Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 36

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 36

.....with thread and cotton what is the real value. She said that it is a kind of eye-catching because of the high price of silk material. He was standing at the big glass window, his eyes were directly fixed on the haram of the mosque of the S A W worker. Even if he will die and become a resident, he has the share of his land to be in the city, what is sacred. He puts on the links of his robe in a deep dive, once again ending the prohibition of viewing. He is a very Westerner, who all go to Maghrib prayer not more than two and a half to three hours, and he wants them to finish their visit because they only have two days left to go to Ethiopia. A kind of light and softness is shining through the haram, because he has never seen a town that has such a quiet and pleasant listening like Madeena, despite the number of visitors from the S A W staff who are always in it. He finished putting the links, he put his hands on the glass and let go of a heavy heart, the heart that comes with a kind of calmness from his soul to his body. After waiting for about a minute to pay.....

Standalone post1,661 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 36*

"Ba numfashi a jikinsa kwata kwata" Daya daga cikinsu ya fada yana duban morsa safiyya gumi yana yanko masa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ta samu kanta da maimaitawa sau babu adadi,ya sulale tana zama dab dashi tana riqe hannayensa sosai cikin nata.

Safeena ce take dawo mata cikin kanta....wancan ranar da ba zata taba gogewa cikin kanta ba,har sai ranar da tata ta sameta.

"Karka tafi ka barni kaman yadda safeena tayimin" Ta motsa labbanta tana fada a hankali tana jin kamar hankalinta yana neman gushewa daga jikinta.

"Likita ya iso Allah ya baki nasara" Taji muryar daya daga cikin hadiman,kai ta daga tana dubansa kamar bata ganewa,sai kuma ta sake matsawa kusa da sultane din da har yanzu ba wani abu nasa daya motsa,kamar tana gaya musu bazan iya tashi daga nan ba.

★★★

*M A D E E N A* _ALMUNAWWARA_

*_InterContinental Dar Al Iman Madinah(presidential suit)_*

Cikin lallausar jubah yake sanye wadda aka samar da ita da zare da auduga me darajan gaske. Fara ce tas me wani irin daukan idanu saboda tsadajajjen silk material me asalin tsada da aka maida audugar zuwa ga saqarsa.

Yana tsaye bakin babban glass window din,wanda kai tsaye idanunsa suke kafe akan haram na masallacin ma'aiki S A W.

Tunda suka zo baya gajiya da tsaiwa a gurin......baya gajiya da kallon gurin da yake fata ruhinsa da gangar jikinsa watarana su dawwama a gurin. Koda zai mutu kuma ya zamana yana da rabon qasarsa ta kasance cikin garin me tsarki.

Links na jubah dinsa yake sakawa a nutse yana sake qarewa haram din kallo. Yammaci ne sosai,wanda duka duka zuwa sallar magariba bazai haura awa biyu da rabi zuwa uku ba,a awannin kuma yakeso su qarasa ziyararsu saboda kwanaki biyu kawai ya rage su wuce Ethiopia.

Wani haske me laushi ke gilmawa ta haram din,tunda yake bai taba ganin garin dake da wani irin shuru me dadin sauraro ba irin madeena,duk da tarin baqi maziyarta ma'aiki S A W da kullum suke cikinsa.

Ya kammala sanya links din,ya dafe hannuwansa jikin glass din yana sauke wata ajiyar zuciya me nauyi,ajiyar zuciyar dake tafe da wata irin nutsuwa daga ruhinsa har zuwa gangar jikinsa.

Bayan tsaiwar da tayi na kusan mintuna biyar bakin qofar bedroom dinnata tana shaqar daddadan qamshinsa cikin fargabar yadda yau zasuyi face to face bayan wannan damar datayanke masa. Tun a makka tun ranar data dawo daga gurin falaak takejin wani irin tsoronsa yana shigarta. Gani take ko yaya suka kebe zai iyayi mata wani abu,saita maida duk wani ziyara da zasuje ko ibada lallai saita jajibo falaak da maleek,haka suka dinga tafiyar bibbiyu bibbiyu. Ta kuma zabi lokutan dawowarta daidai sanda yake haram ko ya kwanta bacci,kwanaki kadan sukaga juna ita dashi har suka taho madeena.

Ko a yanzun wani dan qaramin ciwon kai takeji da mura da tasan bata rasa nasaba da yawan zamzam me sanyi data dinga sha ba adadi.

Kwarjini yake mata sosai bayan wannan tsoron,kwarjinin daya sake daduwa tun bayan guraren da suka ziyarta. Gurare ne da tunda take zuwa saudiyya bata taba sanin akwaisu ba ballanta taje. Gurare na tarihi sosai daya shafi annabi Muhammad S A W da sahabbansa. Ba ziyarar kawai ba.....wani abu qwaya daya daya dinga narkar mata da zuciya.....wani abu guda daya daya tilastata ta dinga satar kallonsa har batasan adadin awannin data dauka ba.....wani abu qwaya daya daya sanyata zubewa lips dinsa idanunta tana kallon yadda yake motsa bakinsa,abinda ya dinga tayar mata da tsigar jiki shine. Duk wani guri da zasuje a tausashe da muryar nan tasa da sau tari idan ta kwanta take jinta cikin kanta.....cikin mafarkinta dama duk wani motsinsa.....da wannan muryar yake basu tarihin kowanne guri idan suka tsaya a gurin,da abubuwan da suka afku a gurin zamanin annabi Mohammad S A W. Idan akwai ayar data sauka zai karantata da kyakkyawan sauti da kuma daddadar qira'ar nan tasa. Bata manta ba.....qira'ar ta sanya mutane da yawa waiwayowa suna dubansa,sannan ta qara yawan mutanen da suka bi tawagarsu,dole ya koma bayani da harshe biyu English da arabic saboda mutanen dake biye dasu.

Sai kuma taji wani abu yana matse qirjinta sanda taga 'yammata na sake qaruwa,suna biye dasu har xuwa sanda suka kammala ziyaran.

Ko a shekaran jiya sunje mazr'a Al'Aaliyah inda nana mariyatul kibdiyya ta haifi sayyadina ibraheem dan manzan Allah S A w. Sunje Daar almadeena museum.... Acan din taga abubuwa masu yawa da aka surantasu cikin killataccen glass da suka shafi ma'aiki matansa da sahabbansa.

Gurare ne da suka dinga saukar da wani sanyi da taushi a zuciyarta. Ashe a baya suna zuwa ne kawai ibada ba tare da sun qarawa ibadar armashi ba?. Bata taba umara irin wannan ba a rayuwarta,bata da tabbacin ibadarta,amma zata iya cewa wannan ce umararta ta farko data karbu dari bisa dari.

Da wani irin yanayi take takowa zuwa living room din,kamar wata qasaitaccen dawisu. Yanayinta haka me sanyi a wasu lokuta,takun tafiyarta da izza da nutsuwa suka yiwa ado,wannan yana sanyawa idan yana tafiya take jan hakalin mutane sosai,bawai maza kawai ba,harda mata 'yan uwanta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Abaya ce me sulbi a jikinta midnight blue,asalin silk blend me wani irin yauqi da daukan hankali. Wani irin zaunannen kyau tayi,color na rigar yayi masifar fita da kalan fatarta. Dan Malaysian hijabs da ya zame mata abokin sawa tun zuwansu qasar ya fidda kyan fuskarta tare da qara bayyanar da quruciyarta.

Ko a yanzun da yake tsaye,motsinta yaja hankalinsa,motsin daya sanyashi waiwayowa a nutse. Wadannan narkkakkun idanun nasa suka sauka saman fuskarta,sai wani abu ya haska cikin idanunsa.

Quruciya.....qananun shekarun nan da yayi masifar rainasu,a yanzun yana sake ganin qarancinsu qwarai da gaske. Can qasan zuciyarsa ya samu kansa da irge hasashe da laluben ainihin shekarunta.

Ya lumshe idanunsa kadan yana budesu a kan fuskarta,yanayin kallon daya qara mata fargaba ya kuma aza mata nauyi me yawa,sai tayi qoqarin kauda kanta kadan tana nufar inda ta ajiye wayarta dazun bayan shigowarta.

"Barka da warhaka" Ta fada da wannan muryartata me wani irin taushi,wadda ko sau nawa zata buda baki tayi magana sai yaji wani abu daban da baisan meye ba a cikin muryar.

Maimakon ya amsata,sai ya gyara tsaiwarsa sosai,ya zube hannuwansa cikin aljihun jubah dinsa yana qare mata kallon dashi kansa baisan dalili ba.

Yadda fararen qafafunta ke sauka saman tattausan carpet din kamar me tausayin qasa......yadda abayar ke budewa sosai ta bayanta tana bada wasu kaloli kaman ba kalar midnight blue ne kawai a jikinta ba......a hankali duka yanayin suka hadu suka saukar masa da wata irin nannauyan kasala. Yana karance da duk wani takunta tun daga wancan ranar.....wani lokaci siririn murmushi kawai yakeyi. Idan da yaso.....idan da yaga dama ba zata kawo wannan gurin ba. Idan da wani abu daban yake buqata daga gurinta yasan duk ta hanyar da zai karba,bazai ma bata daman da zata iya guduwa daga gareshi ba,to amma ba wannan lissafin yakeyi ba a yanxu.

Yana buqatar ta gama sanin wacece ita?,wacce rayuwa tayi a baya?,wacce kalar rayuwa kuma zatayi a yanzu?. Yanaso kuma yaga iya gudun ruwanta gurin qwarewarta wajen guduwa. (Hmmmm Captain.....wata qaddarar tana bada zabi ne?).

Har ta qarasa gurin,ta zare wayarta daga charge tana jin nauyin dukka idanunsa a kanta.

A hankali takejin wani kusanci a tsakaninsu.....cikin jikinta takejin tabbas yana kusantowa gareta. Ta basar ta danne tana mazewa gami da zarcewa da danna wayarta,duk da yadda zuciyarta ke wani irin bugawa a hargitse,tana kuma bata shawarar ta daga qafarta zuwa waje ya sameta a can,amma ta kasa koda motsin kirki.

Ba kasafai ta fiya son a gane lagonta ko faduwarta ba. Batason a gane meye rauninta shi yasa take iya iyawarta ta boye masa tsoronta,saidai abinda bata sani ba.......tana auren wani mutum ne na daban......wani mutum da yake iya karantarka ta cikin qwayar idanunka kadai ba tare daka furta masa komai ba. Motsinka kadai ya isheshi amsa.....motsi kawai wata fassara take bashi me tarin ma'anoni.

Jinsa dab da ita da wannan sassanyan qamshin nasa da kowacce rana idan zata jishi sake dilmiyata yakeyi cikin wani yanayi me wahalar fassara. Ta daga fuskarta da sauri,saidai irin kusancin da ta gani a tsakaninsu yafi firgitata sama da komai. Taku daya tak tayi da nufin janyewa baya amma sai ya saka dogon hannunsa ya riqo tsintsiyar hannunta da kyau,bai kuma bata dama kota second daya ba ya janyota jikinsa,saidai kuma bai bari ta fada faffadan qirjinsa ba ya tareta ya tsaidata dab dashi yana riqe qugunta da dukka hannayensa biyun.

Kallon kallo suka fara yiwa junansu,nata idanun cike da tsoronsa da wani irin shakka.......zuciyarta na bugawa da gudun da ta sani tabbas idan shuru ya sake wanzuwa tsakaninsu zai iya jin qarar bugun.......yayin da nasa idanun ke cike da wani abu dashi kansa baisan meye ba. Wani abu da yake zama kamar wani dan aike daga idanunsa zuwa na akhnan din.....wani abu da ya yiwa zuciya da qirjin akhnan nauyin gaske.....wani abu daya fara ratsata tun daga qwayar idanunsa yana bin kowacce hanya da jini yake iya wucewa yana sauka kai tsaye a zuciyarta.

KAIFI......wani irin kaifi idanunsa ke dashi.....bata taba ganin d'a namiji da yake zarra irin tasa ba. Ba wani namiji data taba kafewa da idanu irin haka bai rusunar da nasa idanun ba.....amma shifa?.

Ko yaushe qwayar idanunsu suka gauraya qoqari yake ya dakushe tata. Qoqari yake ya kashe duk wani kwarjini nata ya mamayeta da nasa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽