Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 21

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 21

.....do it on your husband except for the sacrifice of blood or something important to you. And the easiest thing for you is to sacrifice your womb!" Ayshatu was silent, feeling as if a stone was pressed on her chest. The old woman moved very close, saying "Sacrificing your womb will ensure that all the love you have for your husband is gone. Did you? As for his work, we spent seven days here in this house. They do not pray, there is no mention of God, there is no purity. Until we finish, then you will see how I will get this new bride on her feet - and your husband will return to you with his perfect love." Ayshatu looked at the old woman again, feeling how the fear in her heart began to change into a kind of calmness. She took a deep breath, and smiled with love and strength. I will do whatever you need - because As'ad is very important to me. I don't care, I can sacrifice everything if that will make him come back to me." The old woman laughed for a long time, the fire was burning in the room. She supported Ayshatu's hand calmly, saying "I know that you are ready. Stay here, we will start tomorrow. But you.....

Standalone post2,375 words

SHAFI NA ASHIRIN DA DAYA

Ayshatu ta tsaya cikin tsananin tashin hankali, zuciyarta na bugawa kamar ta tsage. Cikin duhun dakin, tsohuwar ta cigaba da kallon ta da jajayen idanunta masu cike da mugunta. Wuta mai ?yalli tana ci gaba da kuna a tsakiyar dakin, tana fitar da haya?i mai ?amshi mai nauyi.

Tsohuwar ta matso kusa da Ayshatu, tana murmushi da wani irin yanayi na tsoro, tace "Nasan komai game da ke, Ayshatu. Na san duk abinda yake faruwa akan sabuwar amaryar mijinki kike nan ko? Ai tuni sun gama aikinsu. Sun yanka sun sadaukar da jini, sun mallake zuciyar As'ad. Aikinsu mai ?arfi ne sosai - sai sadaukarwa mai ?arfi kafin a kwace shi daga hannunsu."

Ayshatu ta ji wani irin sanyi ya ratsa cikin ?ashinta. Cikin rawar murya, ta ce "Ko nawa ne zan bayar! Amma banda abunda zan sadaukar yanzu bana haihuwa, ban da wanda zan bayar. Ina son mijina har abada, bana son wata soyayya ta shiga tsakaninmu."

Tsohuwar ta ?an yi dariya mai sanyi, tana jinjina kai "Ayshatu. Amma duk wani iko da aka yi akan mijinki sai dai sadaukarwa -yanka na jini ko kuma wani abu mai muhimmanci gare ki. Kuma mafi sauki a gare ki Shine ki bada sadaukarwar mahaifarki!"

Ayshatu ta yi shiru, tana ji kamar an danna mata dutse a ?irji. Tsohuwar ta matsa kusa sosai, tana cewa "Sadaukar da mahaifarki zai tabbatar da cewa duk wata soyayya da aka mallaka wa mijinki ta ?are. Kinji? Aikinsa kuwa, sai munyi kwanaki bakwai munayi, a nan cikin gidan nan. Bazakiyi sallah, babu ambaton Allah, babu tsarki. Har sai mun kammala, sannan zaki ga yadda zan fitar da wannan sabuwar amaryar da kafafuwanta - mijinki kuma zai koma gare ki da cikakkiyar soyayyarsa."

Ayshatu ta sake kallon tsohuwar, tana jin yadda tsoron da ke ranta ya fara canzawa zuwa wani irin natsuwa. Ta ja numfashi mai nauyi, sannan tayi murmushi mai cike da kauna da ?arfi "Indai wannan ne, ai bana jin matsala. Zanyi duk abin da kika bukata - domin As'ad yana da matukar muhimmanci a gare ni. Ban damu ba sadaukar da komai ma zan iya idan hakan ne zai sa ya dawo gare ni."

Tsohuwar ta yi dariya mai tsawo, wuta na ?ara buguwa cikin dakin. Ta tallafi hannun Ayshatu da natsuwa, tana cewa "Ai na san cewa kin shirya. Ki zauna nan, zamu fara gobe. Amma ki sani, babu mai fita daga wannan gidan har sai an kammala aikin. Zaki sha wahala, amma idan kika tsallake wannan gwagwarmaya, duk wata mace da ta kuskura ta shiga tsakanin ki da mijinki zan halakar da ita!"

Ayshatu ta ?an lumshe idanuwa, tana jin wani irin ?arfin zuciya na shigarta. Cikin zuciyarta, ta san cewa wannan matakin da ta ?auka ya wuce hankali, amma soyayyar da take yi wa As'ad ta sa ta yarda da wannan hadaya.

******

Tafiya suke cikin tsananin izza da kasaita, suna sauka daga motar Rolls-Royce Cullinan mai launin toka mai kyalli, direban ya bu?e ?ofa da girmamawa. As'ad ya fito cikin farar babbar riga ta Shadda hula mai adon azurfa, takalmin fata na Tom Ford, yana tafiya cikin izza da natsuwa. Amaryarsa, Haneefah, tana gefensa cikin shiga ta alfarma riga da zani na Lace mai launin ruwan madara da Alkyabba ba?a aji?inta.

Sun shiga cikin falon fadar, As'ad ya dur?usa cikin tsananin girmamawa ga mahaifinsa, ya tsuguna tare da rusunawa kamar yadda ake yi wa mai martaba. Cikin ladabi da murya mai laushi ya ce "Assalamu Alaikum wa rahmatullahi ya Mai Martaba, ubanmu kuma sarkinmu, Allah ya ?ara maka girma da daukaka."

Mai Martaba ya yi murmushi mai natsuwa, yana amsa cikin farin ciki "Wa'alaikumus salam As'ad, ka tashi. Na ganka cikin kwanciyar hankali. Amma yanzu zaka koma birnin tarayya da amaryarka? Na zata ka tsaya a nan saboda kasuwancin ka na gida."

As'ad ya tashi cikin kamewa da izza, yana magana cikin natsuwa "Hakane, Mai Martaba. Amma akwai taruka na kasuwanci da dole na halarta a Abuja, tare da wasu manyan kamfanoni masu zuba jari. Kuma na yanke shawarar tafiya da Haneefah domin cigaba da sabuwar rayuwar mu. Insha Allah, zan kula da ita kamar yadda aka tsara."

Sarki ya ?an gyada kai, yana mai fahimtar dabarar As'ad. Yasan cewa As'ad yana da sanin ya kamata kuma yana da ikon tafiyar da kasuwancinsa ko ina. Ya kalli Haneefah, wacce ta dur?usa da girmamawa, ya ce "Allah ya albarkaci tafiyarku. Haneefah, ki kasance mai biyayya ga mijinki, ki nuna masa kauna da kulawa. Kai kuma As'ad, ka tabbatar da cewa ka kula da ita kamar yadda aka saba a gidan sarauta."

Sun nufi bangaren Hajja, matar sarki ta biyu, wacce ke zaune cikin falo mai yalwa. An kawata falon da kujerun fata masu launin coffe da labulen siliki na Dior. Haneefah ta dur?usa cikin ladabi, tana cewa "Hajja, mun zo muyi sallama."

Hajja ta yi murmushi mai natsuwa, tana kallon As'ad da Haneefah da kulawa. "Allah ya kiyaye hanya. Haneefah, ki ri?e mijinki da kyau. As'ad, ka kula da amaryarka. Allah ya sa kuyi zaman lafiya." Tafada tana kallon yadda gabadaya hankalin ?an nata ke ?an haneefa gaba daya yamakasa magana har suka bar gurinta.

Daga nan suka shiga bangaren Fulany Maryam, wacce take cikin shiga ta alfarma riga mai launin baki. Tana kallon Haneefah da murmushi, tana cewa "Haneefah, kisani zamantakewar aure tana bukatar hankali. Ki kula da magungunan da na baki, kada ki yi sakaci. Ki tabbatar cewa kin bi duk umarnina don ki samu zama mai nagarta a gidan mijinki."

Haneefah ta amsa cikin biyayya "Mama, insha Allah zan bi duk umarninki. Zanyi yadda kika ce."

Sun fita cikin tsari da izza, suna tafiya zuwa filin jirgin sama a cikin motar Mercedes-Maybach S650 mai launin kore. Jirgin masarauta - Bombardier Global 7500 Private Jet yana jiran su. Suna shiga, aka gaishe su cikin kulawa, sannan suka zauna a cikin kujerun fata masu laushi, yayin da masu hidima suka kawo kayan sha na alfarma.

As'ad ya kalli Haneefah yana cewa "A nan Abuja ne zamu ci gaba da rayuwa, zan tabbatar da cewa komai ya kasance cikin tsari da alatu kamar yadda aka saba. Ki kasance mai biyayya kamar yadda kike yanzu."

Haneefah ta yi murmushi mai kyau, tana jin zuciyarta na farin ciki. Jirgin ya tashi daga Zaria cikin nutsuwa, yana nufin birnin tarayya Abuja, inda sabon zamani na soyayya da iko zai cigaba.

Jirgin masarauta ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport cikin nutsuwa da tsari. A waje kuwa, tawagar motoci na alfarma sun tanada, babu abin da aka gani sai jerin motocin Mercedes G-Wagon guda biyar masu launin ba?i mai kyalli, da kuma wani babban Range Rover Autobiography a tsakiya.

Haneefah ta fito daga cikin jirgin, tana kallon motoci da tawagar da suka taho don tarbarsu. Cikin tsananin mamaki da ruduwa, ta yi shiru tana nazari. Duk da cewa ta san As'ad yana da kudi fiye da sauran 'yan uwansa, sai da wannan al'amarin ya bata mamaki sosai. Cikin zuciyarta, tana tunani "Ashe As'ad yana da kudi fiye da yadda nake tunani! Na dade ina jin labarinsa, amma yau na tabbatar!"

Daya daga cikin direbobi cikin rigunan manyan dogarai ya bu?e ?ofar motar a girmamawa, yana cewa "Barka da zuwa, Hajiya Haneefah. Muna murna da zuwanku."

Ta shiga motar cikin kamewa da izza, tana jin tamkar ta isa wani wuri mai alfarma. As'ad kuwa yana magana da wani daga cikin masu tsaro kafin ya dawo ya shiga motar tare da ita. Haneefah ta kalli fuskarsa tana murmushi, tana jin kamar ta cimma mafarkinta.

Tafiyar ba ta yi nisa ba kafin su isa gidan wani katafaren gida mai tsawo da aka zagaye da babban ganuwa mai launin fari.A kofa, akwai tsararrun dakunan masu gadi masu sanye da kayan tsaro na alfarma, suna tsaye cikin izza.

Bayan motoci sun kutsa cikin farfajiyar gidan, an bu?e ?ofar babbar falon da alama mai ku?i ne ya gina - ko'ina zinariya da ?amshi na turaren Creed Royal Oud ya mamaye. Harabar gidan cike take da fulawowi masu kala-kala da fure-furen alfarma.

As'ad ya fita daga motar cikin kamewa, yana duban fuskarta yana cewa "Maraba da zuwa gidan ki, Haneefah."

Ta yi murmushi amma har yanzu kanta a ?aure yake. Da yake ita ta taso daga gidan kudi amma wannan gida ya fi komai da ta ta?a gani. Tsan-tsan kauyanci ya bayyana a fuskarta duk da cewa tana ?o?arin ?oye.

As'ad ya juya yana kallon daya daga cikin dogarawan dake tsaye a kofar wani babban sashe mai launin toka da zinariya. "Ku tabbatar an kaita bangaren ta. A nan ne zata zauna."

Ta dan matsa kusa da shi tana cewa "Kana nufin na shiga bangaren ka ne ko?"

Wani daga cikin masu tsaron gidan ya tsaya, ya ce da ladabi "Hajiya, a gidan sarauta, sai miji ya amince kafin amarya ta shiga turakarsa. Anan mulki da tsari na gado ne."

Haneefah ta ?an yi tsaki cikin ranta, tana jin wani iri. Duk da cewa ta san tsarin sarauta yana da tsauri, bata zaci haka ba. Dole ta bi ka'ida kafin ta shiga dakin mijinta.

Suka shiga wani katafaren bangare mai yalwa wanda aka tanada don ta. Dakunanta ya cika da kayan alfarma gado mai babbar murfin mudubi, fitila mai kyalli na krista, da manyan madubai na Louis Vuitton. Ta tsaya tana kallon ko'ina, tana mamakin yadda dakin yake da kyau fiye da tunaninta.

Lokacin da ta dube ta taga daga baranda, sai ta hangi wani bangare na gidan da aka yi da alamar tsari da tsabta. Wata dogara ta le?o cikin ladabi tana cewa "Hajiya, wannan bangaren na Uwargida Aysha ne."

Ta dan yi tsaki cikin zuciyarta, tana tunanin yadda zata samu hanyar cire wannan mata daga gidan.

Ta yi wanka sannan ta shafa turaren asiri na musamman da Fulany Maryam ta bata wanda aka ce yana kashe duk wata soyayya ta daban da zata shiga tsakanin ta da mijinta.

"Hajiya, muna yi miki barka da zuwa. Mune masuyi miki hidima daga yanzu."

Ta yi murmushi mai dauke da izza, tana kiran wayar As'ad, amma bai dauka ba. Zuciyarta na kara tsananta da gajiya, tana jin cewa dole ne ta tabbatar da cewa babu wata mace da zata kuskura ta shiga tsakanin su.

***** As'ad ya shiga bangarensa, zuciyarsa cike da wani irin yanayi na rashin nutsuwa. Duk da yadda dakin yake a tsare tsaf tsaf da kamshin turaren Creed Royal Oud mai cike da sanyin zuciya bai ji kwanciyar hankali ba.

A hankali ya cire rigarsa, ya shiga wanka don kwantar da hankalinsa. Yayin da ruwan ke malala a jikinsa, yana jin tamkar wani nauyi ya ragu daga jikinsa. Da ya gama, ya sanya jallabiya mai launin toka mai taushi, ya feshe jikinsa da turare na Tom Ford Oud Wood.

Ya kwanta a gado, yana jin yana bukatar hutawa,Atake bacci mai nauyi ya dauke shi ba tare da ya shirya ba. Bai farka ba sai wajen karfe hudu, yashiga mamaki yadda ya yi bacci har ya wuce lokacin sallah. Shi da bai saba barin sallah a jam'i ba, amma yau sallar ya kasance a dakinsa.

Da zarar ya gama sallah, sai wani yanayi na rashin nutsuwa ya sake kamashi. Bai iya jurewa ba, sai ya sa takalmin fata mai sauki, ya fito zuwa bangaren Haneefah.

Tunda ya kusanto bangaren, masu aikin da aka tanadar mata suna gaishe shi da girmamawa, suna daga kai cikin ladabi. Yana shiga, ya hango ta daga cikin dakin nata mai kyau, tana zaune a gaban babban madubi mai haske, tana shafa jambaki mai ja a le?enta.

Ta dan yi murmushi tana kallonsa ta madubi, sannan ta juya kanta gefe kamar mai jin haushi. As'ad ya ?an yi murmushi yana kallon yadda take ha?a fuska da tsare jikinta cikin shigar abaya mai launin ruwan madara, da gyale mai kyalli na zinariya.

Ya matso kusa da ita cikin salo, yana cewa da murya mai laushi "Haneefah, nadanyi bacci ne Ki yi hakuri."

Ta ?an yamutsa fuska tana tsaki a hankali, tana cewa "Ni kam ba matsala, ai dama haka kake. Kaga yadda ka barni Ni ?aya Tun safe?"

Ya ja numfashi cikin sanyi, sannan ya dur?usa a gabanta, ya ?auki hannunta cikin natsuwa. "Ki yi hakuri. Ban yi nufin takura ki ba. Ki gafarce ni."

Tana jin murya mai laushi daga bakinsa, sai tsananin so ya mamaye zuciyarta. Ta ?an yi murmushi, ta ce "Yanzu na yafe maka, amma fa ka yi min alkawari cewa ba za ka sake ba."

As'ad ya kalle ta, yana ganin yadda kyanta ke ?ara bayyana a ?ar?ashin hasken fitila. Bai jira amsar ta ba, ya matso kusa da ita, yana kamo hannunta da salo, ya ja ta ta zauna a kan cinyarsa.

Ta ?an yi dariya mai laushi, tana ?ara matse jikinta a jikin sa. As'ad ya rungume ta, yana jin yadda numfashinta ke tsananta. Haneefah ta sa hannunta a wuyansa, tana zagaye masa gashinsa cikin natsuwa.

Ya dube ta da ido mai cike da soyayya, yana cewa da murya mai laushi "Kin san kina da kyau, ko?"

Ta lumshe idanu, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. Ta matsa da fuskarta kusa da shi, tana jin kamshin turaren sa yana narkar da zuciyarta. Hannunta ya gangaro zuwa ?irjinsa, tana shafar jikinsa da laushi, tana jin yadda sanyin fatar sa ke tsuma zuciyarta.

A hankali ya sa hannu a cikin gashinta mai laushi, yana ?an ja da salo, sannan ya sumbaci goshinta cikin tsananin nutsuwa. Tana jin yadda hakan ya shiga jikinta, ta rungume shi sosai, tana jin tamkar ta narkar da kanta cikin jikin sa.

Ya ?aga fuskarta da hannu biyu, yana kallon idanunta masu kyalli, sannan ya ce cikin murmushi "Kin san ke ce farin cikina? Babu wata mace da zata iya shiga tsakanina da ke."

Ta yi murmushi mai cike da jin dadi, tana lumshe idanu, sannan ta kai bakinta zuwa nasa, suna jin yadda zuciyoyinsu ke bugu da sauri. Ya sauke numfashi mai nauyi, yana jin wani irin farin ciki na musamman ya lullube shi.

"Ni fa, Haneefah, ban taba jin irin wannan soyayya ba. Kina da wani irin salo da ke sa na kasa jurewa," ya furta da gaske. Hankalin As'ad gaba daya ya fita daga hayyacinsa, yana jin yadda Haneefah ke sarrafa shi da salo mai dadi da soyayya.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH