Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 29

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 29

.....what happened to you that you would come to fight with me and cry like that?" Haneefah said, "God bless you, Asad... he is not well! He could not fulfill his right to marry. It was completely different for me. By God, I am tired of living with someone who cannot fulfill my marital rights. He released me and I returned home. By God, I will not go back to him." Her voice was full of pity, hiding her face in the palms of her hands. This statement shook the hall. Everyone in the palace was amazed and shocked. In anger and violence, His Highness heard a voice and said to his chief servant, "Wambai! Send it to As'ad. I want to see him in front of me early in the morning when he appears!" Wambai answered politely, "Your soul is long gone! Fulani Maryam, her heart was beating with joy, but she was trying to hide her smile so that it would not be obvious. She was saying in her heart, "God has brought me the end of this child to work." She was looking at Hajja Sa'adatu, the wife of His Highness and the mother of Asad, looking from the side. Of course, this thing shook Hajja's heart, because tears had already gathered in her eyes. ra?a?i?in her heart is.....

Standalone post2,041 words

******

A fadar Mai Martaba, hasken fitilun lantarki sun kawata falon zauren masarauta, suna she?i bisa ?ayatattun shimfi?un da aka tanada musamman ga manyan masu fada-a-ji. Masu hidimar fada suna tsaye cikin girmamawa, yayin da manyan matan gidan sarauta suka ha?u bisa ga alfarma da ?asaita.

Fulani Maryam (Mahaifiya ga haneefah) uwargidan Mai Martaba, tana zaune cikin shiga ta musamman mai bayyana matsayinta a gidan sarauta, tana lumshe idanu cikin wata irin annashuwa da farin ciki, Hajja ma da sauran matan Nasa suna zaune cikin shiga ta alfarma.

Cikin wannan yanayi ne Haneefah ta shigo zauren, kuka da hawayenta suka mamaye hankalin kowa da ke cikin zauren. Ta zo da sanyin jiki, tana tafiya cikin rawar kafa har zuwa gaban Mai Martaba Sarkin . A hankali ta zube bisa guiwowinta, ta fashe da kuka mai ban tausayi.

Gaba ?aya idanun fada suka dawo kanta. Zuciyar Mai Martaba ta tsananta bugawa da zafin fushi. Muryarsa ta fito cikin ?asaita da izzar sarauta.

"Menene ya faru, Haneefah? Wane abu ne ya sameki har zaki shigo mini fada da kuka irin haka?"

Cikin rawar murya da shesshekar kuka, Haneefah ta ce, "Allah yakara maka lafiya As ad... ba shi da lafiya! Ya kasa cika haqqinsa na aure. Gaba ?aya ya zame min wani abu daban. Ni wallahi na gaji da zama da wanda ba ya iya sauke haqqin aurena. Ya sake ni na dawo gida. Wallahi bazan koma masa ba."

Muryarta ta ?are cikin kuka mai cike da tausayi, tana ?oye fuskarta cikin tafukan hannuwanta.

Wannan magana ta girgiza zauren. Duk wanda ke cikin fadar ya shiga al'ajabi da razana.

Cikin fushi da tashin hankali Mai Martaba ya ?aga murya yace da babban hadiminsa, "Wambai! Ka aika wa As'ad. Ina son ganinsa a gabana da sassafe ya bayyana!"

Wambai ya amsa cikin ladabi, "Ranka ya da?e! an gama."

Fulani Maryam, zuciyarta na rawa da farin ciki, amma tana kokarin ?oye murmushinta domin kar ya bayyana fili. A cikin zuciyarta tana cewa, "Allah ya kawo mini ?arshen wannan yaron aiki yaci."

Tana ?an ?arewa Hajja Sa'adatu, Matar Mai Martaba kuma mahaifiyar As ad, kallon gefe. Tabbas wannan abu ya girgiza zuciyar Hajja, domin tuni hawaye sun taru a idanunta. Ta ?auko mayafinta ta share kwallarta da sanyi, muryarta na ra?a?i cikin zuciyarta tana cewa, "Allah ka ji?an zuciyar ?ana. Ya ubangiji ka kawo masa sau?i."

?an uwa da sauran matan Mai Martaba suna gefe suna ra?a-?i tsakanin su, wasu da al ajabin faruwar lamarin, wasu kuma cike da rashin jin da?in wannan abu da ke neman ?auke martabar gidan masarautar.

Mai Martaba ya juya ya dubi Haneefah cikin yanayi na tausayi da izza, yace, "Ki kwantar da hankalinki, Haneefah. Duk wanda ya ?ata miki rai, babu shakka zai gane kurensa. Fadana ba wurin wulakanta jinina ba ne."

Haneefah ta ?ago kanta cikin shaukin kuka, tana duban sarki cikin soyayya da godiya, amma zuciyarta ta riga ta gama yanke hukunci. Auren ta da As ad ya gama zama tarihi a zuciyarta.

Cikin wannan yanayi ne dukkan wanda ke cikin fadar suka ji sanyin fargabar abinda zai biyo baya idan gari ya waye.

**********

Yau dai ranar As'ad ce ta kasance mai cike da ?alubale da aiki tun daga safe har zuwa lokacin da rana ta yi zawali. Fitattun fitilun zinariya na office ?insa ne suka haska ko'ina, suna ?ara bayyana ?aukakar dukiyar da Allah ya mallaka masa. Kujerarsa ta fata mai launi irin fari da duhun ruwan kasa tana zagaye da kyawawan teburori masu ?auke da litattafai da takardu masu muhimmanci.

A zaune yake a kujerar mulkinsa, cikin wata irin yanayi na tsananin damuwa da tunanin da yake ?o?arin samun mafita. Kwana biyu kenan yake fama da wani irin azababben ciwon kai wanda ya hana shi sukuni sosai. Amma babu abinda ke damunsa fiye da yadda zuciyarsa ta sauya gaba ?aya tun bayan dawowar Ayshatu.

Ya rasa dalilin da yasa soyayyarsa ga Haneefah ta fara mutuwa sannu a hankali. Yana zaune zai yi tunani, zuciyarsa ta fara tambayarsa "As'ad wai me yasa har ka aure ta? Me kake tunani lokacin da ka amince da wannan yarinyar da yanzu ta zame maka ?alubale a zuciyarka?"

Sai kuma wani sashe na zuciyarsa ya raya masa wani abu daban. "Amma fa, Haneefah ta iya sarrafa namiji sosai. Ba kamar Ayshatu ba, wacce aikinta kawai shi ne kwanciya a yi mata romancing. Haneefah mace ce cikakkiya mai zafin nama, mai iya sarrafa namiji ta kowanne ?angare."

Wannan tunanin na Haneefah ya sa tsigar jikinsa mi?ewa cikin wani yanayi mai ?arfi. Amma sai wani mugun ra?a?i ya sake tunasar dashi matsalarsa ta rashin lafiyar da gabansa ke fama da shi. Nan take yanayin jikinsa ya sauya, zuciyarsa ta ?au zafi sosai.

"Ya zama dole in nemi likita cikin satin nan har ?asar Turkey. Dole na duba lafiyar nan," ya fa?a da zuciya cike da ?udiri.

Wayarsa ta shiga ?ara cikin ladabi da nutsuwa. Ya ?aga wayar yana fa?in, "Assalamu alaikum."

Cikin girmamawa, hadimi daga fadar masarauta ya sanar masa cewa, "Mai Martaba yana bukatar ganinka da sassafe gobe cikin gaggawa."

"To, na ji. Za a same ni," ya ce cikin sanyin murya yana sauke numfashi.

Cikin zuciyarsa sai ya raya, "Kenan Haneefah ta kai ?arar nan zuwa fada? Ashe ta gama tsinke igiyar zamanmu kenan?"

Nan take ya kira P.A ?insa yace masa, "Ka shirya tafiya nan da ?arfe takwas na dare. Ina so komai ya zama shirye."

Da isa gidansa, As'ad bai tsaya ko'ina ba sai kai tsaye zuwa bangaren Ayshatu, wanda aka kawata da kayan ado na zamani, dukiyarsa ta bayyana ta ko'ina cikin ?akin. Ayshatu tana zaune kan kujerar alfarma, tana waya cikin yanayin ?asaita, kafa ?aya kan ?aya tana wasa da igiyoyin gyalen jikinta.

Ganin As'ad ya shigo yasa ta yanke wayar cikin sauri, ta taso cikin ?an kissa da ladabi, ta rungume shi cikin wani ?an sanyi da sassanyar murya tana cewa, "Sannu da zuwa, Habibie. Na jima ina jiran dawowarka."

As'ad ya yi murmushi ka?an yana dubanta da tausasawa, "Ayshatu, yaya gidan yau?"

"Lafiya ?alau, Alhamdulillah." ta amsa masa cikin wata irin ?ayatacciyar murya mai cike da jan hankali.

Ya ?an lumshe ido cikin ?an gajiya yace mata, "Ina da kiran gaggawa daga fada. Mai Martaba yana nema na yanzu. Ko za ki iya shirya wa mu tafi tare?"

Ayshatu ta ?an yi murmushi cikin salo da jan hankali tace, "A'a Habibie, yau kam jikina ba ?wari sosai. Har yanzu ban huta ba. Amma ka je dai, ka gaida min Mai Martaba sosai, Allah ya kiyaye mini kai."

Ya ?an murmusa ya ?aga kai, ya fita cikin sanyi da girmamawa.

Amma yana fita, Ayshatu ta koma zaune cikin wata irin muguwar dariya ta mugunta da ?issa. Dukiyar gidan da ?ayatattun kayan ado da fitilun zinariya suka haska fuskarta mai cike da murna. Tuni direbanta ya sanar da ita cewa Haneefah ta bar gidan, kuma wannan abu ya zame mata babban farin ciki mara misaltuwa.

"Ai wallahi babu kai babu wata diya mace a duniyar nan, As'ad. Yanzu na gama cin nasarar mallake zuciyarka gaba ?aya." Ta ce cikin yanayin kissa da cikar buri, zuciyarta cike da alfahari da gamsuwa.

*****

Hajja zaune take a saman wata babbar kujera ta zinariya mai shimfidar tattausan bargon alharini. Fuskar ta cikin damuwa sosai, idanunta sun yi jajir saboda zafin hawaye da ke neman cinyeta. Kanta ya sunkuye tana ta share kwallar da take fita, zuciyarta na cigaba da ra?a?i kamar ana watsa mata garwashin wuta.

Fiddausi dake zaune kusa da ita, cikin tsananin bacin rai ta sake kallon mahaifiyar tata ta ce cikin yanayi mai kaifi, "Hajja wai ba kuka za ki yi masa ba? Kin manta irin abinda kika yi mini lokacin da matsalar mijina ta taso? Wannan abu da kika yi maraba da shi ne, kika goyi bayana . To yanzu me ya canza da kika shiga damuwa haka?"

Hajja ta ?ago da idanuwan da suka yi jajir saboda kuka, tana kallon Fiddausi da wani irin yanayi na rauni da takaici. Baki na rawa tace, "Ba za ki gane ba Fiddausi. Wallahi ba za ki fahimci irin tozarci da wannan yarinyar ta jawo mana ba. Ba za ki iya fahimtar yadda zuciyata ke ra?a?i yanzu ba. Wannan magana ta rage wa As'ad daraja, girmansa ya sauka, mutuncinsa ya karye! Kuma wallahi zuciyata bata yarda cewa Haneefah gaskiya take fada ba. Wannan makircin Fulani Maryam ne! Ina sane da yadda take!"

Fiddausi ta girgiza kai cikin takaici tana cewa, "To ai ni na san wannan. Wallahi ni ba zan yi kaffara ba! Kin san wannan matar nan tasa mai suna Ayshatu? Wallahi malamai take bi tana hana masa zama da matansa. Wannan matsalar ba daga As'ad ba ce, daga wannan matar ce! Ku dai kalle ta fa da kyau, baku ganin yanayinta?"

Hajja ta ?an dago hannu tana jan numfashi cikin rawar murya tace, "Ke Fiddausi ki yi shiru mana! Ai matar mutum kabarinsa ce. Duk yadda kika ga mutum da matarsa, to, Allah ya tsara hakan. Idan akwai matsala to daga Ubangiji ce. Amma wallahi matan As'ad ba masu zama bane, na riga na san haka tun farkon faruwar wannan lamarin."

Fiddausi ta ?an yi shiru, sai kuma ta ce cikin yanayin sanyin murya da tausayi, "To Hajja na yi shiru, amma gaskiya ki daina kuka, ki koma ga addu'a domin ita kadai ce mafita. Kukan ba zai magance komai ba. Yanzu lokaci ne na addu'a da neman taimakon Ubangiji."

Hajja ta sake gyara mayafinta, zuciyarta na cike da damuwa, hawaye kuma na cigaba da bin kuncinta a hankali cikin zafin zuciya.

***

A wannan lokacin kuma, a wani ?angaren daban na garin, As'ad yana cikin wani yanayi na tsananin kunci da damuwa. Duk da cewa ciwon kai yana yi masa azaba, amma zuciyarsa ce ta fi jin ra?a?i saboda wannan mummunar magana da Haneefah ta kai fada.

Zuciyarsa ta ?aure tamkar an yi masa ?aure da igiyar azaba, yana ganin yadda wannan abu zai yadu cikin gidan sarauta, za a zagaya da zancen ko'ina. Wannan ba ?aramin tozarci bane ga mutum mai daraja irin tasa. Duk dukiya da izzar da yake ji, sai ya kasa jure wannan tozarci da aka masa.

Ya zauna a gefen gadon alfarma mai shimfida ta musamman, idanunsa suka cika da hawayen zafi. Ya lumshe ido yana ambaton sunan Allah, zuciyarsa ta cika da ra?a?in takaici, "Ya Allah... Wannan tozarci ne fa da aka yi mini haka? Ta yaya zan iya kallon fuskar Hajja bayan wannan abun kunyar da aka yi mini? Ta yaya zan sake tsayawa cikin jama'a?"

Da wannan tunanin yaji tsigar jikinsa na tashi saboda tsananin ?acin rai. A gaggauce ya mike ya shiga cikin bandaki wanda aka kawata shi da fitilu masu ?yalli da madubai Ya yi wanka cikin hanzari, ya shirya cikin wasu kayan alfarma masu kyau da ?aukar ido.

Da ya fito daga ?akin nasa kai tsaye motarsa Mercedes Benz ta alfarma ce mai launin ba?i ta fisgi hanya zuwa filin jirgin saman da jirginsa ke jira domin ?aukarsa. A cikin yanayi na damuwa da tashin hankali suka isa garin da za su sauka.

Ko da suka isa babban otel ?in da aka kama masa, mai ?auke da ?akuna masu ?yalli da alfarma, duk wannan bai hana zuciyarsa ra?a?i ba. Duk gajiyar da ta yi masa yawa a jikinsa, amma bacci ya ?i zuwa gare shi. Ya juya gefe gefe yana jin zuciyarsa na tafarfasa cikin damuwa.

Ya sake ?ago idanunsa da suka yi jajir da zafin damuwa ya kalli halittar gabansa wadda take kwance ba tare da wani motsi ba. Ya ji wani azababben ra?a?i yana cizon zuciyarsa, cikin wata irin damuwa da takaici ya lumshe idanunsa yana furta, "Ya Allah, ka kawo mini mafita daga wannan jarrabawar da ka jarrabce ni da ita. Wannan abu ya fi ?arfin zuciyata da tunanina."

Sai dai ko yaushe ya rufe idonsa wannan mummunar magana ce take cigaba da yawo cikin zuciyarsa da tunaninsa, tana ?ara masa ra?a?in da ya gagara zama cikin ransa.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH

SHAFI NA TALATIN

Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435

Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********