Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 27

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 27

..... looking for any movement from his body. She just quickly withdrew her hand and pulled away. She started talking in a hot voice. Since you can't do it, I will leave this house for you. As for me, I will not live with a man who cannot satisfy me! It's not just a palm without smell! Asad stood with two eyes and blinked them. He didn't say anything. When Ayshatu left Haneefah's room, she did not say anything. But her body showed everything. Her journey showed pride and courage. Even if her heart is boiling, she doesn't let anyone know. Her eyes filled with tears. As she entered her side, she closed the door slowly. She did not sit; She stood in front of the mirror, took off her clothes, and looked at herself. How did I get here? she said coldly. A painful cry filled her eyes. She slowly sat on the side of her smooth bed. She took off her high heels and put her feet on the bench. She took her phone, put it down, and let out a painful cry. I saw what I saw. You made your choice. I m not a woman you play with, As ad. God bless you and your wife, forever. She said, knocking her phone aside. She was breaking down and crying violently. **** As he turned and left the room in silence, hi

Standalone post1,512 words

Ayshatu ta tsaya a bakin ?ofar shashen Haneefah, cikin nutsuwa da izza. Kallon da ta yi musu ya nuna cewa ta fahimci komai.

As ad da Haneefah suna manne da juna. Fuskar As ad na kwance a wuyan Haneefah, bakinsa na goge fatarta. Hannuwansa biyu a bayanta, kamar yana ri?e da wani sirri. Amma da Ayshatu ta shigo, dakin ya yi shiru. Idanunsu suka ha?u da nata cikin razana da rikicewa.

Ayshatu ta tsaya da kafafunta cikin takalman Louis Vuitton stilettos. Rigar jikinta siliki ce, tana ?auke da ?amshi. Idanunta na cikin gilashin baki, amma kallon da ke cikinsu ya bayyana komai.

Murmushi ta saki ba na farin ciki ba, murmushi ne mai ciwo, irin wanda ke ?one zuciya amma ba ya hura hayaki.

Ta ce da laushi, amma da ?arfi a sautin kalmarta

Na zo ne mu gaisa da amarya. Ashe kuwa na yi kuskuren shigowa ba knocking. I m sorry... ku ci gaba da soyayya lafiya.

Ta juya, da siririyar dariya a la??anta.

Haneefah ta bita da harara, cike da zafin rai. Ta juya ta kalli As ad, ta sa hannu cikin wandonsa tana neman jin wani motsi daga jikinsa. Sai kawai ta janye hannunta da sauri, ta ja tsaki.

Ta fara magana cikin murya mai zafi

Tunda ba zaka iya ba, wallahi ni zan bar maka gidan nan. Ni fa ba zan zauna da namiji da ba zai iya gamsar da ni ba! Ba dai dabino mara ?wari ba!

As ad ya tsaya da ido biyu, ya lumshe su. Bai ce komai ba.

Da Ayshatu ta fita daga falon Haneefah, ba ta ce komai ba. Amma jikinta ya nuna komai. Tafiyarta ta nuna izza da ?arfin hali. Ko da kuwa zuciyarta na tafasa, ba ta bari wani ya gane. Idanunta sun cika da hawaye.

Tana shiga bangarenta, ta rufe ?ofa a hankali. Ba ta zauna ba; ta tsaya a gaban madubi, ta cire rigar jikinta, ta zuba wa kanta ido.

How did I get here?

ta furta cikin sanyi. Wani azababben kuka ya cika mata idanu. A hankali ta zauna a gefen gadonta mai santsi. Ta cire takalmin kafarta mai tsayi, ta ?ora kafafunta kan benci. Ta ?auki wayarta, sai kuma ta ajiye, ta ja wani azababben kuka.

I saw what I saw. You made your choice. I m not a woman you play with, As ad. Wallahi kai da mace, har abada.

Ta fa?a, tana buga wayarta gefe. Tana kara rushewa da kuka mai tsanani. ****

As ad ya juya ya fice daga dakin cikin shiru, zuciyarsa tana cike da rikicewa da nauyin damuwa.

Ya wuce sashensa kai tsaye. Ya cire kayan jikinsa, ya sa farar riga da navy blue suit. Ya gyara agogon hannunsa, ya shafa turare mai ?amshi. Amma saboda yadda zuciyarsa ke masa zafi, sai kawai ya tsaya yana duban kansa a madubi. Fuskarsa na nuna rauni da rudani.

Ya sake juyowa, ya koma sashen Ayshatu.

Yana shiga, dakin ya cika da ?amshi mai laushi kamshin lavender da vanilla. Falonta na da tsari da tsafta. Fitilun dakin suna haskaka komai cikin kwanciyar hankali. Yana takawa cikin nutsuwa har ya isa bakin dakinta.

Ayshatu ta fito daga toilet sanye da tawul ?aya. Ruwa yana gangarowa daga fatarta mai she?i. Ganinta ya tada masa wani abu a cikin zuciyarsa, kamar an ?auke masa wani dutse daga kirji.

Bai ce komai ba. Ya rungumeta kai tsaye. Ya lumshe ido, yana zura kansa a gefen wuyanta, yana sauke numfashi kamar wanda ya dawo daga tafiya mai nisa.

Aysha... na yi kewarki. Kin tafi, kin barni ni ka?ai. Kin bar zuciyata a cikin duhu.

Ayshatu ta tsaya a rungumarsa, ba ta motsa ba. Sai kawai ta dan saki murmushi murmushi mai laushi da sanyin zuciya. Ta kalle shi cikin ido.

Ya ce da murya mai rauni

Ke ce ka?ai nake da kwanciyar hankali tare da ke. Don t let go. I m losing myself.

Ya shafa wuyanta da hannunsa. Yaji wani mugun sanyi a ransa. Ya rasa wacce kalar so yake yi mata.

Ta dafa kafadarsa, ta ce a hankali

Ka ce ka yi kewata? To ka tabbatar. Ba da magana ba, da aiki.

As ad ya sauke ajiyar zuciya. A hankali, jikinsa ya motsa kadan. Ya saki murmushi yana kallonta cikin ido.

Har yanzu fishi kikeyi dani akan abin da banda ikon canzawa, Ayshatu? Kin fi kowa sanin idan tanine to tabbas mu mutu mu biyu. Idan dan nene, Ayshatu, ba zan tsaya ga kowacce diya mace ba. Ke kadai nake gani mace ta kwarai, mai kaunata, mai kuma girmama ni. Don Allah.

Wani kallo ta juyo tana yi masa, mai cike da takaici, ta ce

Habibie, shikenan! Kullum iyayenka cikin yimaka aure. Kullum kawai dan a kuntatamun. Ina kai, ina Haneefah yarinyar da ta gama raba jikinta ga maza? A cikin masu daraja, ba za a taba ambatarta ba! Ita ce za a baka?! Ina kishinka, ina kaunarka. Duk wa?anda ake aura maka, ban ta?a tofa komai ba. Amma Haneefah bata cancanci tsaftataccen mijina ba, wallahi.

Tsayawa yayi yana mata kallon kauna. Sai ya ?ago fuskarta, ya aza bakinsa a kanta, ya ?an ?auki lokaci yana kissing nata. Bayan ya janye, ya ce

Allah ya yi miki albarka. Amma umarnin iyayena ba zan iya ja ba, Ayshatu. Ki yi ha?uri, kin ji? Matar Habibie... Zan je meeting yanzu. Amma idan na dawo, sai mu yi magana.

Ayshatu ta ce da laushi

Allah ya dawo min da kai lafiya. Duk abinda ka je nema, Ubangiji Allah ya baka, Habibie. Ya kula min da kai...

Wani sanyi ya ji a ransa sosai. Ya sumbaci gefen kumatunta, sannan ya fita.

Wani zafi mai ra?a?i ne yake fita daga cikin kirjinta. Ta tuna yadda ya rungumo Haneefah jin hakan ya ?arke mata da wani hukuncin zuciya cewa rabuwarsu ba ta isa ba. Ya kamata ta ?ara ?aukar mataki, dan kwanciya da mijinta ba za ta bari kowace mace ta yi ba.

Wani irin ciwon ?ishi take ji, amma kasancewarta mace mai tabbataccen tunani, ta san cewa rabuwarsu tuni ta kammala. Wannan ya sa wani sanyi ya fara shiga ranta sanyi mai ha?e da tsananin ra?a?i.

***

Da zarar As ad ya fice daga shashen, Haneefah ta birkice. Masifa ta ko ina. Tana yawo cikin ?aki kamar wacce aka watsa wa ruwan zafi.

Zuciyarta na tafasa da ?iyayya, kamar an zuba mata toka a rana. Tana jin kamar ta fashe da kuka, amma ta fi za?ar zagi.

To wai waccan ita ce Ayshatu yanzu?! Na yi mamaki wallahi! Ashe dama haka ta koma? Yar gayu ce? Kyakkyawa?!

Ta ja dogon tsaki mai cin rai, ta nufi gaban wardrobe. Tana bu?ewa da hanzari, ta ciro trolley. Ta zazzage kayanta mafi muhimmanci passport, kaya masu tsada, da 'yan kayan shafe-shafe tana ajiye su a ciki.

Ta ?auki wayarta, ta kira ?aya daga cikin direbobin gidan.

Ka shirya mota. Zan je filin jirgin sama yanzu.

Ba ta tsaya jiran amsa ba. Cikin gaggawa, ta fara yin online booking na jirgi, ba tare da wata tantama ba. Zuciyarta tana bugawa da wani nau in ?iyayya da ba ta saba da shi ba. Ji take kamar ta yi ihu, ko ta mare iska.

Wallahi ba zan zauna da namiji mai kama da mata ba!

A cikin kasa da awa biyu, tana tsaye a layin shiga jirgi. Ba ta wa kowa sallama ba. Ba ta waiwaye gidan ba. A zuciyarta, ta rufe shafin As ad har abada.

Da ta sauka a garinsu, ta kira gida

A aiko min da direba yanzu-nan. Ina filin jirgi.

Lokacin da ta isa gidan sarki, ta nufi dakin Hajja kai tsaye. Da ta shiga, sai ta fa?a kan Hajja da kuka sosai.

Hajja, Fiddausi, da Abba suna zaune suna hira. Cikin sauri suka juyo da mamaki. Sai dai Fiddausi ta yi murmushi ?asa-?asa, kamar wadda ta san abin da ke faruwa. A ranta, tana fadin Ai duk fitinar uwarki ba ta kai matar yaya ba. Ita fa bata ta?a bari ki zauna.

Hajja ta ?aga murya

Haneefah, Subhanallah! Lafiya? Me ya faru haka da daddare? Kodai tare kuke da shi ne?

Haneefah na kuka sosai, tana girgiza kai cikin rashin iya magana. Ni ba zan iya zama da losarin namiji ba, wallahi! Ni dai ya sake ni! Na gaji da shi. Ko ya ha?ura, ko kada ya ha?ura wallahi Allah, na gama! Namiji ne, Hajja mai kama da mata!

Ta fashe da kuka mai ?arfi, kamar zuciyarta na ?o?arin fasa ?irji ta fito.

Abba ya mi?e a hankali, yana kallon Hajja da damuwa a fuskar sa. Kamar yadda sauran matan 'yan uwansa suke zuwa suna cewa ya sakesu, wannan kuma ita ce ke ambatar asaketa. Wannan ya sa ya kulle zuciyarsa.

Hajja ta yi masa alama da yaje ya sanar da Mai Martaba. Ya jinjina kai cikin ladabi, ya tafi.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS

Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435

Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693