Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 28

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 28

.....you can hear Ramlah... is it her birth? But I didn't do it. God bless her. From there, I heard Abba ask with concern, "Did you take care of them?" Ramlah's head looks old as if she has not washed her hair. Mumy answered quickly, saying, I really want you to tell me about the lack of hygiene. Yesterday there was no way I could not do it with her, of course Billy washed her head, but she insisted that not today. Abba didn't say anything, he just looked at himself and said, God bless you. I'm sitting in my bed, you can only hear my breathing. In a state of sadness and grief, I felt tears fill my eyes. I pushed them slowly and they started pouring on my cheeks like rain in front of the night window. What kind of plot is this Mumy for me? I asked my heart. I have acne on my face, acne that causes pain, smell, and embarrassment. No matter how much I endure, there is nothing I can say to her, because every attempt to speak turns into trouble from her. Even now, I have collected hot water and salt, I am about to try to wash my face, will God make it easy for me? But she was there in the living room telling Abba to lie about the truth, she was defaming me in his eyes. By God, the day

Standalone post2,179 words

Wajen ?arfe tara na dare, ina zaune a dakina lokacin da na jiyo muryar Abba daga cikin falo. Yana cin abinci yana magana da Mumy cikin lallashi da salo mai sau?in kai.

Ina ganin lokaci yayi da zan fitar da Ramlah waje... ko India ma ne inda Yaya Usman ke zaune. Na san zai kula da ita sosai, kuma zata iya cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali.

Ya ?an yi shiru sannan ya kara da cewa, Kinsan Usman da Auta, sai Allah zaiji dadi sosai idan Ramlah taje can.

Sai da Mumy ta ja lokaci sosai tana gyara zancen kafin ta bu?e baki tace, Abban Ramlah ban ce Auta kada ta tafi ba. Amma danAllah, kada ka dauke min Ramlah. Wallahi zan shiga damuwa. Ka samo mata makaranta anan kusa da mu, ko babbar jami a ce, zan fi jin da?i. Ita kadai nake da ita yanzu da ke bani nutsuwa.

Na ji Abba yayi shiru na ?an lokaci, kafin ya ce da ?asa da murya, Kai Zainab Allah ya zuba miki son yara. Allah ya saka da alheri.

Na ji Mumy tana sauke ajiyar zuciya tana cewa, Bazaka gane ba, Abban Ramlah. Wallahi yadda nake jin Ramlah... haihuwarta ce ka?ai ban yi ba. Allah ubangiji ya raya ta.

Daga can, sai na kuma jin Abba ya tambaya da damuwa, Kin basu ku?in kula da kansu kuwa? Naga kan Ramlah ya tsufa kamar bata je wankin kai ba.

Mumy ta amsa da sauri, tana cewa, Ni wallahi so nake ka yimata fa?a akan rashin tsafta. Jiya babu yadda ban yi da ita ba, tabi Billy ta wanke kai, amma sai ta nace wai ba yau ba.

Abba bai ce komai ba, sai kawai ya ?aga kansa yace Allah ya kyauta.

Ina zaune a ?aki na, shiru kake ji sai hucin numfashina. Cikin yanayi na ba?in ciki da ?acin rai, na ji hawaye sun cika min ido. Na turo su a hankali suka fara malala kan kumatuna kamar ruwan sama a gaban tagar dare.

Wanne irin makirci ne haka Mumy ke min? Na tambayi zuciyata. Ni ina fama da kuraje a gabana, kurajen da ke sa min zafi, wari, da kunya. Duk yadda nake jurewa, babu abun da nake iya fa?a mata, domin kowane yunkuri na zama magana sai ya koma masifa daga gareta.

Yanzu ma, na tara ruwan zafi da gishiri, ina shirin gwada wanke gaban nawa, ko Allah zai bani sau?i. Amma ita can tana cikin dakin falo tana ?ora wa Abba karya akan gaskiya, tana ?ata mini suna a idanunsa.

Wallahi ranar ranar da zazzabi ya rufeni sosai, har jikina ya kasa, shine da asubah Abba ya tashe ni wai in masa koko kafin tafiyarsa. Duk da cewa jikina babu ?wari, na nace na tashi. Na gyara masa wajen, na dafa masa koko, nahada masa harda kosai, sannan nagyara gidan a daddafe tunda Mumy ba za ta kar?i uzurina ba.

Yayin da Abba zai fita nace masa Abba... inason zuwa asibiti...

Yace da mamaki, Me ke damunki?

Na ?an duburburce cikin ru?ani, nace, Zazzabi...

Caraf! Sai naji muryar Mumy daga falo kamar tana jirana Yanzu dan zazzabi ne zaki tafi asibiti? Ko kinsanar da? Yanzu auta ina gidan nan amma baki samuna kisanar dani? ni inada maganin zazzabi Zan dakko miki.

Na kalle ta, na lumshe ido, nace, To Mumy

Na mike jiki a sanyaye, ina jin ciwon wannan yaudarar datakeyiwa abba Nabar gurin cikin kamewa da shiru. Zuciyata kamar tana ?una. Amma ban ce uffan ba. Saboda nasan komai zan fa?a, cikin tsautsayin zuciyarta, bazata ta?a fahimtata ba.

Kwanaki uku kenan ina cikin rashin da?in jiki. Ba kamar da ba, duk motsina sai da wahala. Amma Mumy, kamar ta fahimci cewa ina cikin bu?ata musamman bu?atar ku?i sai ta fara saka ido kan duk wani motsi na. Ta hana ni kusantar dakinta. Ko da canjin aike ne, sai ta duba ni da idanu masu cike da tambaya, ta ce sai na ba ta kudinta. A wasu lokutan har matsawa take yi akan nadaina ?oye mata kudinta bata son sata.

A yanzu haka, Islamiyya ka?ai ce mafakata. Na saba fita da safe, na je Makaranta amma yanzu munyi candy muna ma jiran result dinmu ne wannan satin sai dai dayake ina zuwa Islamiyya, daga nan na dawo gida cikin shiru da kadaici tunda banda iko yanzu ko zaman palon danakeyi ina kallo shima sai yazamana laifi tace Indaina samata ido a falonta.

Yau ma dai, na tashi da niyyar kar?ar system ?ina daga inda na ?oye shi. dayake musa idan yakawomun sai yasanya acikin fulawowi na gidan mu Na lallaba naje na dakkona saka shi cikin kayana yadda babu wanda zai sani nasan da momy tasan da system din da tuni tasanya abba ya kwaceta amma kasancewa ta manta inada ita yasanya bata Sanyashi ya ?arba ba. Na gyara gidan nakuma dora spaghetti da miya da salad dana gama sannan nagyara gurin sannan na nufi Islamiyya kamar yadda nake yi kullum.

A hanya, zuciyata na cike da tunani abaya momy tazama tamkar uwata Ayanzu kuwa duk duniya nice makiyarta ko kallona bataso tayi. Amma da na isa Islamiyya, sai Shamsiyya ta kar?e ni da murmushi. Ta dubeni da kulawa, ta ce Lafiya kuwa? Naganki wani iri yau badai mumy bace ba? Na ?an yi shiru, sannan na ce, Lafiya lau kawai yau ne banajin dadi. A zahiri dai ita ce ka?ai nake iya fa?a wa damuwata saboda ta fi kowa fahimtata sannan tana bani shawara Kuma tana cewa in dage da Addu'a.

Na nemi alfarma a wurinta. Na ce mata, Dan Allah, idan mun gama, ki raka ni gidan Kakata. Ta ce, To, ba damuwa. Har ma ta ara mini ku?in mota ba tare da wata gardama ba. Wannan abin ne ya ta?a zuciyata irin kulawa da fahimtar da ban saba samu ba.

Da ?arfe hu?u, muka nemi uzuri a wurin malam ?inmu, muka fice. Mun isa gidan Kakata cike da fatan samun nutsuwa ko mafita, amma muka tarar kofar a kulle. Wani makwabci ne ya bayyana mana cewa har yanzu ba ta dawo ba. Na yi masa godiya cikin ladabi, sannan muka juya muka koma gida.

Washegari yakama laraba Haka Abba ya yi sallama da kowa, ya fice daga gidan cikin natsuwa, kamar yadda na saba ganin sa idan zaiyi tafiya mai nisa. Na ji yana gaya wa Mumy cewa zai kwashe kusan sati biyu cameroon. A zuciyata, da?i ya fara lullu?eni na zaci zai bani ko da kadan ne na kudi. Ina fatan zai ce Ramlah, ga wannan, ki siya magani ko ki yi wata bu?atarki da shi.

Amma har ya ?arasa mota, har motar ta tashi ta ?ace da kura a kan filin gidanmu ko sisi bai bani ba. Na tsaya a tsakar gida ina kallon ?ofar da ya bi, zuciyata cike da ba?in ciki da tambayoyi marasa amsa.

Tun jiya jikina ke fama da zazzabi, yana min illa sosai. Amma Mumy, wadda a da take da tausayi, yanzu kamar bata damu ba. Ko cikakken kallo ban isheta ba yanzu ko sannu Ko magani bata bani. Ko kallon damuwata ma bata yi. Ina kwance a ?aki, jikina kamar an cika shi da ?aya, amma babu mai damu da ni ko ya tambayi lafiyata.

Na lallaba da ?yar na tashi, na nufi wajen Yaya Billy. Na tsaya a gabanta cikin ladabi da kwanciyar murya, nace: Don Allah, ki taimake ni da dubu ?aya ko da aro ne, sai na biya. Sai ta ?ago kai tana kallona da raini, tace: Idan kika ?ara damuna da irin wannan maganar, wallahi sai da mari! Tunda ba ni ce na haifeki ba, to ki sani kar ki raina ni!

Na tsinci kaina cikin ba?in ciki. Na cije lebena na ?asa, hawayen takaici suka cika idona. Nace mata kawai: To. Na juya da baya, cikin shiru da nauyin zuciya.

A wannan rana na gane cewa ba?in ciki da ?unci ba wai daga talauci kawai yake ba wani lokaci daga rashin ?auna da kulawa ne daga wa?anda kake ?auka tamkar iyayenka.

Yau ba mu da islamiyya, haka kawai na tsinci kaina a zaune a farfajiyar gidanmu ina sauraron rediyon da Musa ya kunna. Shirin "Indaranka" nake sauraro, wanda yanzu ya zama tamkar abokina mai debe mini kewa, musamman da yanzu nake cikin rashin walwala saboda rashin kudi da rashin yadda zan samu Korean films da na saba kallo a computer dina. Har sau uku Musa yana turomin, amma yanzu naji kunya na sake zuwa na ro?e shi ya ?ara turawa. Ina cikin wannan tunanin, sai ga Mumy ta fito daga cikin gida, cikin wani ha?a??en lace mai launin shu?i da fari wanda ya matu?ar yi mata kyau. Gaskiya, in banda ?yashi, Mumy ba ?aramar kyakkyawa ba ce, musamman idan ta shiga irin wa?annan kayan da suke fidda ainihin kyau da kamalarta. Ta iso gabana tana kallona da ?an murmushi kadan. "Ke, Ramlah, ni zan fita zuwa bikin gidan Alhaji Wakili. Ki tabbata kin ?ara gyara gidan nan sosai kafin na dawo. Sai wajen ?arfe tara na dare zan dawo. Kuma ki bar girkin yau, sauran shinkafar da ke tukunya ku ci ita da masu gadi." Cikin girmamawa na amsa mata, "To, Allah ya kiyaye hanya Mumy. Sai kin dawo lafiya. Yaya Billy ma Allah ya kiyaye." Yaya Billy tana kallona ta watsamin wata muguwar harara, ko amsa sallamar ba ta yi ba. Ta ?auke kai kamar ban wanzu ba, suka shiga mota, suka ja suka fice. Wani mugun da?i ne ya ziyarci zuciyata, na shiga cikin gida da sauri kamar wanda aka ce masa an raba ku?i. Na tafi kai tsaye saman gidan, ?akin Mumy na nufa, zuciyata tana bugawa saboda tashin hankali da fargaba. Na bu?e ?akin a hankali, turaren alfarma da ?amshi ya kar?e ni nan take. Na nufi inda ta aje turarukanta, na ?auki kwalabe na tsiyaya cikin wata ?aramin leda, zuciyata na bugawa da sauri saboda tsoron a kama ni. Na duba cikin ?akin ko zan samu ku?i, ban samu ko sisi ba. Sai da na juya zan fita, sai idanuna suka kai ga wardrobe ?inta wanda yake bu?e ka?an. Cikin hankali na matsa kusa da wardrobe ?in, zuciyata na cigaba da tsananta bugawa. Sai kawai na hango wasu sababbin ku?i 'yan dubu-dubu masu yawa sosai. Take wani sanyi ya ratsa jikina, naji wani irin farin ciki mai gauraye da tsoro yana ziyartar zuciyata. Hannu na rawa, jikina na ?an karkarwa, na tsamo guda goma sha biyar. Wallahi idan ka ga yawan ku?in nan zai fi dubu ?ari biyu! Na tabbata babu yadda za ayi Mumy ta lura. Na lullu?a ku?in cikin ledar da na ?auko na saka turarukan, sannan na zuba ?an maclean guda biyu ciki don na ?oye sirrina. Cikin sassarfa da taka tsan-tsan na fito daga ?akin, na kulle ?ofa yadda babu wanda zai gane cewa wani ya shiga. Na sauka ?asa da ?afafu masu nauyi da zuciya mai nauyi amma cike da farin ciki na shiga ?akina. Nan na adana ku?in ?ar?ashin kayan jikina, na ?an yi ajiyar zuciya sannan na kwanta a kan gado ina kallon saman rufi, zuciyata tana faman tunani. Wallahi babu wanda zai fahimci irin radadin da zuciyata take ji saboda halin da nake ciki, sai wanda ya gani da idanunsa. Na sani wannan abu ne mara kyau, amma kuma ban da wata mafita da ta wuce wannan a yanzu. Ina tsaye a harabar gidanmu cikin ?an nisa daga ?ofar gida, sai ga Musa ya nufo ni cikin sauri. Ya tsaya a gabana yana huci kamar wanda ya zo da sa?o mai matu?ar muhimmanci.

Ramlah , ya kira sunana da wata murya mai ?auke da damuwa, ga wata baiwar Allah a waje tana nemanki. Wai tana cewa danAllah ki fito.

Na ?an runtsa ido, zuciyata ta buga. Wacece? na tambaye shi, ina ?o?arin fahimtar me ke faruwa.

Musa ya ?an sunkuyar da kansa, sannan yace, Tace wai tana kama da abbanki...

Baki na na ?an bu?e, amma ban ce komai ba. Na ?auki hijjab dina na zura a hankali, zuciyata cike da tambayoyi da shakku. Ina fita daga ?ofar gidan, idona ya sauka kan wata mota mai launin toka da ta ke a bakin titi. Na le?a cikin motar a hankali

Sai ga Umman Khalil...

Zaune take, idonta jajir kamar wacce ta shafe sa'o i tana kuka. Fuskar ta kumbura, ta cika da damuwa. Na matso da takaici da fargaba, zuciyata na bugawa da karfi.

Umma lafiya? na tambaya cikin murya mai sanyi, amma da karfin tashin hankali.

Ta bu?e kofa tana cewa, Ramlah danAllah ki shigo. Mu tafi wajen Khalil...

Zuciyata ta ?aukaka kamar za ta tsinke. Kafafuna suka yi sanyi. Naji kamar ana janyo zuciyata da igiyar ba?in labari. Babu shiri na shige cikin motar. Driver ya ja motar, numfashina na rawa, zuciyata na doki da fargaba me ya faru da Khalil?

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ASHIRIN DA TARA

Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435

Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********