Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 30

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 30

.....hundreds of people were walking around the place, but her eyes saw him alone among them. He married many men, but whoever married him, there was a big difference between him and him. Increase the body's fullness and flexibility and energy levels. Every time he passed by, before they met again, she felt a kind of loneliness that slowly descended and enveloped her. Every time he slipped his hand from hers, she felt as if she had returned to an empty place.....as if she was the only one left in the world. "Subhanallah" She said lowering her eyes to the ground slowly trying to turn herself to worship. She had a kind of worship with her faith that she had never seen before in all her visits to the place. The whole night in the sanctuary, they called him, he offered her to go to an inn, but she didn't want to stay here. For the third part, he said that she left, but she did not go until after the morning prayer, sleep started to really affect her face and she went to the inn without searching where he was. She just changed into a long nightgown and fell on her bed, it didn't take long for her to fall asleep. He woke up from the knocking that he heard. She barely opened her eyes as s

Standalone post1,723 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 30*

A yau da suke sa'ayi tsakanin safa da marwa din,wani mutum take gani na daban......wani muhammad haisam take gani ba wanda take gani ba. Wata siffa tasa....other side nashi da bataga komai ba a baya sai yanzu. Batasan adadin sau nawa ta saci kallonsa ba,a sanda ta lura zuciyarsa tayi wani irin zurfi da nisa gurin ibada. Hatta da kamanninsa a yau sai take ganin na dabanne. Bai bata qafarsa ta taka kama jiya ba......amma yau dinma hannuwasa suna zagaye da kafadunta dako ta ina. Ko sau daya bai bari wani d'a namiji ya gogi kafadarta ba.....ko sau daya bai bari ta shiga inda za'a matseta ba.

Wani double peace takeji.....wata irin nutsuwa.....wani kusanci......kusancin daya sanyata ta bishi da kallo a sanda sukazo daidai green light,inda maza ya wajaba suyi tafiya da sassarfa. Ya soma zame hannunsa cikin nata......ya soma takawa da sassarfa da wani irin energy kamar jarumin da zai shiga fagen yaqi tsakiyar abokan adawa.

Mazane daruruwa ke tafiya cikin sassarfa a gurin,amma sai nata idanun suka tsinceshi shi kadai a cikinsu. Ya qetare maza da yawa,amma duk wanda ya gifta sai taga banbanci me yawa tsakaninsa dashi. Tsaho cikar jiki da murjewa dama yanayin kuzari. A duk sanda ya wuce da sassarfa kafin su sake hadewa sai taji wani irin loneliness ya sauka a hankali ya lullubeta. A duk sanda ya zame hannunsa daga nata sai taji kamar ta koma wani empty.....kamar ita daya tayi saura a duniya.

"Subhanallah" Ta fada tana sauke idanunta qasa a hankali tana qoqarin maida kanta ga ibada.

Wata irin ibada tayi da iyakacin imaninta bata taba irinta ba duk zuwanta gurin. Daren ranar gaba dayansa cikin harami suka qarar dashi,ya mata tayin tafiya masauki amma sam sai taji tafi qaunar zama a nan din.

Har kashi uku yana cewa ta tafi,amma bata tafin ba sai bayan an idar da sallar asuba,bacci ya soma fusgarta da gasken gaske sannan ta wuce zuwa masaukin ba tare data nema inda yake ba.

Doguwar rigar bacci kawai ta sauya ta zube saman gadonta,bata dauki dogon lokaci ba kuwa bacci yayi awon gaba da ita.

Baccin da knocking din da taji ana mata shine ya tasheta. Da qyar ta bude idanunta tana jin kanta ya mata nauyi. Ta buda bakinta don tambayar waye ma taji ba zata iya ba,don tana kyautata zaton birra ce,don haka kanta tsaye kawai ba tare da tunanin komai ba ta sauka qasa sa hargitsatsen gashinta da rigar baccin data lafe mata a jikinta da ko brazier babu ta doshi qofar.

A kasalance ta bude qofar tana murza idanunta tana shirin fara yiwa birra qorafi.

Narkakkun idanuwansa ya zube saman fuskarta a farko....fuskar da tayi wani yanayi daya qara mata kyau saboda qananun gashin gaban goshinta zuwa kunnuwanta da suka kwanta sosai suka qawata baby face dinta. Uwa uba kuma gashin kanta daya hargitse yana rufe wani sashe na fuskarta wanda taketa qoqarin janyeshi kada ya shigar mata baki,bakin da taketa qoqarin son budeshi tayi masifar daya lura ta iya ta musamman akan birra idan ta mata ba daidai ba.

Ba tare daya shirya ba.....cikin wani irin yanayi idanunsa suka zarce a hankali suna sauka saman qirjinta. Kallon daya zama guda daya tak amma me wani irin qarfin da yaji kamar an saka wani abu me matuqar qarfin magnet an zuqi kowanne jini dake zagaye da jijiyoyinsa.....kamar an mannashi da wata na'ura dake bada sinadarin shocking dake iya girgiza kowacce gaba ta jikin dan adam. Suna tsaye kyam tamkar an haliccesu ne saboda su tsaya a gabansa a wannan rana. Sun bayyana kansu tun daga shape dinsu da yadda suka tsaya cas a qirjinta kaman an daidaitasu. Komai na siffa da kamanninsu sun fito.....abinda kawai ya zama hijabi a tsakaninsa dasu shine yaloluwar rigar baccin data manne jikin fatarsu.

Sai da ta samu nasarar maida gashin nata kafadar hagunta yabi dogo fari tas din wuyanta sannan ta daga idanunta taga kuma waye tsaye a gabanta. Wata iri mahaukaciyar razana tayi,taja baya da sauri da siraran qafafunta dake rawa,ta saka hannu da nufin maida murfin qofar ta rufe.

Saidai kuma hannu daya kawai ya saka ya tokare qofar ta gaza rufeta. Da hannu daya ya dakatar da motsin qofar,sannan a wahalce cikin wani yanayi me wahala ya daga wayarsa yana miqa mata,yana kallon qwayar idanunta da idanunsa da suka canza kala cikin qasa da minti daya,don bazai kuma gangancin kallon qirjinta ba duk da ta saka hannayenta dukka biyun ta cukuikuye gaban rigar.

"Magana akeson yi dake" Ya fada muryarsa tana harhadewa. Hannu daya ta saka ta karbi wayar kamar walqiya sannan ta koma bayan qofar tana qoqqarin turata. Ta turata din kuwa ta rufeta bam alamun yabar bakin qofar kenan.

Ta jima tana maida numfashi,hannayenta dukka suna kakkarwa kamar wadda aka yiwa wanka da ruwan qanqara cikin tsakanin hunturun sanyi.

Wani dogon numfashi ta aikewa hunhunta sannan ta fesar a waje,abinda ya dawo mata da wani sashe kadan na nutsuwarta.

Wanne tsautsayi ne ya kaita rayawa birra ce tayi mata knocking?,wanne tsautsayi ne ya kaita buda qofa a haka?,abinda sam ba halinta bane?.

Tunaninta ya katse sanda wayar ta dauki wani daddadan sauti,ta maida dubanta kan wayar da bata gane wacce irin waya bace ballantana kamfanin data fito. Abu daya ta iya ganewa inda zata daga kiran,saita daga din kai tsaye saidai da dan mamaki tattare da ita ganin sunan maleek ne akai.

"Tantiii...." Taji muryar falaak can qasa kamar sautinta baya fita. Gaban akhnan yadam fadi,saboda yanayi ne da bata taba jinsa tattare da falaak ba.

"Tanti......don Allah kizo......mutuwa zanyi wallahi.....maleek ya kasheni". Sai kuka ya ballewa falaak din.

Dukkanin ilahirin jikin akhnan ne ya dauki rawa,wani irin tashin hankali ya rufto mata.

"Falaak" Ta kira sunanta da wani irin tsoro da kuma nauyi a muryarta.

"Kisa falaak?.....kina ina?".

"Haisam zai kawoki" Taji muryar maleek a raunane maimakon ta falaak da suke magana. Abinda ya sake rudata kenan,duk jikinta ya sake daukan rawa,batasan sanda ta bude qofar da hannunta ba cikin sassarfa ta nufi dakin haisam din ba tare data tuna yanayin rigar dake jikinta ba,tana jin zuciyarta kamar zata ballo qirjinta ta fado,tsoro da tashin hankali suna mamayeta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Bai taba jin yanayi irin na yau ba tunda yake a rayuwarsa dangane da mace. Bai taba tsintar kansa a mawuyacin yanayin da yakeji a yanzu cikin jikinsa ba game da d'iya mace.

Ya sani basai an gaya masa ba,tun daga farkon balagarsa ya fahimci irin nau'in halittarsa,tun daga sanda ya fara fama da wani matsanancin ciwon ciki daya danganashi da asibiti. Bai fahimci bayanan da aka yiwa nanay ba,amma tun sannan yake samun wani irin kulawa daga wajen nanay. Ja a jiki,yawan gaya masa yaji tsoron Allah,yadda zai kare mutuncinsa dana mahaifansa. Sannu a hankali ya fahimci nanay ta sanshi.....ta sanshi sani irin na kar da kar.....ta sanshi irin sanin da uwar da tasan kanta ne kawai takewa yaronta.

Tasha ajiye masa litattafai da suke magana akan illolin zina kowacce iri,tasha zaunar dashi ta masa wasu tambayoyi da yakanji kunya qwarai.....amma daga sanda ya soma mallakar hankalinsa......daga sanda ilimin addini ya ratsashi sosai sai ya fahimci yadda zai bawa kansa kulawa,yadda zai kare kansa daga kowacce irin illa ta zina.

Tun daga sannan.....tun daga wadannan shekarun ya tsaya akan azumin litinin da alhamis.....tun daga sannan ya sake nesanta kansa da kalar kowacce mu'amala data hada da mata a ciki,kowacce iri ce idan bata zama dolen dole ba. Daga sannan ya maida kansa busy sosai akan aikinsa......akan komai da yasan zai dauke masa hankali daga kowanne tunani na diya mace.

Ya sake cusa kansa akan cases masu hadari da wahala sosai a national intelligence security service saboda ya samu ya nisanci kowanne tunani. Yana da burikan da yakeson cimmawa tukunna.....yana da tsarika masu yawan gaske da barin mace ta shiga rayuwarsa a wannan lokacin karyewarsu ne kawai.

Bai taba ganin halittar kowacce d'iya mace muraran irin haka ba kaman yau......shi daya yasan da yadda yayi controlling qafafunshi suka dawo dashi daki.....shi daya yasan da yadda yaketa kokawa da numfashinsa.....idanunsa da yakejin wani abu ya cika masa su.

Ya isa gaban dressing table din dake dakin,ya xube dukka hannayensa akai gami da sadda kansa yana qoqarin daidaita nutsuwarsa da numfashinsa dake masa wani wahalan zuqa da daidaituwa cikin hunhunsa.

Idanunsa a lumshe suke sosai,saidai still hotonta gake gani a ciki,ya dunqule hannunsa guda daya ya daki dressing table din yana kiran sunan Allah. Ji yake kaman hankalinsa zai rabu da gangar jikinsa.....ji yake kaman ya koma.....kaman ya koma ya sameta.....ya rungumeta cikin jikinsa da yanayin da zata mannu sosai a qirjinsa. Ji yake kaman yaje ya kamota cikin jikinsa ta kuma tabbata cikin jikin har sai abinda yakejin ya lafa.

A daidai wannan yanayin da yake ciki ta fado fadin. A gigice take,gigicewar da bata barta ta lura da halin da yake ciki ba,sai kawai qoqarin riqo hannunsa da takeyi tana magana a rude.

"Falaak......falaak tace zai kasheta.....don Allah ka taimakeni muje....kada wani abu ya sameta". Duk da a rude take amma shi a tsaye yake cak......a tsaye yake cak yana binta da kallo,a tsaye yake kaman an dasashi yana bin sassan jikinta da kallo,yadda take maganan tana girgiza hannunsa sai ya zamana kamar suna suna motsawa ne don su nuna motsin da take ya isa har inda suke.

"Ya salam.....ya Allah.....wai bata gani ne ba?,bata fahimta?" Ya fada yana jin 'yar guntuwar nutsuwar daya soma kokawar samowa tana silalewa.

"S’il vous plaît(please)" Ta qarasa fada tana riqe hannunsa da kyau har tana shigewa jikinsa ba tare data ankara da abinda takeyi ba.

"Najiiiiiii" Ya fada yana fusgar kalmar da qyar gami da dan tureta kadan daga jikinsa yana jin kamar zai zauce tafukan hannunsa akan kunnensa duka biyun kamar wanda numfashinsa ke shirin daukewa.

_busy,sorry please_🙏🏽

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽