
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 29
.........it is not the original of everything. Everything has changed in some way. She turns them and looks again, everything is in a certain order and it is impressive, as everything shows its original price. The wind blew gently, she noticed the difference, she was surprised to hear herself, but she thought it was Birra's plan. Today, in the midst of drought, she prepared herself. The white background is like some kind of shiny stones and silver water that changes the light and everything that reflects them. She wore silver ash snickers and covered herself with a Malaysian hijab, also the same color. She looked at herself in the mirror and she closed her eyes, a smile came over her, a kind of cold smile. She never knew that this type of dress would look good on her until now, she never knew that it would be one of the clothes that would fit her body until now. She went back and checked the time, set the clock and went out of the living room and found a lemon tree before they passed. The phone was stuck in his ear because he left his Bluetooth in the room, that's when he came out of the bath and she called him. He picked up the phone but the thirst.....
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 29*
"Ki shiryamin komai ki wuce,zan qarasa shiryawa da kaina" Tace da birra tana zare qaramin hijab din data dora saman abayar jikinta. Karon farko da tayi ta'ammali da hijab har haka a rayuwarta,wadannan hijabs dinma data gani cikin kayanta batasan waye ya dinkosu ba. Haka kawai taji a yau din tanason shiryawa da kanta,kaman bai dace ba kuma birra ta wanzu a suit din nasu ba.
"Wai fa...." Ta fada tana duban birra dake shirin wucewa ciki.
"Hijabs dinnan fa?" Qasa birra ta danyi da kanta tana sake boyayyen murmushi.
"Ba iya su kadai ba.....duka kayan cikin luggage din......dama wanda na shigo miki dasu dazu,sheikh muhammad ne...."
"Ya isa" Akhnan ta fadi a nutse tana miqewa,sai birran bata sake cewa komai ba ta wuce ciki itama ta bita.
A baya bata damu da tsaiwa duba komai ba,amma a yanzun bayan ta fito a wankan saita samu kanta da bin komai da kallo.
Abayas din....hijabs.....bathsetdinta......set na mayukanta dama komai......ba asalin komai nata bane. Komai ya canza da wani irin tsari. Juya su take tana sake kallo,komai cikin wani tsari yake da burgewa,kaman yadda komai din yake nuna asalin tsadarsa.
Iska ta fesar a hankali,ta lura da banbance babancen,tayita mamaki ita kanta a karan kanta,amma ta dauka shirin birra ne,saidai ko data raya hakan a ranta ta danyi kokwanto,yaushe birra tasan abubuwa masu tsada irin haka?.
Yau cikin shigar fari ta shirya kanta. Farar baya ce me wani irin duwatsu masu sheqi da walqiya ruwan silver dake cancanza kaloli da duk abinda yayi reflecting nasu. Silver ash din snickers ta saka,sannan ta rufe kanta da Malaysian hijab shima daya kasance color din. Ita kanta data kalli kanta da kanta a madubi saida ta lumshe idanu,murmushi ya qwace mata,wani irin murmushi me sanyi. Bata taba sanin irin wannan shigar zata mata kyau ba sai yanxu,bata taba sanin zata zama daya daga cikin suturu da zasu dace da jikinta ba sai yanzu. Taja da baya tana duba lokaci,saita yanke ta fita ta living room din ta samu koda lemo ne tasha kafin su wuce.
Waya ce maqale a kunnensa saboda barin Bluetooth dinsa da yayi a daki,fitowarsa kenan daga wanka khansaaa ta kirashi. Ya daga wayar amma qishirwar da yakeji ta tilasta masa fitowa neman ruwa sannan ya koma ciki ya shirya.
Daure yake da farin towel,fari qal dashi me matuqar laushi. Daga qugunsa ya daureshi sosai,ya kuma tsaya masa iya qasan gwiwoyinsa.
Faffadan qirjinsa.......dogaye kuma tsayyayun qafafunsa.......yalwatacciyar kafadarsa......lallausar gargasar dake kwance saman qirjinsa dama duka sassan jikinsa sun bayyana suna zamewa fatarsa me cike da sulbi da wani haske na musamman ado. Shafaffen cikinsa ya taimaka wajen bayyanar qirjinsa dake cike da muscle,da wasu muscles din dake lullube da fatar saman shafaffen cikinsa.
Bai kula da ita ba kaman yadda bata kula dashi ba,don ba magana yakeyi ba yana dai sauraren khansaaa ne kawai kaman yadda al'adarsa take sauraro kafin yayi nasa bayanin,yana kammala zuba ruwan ya soma rufe gorar ruwan,daidai sannan ta daga idanunta daga latsa wayarta da takeyi cike da mitar ba wanda ya kirata tun daga jiyan zuwa yau?. Koda sultane kuwa?,koda aisa?,koda shehnaz?.
A hankali ta daga idanunta don ganin inda zata zauna,saidai maimakon ganin gurin zama sai idanunta sukayi wannan kyakkyawan ganin,daidai sanda shima ya aza idanunsa cikin nata.
Hannayenta ne suka dauki rawa,ta furta.
"Subhanallah" Da dan raunin murya muryartata tana shaking,sannan ta juya da sauri tana bashi baya,juyawar data sanya wayar hannunta sulalewa ta fadi a qasa.
Idanu ya zuba mata ta baya yana karantar yadda ta rude duka lokaci guda.
"Zan kiraki.....minti daya" Yace da khansaaa,sai ya zare wayar daga kunnensa ya kashe ya ajiye saman dan table din dake kusa dashi.
A nutse ya taka zuwa saman daya daga cikin kujerun,ya dauki bathrobe din dake ajiye gefanta ya zura ya kama igiyoyin ya daure ba tare da yace da ita komai ba.
Wata irin kunya cakude da wani nau'in tsoro ne suke dabaibayeta. Wani yanayin buguwa zuciyarta keyi tamkar wadda tayi tseren gudu na kilometers masu yawan gaske.
"Banyi tsammamin zaki fito ba" Ya furta a hankali don ya bata relief daga yanayin daya lura ta shiga,don har yanzu jikinta rawa yake idan ka lura sosai.
"N....nima b....ban sani ba" Ta amsa mata muryarta na rarrabewa saboda bugun da zuciyarta takeyi.
Taku kadan yayi ya isa bayanta don ya dauki daya towel din dake gefanta saboda tsane damshin sumarsa.
"Kina iya juyowa". Dab da ita ta jishi,dab da itan da takejin ko yaya ta juyo tabbas cikin jikinsa zata fada,saita kasa motsawa,qamshin shower gel dinsa yana buso mata a hankali,saita lumshe idanunta tana jin zuciyarta kamar tana shirin rikitowa daga qirjinta. Ya dauki towel din a nutse ya taka yana matsawa daga gurin. Wayarsa ya koma ya dauka sannan ya nufi qofar dakinsa yana shirin sake kiran khansaaa.
Ajiyar numfashi ta dinga saukewa a jejjere,ta saka tafin hannunta tana dafe qirjinta a hankali,sannan taja jikinta ta zauna saman kujerar.
"Wai Allah na..." Ta fada tana zare idanu,sai kuma murmushi ya qwace mata,kafin kuma a hankali idanunta ya sake dauko mata hoton yadda ta ganshi.
"lean, well-built body" Ta furta a hankali,sai kuma ta kama bakinta tana rarraba idanu.
"Me ya kaiki?,ina ruwan ki da jikinsa?,idan ya jiki kuma fa?"
"Baiji ba bazai kuma ji ba in sha Allah" Ta fada tana qoqarin ture tunanin ta hanyar kiran shehnaz,saidai kuma hoton ya kasa barin idanunta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Haka jikinsa yake?" Taci gaba da fada cikin ranta. Favorite qirar da tasha kwatanta son samu jikin namiji,saidai abinda ya fara sare mata shine.....yawan mazan da muke dasu a qasashenmu basu maida motsa jiki a bakin komai ba. Kusan dukkaninsu qirar jikinsu irin na matansu ne.....damtsen miji da mata duka baka banbancewa kusan iri daya ne. A nata tsarin.....a nata ra'ayin komai na mijin da takeso ya zamana yasha banban dana mace.....asalin qira da siffar jarumta sosai,jarumi takeso....zakin gaske.....amma kuma" Saita dakata da tunanin a ranta kadan.
"Akwai wasu siffofi kaman....." Nanma ta katse tunanin kamar me tsoron tattaunawar yau da zuciyartata ma.
Jin muryar sultane ya yanke kowanne tunani daga ranta. Cikin doki kewa da qauna ta soma gaidashi. Daga nasa bangaren ya fita farinciki da jinta.
"Komai lafiya ko?,duk da muhammad ya tabbatar min" Kai ta daga tana murmushi.
"Lafiya alhmdlh....bappi ka manta dani,baka nemeni ba" murmushi yadan saka me sauti kadan.
"Inde muhammad ya kirani muka gama waya lafiya dashi,to na tabbatar kema lafiya kike".
"Amma bappi....kana lafiya?,muryarka si faible(so weak)" Murmushi ya sakeyi,tabbas idan yaje yana jinsa lafiya lau a kwanakin to yayi qarya,amma kuma ba buqatar ya gaya mata hakan. Nutsuwarsu da sake gamsuwa da zama da junansu yafi buqata a yanzu,ba wani buri da yake dashi sama da wannan a yanzu.
"Lafiya qalau nake,ina hutawa ne kawai" Kai ta daga a hankali. Hira kadan sukayi ahmad almaz ya karba.
Taji dadin magana dashi sosai,yayi magana da ita kaman yadda yaya zaiyi da qanwarsa,wani feeling wani yanayi data rasa a yanzun data sameshi sai takejin kamar ta fara zama completed.
Daga nan shehnaz ta kira,tana kira din kuwa ta daga kamar zaman jiranta takeyi.
"Ina da niyyar nemanki kenan kiranki ya riga nawa shigowa".
"Me ya faru?" Tambayi shehnaz din daidai sanda qofar dakinsa ta bude ya fito.
Da sauri ta yiwa kanta linzami ta hanyar zare idanunta daga inda yake takowa. Ta yiwa kanta alqawari ba za'a sake maimaita abun jiya ba duk yadda zaikai gayi mata kyau,saita tattara hankalinta akan shehnaz.
"Kwana aisa tayi tana kuka.....ta iso cikin wani yanayi daya daga hankalina. Sahel couture ya samu matsala biftu......dole ne na gaya miki wannan saboda kina gurin da ake amsar kowacce addu'a ta alkhairi. Anyi asarar maquden kudaden da idan ba wani ikon Allahn ba sahel ya tsaya da aiki har abada......tace batasan ya akayi ba,amma dukka kudaden sun fita dasa hannunta ne da sahalewarta,batasan kuma ya akayi haka ta faru ba......mammina ta yanke hukunci.......ta dakatar da aisa.......ta kuma ce zata kafa committee na bincike a kanta......kuma zata fuskanci duk hukuncin da aka tanada akan wanda irin haka ta faru ta sanadinsa". Wani irin sanyi hannu da qafafuwan akhnan sukayi.....wani irin yanayi da ta gaza tantance ame take?.
Aisa kuma?......aisa dai?. To me zatace?,me zatayi?. Sahel couture din daya zama alfaharin sultane?,sahel couture din data dauki alqawarin saita kaishi matakin da sultane sai yayi alfahari da mallaka mata shi din da yayi?,to me yake faruwa haka?.
A hankali taji an zare wayar daga hannunta,don dama a handfree take amma da lower volume bame qarfi ba. Daga idanunta tayi a hankali sai ta bishi da kallo,yana tsaye a gabanta,ya kuma sanya wayar a kunnensa. Tana jin sallamarsa da yadda shehnaz ta amsa da sauri ta fara gaidashi.
"Ki sanar da aisa.....ni nace ta koma Niamey yau.....ta bude office taci gaba da aiki,duk wanda ya tambayi dalili kome yasa......kice ta fada masa CEO tace ta koma......ki fada mata.....zan nemeta qasa da awa shirin da hudu zamu tattauna" Daga akhnan din har shehnaz mamaki ne ya kamasu.
Shehnaz dai ta sani......ba wanda keda qarfin ikon tada hukuncin mammina duk fadin niger ma ballantana agardez......agadez dinma cikin masarautar da kowa ya sani tana da cikakken iko a kanta?.
Ta dauka zai miqa mata wayarta ne......amma maimakon haka sai taga ya kasheta ya jefata cikin aljihunsa.
"Muje" Ya fada da wata nutsuwa yana dubanta,sai ta miqe tsam ta soma takawa tana wucewa ta gabansa zuwa waje.
Duk da zuciyarta a nauyaye take sosai da tarin tunane tunane,amma hakan bai hanata ganin idanuwan mata sosai akan haisam din ba. Jifa jifa idanunta suna gane mata,saidai abinda bata sani ba shima yana gani?,ko ita kadai take gani?. Still idanunta basu gaza gane mata wannan soyayyar ba.....wannan soyayyar da kake iya ganinta ko ina a sararin masallacin dama gurare daban daban. Ma'aurata cikin shauqin soyayya,wasu da yara wasu babu sai iya su kadai. Wannan yanayin ya dinga debe mata kewa yana ware mata zuciyarta a hankali,musamman da taji lallausan sautin nan nasa yana fadin.
"Allahu akhbar.....Allahu akhbar....subhanallahi wabihamdih......subhanallahil azeem" A sanda suke tattakawa saboda gabatar da sa'ayinsu.
Akan safa suka tsaya kaman yadda tsarin yake,suka fuskanci ka'aba ita dashi. Sukayi dukkan kabarbari da addu'o'in da akeyi sannan suka soma nasu personal.
Ta kammala nata addu'o'in amma tsaiwarsa da irin nutsuwa da take hanga a tattare dashi ya zama wani abu daban.......dukka tsarinta na hanawa kanta satar kallonsa a wannan lokacin ya wargaje. Wani irin kushu'i take hanga da zallar qanqan dakai gaban ubangiji,yanayin daya qara mata qaimi,takejin kamar akwai tarin addu'o'in daya kamata tayi batayisu ba.....kaman tana da sauran buqatu daya kamata ta roqa,kawai sai taji zuciyarta tana narkewa sosai a gurin.
Sake maimaita addu'o'inta take,sai taji wasu suna shiga cikin kanta suna kutsowa ta bakinta. Aisa lamarin sahel duk sai taji kaman ya kamata takai lamarin gaban sarkin sarakuna. Ko meye ya kasance da sauqi.....sahel couture nada matuqar muhimmanci a gurinta.....kamar yadda aisa keda nata tarin muhimmancin.
Da wani irin taushi ya sauke hannuwansa,maimakin ya barsu a qasa a hankali kamar jiya.....da wani sanyi taji ya kusa tafin hannunsa tsakiyar nata. Ta sauke wata irin ajiyar zuciya tana jin nutsuwa na saukar mata. Wani irin yanayi da ta kanji a duk sanda ya riqe hannunta ya fara bin jikinta,suka fara takawa suna gangarawa zuwa marwa da tarin addu'o'i da cikakken koyi da yadda ibadar take.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽