
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 23
.....she went abroad to her sister's place. I sat alone, the tears flowed down without stopping... How Billy Kuwa the bird of hatred that was working with her heart on me reached a level that words could not solve. Many times I realized that she was trying to pour something into tea or lemon, but God protected me. Every time I notice something wrong, I just stop drinking wisely. I realized that there is no trust in her hands, her heart is full of a kind of burning hatred. On Friday, it came with a new evil. She said that I stole a thousand dollars from her. Before saying a penny, the house became full of noise! The money was searched for till the end, but it was lost. Even though I know it's a lie, that doesn't stop Abba from getting angry at me. He accused me of stealing. I stood aside, my heart trembled, I lost the words to defend myself from what I did not do. My life is full of happiness. I don't have a penny to buy pant or oil to anoint my body. The day I asked mommy for money, she looked at me with disdain and said: Go to the barracks, they will give you money. This statement broke my heart. What kind of mother says that to her daughter? Abba then supported her. He said sinc
SHAFI NA ASHIRIN DA UKU
Arewabook @nanadiso10
Kullum cikin kuka nake, zuciyata cike da ba?in ciki da gajiya. Yanzu haka, ba ni jin da?in komai a rayuwa. Wani lokacin ina ji kamar mutuwa ce kadai mafita. In bi mamata in huta da wannan wahala da azabar da nake ciki kullum.
Na zama kamar baiwa a gidanmu. Aiki kawai nake kamar wadda ba ta da wani amfani sai gyara da kwashe-kwashe. Momy na nuna min tsana sosai fiye da yadda zuciya zata iya ?auka.
Mun gama jarabawar WAEC, yau kusan makonni uku kenan. Amma rayuwa ta ?ara tsananta. Abba kullum cikin zargi da tuhumata yake, ko motsi kawai na yi, sai Momy ta ga laifi a cikinsa.
A cikin wa?annan makonnin, na zama kamar jaka, babu kima. Na rasa komai tun da Abba ya kwace wayata. Wayar ce ka?ai nake amfani da ita don in ?an ji da?i a lokacin da muke jiran sakamakon jarabawar. Yanzu komai ya lalace.
Gaba ?aya na cika da damuwa, ba kudi, ba walwala. Abokiyata Fatima ce kadai take ban 'yar tallafi ta bani ku?in makaranta da sauransu. Amma yanzu itama ta tafi ?asar waje gurin yayarta. Na zauna ni ka?ai, hawaye na gangarowa ba tare da ya tsaya ba...
Yaya Billy Kuwa Tsuntsuwar ?iyayya da take ?awainiya da zuciyar ta a kaina ta kai matakin da kalmomi ba za su iya warwarewa ba. Sau da dama na gane ta na ?o?arin zubamin wani abu cikin shayi ko lemo, amma Allah ya tsare ni. Duk lokacin da na lura da wani abu ba daidai ba, sai kawai na daina sha cikin hikima. Na gane cewa a hannunta babu amincewa, zuciyarta cike take da wata irin ?iyayya mai zafi.
Ranar Juma ar nan, ta zo da wani sabon sharri. Tace wai na satar mata dubu ?ari. Kafin a ce kwabo, gida ya rikide hayaniya ta cika ko ina! Aka nemi ku?in nan har ?asa, aka rasa. Duk da nasan ?arya take, hakan bai hana Abba zafafa fushinsa akaina ba. Ya zarge ni da sata. Na tsaya gefe, zuciyata na rawar jiki, na rasa kalmar kare kaina daga abin da ban aikata ba.
Rayuwata ta cushe da ?unci. Bana da ko sisin kwabo da zan iya siyan pant ko mai da zan shafawa jikina. Ranar da na nemi Momy tabani kudi, sai ta kalleni da raini, ta ce: Je gurin yan bariki, su ne zasu baki. Wannan magana ta fasa zuciyata ?iriri?i. Wace irin uwa ce ke fadi wa yarta haka?
Abba kuwa sai ya mara mata baya. Ya ce tunda na fara sata, to ko naira biyar ba zai sake bani ba. Na shanye ?uncina. Na fi kowa jin zafin yadda ya yarda da duk wata magana da ta fito daga bakin Momy. Shi kuwa bai san Momy ba kamar yadda na santa mace ce da ta kware wajen ?ir?ira da tsara sharri.
A cikin wannan duhu da zuciyata ke ciki, akwai fitila guda ?aya da ke haskaka Shamsiyya, makociyarmu. Ita kadai ce take nuna min dan tausayawa. Watarana tana taimaka min da aikace-aikace, tana bani kwarin gwiwa. Ita ce kadai ta tabbatar min cewa har yanzu akwai wanda zuciyarsa ke da laushi a duniyar nan.
*****
Ina zaune yanzu haka cikin ?aki, nayi tagumi kai na lullu?e da zullumi. Gajiyata ta zarce ta jiki har cikin ?ashi na nake jin nauyi. Na gama tuka tuwo da rana, na gyara falo, na wanke kayan girki, amma har yanzu babu wani abu da ya sanya zuciyata farin ciki. Na yi iya ?o?arina, amma kamar ruwa ne nake shanya a dutse.
Ba komai nake nema ba ?an nishadi ka?an ne kawai. Ko fim ?in Korea da na saba kallo, wanda ke saka ni dariya, ya ?an mantar da ni da damuwa. Amma yanzu, ko ?100 da zan biya na kalla bani da shi.
Rayuwata ta dame ni. Gidan da nake ciki kamar gidan da aka kulle albarkacin zuciya. Ina aiki kamar baiwa, amma kamar ina hasken rana a idon makaho. Na rasa wani da zan bude masa zuciyata na fa?a masa ha?i?anin abin da ke ci min rai, abin da ke rarrafe a cikin dare yana hana ni barci.
Na tuna da Fatima. Da na saurare ta, da na rungumi salon da ta bi Na kula samari don ?an ku?i. Watakila da yanzu ina da ?an abu da zan biya matsalata da shi. Amma ban iya haka ba. Na tsaya da mutunci.
Yanzu ma wani kaikayi ke damuna, wani irin zafi kamar ana cizon wuta ne a gabana. Amma bana da ku?in shaver, ko man cream, balle in iya zuwa asibiti. Na gwada shiga ?akin Momy jiya na zaci zan ?auki ?an abu, amma gashi ita ke kallona kamar baiwa da aka aje a gaba marar daraja, marar murya.
Na mi?e a hankali daga inda nake zaune, na ?auki laptop dina, sannan na fice zuwa harabar gidanmu. Iska mai laushi na busawa fuskata, tana ?an shafa gajiyata da salama. Idona ya sauka a kan Musa, mai aikin gidanmu, yana share ?asa a ?asan bishiyar mangwaro. Na nufe shi da fara a mai launin ?aci.
Ina wuni Musa, na ce masa da ?an?anin murya, kamar wadda ke boye wani sirri a zuciya. Don Allah, idan zaka iya, ka taimaka ka turomin wasu fina-finan Korea masu kyau. Amma dan Allah, kada kowa ya sani. Ni da kai ne kawai.
Musa ya tsaya, ya ?ago da murmushi mai sanyi, ya ce, Haba Hajiya Ramlah, ba matsala kwata-kwata. Abokina ne mai turawa, ai ni ma fina-finai kawai nake kar?a, ba sai kin bada ko sisi ba.
Na ji wata ?ara mai sanyi ta zuba a zuciyata. Na mi?a masa laptop ?in da hannayena biyu, cikin ladabi da godiya.
Na murmusa, zuciyata ta ?an lafa. Nagode sosai, na fa?a a nutse, sannan na juya na koma cikin gida, kamar wata baiwar da aka samu nata ?aramin nisha?in da zai dan shafe gajiyar zuciya.
A yau ba zan ji kunya ba, na fa?a wa kaina. Ko 10,000 ce, zan tambayi Momy. Komai za ta ce, ko yaya za ta yi, in har ba zan mutu ba, zan fuskance ta.
Na ?aura ?ankwali da hanzari, Na hau saman bene kamar wadda zuciyarta ke harbawa da fatan samun ?an?anin jin ?ai.
Tun kafin na karasa palon, idanuwanta ta zuba min. Tana zaune kan kujera kamar sarauniyar da aka gaji da mulkinta, tana kallon tashar da babu sauti.
Lafiya? Me kike nema da rana tsaka zaki hau min sama haka?
Na tsugunna a gabanta kamar wadda ake shirin yanke wa hukunci.
Momy Na da?e kafin na iya ci gaba. Muryata na rawa kamar tana kokarin fita ba tare da izini ba. Dan Allah, ko 10k ce kibani. Akwai kayan gyara da nake so nasiya. Wallahi gaba ?aya jikina wari nake ji. Ga gashi...
Sai na ji saukar wani abu mai zafi. Hannunta ya buge min baki kamar ana yanka tunani a idanuwa. Na lumshe ido da sauri, hawaye suka taru amma suka tsaya gefe da gefe.
Ubanki ya bani kudi nace? Bazan bayar ba! Ina mazan da kike bi? Je ki su baki mana! Ni bana son damuwa fa Ramlah. Kada kiga ina yi wa Bilkisu komai, ita cikakkiyar yata ce. Ke kuwa? Ke yar kishiya ce. Kishiya dai dai da a?alla? Ki tashi ki farka, kin ji? Wani sai kin bi hanya irin ta Fatima sai ku?i da ake nema cikin sharri!
Tana magana, zuciyata na fashewa a ciki kamar madubi mai tsufa da aka jefa a ?asa. Kowace kalma kamar tabarya ce aka zuba min a rai.
Tashi ki bani guri! Wata shegiya! Sai kiba kikeyi kin sha ne har kin manta me kika zo nema? Ko maganin ?arin kiba kika kara siya?
Zan iya jure yunwa, zan iya jure gajiya. Amma wannan kalmomi? Su ne suka fi komai fasani.
Na daure fuska cikin kwanciyar hankali da hawaye ke bijiro min daga zuciya ba daga ido ba. Na ce
Mama A a.. Na sauka da ?asa da murya, na dur?usa na juya kamar wadda ke ficewa daga duniyar da ba ta ?ara yi mata amfani ba.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH