
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 37
...... She felt some dummmm.... his last words should have made her happy..... his last words should have made her happy....... but she didn't get it. That's what she was running for. He didn't know what made her put her hand on top of his hand on her waist, and she gently squeezed him to loosen his hold on her. "What you are thinking is not in my mind..... let's worship... the sultan said let's do it..." He squeezed her hips even more, until she could feel his fingers in the skin of her stomach. He eased this height of his and bent down to her mouth, which wasted a great opportunity to stop his eyes looking more than usual. These eyes, which have abundant eye lashes, are white as if they are not the eyes of a man. "Worship?...... there are different types of worship...... it's not Umrah, it's just worship...... that's also a thing of worship". It was as if he blew the wind out of her in the winter, so the extreme shyness made her start to feel it in her body. She was searching for a place to heal but there was none, only his body was standing in front of her. Now, what has brought this talk of fisabilillahi?. Is it the same?, is it the same as the others? "Are you afraid?........y
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 37*
"Kina zaton idan naso kamaki kina da wani sauran dabaran guduwa ne a hannuna princess akhnan?" Yayi maganar da wani coolness daya daki zuciyarta. Halittar BURGEWA taji tana kafa sansani cikin ruhinta. Burgewa......yadda yayi maganan ya wani burgeta,ya wafci idanu da hankalinta,har ya sanya zuciyarta ta wani irin motsawa da kalar qarfin daya sanyata taji kamar iska dake dakin ta mata kadan,ko kuma shi ya zuqeta tas.
Idonta ta kalmashe kawai tana sauraren kalmominsa dake fita a jejjere da wani irin isa da izza.
"Kin gama wasan buyan?.....ko na qara miki lokaci biftu?" Ya sake kiran sunanta a qarshe da wani yanayin data tabbatar inda qwayoyin idanunta a bude suke......tabbas da ya gama cutarta......inda qwayoyin idanunta a bude suke........tabbas......ba iya zuciyarta kadai ba.....zai iya karanta rayuwarta ta baya ma gaba daya.
"Ki sassauta........bana nufin abinda ke kike tunani" Ya fada yana sassauta riqon da yayi mata.
Wani dummm taji....kalamansa na qarshe daya kamata taji farinciki.....kalmarsa ta qarshe daya kamata ta faranta mata rai.......amma saitaji batayi mata ba.
Abinda take gudu don shi.......a fakaice ya gaya mata baya gabansa kenan?.
Batasan me ya sanyata dora hannunta saman nasa hannun dake qugunta ba,ta kuwa xameshi a hankali don ya sassauta riqon da yake mata din.
"Abinda kake tunani ba shine a raina ba.....ai ibada mukazo yi.....ita sultane yace muyi...." Sake matse qugunta yayi fiye da dazu,har tana jin yatsunsa sosai cikin fatar cikinta.
Ya sassauta wannan tsahon nasa yana sunkuyowa daidai bakinta,abinda ya bata wata babbar dama na qarewa idanunsa kallo fiye da kullum. Idanun nan dake dauke da wadattatun eye lashes,farare qal kamar ba idanun namiji ba.
"Ibada?......ai ibadar ma nau'i nau'i ce......ba umra bace kawai ibada......shima wancan abun ibadar ne". Kamar ya kada mata sassanyar iska cikin hunturu haka matsananciyar kunya ta sanya ta fara ji cikin jikinta. Neman inda zata cure ta cukuikuye takeyi amma babu,sai jikinsa kawai dake tsaye a gabanta.
Yanzun me ya kawo wannan maganar fisabilillahi?. Shima haka yake?,shima d'aya yake da sauran?.
"Kina tsoro?........bai kamata ki dinga tsoro kan abinda yake da nisan tazara tsakaninki dashi ba" Ya fada yana zare yatsunsa daga qugunta a hankali.
"Idan naso......numfashinki me zai zama ba naki bane......a duk sanda zai fita daga qirjinki zai fita ne yana ambaton sunan muhammad haisam......zan sace baccinki......zan gudu da nutsuwarki.......tunaninki gaba daya zan mallakeshi.......ta yadda zaki zama baki da wani sauran xabi.....bakya gane komai sai abinda haisam ya shirya ya kuma tsara miki". Wani irin ego nata ya motsa......wanda yake cakude da tsoro.
Anya batayi wani abu na ba daidai ba kuwa da yasa yake ganin yana da dukkan wadannan damarmakin.
"Allah ya sawwaqe" Ta fada da wata karyayyar murya. Batason yasan me take struggling dashi.....bata shirya bashi kowacce qofa ba.....saboda bai dace ya fara fitowa daga sashenta ba......bai kamata ace daga bangarenta bane komai ya fara.
"Allah ya sawwaqe?,really?" Ya fada fuskarsa tana fadada da wani abu da yafi kama da murmushi,ya dage dukka girarsa sama da alama yanason samun amsa ta gaskiya.
"Eh......Allah ya tsareni......har yanzu......ba wani namiji daya cika wadannan sharuddan da qa'idojin" Wani sassanyan murmushi daya sanya har fararen haqoransa a jere reras ya saki,ya sake taku biyar baya yana bada tazara a tsakaninsu,idanunsa kuma still cikin nata,ya riqe qugunsa da hannayensa gaba daya kamar me nazarin wani abu daga gareta.
"Au.....eh fa.....na manta wannan din me tsada ce,princess of agadez.....bai kamata almajiiri irina yayi tunanin samun komai haka da sauqi bafa ko?" Ya qarashe da sigar tambaya.
"Basai ka yaudarar dani ba bayan yaudarar da sultane da kayi......na sani.....wanda yake magana kamar yana da ikon mallakar zuciya da numfashin mutum… ba almajiri bane.” samun kansa yayi da harde hannayensa a qirjinsa da wani kalar murmushi dashi kansa yasan yakan jima adane a fuska da qirjinsa kafin irinsa ya fita. Sai abu na matuqar burgeshi da daukan hankalinsa tukunna.
"Amma kuma......idan kana ganin zaka mallaki tunanina......to har yanzu baka sanni ba tukunna. Don kana magana ne kamar wanda ya riga ya samu nasara......amma kuma har yanzu ban baka wannan damar ba"
Wannan karon murmushinsa yafi na dazu fadada. Ya zare hannunsa yana tafashi a hankali.
"Bravo princess......." Ya fada da murmushin nan akan fuskarsa.
"Shi yasa kika dinga bincike a kaina a boye?" Ya dan matsa gabanta kadan
"Kina tunanin na yaudareki harda sultane?" Ya sakeyin shuru na second biyu.
"Kinason sanin wanene ni?...." Ya qara fada da wani softness cikin sound dinsa.
"Da gaske?" Ya mata tambayar kaman da gaske amsarta yakeson ji,sai kuma ya dora yana maida mode dinsa na farko,miskilanci da izza
"Ki kula da abinda kike bincike sosai a kai"....
Wannan karon tsoron dake ranta ya ninka wanda takeji a kansa a baya.
" Ta yaya?,ta yaya ya sani?,ta yaya yasan ta fara bincike a kansa?,saidai izzarta ba zata bari yaci nasara a kanta ba.
"Bincike?" Ta fada tana jan numfashi a boye,saidai duk yadda takai ga boyewar ya ji kaman yadda yake da kaifin jin abu komai qanqantarsa.
"Ba kowanne abu bane ake kira bincike....." Ta furta da confidence tana qoqarin kaucewa haduwar idanunsu.
"Wani lokaci mutum yana qoqarin fahimtar abinda yake gabansa ne kawai......idan hakan ya sanyaka kaji kamar ana leqenka....." Saita dan dakata tana tattara courage dinta.
"To wataqila akwai abinda kake boyewa fiye da yadda kakeso a gani".
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Wow" Wani bangare na zuciyarsa ya amsa a nutse ba tare daya furta ba da dukkan qarfin da suka amsa cikin bangwayen zuciyarsa. Tsakiyar idanunta kawai yake kalla. Wannan qwarin gwiwar......wannan zarrar......wannan tsaiwar kafiya da taurin kan......dukkansu.....dukkansu wasu abubuwa ne daya karanta tattare da ita,wasu halaye da yaji sunyi masa.
Taurin kai.....zarra kafiya da tsaiwa kan ra'ayi.....ba'a samunsa tattare da lusarin mutum da baisan yau dinsa ba ballantana gobensa. Wasu alamomi ne dake nuna CIKAR MUTUM na sani da ikon zabar meye ya dace dashi.
"Okay.....na baki daman ci gaba da bincikata....saidai na miki alqawari........ina miki albishir ba zaki samo komai tattare da wannan muhammad din ba.....kince Allah ya sawwaqe ko?" Yayi maganan duka lokaci daya.
"Let's play a game mana......ni dake.....duk wanda yayi winning........i mean,duk wanda yayi nasarar hana dan uwansa satar zuciyarsa......ko ni nayi nasarar saceta.... Akwai wata sadaukarwa da daya zaiwa daya,zai.bashi abinda bai taba tsammani ba....agreed?"
Cikin jikinta takejin kamar akwai wani abu daban.....kamar akwai wani abu da bazata iya daukarsa ba.....
"Ni ban iya satar zuciya ba.....amma nasan yadda zan kare tawa" Ta furta ba tare data shiryawa fadin hakan ba. Dariya ce taso qwace masa saboda yadda tayin......dariyar daya manta rabonsa da yayita,saidai wannan ginshirar da izzar ta danneta ta maidata qasaitaccen murmushi.
"Kina tsoro ne?"
"Ni.....tsoro?....."
"Yes.....kada ayi nasara a kanki".
"Ba'a nasara a kaina....koda yaushe nice nake nasara a rayuwata"
"Har a hippodrome?" Ya jefa mata tambayar a bazata,ta kuma sauka a kunnuwanta a bazata din data tilastata waigowa da wani irin zafin nama.
Fes idanunta suka samu kyakkyawan matsugunni cikin nasa. Idanun da suka soma narke mata a hankali.....a hankali suna dawo mata da komai yadda ya faru. A wancan ranar.....a wancan lokacin.
"Boyayyen mutumin Niamey?,hippodrome?" Labbanta suka motsa a hankali ta furta da wani irin low tone. Zare nasa idanun yayi a hankali,sasaauqan murmushi yake saki,bai kuma bata amsa ba ya fara takawa a hankali yana zura tattausan takalminsa cikin qafafunsa. Takalmin da yayi wani kyau yayi ladabi sosai cikin qafarsa....asalin takalmin gidajen sarauta na oromo.
"Game started" Kawai ya fada a hankali yana nufar qofa. Har yakai qofa bata motsa ba,sai daya bude ya sanya qafafunsa a waje sannan yace
"Dates farm zamu in sha Allah" Maganan ya bata qaimin data iya cira qafafunta da qyar.
Range Rover Autobiography ita ga ya nufa a nutse. Ba yadda ya doshi motar kai tsaye kawai ba.....asalin tsada da darajar motar......yadda ya buda motar da muqullin dake hannunsa kai tsaye ya sake d'aureta kaman yadda ya saba. Ya taka a hankali ya zagaya seat me zaman banza,ya bude mata murfin.
Kallonsa tayi kadan,har yanzu kokwanto a kansa yana sake nuqurqusar zuciyarta,amma saita dake ta taka tana shiga motar. Hannunsa ya saka ya tattare mata rigarta cikin nutsuwa,sannan ya rufe murfin motar softly.
Yadda yake zagayawa ta gaban motar zuwa nasa seat din cikin karsashi da wani irin kuzari yaja hankalinta. Da idanu ta bishi,maganganunsa suna dawo mata.
"Yana da zarra.....yana da zarra irin ta isashen namiji" Ta gayawa kanta da kanta tana lumshe idanunta a hankali. Tako ta ina nema yake ya qure mata,salon iya maganarshi daban ne,kaman sai ya zabi kalmomi yake amfani dasu,kamar kuma yana da iyakacin kalmomin da dasu kadai yake amfani idan zaiyi magana.
Qamshinsa ya mamayeta,kusancin dake tsakaninsu ya mata girma,mamakin kuma yadda zai tuqasu da kanshi ya sanyata kasa motsi.
"Bismillah" Ya fada yana qoqarin tayar da motar. Kasa jurewa tayi jin ya kunna motar,cikin tsoro takai hannunta saman nasa ta riqe sosai.
A nutse yadan daga idanunsa yana dubanta,idon nata ya masa wani irin kala da wani irin haske sanda ta juyashi tana dorashi saman dashboard din motar,tsoro fal cike da blue eyes dinnan nata.
"Ka tsaya!" Ta fada adan rude da muryarta data fara rawa.
"Me ya faru?" Yayi tambayar a nutse ba tare daya zame hannunsa daga cikin nata ba,saidai ya taka motar da kyau ta fara gangarawa da wani kyakkyawan tuqi.
Zuciyarta tadan tsaya cak,ta soma bin gabanta da kallon,yadda yake sarrafa steering cikin wani irin qwarewa kadai ya isa ya bata amsar abinda take kokwanto.
A kunyace ta zame hannunta daga cikin nasa,ta danyi qasa da kanta,yadda yayi shuru yana saurarenta nauyi yake sake mata akai,saita yanke kawai kawo qarshen shurun.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽