Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 22

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 22

.....she seems to possess him, not only his heart, but also his whole mind. She returned home disappointed. By God, I'm starting to get scared, Hajja." Hajja held her head as she felt how the situation was getting worse. She let out a heavy breath, feeling pain in her heart. She looked at Abba with worried eyes. I begged His Highness but the King said not to force him since they are in peace." "Peace?" Abba took a deep breath in frustration, "Hajja, by the way, this is not peace. Fulany Maryam won. Didn't you hear? Her granddaughter who was in Asubuti died, but she didn't even go to work. If a woman can do this, what will stop her from stealing As'ad's heart?" "By God," Hajja replied, shaking her head, "I am very worried. I know Asad's business and hard work, but now he does not call me, he does not ask for advice, he does not even answer the phone. This is not his character." Abba lowered his voice, y.....

Standalone post1,643 words

SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU.

Arewabook @nanadiso10

Kusan mako biyu kenan babu wanda ke iya samun As'ad. Tun lokacin da ya koma Abuja tare da Haneefah, babu wani labari daga wurinsa. Abin mamaki shi ne, ko Mai Martaba Sarki ya kira wayarsa, ba ya amsawa. As'ad, wanda aka sani da biyayya da mutuntawa, yanzu tamkar ya bar duniya, ya koma bangaren Haneefah kacokan.

Hajja tana zaune cikin falonta mai yalwa, cikin damuwa da tunani. Ta kishin?ide cikin riga mai launin ruwan toka, tana fuskantar Abba, kanin As'ad, wanda ke tsaye a gefenta, cike da damuwa.

"Hajja, wallahi na kira shi sau da dama, amma ba ya ?auka. Har P.A dinsa ma na kira, ya ce yanzu As'ad ba ya sauraron kiran kowa sai dai abinda Madam Haneefah ta fada."

Hajja ta sauke numfashi mai nauyi, tana jin yadda zuciyarta ke kuna. Ta girgiza kai cikin takaici "Abba, akwai babbar matsala akan wannan lamari. Ni kam na kasa gane abin da ke faruwa. Ashe Fulany Maryam ta ci nasara akan As'ad? Na ce tun farko kada ku yi wasa da addu'a. Yanzu da alama ta mallake shi, ba kawai zuciyarsa ba, har da hankalinsa gaba ?aya."

Abba ya tsaya yana nazari, yana jin yadda wannan magana ke tayar masa da hankali. Yana kallon yadda Haneefah ta yi nasarar canza As'ad cikin lokaci kadan. "Hajja," Abba ya yi ?asa da murya, "Mamy ta je gidan As'ad a Abuja domin ganinsa, amma aka ce mata ba za ta shiga ba saboda Madam Haneefah bata bada izini ba. Ta dawo gida cike da takaici. Wallahi, na fara jin tsoro, Hajja."

Hajja ta rike kai tana jin yadda lamarin ke kara dagulewa. Ta sauke numfashi mai nauyi, tana jin zafi a zuciyarta. Ta kalli Abba da ido cike da damuwa Na ro?i Mai Martaba amma Sarki yace kada a takura masa tunda zaman lafiya suke yi."

"Zaman lafiya?" Abba ya ja numfashi cikin takaici, "Hajja, wallahi wannan ba zaman lafiya ba ne. Fulany Maryam ta yi nasara. Ba ki ji ba? Jikarta da take a Asubuti ta rasu, amma ko ajikinta ba ta je ba. Idan mace ta iya haka, me zai hana ta kwace zuciyar As'ad gaba ?aya?"

"Wallahi kuwa," Hajja ta amsa tana girgiza kai, "ina cikin tsananin damuwa. Na san As'ad da kasuwanci da aiki tukuru, amma yanzu bai kira ni ba, bai nemi shawara ba, ba ya ko amsa waya. Wannan ai ba halinsa bane."

Abba ya rage murya, yana kallon yadda Hajja ke nuna tsananin damuwa "Hajja, ko dai ayi masa ru?iya ne? Ni kam na fara jin tsoron Haneefah."

Hajja ta zura ido cikin tunani, ta ja numfashi da kyar "Ru?iya kuma? amma fa tayaya za a yi masa ita idan Haneefah ce ke iko da shi gaba ?aya? Wallahi, ba ni da wani iko a yanzu. Za mu cigaba da addu'a, Abba. Na san cewa babu wani abu da ya fi addu a ?arfi. Amma a wannan lokaci, ku ma ku tsananta addu'a a ko da yaushe. Kada ku yi sakaci. Domin idan da gaske Fulany Maryam ta yi nasara, to kuwa As'ad zai iya rasa dukiyarsa da hankalinsa gaba ?aya."

Abba ya amsa cikin jin ?warin guiwa "Toh, Hajja. Zamu yi duk mai yiwuwa. Allah ya bamu damar ceto shi daga wannan kunci."

Hajja ta kalli Abba da idanu masu cike da damuwa, sannan ta ce "Allah ya sa haka. Yanzu dai zan tsananta addu a, ko Allah ya warware wannan asiri da aka yi masa."

******

Fulany Maryam tana zaune a falonta tana hutawa sai ga wayarta tana kara. Ta duba sunan mai kira, ta ga Haneefah ce. Ta ja tsaki, sannan ta dauki wayar cikin bacin rai

"Dan ubanki! Ina ce kwanciya da namiji na turaki? Na ce, kwanciya da saduwa na turaki! Sha sha sha! Ke kuwa wacce irin macce ce wacce batasan me ke mata ciwo ba! Kin zuba masa maganin a abinci kuwa?"

Haneefah ta tsaya daga gyaran kanta a madubi, ta turo baki kamar wata yarinya tace "Mama, wallahi na manta ne."

Fulany Maryam ta sake jan tsaki "Lallai kin manta! Yanzu kina son ya dawo hayyacinsa ya kore ki kenan? Kin san wannan aure na ikon asiri ne. Ko kallo wallahi baki ishesa ba idan babu magani. Ke kuma sai ki tsaya soyayya? Babu abinda ya dame ni da soyayya!"

Haneefah ta sauke numfashi mai nauyi, ta yi kasa da murya "Mama, zan gyara. Wallahi, ba zan sake sakaci ba."

"To ki tabbatar da haka! Kada ki sake sakaci. Idan ba haka ba, wallahi zaki rasa komai. Ba soyayya ake ba, iko da mulki ake yi. Da an barki da soyayya, da tuni kin koma gida kina kuka."

"Na gane Mama, zan kula sosai," Haneefah ta amsa cikin ladabi, sannan ta kashe wayar.

Bayan ta kashe wayar, Haneefah ta mike da sauri, zuciyarta na harbawa. Ta nufi wardrobe dinta, ta bude drawer, ta dauki maganin sannan ta nufi dining. Ta bude abincin da ta shirya masa, ta zuba maganin cikin miyar, sannan ta gyara teburin cikin tsari.

Bayan ta gama, ta shiga wanka, ta feshe jikinta da turaren Gucci Bloom, sannan ta zabi wani leshi mai launin ruwan madara mai laushi wanda ya matseta sosai.

*** As'ad ya shigo bangaren nata cikin gajiya, yana jin kansa yana sara masa. Duk da haka, ya yi murmushi da kyar lokacin da ya ga yadda ta nannade kanta da gyale mai kyau.

"Sannu da zuwa, Ya As'ad," ta furta cikin shagwaba, tana matsowa kusa da shi. "Na shirya maka abinci na musamman."

Ya zauna a kan kujerar falo, yana kallonta da kyar. Haneefah ta zuba masa abinci cikin kulawa, tana masa shagwaba, tana taba hannunsa a hankali.

Yana ci, wani irin dadi da sanyi yana ratsa jikinsa. Amma daga bisani ya fara jin nauyi da sara-saran kai. Ya dubi Haneefah da alamar tambaya "Kaina na ciwo... Bari na je na kwanta can na huta."

Haneefah ta dan ja hannunsa tana murmushi "Ya As'ad, ka huta a nan mana. Banson naganka nisa dani.."

Ya girgiza kai da kyar "Babu komai... kawai kaina ne ke ciwo sosai."

Duk yadda ta so ya tsaya, sai ya dage cewa zai koma bangarensa. Ya bar dakin yana jin kamar kansa zai tsage. Haneefah ta dan tsaki cikin takaici, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da karfi.

Bayan ya fita, sai ta kira P.A dinsa "Kawo min takardun gidansa na Abuja da ya mallaka mata . Ajiye su nan." Tafada tana binsa da harara..

P.A din ya kawo takardun cikin natsuwa, ya mi?a mata, sannan ya fita. Haneefah ta duba takardun cikin natsuwa, ta nannade su a cikin wata jaka ta boye su a cikin drawer.

Yana kwance a daki, wayarsa ta fara kara. P.A din ya kawo masa wayar yace "Ranka yadade hajja Nason magana dakai tace Na nema mata izini yafa?a yana dan mi?a masa wayar tasa.

Da kyar ya iya daga wayar, yana jin muryar Hajja cikin damuwa "As'ad, me ke faruwa da kai ne? Na kira baka dauka. Ka dage da addu a, kaji? Ga kuma maganin nan da na turo, ka sha yanzu."

"To, Hajja," ya amsa da rauni, yana jin yadda kansa ke sara masa.

P.A din ya zuba maganin a cikin ruwa, ya mi?a masa, sannan As'ad ya sha. Bayan ya gama, bacci mai nauyi ya dauke shi.

Bayan bacci mai nauyi, As'ad ya farka da tari mai karfi, yana jin yadda hayaki ke cika dakin. Ya rike kansa, yana jin amai na taso masa.

Sautin karatun Al-Qur ani ya fara tashi daga pop speaker. As'ad ya rike kansa, yana jin yadda wannan karatu ke ratsa zuciyarsa. Bai ga remote din ba, kuma ya rasa yadda zai kashe sautin.

"Me ke faruwa da ni?" Ya furta cikin rawar murya.

Ya kira P.A dinsa Amma Baya kusa kwatakwata wayar tashi ma akashe take "Wannan abu ya yi yawa," ya furta da kyar, yana jin zuciyarsa tana tafarfasa.

***** Baba Asabe tana zaune a tsakiyar dakin tsafe-tsafe, wuta tana ci a tsakiyar ?akin, hayaki mai kauri na tashi sama yana cike da ?akin. Hotunan tsafe-tsafe sun zagaye bangon, yayin da ?amshi mai ?aci ke ratsa hancin Ayshatu. Ta tsaya a gaban Baba Asabe, tana jin zuciyarta na bugawa da tsanani.

Baba Asabe ta daga murya da ?arfi, tana cewa "Yau kwanaki uku kenan da kamala aikinmu. Aysha, kin yi nasara! Sadaukarwa ta yi aiki! Zaki kasance sama da duk wata mace. As'ad Mallakin ki ne babu aure da wata mace. Iyayensa ma ba zasu kara yi masa maganar aure ba. Mulkin gidan As'ad yana hannunki."

Ayshatu ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, amma duk da haka, wani abu na damunta. Baba Asabe ta lura da yanayinta, ta ce "Amma fa, Aysha, na gano wata cakwakiya. Ba mu iya magance ta ba."

Ayshatu ta rike hannunta cikin damuwa "Baba Asabe, wace cakwakiya ce wannan?"

Baba Asabe ta yi dariya mai mugunta: "Ba wata matsala mai girma ba ce. Amma fa akwai ?an cikas. Idan har kina son As'ad sosai, zaki yi biyayya ga umarni. Wannan layar zata tabbatar da nasararki."

Ta zaro wata layar daga cikin kwando, ta mika mata "Idan kin shiga bangaren As'ad, ki jefa layar a kasa. Haka kuma, idan zaki shiga bangaren amaryar, ki jefa ta kusa da sashjnts. Da zarar kin yi hakan, zamansu ya kare!"

Ayshatu ta dauki layar, tana jin tsoro "Idan aka gani fa, Baba Asabe?"

Baba Asabe ta dara "Ki kwantar da hankali. Duk lokacin da kika ajiye layar, zata bace kamar iska."

Ayshatu ta yi shiru, zuciyarta cike da fargaba. Baba Asabe ta ci gaba "Ki tabbata kin yi yanka ranar Lahadi da Laraba. Kada ki Sallah da Asubahi ko La asar. Idan kika saba, duk abinda kika yi zai lalace."

Ayshatu ta gyada kai, tana jin nauyin alhakin da ta ?auka. Amma a zuciyarta, ta sha alwashin yin komai don ta mallaki As'ad.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH