
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 30
..... seeking to shake our honor and dignity. By God, my sadness is stronger than what I can explain to you." As'ad closed his eyes weakly, feeling his heart grow more worried. "I'm sorry Hajja. God knows that this thing happened without my knowledge, and by God, I have tried many different medicines but we could not see the problem in medicine. It is said that I am weak, but I went to see a great doctor. I am in a situation that I cannot explain to you." And this is how God tests his servants. Keep your heart open, accept the risk, but do your best to find a way to solve your problem secretly and wisely. And don't forget that prayer is the solution to everything." Hearing this, he nodded his head as if she saw him, and said, "Insha Allah, Hajja, I will do it. Thank you for this word of strength." She said to him again with care, "I pray for you day and night, may God show you the truth and give you your dignity. Don't let this thing break your heart or your dignity." He said with a heavy heart, "Thank you Hajja. God bless you." He turned off his phone.
Da ?yar As'ad ya samu bacci ya ?auke shi, amma kafin gari ya waye sai ya farka, idonsa na cigaba da ra?a?in da damuwa ta haifar masa. Da asubah ya tashi ya yi sallah cikin wata irin zuciya mai nauyi, daga nan ya zauna yana ambaton Ubangiji da addu'ar neman mafita.
Bayan ya gama addu'o'insa, sai ya ?auki wayarsa cikin sanyin jiki ya kira Hajja. Duk da cewa zuciyarsa tana cike da kunya da nauyin wannan magana, bai iya hana kansa neman ta ba, saboda yasan tana cikin damuwa sosai hajja uwa ce wacce take mutukar son yaranta kasancewarta ita ba jinin sarauta ba Allah yayi ne dai ta auri sarkin.
Kusan sau uku wayar tana ?ara amma babu amsa, sai daga baya Hajja ta ?aga murya a sanyaye cikin tsananin raunin zuciya tace, "Assalamu Alaikum, As'ad."
Sai da muryarsa ta ?an yi rawa kafin yace, "Wa'alaikumus salam Hajja. Ina kwana? Ina fata lafiya lau."
Hajja tayi ajiyar zuciya sosai, ta share kwallar da ta fara zubo mata tace cikin nutsuwa, "As'ad, ba lafiya ba ce ka sani. Wannan abu da ya faru yana neman girgiza mana mutunci da martaba. Wallahi ba?in ciki na ya fi ?arfin abinda zan iya bayyana maka."
As'ad ya lumshe ido cikin rauni yana jin zuciyarsa ta ?ara damuwa. "Ki yi hakuri Hajja. Allah ya sani ba da sanina bane wannan abu ya faru, kuma wallahi Na gwada magunguna kala kala amma munkasa ganin matsalar a likitance ance kalou nake amma zanfita asatin nan naga wani babban likitan ina cikin wani irin hali da ba zan iya bayyana miki ba."
Hajja ta ?an yi shiru kafin ta ce da shi cikin hikima da nutsuwa, "As'ad, ka san kai ?an gidan sarauta ne. Kuma haka Ubangiji yake jarrabar bayinsa na ?warai. Ka daure zuciyarka, ka karbi ?addara, amma ka yi ?o?ari ka nemo hanyar magance matsalarka cikin sirri da hikima. Kuma kar ka manta addu'a ce mafita ga komai."
Cikin jin da?in wannan magana ya gyada kai kamar tana ganinsa, yace, "Insha Allah Hajja, zan yi ?o?ari. Na gode da wannan kalmar karfin guiwa."
Ta sake cewa da shi cikin kulawa, "Ina maka addu'a dare da rana, Allah ya fito maka da gaskiya kuma ya ?aukaka maka darajarka. Kada ka bari wannan abu ya karya maka zuciya ko kuma martabarka."
Cikin ra?a?in zuciya yace, "Na gode Hajja. Allah ya saka da alheri."
Ya kashe wayar zuciyarsa ta ?an yi sassauci, amma kuma nauyin damuwa bai sauka ba.
*****
Dagarin Allah yawaye, As ad ya sakko kasan hotel din inda motar alfarma ta fada ta zo ta ?auke shi kai tsaye zuwa fadar mai martaba. Zuciyarsa tana cigaba da buguwa cikin damuwa da fargaba, saboda ba shi da tabbacin yadda mai martaba zai kar?e shi.
Lokacin da aka sanar da isowarsa, Wambai ya shigo da sauri cikin ?akin mai martaba ya sanar da zuwansa. Mai Martaba ya ?aga hannu cikin alfarma ya ce, "A shigo da shi."
A hankali As ad ya shigo cikin fadar, inda ya samu mai martaba zaune cikin matsayinsa na sarki, sauran manyan fadawa da sarakuna masu martaba suna zaune cikin girmamawa. Ya dur?usa gaban mai martaba cikin ladabi yana cewa, "Ranka ya da?e, barka da safiya."
Mai Martaba ya ?an kalle shi da ido mai cike da iko da izza, sannan ya ce, "As ad, kana sane da abin da ya kawo ka nan yau. Wannan magana da ta fito daga bakin matarka, ta girgiza martabar wannan fada kuma ta girgiza martabarka kai kanka."
Cikin sanyin murya, As ad yace, "Ranka ya da?e, wallahi wannan abu ya fi ?arfin tunanina. Yafada yana jin wata matsananciyar kunya da kuma tozarta.
Mai Martaba ya ?an daure fuska yace, "Ka san dai irin gidan da ka fito, kuma ka san darajar da ke gare ka. Ban yi tsammanin zan taba jin irin wannan magana a cikin dangina ba. Amma saboda na san kai mutum ne mai hankali da nutsuwa, zan ba ka damar ka binciki matsalarka cikin sirri, kafin wannan magana ta fita daga ikonmu gaba daya."
As ad ya yi numfashi cikin jin sau?i, yace cikin ladabi, "Na gode ranka ya da?e.
Bayan anyi sallar azahar Mai Martaba Sarkin zaune yake a saman kujerar sa, yana sauraron karar Haneefah da As ad cikin natsuwa da izza, a gefe kuma manyan fadawa da dattawan gidan sarauta na kallon shari ar da zuciya ?aya.
Haneefah ta shiga zauren cikin tsantsar kamala da nutsuwa. Shigar alfarma ta mata ce a jikinta, fuskarta cike da tsantsar ladabi.
Da ta dur?usa cikin ladabi, ta ce cikin muryar da ta cika zauren Mai Martaba, ranka ya da?e. Ni Haneefah, bana iya ci gaba da zaman aure da As ad.
Wani ?aramin surutu ya fara tashi daga gefe, amma Mai Martaba ya ?aga hannu alamar shiru. Me yasa, Haneefah? ya tambaya cikin tsantsar natsuwa da hikima.
Ta sadda kanta ?asa, ta ce Auren da ba ya cika min bu?atata a matsayin mace bai da daraja a wurina. Ina girmama As ad, amma gaskiya itace zan fa?a gabansa ba ya aiki. Kuma ni ina bu?atar zaman aure na gaskiya.
Zaure ya dauki shiru. As ad ya dur?usa, bai ce komai ba. Kamar dutse, ya makale a inda yake. Kamar izzar da ke jikinsa ta narke gaba ?aya.
Mai Martaba ya dafe sandar zinariya, ya ?an jinjina kai cikin takaici. Zancen da ya fito daga bakin mace cikin gaskiya, ba a rufa shi da ?arya. Idan har haka lamarin yake, kuma ba wata mafita, to
Ya juya ya kalli As ad, "Ka saketa cikin mutunci. Kuma na baka izinin a ?aura maka aure da mace mai nutsuwa da hikima wadda zata kula da kai da darajar gidan sarauta."
As ad ya kasa ?aga kai. Cikin sanyi da radadi, ya furta: "Na saketa."
*****
Cikin sanyin dare mai cike da sanyi da hasken farin wata, motar As ad ta fice daga farfajiyar fadar sarki cikin wata irin hanzari. Duk da ?an?anin wannan tafiyar, ya ji kamar ya shafe shekaru masu yawa yana barin wurin. Ba haka ya so ba, ba haka ya yi tunani ba, amma shi fa mutum ne, ba shi da iko akan ?addarar Ubangiji.
Gaba ?aya fuskarsa ta sauya daga As ad ?an gidan sarauta zuwa As ad wanda aka ?ora masa tozarci mai zafin gaske. Kamar wanda aka ?aure wa igiyar kunya da takaici, zuciyarsa tana azabtar da shi, tana ?ara masa ra?a?in jin cewa ya rasa abin da ya fi kowane abu daraja ga namiji girman mutunci.
Direbansa ya kai kallonsa a hankali cikin madubin mota, sai dai kuma bai iya tambayar komai ba, domin ganin yadda zuciyar Yarima As ad ta matse cikin mayuwancin hali.
Lokacin da suka iso hotel , ko tsaya gaisawa da masu hidima bai yi ba kai tsaye ?akinsa ya nufa, yana jin kansa kamar an ?aure masa nauyin da bai ta?a jin makamancinsa ba. Bai cire tufafinsa ba, bai yi wanka ba, ya zauna bakin gadonsa cikin tashin hankali, idanunsa suka cika taf da hawaye masu dumi.
Ya Allah, wannan wane irin abu ne ya same ni haka? ya furta cikin sanyin murya mai cike da ra?a?in zuciya. Ni As ad, an kira ni mara kuzari, rago, wanda mace ba ta bukata?
Ya lumshe idanunsa, zuciyarsa ta yi masa zafi sosai har yake jin kamar tana ?una. Tunawa da yadda Haneefah ta zubar masa da mutunci a gaban Mai Martaba da manyan fada ya ?ara cizon zuciyarsa. Ya rasa yadda zai iya ha?a ido da kowa a cikin gidan sarautar nan, musamman mahaifiyarsa Hajja Sa adatu.
Babu wata uwa da za ta so jin cewa an kira ?anta da marar amfani, wanda ba shi da wani ?arfi ko kuzari, ya sake fa?a wa kansa cikin tashin hankali, yana jin numfashinsa na fita da ?yar saboda ?uncin zuciya.
Gaba ?aya ya kasa kwanciya, bacci ya ?aurace masa, kuma duk lokacin da ya lumshe ido, sai maganganun Haneefah suke dawo masa suna zagaye masa cikin kai kamar faifan rediyo. Ba zai iya jure wannan tozarci ba, ba zai iya zama ya zuba ido ba. Sai kawai ya ?aga waya cikin hanzari, ya kira PA ?insa yana umarnin cewa
Ka shirya komawa gida, bana son ko da kwana ?aya ya riske ni a wannan gari.
PA ?in nasa ya yi ?o?arin yi masa magana, amma muryar As ad ta fito da tsananin damuwa da ?arfin zuciya
Ban bu?atar tambaya, kawai ka tabbatar jirgin ya shirya kafin gari ya waye.
A cikin wani ?an lokaci ka?an, komai ya shiryu domin tafiyar Yarima As ad. Da sassafe, jirgin As ad ya bar filin jirgi yana mai ?auke da zuciya mai cike da damuwa da nauyin kunya.
Yana zaune cikin jirgin, idanunsa sun yi jajir da rashin bacci, zuciyarsa ta ?ara cika da ra?a?in da ya hana shi nutsuwa.
Hawayen da suka taru cikin idanunsa suka fara gangarowa kan fuskarsa a hankali. Bai yi tunanin ranar da zai shiga irin wannan halin ba. Sai dai babu yadda zai yi, domin haka Ubangiji ya tsara masa ?addararsa.
******
A wannan lokacin kuma, gidan sarautar ya zama tamkar an kunna wutar gulma wacce ke bazuwa da hanzari a dukkan lungu da sa?o na fada. Ba wani abin da ake magana sai tozarci da abinda ya sami Yarima As ad.
Wasu daga cikin fadawa sun taru suna hirar ?asa-?asa da ?anana maganganu masu cike da izgilanci duba dashi As ad baya shiga harkar kowa baya magana da kowa komai nashi daban da yaran sarki shiyasa dayawa aka tsanesa duba kuma da irin dukiyar da Allah yabashi fiye da kowa ci?insu.
Wai ku ji As ad Ashe wannan girman kan nasa duk na banza ne kawai! Mutum kamar shi ace wai bai iya komai ba wajen mace? wani daga cikinsu ya ce cikin dariyar ?as?anci.
Wata kuma ta ?auki zancen tana cigaba da fa?in
Wannan magana ta wuce tunanina. Ai wallahi sai yanzu na gane cewa duk wannan izzar da yake yi mana a fada, babu komai a ciki sai rawar kai kawai. Ashe gabansa ma bai iya tashi ba?
Wata mai hidima tana zaune tana tsintar wake ta ce cikin sigar zargi
Ai ina ganin laifin matan nan nasa ne, wato Haneefah. Duk yadda mutum yake ai kamata yayi ta rufe masa sirri. Wannan fa ba karamar magana ba ce, sai ga shi har gidan sarki ta kai shi!
Wata kuma mai hikima ta jinjina kai tana cewa cikin sigar nasiha
Ai gaskiya ba abin dariya ba ne. Wannan magana ta shafi martabar gidan sarautar gaba ?aya. Amma yanzu an riga an yi, kuma an ji da kunne, an gani da ido. Yarima As ad dai ya gama shiga tasku a idon duniya.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TALATIN DA DAYA
Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435
Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********