
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 35
.....any, she threw it and it came back to her). Alhaji Nasiruddeen gave a hand glove to one of the children after all of them had also lost their hands. A thin knife was opened by the children, and they arrived in front of the rope of all of them. From the ground they started to wake up and search, but they didn't find anything. They were about to reach half of the phone and some white things started to appear. "Keep cutting them," Alhaji Nasiruddeen said. "Innalillahi wainna ilahi raji'un" He just repeats. Not her, the sultan's dignity is watching. With which eyes will his people look at the house and the kingdom as a whole? An elephant.....the king's wife?. *S U L T A N E* There was a kind of silence in the place after they took Alhaji Nasiruddeen to the investigation, the silence that morsa safiyya felt, she could not stand it, she came down in front of the sultan and sat smiling at him again. "It's been a long time...we talked to the bride yesterday." He raised his head as he heard her words conveying something to him. "Bride? Who is inside?" She smiled back at him. "Daughter...my daughter is akin to us" "Do you like mornings?" The way he spoke made me smile. "Falaak is good f
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 35*
Idan ya tuna a baya shi din tantirin dan shaye shaye ne.....idan ya tuna a baya yadda ya rayu cikin maye,buguwa da shan kowanne irin nau'in kayan maye sai yaji kaman ya dawo da baya ya goge komai. Denawarsa wani abune da ko iya shi kadai haisam yayi masa bazai manta dashi ba. Wani irin dainawa ta farat daya cikin taimakon wasu addu'o'i daya bashi da wanda yake masa da wanda yake bashi yasha. Cikin sauqi komai ya dinga zarewa daga ransa bayan uban amai da yayi kwanaki uku yana yinsu a jere. Wannan shine ya bashi experience na iya gane gurin da ake ajiyar kayan maye da qwayoyo,yake iya kuma sansanosu. Ya sauke ajiyar zuciya yana furta
"Alhamdulillah"
(Dama ita rayuwa haka take,duk wanda ya shuka tsiya wallahi wallahi wallahi sai ya girba,ruwanka ka shuka alkhairi ruwanka ka shuka sharri,ta cutar da rayuwarsa da plan din ta ruguzashi......gashi a qarshe shine ya zama silar tonuwar wani birnannen sirrinta da ba wanda ya sani,tayi jifa ya dawo mata).
Hand glove Alhaji nasiruddeen ya bawa daya daga cikin yaran bayan dukansu suma sun sakashi a hannunsu. Wata siriryar wuqa yaran ya bude,suka isa gaban igiyar dukkaninsu.
Daga qasa suka fara farketa suna fedeta,saidai basuga komai ba. Suna dab da isa rabin wayar wasu fararen abubuwa suka fara bayyana.
"Ci gaba da tsinkesu" Alhaji nasiruddeen ya fada.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Kawai yake maimaitawa. Ba ita ba,darajar sultane yake kallo. Da wanne idanu mutanensa zasu kalli gidan da masarautar gaba daya?. Giwa.....matar sarki guda?.
*S U L T A N E*
Wani irin shuru ne ya ratsa gurin tun bayan fitarsu Alhaji nasiruddeen zuwa ga binciken,shurun da morsa safiyya taji ita ba zata iya ba,ta sauko gaban sultane sosai ta zauna tana sake masa murmushi.
"Ranka ya dade......munyi waya da amarya jiya fa" Kansa ya daga yana jin kalamanta suna sauke masa wani abu.
"Amarya?,wacce a ciki?" Murmushi itama ta maida masa.
"Yata......'yata akhnan mana"
"Sonkai safiyya?" Yadda yayi maganan ya sanyata sakin murmushi.
"Falaak dai nabar muku,amma akhnan har abada tawa ce.....kuma tamu ce" Tayi maganan da manufa biyu.
Manufar kuwa takai,ta isa inda takeal taje. Daga kai tayi tana duban morsa safiyya,duk da yanayin jira da dako irga mintunan da suke shudewa da takeyi amma hankalinta yana kai. Har akhnan tayi kira?,tayi waya amma ita bata kirata ba?,bata nemeta ba?.
Anya batasan waye almaz a gurinta ba kuwa?,banbance babancen suna qara yawa......sauyawar yarinyar haka da sauri yana bata tsoro. Idan har shine yake hure mata kunne.....saita sanyasu dukkaninsu sunyi dana sani. Akan ta kasa nasara a rayuwarta......gwara ta rasa rayuwarta. Bata shiryawa tsaiwa don ta fadi ba.....bata shirya kallon toxarta da idanuwan data tanadesu domin kallon nasararta ba.
Da ita dake tunanin,da sultane dake hira a hankali cikin taushi da morsa safiyya magana ta neman iso daga me wada ne ya dakatar dasu.
"Sun kammala sun dawo,suna neman izinin shigowa"
"A gaya musu su qaraso" Sultane ya fada yana gyara zamansa,morsa safiyya ma tana sake gyara lullubinta.
A jere suke shigowa,Alhaji nasiruddeen da kansa yana riqe da babbar baqar leda......babbar baqar ledar da kallo daya tak mammina tayi mata taji wani abu ya karta a mararta jini me dumi taji yana tsinke mata.
"Wannan alamace ta tashin hankali.......amma ni zaituna bana taba yarda na fadi" Ta fadawa kanta da kanta,
"Bana ja da baya,bana bada kai.....giwa ko ta fadi tafi qarfin wawa" Ta sake jaddadawa kanta tana hadiye wasu abubuwa masu tsananin tauri razani da firgici zuwa cikin cikinta.
Gaban sultane ya matsa kansa tsaye ya zubesu yana zazzage ledar. Idanu sultane yabi kayan dashi zuciyarsa tana bugawa,Alhaji nasiruddeen ya koma da baya a nutse ya zauna yana fuskantar sultane.
"Bincike ya kammala......kuma zarginmu ya tabbata......ga irin nau'in kayan da muka samu cikin dakin". Zuciyar sultane tayi wani irin nauyi,ba jiya yau ko dazu dazu yasan Alhaji nasiruddeen ba. Mutumne daya qware gurin aikinsa,cikin tarin gaskiya da amana. Uwa uba qasarsa ta niger qasace da take da tsauri akan sha'anin cin hanci da rashawa. Babu ta inda za'a shirya komai saboda cin hanci ko toxarci. To amma abin yazo mata wani iri,ta wata sigar daya kasa yarda dashi.
"Ayimin afuwa Allah ya taimakeka......inaso a bani daman yi mata wasu tambayoyi a nan....idan kuma hali yayi zamu wuce da ita zuwa office dinmu" Maganan ta zowa mammina a bazata,wanne office?,ita din zasu dauka don tuhuma?
"Na baka nasiruddeen" Sultane ya fada kansa tsaye a sanyaye. Bashi kadai ba,hatta da morsa safiyya a sanyaye take kallon komai. Tafi kowa sanin wacece zaituna kaf fadin agadez,bata tunanin akwai wani wanda zai gaya mata wacece ita......amma wannan lokacin abun ya girme mata itama.
"Ranki ya dade......wadannan qwayoyin da hodar iblis......"
"Ba nawa bane" Ta amsa kai tsaye tun kafin yakai qarshen tambayar tana qoqarin cusa nutsuwa cikin maganganunta da reaction dinta. Shuru ya ratsa bayan amsar data bayar. Shurun ya zarce na wasu sakanni,sannan ya sake magana.
"Amma an samesu cikin dakinki".
"Eh ba nawa bane" Ta sake maimaita amsa daya dai. Dole akwai wani yanayi na aiki,da muddin ya biyo ko ta kan waye a danne sanayya,banda ita dince.....ba wanda za'a kama red handed da wadannan kayan a tsaya masa tambaya cikin gida.
"Bedroom dinki......dakin kwananki,waye yake amfani dashi?" Yayi tambayar yanayinsa yana nuna mode na aiki ya shigeshi. Idany ta zuba masa itama sosai,tamkar tana gargadarsa,tamkar tana gaya masa cewa.
"Kabi a hankali.....ina da hadari sosai".
"Nice" Ta amsa kai tsaye.
"To me yasa suke cikin dakin?" Ya maimaita. Shuru ya ratsa na sakanni,sannan ta amsa
"Ta iya yuwuwa wani ya saka saboda ya batamin suna kamar dai haka"
"Wani?.....kamar wa kenan?" Ya sake tambaya yana dubanta ta tsakiyar idanunta. Duk amsar data kamo sai taji ta subuce,akwai sunaye da yawa da takeso ta furta amma sai koda qwaya daya yaqi fita a bakinta,wannan ya sake bada shuru me nauyi,har sai daya sake magana.
"Sun kasance cikin wani irin boyo na sirri,da dukkan alamu dake nuna ba'a son kowa yasan dasu,da dukka wata kalar dabara dame laifi yake iya boye kayan laifinsa...."
"Kana zargina kenan yanzu?" Ta fada fushi yana nunawa saman fuskarta. Idanu ya zuba mata,yana karantar muddin akaci gaba a nan,muddin yaci gaba da biye mata zata nannade tabarmar kunya da hauka ne,kuma ya tuna,wannan umarnin da aka ruba masa shi da manyan baqi BA'A GABAN SULTANE KOMAI ZAI KASANCE BA. sai ya tausa muryarsa
"Ba tuhumarki nake ba.....tambaya ce kawai". Kalmar tasa ta qarshe ta danneta,shurun da yayi mata nauyi da yawa ya biyo baya,kamar an daure harshenta,kamar an daure kowacce kalma daga bakinta,tana jin sanda ya juya ga sultane.
" Ayimin aikin gafara ranka ya dade,a bani dama mu wuce da giwa zuwa hukuma mu qarasa bincikenmu a can,idan komai ya daidaita zamu dawo da ita har gida in sha Allah". Tayi zaton zataji muryar sultane yana fadin bai yarda ba,ta dauka zaice sam sam,amma ga tarin mamakinta sai taji muryarsa cikin rauni yana cewa.
"An baku izini".
" Muhammad?" Ta kira sunan sultane kai tsaye idanunta kafe cikin nasa. Yadda ta kirashi gatsal din ya jawo hankalin kowa da kowa a gurin hatta dashi sultane din. Zare idanunta tayi ta maida kan ma'aikatan daidai sanda sultane yake cewa Alhaji nasiruddeen su dan basu mintuna biyar. Ba musu dukka suka juya suka fice,gurin ya rage daga ita sai morsa safiyya sai sultane din,morsan da sam mammina ta manta da wanzuwarta a gurin saboda tsananin rudewar da taketa pretending tana boyeta.
"Kai da kanka ka miqa matarka inda za'a wulaqantata?,da kanka ka amince wasu jami'ai su tafi dani?". Idanunsa ya lumshe sannan ya bude lokaci guda.
" Ba tozarci ko wulaqanci bane.....haka tsarin yake,dokar ce a haka,muke gyara doka da bayar da ita.....ba zamu taba zama masu karyata ba.....idan na hana su tafi dake ashe bamu da gaskiya kenan?, a duk inda kake gaskiyarka ce take fidda ka,ita take kunceka ta dawo dakai mataki da matsayinka" Maganan ya mata kama da jirwaye me kama da wanka. Har ta bude bakinta zata sake magana sai idanunta suka sauka kan morsa safiyya,abinda ya sanyata shanye duk abinda take da niyyar fada,ta maye gurbin abinda yake kan fuskarta da murmushi
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Na yarda dakai,na amince ba zaka taba sakin hannuna ba a sanda nafi buqatarka. Ko waye ya qulla wannan abun zai warware in sha Allah.......rabuwarmu ko toxartata saidai a jira" Idanu morsa safiyya ta kawar kawai,can qasan ranta abubuwa da yawa suna kai kawo. Ta sani.....zaituna nada wani irin hatsari.....ta sani,zaituna din wata halitta ce da komai akace zata aikata zai farun,sai abinda Allah ya tsare kawai,wadannan maganganun duka ta sani tana yinsu ne saboda ita.
Ita da sultane din duka sukabi zaitunan da kallo sanda take ficewa gurinsu Alhaji nasiruddeen.
Motarsu suka bude mata,don baya cikin doka mutum ya tafi a motarsa kaman yadda zaituna taso tayi da farko. Inda tuhuma ce kawai ba'a kamata da komai ba ana iya bata wannan damar. Da farko ta tsaya kai da fata bata shiga motarsu saidai ta taho a tata motar,duk da tasan cewa doka bata bata dama ba. Amma sai tawagar 'yan jaridar da sukayo kansu.....'yan jaridar da basusan waye ya kirasu ba suka sanyata da qafafunta ta shige motar,musamman da idanunta suka sauka kan biyu daga cikinsu. Suna cikin 'yan jaridar wancan ranar......suna cikin 'yan jaridar da suka yada labarin takardunta na wancan ranar,har abun yake neman zame mata barazanar da a yanzu ake d'ari d'arin karbar taimako daga gurinta daga kowanne asibiti ko gidajen marayu da sauransu.
"Da gaske ne an samu qwayoyi a tare dake......da gaske ne tafiya zakuyi don tuhuma?" Tambayoyin da suka ratso glass din window din da take zaune suka isa ga kunnuwanta,tambayoyin da suka tilasta mata runtse idanunta tana jin zuciyarta da idanunta suna zugi.
"Ina tafisu da nace zamu tafi tare?"
"Ba'a ganta ba......amma ko daga baya ne zata iskemu a can" Driver din motar ya bata amsa yana tayar da motar.
*S U L T A N E*
Idanu morsa safiyya ta zubawa sultane,wanda tun bayan tafiyarsu mammina bai sake cewa komai ba banda shurun. Koda ba'a gaya mata ba tasan yanayinsa,tasan kuma halinsa,alamu ne na zurfafa cikin tunani,tunanin data tabbatar baida fa'ida gareshi da lafiyarsa,musamman yanzun da yake yawan qorafi akan yanayin qarfi da lafiyar jikinsa.
"Bappin akhnan" Ta kirashi da sunan da tasan yana masa dadi sosai. Kansa ya daga yana dan sake mata murmushin qarfin hali.
"Nace ko zaka tafi ka kwanta ne?,zuwa anjima qilan idan ka samu kayi bacci zakaji dadin jikin naka?" Kai ya daga mata a hankali,shi kansa baya marmarin ci gaba da zaman. Wani irin abu yakeji yana taso masa game da mammina. Wani irin yanayi da yafi kama da zargi rashin yarda da rashin aminci. Ya sani,gidansa cike yake da tsaron da ba wanda ya isa ya keta sassan matansa ta sauqi haka har yayi ajiya makamanciyar wannan,ballantana sassan mammina din,da kusan ko sashensa bazai nuna masa tsari tsaro da kulawa ba.
"Muje" Ya fada yana yunqurin miqewa. Koda ya miqe sai yaji kamar ana jijjiga jikinsa da qafafuwansa. Sai yaji kamar komai yana shirin bace masa a lissafinsa,kafin ya iya yin komai wani jiri ya debeshi.
Salatin morsa safiyya da hailalarta kawai ya iyaji,yana jin sanda ta tareshi amma bata da wannan qarfin,dole ita dashi din duka suka zube a qasa.
Da wani irin tashin hankali take kiran sunansa tana tattaba fuskarsa ganin idanunsa suna komawa gami da rufewa ruf. Iyakar yadda zatayi ya gagara,sai ta miqe a birkice tana kama sunayen duk wani hadimi da tasan za'a sameshi a kusa dasu.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽