Ta buda qofar ta tura,ba alamun akwai mutum cikin suit din nasu.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽