
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 38
.....the car. Another thing to note is that he is not a fan of AC cooling at all. "Salman al-Farisy... is a great companion of the prophet S A W, his origin is a Persian man which is Iran now, He traveled a long time in search of the truth (Islamic religion) He researched from different religions until he reached Islam. The palm farm of salman al-faris, a history shows that the prophet planted 300 date palms in the whole place because salman al-farisy avenged himself and his master. he gave fruit, he did that because he did not intend to be free, because each date palm normally takes seven or eight years before it gives fruit that will reach ten. When he cried to the prophet S A W, they met him with a palm tree, the prophet S A W kept taking it and planting it, and they planted 300 heads in a short time and they gave fruit as the master said. demand.....so salman al-faris got his freedom in a short time. But some parts of history say that it is not so.....but how is it.....palms are precious things in the place of the prophet SAW, we will love dates, we will continue to eat them, we hope to get the reward of imitating the sunnah of the best creature.....
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 38*
"Na tsorata ne,ban dauka ka iya tuqi ba" Maganan ya sanya murmushi me yawan saman fuskarsa,wannan karon har ya gaza boyewa
"Kina rainani ne?" Tambayar ta sake sakata jin kunya,sai kawai tayi kamar bata jishi ba.
"Yana da kyau ki koyi tambaya kafin ki yanke hukunci" Ya fada calmly. Har cikin ranta taji maganansa yana kan gaskiya,to amma ta yaya zata iya controlling kanta da dukka wadannan baqin abubuwan da take gani tattare dashi?,ta yaya zata aminta dashi?,ya zata bari ta yarda dashi?.
Tana yarda su kasance a muhalli daya ne kawai don suna amintaccen gurin da babu cutarwa a cikinsa. Amma bayan nan gurin.....wannan gurbin....wannan muhallin.....zata sanya idanu da lura sosai a kansa......zata taqaita wanzuwa dashi a muhalli daya har sai ta gano anihi da gaskiyar WAYE SHI?.
Shuru motar ta sakeyi,shurun da sam baiyi mata dadi ba. Kaman yasan me yake kai kawo cikin zuciyarta,sai yasa hannu yana daidaita iskan Ac din dake motar. Wani abu data lura dashi,kwata kwata shi ba ma'abocin son sanyin Ac da yawa bane.
"Salman alfarisy......wani babban sahabin annabi ne S A W,asalinsa mutumin farisa ne wato iran a yanzu,Ya yi tafiya mai tsawo yana neman gaskiya (addinin musulunci) Ya yi bincike daga addinai daban-daban har ya kai ga Musulunci. Gonar dabino ta salman alfaris,wani tarihi ya nuna annabi ya shuka dabino 300 ne a gurin dukka saboda sakawa salman alfarisi fansar kansa da ubangidansa yayi,akan saiya shuka dabino 300 kowanne ya fito ya bada 'ya'ya anci,yayi hakanne don baiyi niyyar 'yantashi ba,saboda kowanne dabino a qa'ida yana daukan shekara bakwai ko takwas kafin ya bada 'ya'yan da za'aci zuwa goma. Da yakaiwa annabi S AW kukansa,suka hadu shi da sahabbai kowanne da irin dabino,annabi S A W ya dinga karba yana dasawa,sai daya dasa 300 cif,suka kama cikin qaramin lokaci suka kuma bada 'ya'ya kaman yadda ubangidan ya buqata.....da haka salman alfaris ya samu 'yancinsa cikin gajeran lokaci. Amma wasu bangare na tarihi sunce ba haka bane.....amma koma dai yaya ne.....dabino abune me daraja a gurin annabi S A W,zamu so dabino,zamuci gaba da ci,muna fatan samun ladan koyi da sunnah na fiyayyen halitta S A W" Suka qarasa masa salati tare.
Kai take juyawa a hankali,tana jin dadin tarihin sosai. Wata dabi'a data fara shigarta,har ta siya litattafai da dama na tarihin sahabbai tsakanin makka da madeena,tana son kuma ta samu dama ta karancesu gaba daya da kanta.
A hankali yaci gaba da bata tarihin salman alfarisy,jarumtarsa....hikimarsa gwagwarmayarsa da yaqunan da akayi dashi.
Shuru kawai tayi,kanta saman cinyarta,wani irin shuru me cike da nutsuwa,muryarsa kawai take tashi da wani irin laushi da sanyi.
Yana fadin komai da cikakken details.....kwanan wata da shekarar da komai ya faru. Sunayen sahabban da suke gurin da sauran abubuwan da suka wakana bayan da kafin sannan tamkar yana gurin a lokacin.
Sanda ya fara lissafa mata falalar da madeena ke dashi sai da taji tsigar jikinta tana tashi. Da gaske sunan umara da hajj kuwa take zuwa.....da gaske batasan komai akan guraren ba. Zuciyarta tayi wani irin laushi,hawaye sosai suka cika mata idanunta,qaunar gurin tana sake kamata da gaske,inama tun zuwan da take tasan duk da wadannan falalar da sauran gurare masu daraja haka.
(Ya Allah,dukkan musulmin dake da burin zuwa gurin nan don isar wanda ke kwance a gurin muhammad S A W Allah ya qaddara zuwansa......masu niyya da son komawa Allah ya cika mana burikanmu gaba daya,Allah kasa miyita zuwa,ka qaddara shahadarmu acan son hasken fuskar masoyinka muhammad S A W🙏🏽🙏🏽).
Batasan sun isa gurin ba,sai da taji motar na magana da yanayin isowarsu gurin,ya kashe motar a hankali,ya waiwaya yana dubanta. Zare seatbelt dinsa yayi,ya ya bude motar ya sauka ya zagaya ya bude mata.
Ta jima fuskarta a kife tana qoqarin daidaita hawayenta,yana tsaye harde da hannuwansa kawai yana kallonta,baice mata komai ba har sai data debi adadin mintunan da sukayi mata sannan ta gyara hijab dinta,ta daga kanta idanunsu suka hadu guri daya,saita dauke dubanta a kanshi da sauri.
Wani kyau blue eyes dinta yayi masa,wani kyau daya sanya tsigar jikinsa wani irin zubawa harsai daya dunqule hannunsa,yadan cije lips dinsa na qasa kadan,yayi taku biyu baya yana bata daman fitowa.
Tun daga farkon gurin tasan gurine bana wasa ba,gurine cike da wata ni'ima da qananun qoramu,wanda iyasu kadai sun isa sanyaya ran mutum.
A hankali zuciyarta ta dinga haske tana washewa,ta dinga taka gurin tana ganun nau'in dabinai kala daban daban,wanda tunda take bata taba ganin kalar wani ba. Kowanne kuma da sunansa da launinsa. Dandano ne ta kasa sawa a bakinta,sai taji kaman zai kalleta,zai kalle mata baki yaga yadda take tauna.
Tsaiwa kawai tayi tana kallon yadda ake loda dabino cikin boot na motar,idanunta sunyi laushi kaman yadda takejin jikinta gaba daya yayi laushi. Kanta ke mata ciwo tana jin kuma yadda zazzabin jikinta yake sake daduwa,amma kuma ba zata iya gaya masa ba.
A hankali ta sake curewa guri daya tana jin sanyin Ac din motar kamar yana son mata yawa,duk da tasani bai saka sanyin da zai dameta har haka ba.
Idanunsa akan kyawawan titunan madeena,amma haka kawai hankalinsa yake jin yana kanta. Shurun yayi yawa,ba irin shirun dazu bane wannan. Ya juya a hankali ya zuba mata idanunsa kadan sannan ya janyesu,hannunsa ya miqa kan Ac din motar ya kasheta gaba daya. Zaman da tayi yafi masa kama dana wanda yakejin sanyi.
"Kina lafiya?" Ya fada sanda ta taka a hankali zata shige dakinta. Kadan ta waiwaya ta kalleshi,sai ta daga masa kai a nutse ta tura qofar tana wucewa. Minti kusan daya yana tsaye kafin ya janye idanunsa yana duba lokaci. Already sunyi sallar isha'i a can,yau kam jikinsa hutu yake buqata,don ya samu energy na shiga Ethiopia jibi.
Ya sake ninkawa kansa nisantar masaukinsu ne saboda ita. Tun daga wancan ranar da abun ya faru.....tun daga wancan lokacin sai abun ya zame masa kamar wani jarrabi. Zai wahala ya kwnata barci bai ganshi cikin wani irin yanayi ba ita dashi. Zai wahala yayi bacci biyar guda hudu bai farka cikin buqatar wankan tsarki ba. Ya tabbatar ci gaba da mu'amalarsa kusa da ita sosai.....zuciya ce bata da qashi,komai zai iya wakana,amma a yau yadda ya gaji sosai,yana saka rai zai kwanta ne yayi bacci me dadi da bazata zame masa barazana cikin mafarkinsa ba.
_hmmmm.....anya kuwa?,yau daikam Allah yasa a tsaya iya mafarkin ma_
Ruwa me dumi sosai ya cika bathtub dashi,ya zare kayansa cikin kasala da gajiya ya shige ciki yayi luf abinsa yana jin yadda dumin ruwan ke ratsa qasusuwansa. Kusan mintuna talatin da biyar ya bata sannan ya wanke jikinsa ya fito. Sosai sumar kansa ya kwanta saboda ruwan data nada,hakanan duk wata gargasa dake a jikinsa qirjinsa da hannuwansa,ya daura towel sannan ya dauki qaramin yana rage damshin dake saman kansa.
Kaman jira ake ya fito kira ya shigo wayarsa,koda ya duba sai yaga omar ne.
"Ya salam" Ya fada yana murmushi,omar ne ya sani,bazai kirashi haka siddan ba sai ya matsanta masa,tabbas sai ya takura masa hankalisa zai kwanta. Baya raba dayan biyun kuma sai da suka gama magana da maleek sannan ya kirashi.
"Ya akayi?" Yace da omar yana daga wayar. Wata dariya omar ya saki. Baqon abune a gurin haisam din ya daga wayarka bai fara maka da sallama ba.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Captain.....kome zaka fada ka fada........amma tsokana dole ne".
" Halan kana da isashen lokaci ne ko?"
"Ko babu zan qirqirar maka".
"Alright.....bismillah" Ya fadi yana jan stool ya zauna kawai akai. Ya sani,kafin omar din ya gama iskancin tsokanarsa har jikinsa ma qila ya bushe,don haka bai damu da neman handrayer da zai busar da sumarsa ba,sai kawai yaja body cream da perfume lotion da suke sake sanya gargasarsa ajiye wani irin fitinannen qamshi ya soma shafawa yana jin omar yana duk kalar shaqiyancin da yaga dama.
Da qyar ta zare kayan jikinta ta maida gurbinsu da wata tattausar sleeping dress data tsaya iya gwiwa data zo ta tarar birra ta aje mata. Tun da yamman ta sallami birra din bayan birra ta gama komai da tasan zata iya nema a daren,don daman tasan zasu iya kaiwa dare.
Saman lallausan gadon da nannade wanda yasha shimfidar offwhite din comforter bedsheet da duvet dukka kala daya.
Sannu a hankali zazzabin dake jikinta ya fara yawa,ta soma jin zafin ita kanta a karan kanta wanda yake tafe da wani irin ciwon kai. A hankali takejin zafin zazzabin har cikin idanunta da labbanta,ta sake curewa guri guda tana fesar da iska me zafi daga bakinta.
"Bappi" Ta fadi a hankali lokacin da ta soma jin jikinta dukka yana mata nauyi,ta lumshe idanunta tana jin wani irin kadaici yana saukar mata.
A hankali ta soma jin yanayin nata yana sauyawa,daga zafin zazzabi zuwa wani irin sanyi me ratsa qasusuwa,sanyin da takejin kamar ba cikin comforter take ba,kamar wadda ke kwance a sararin da babu komai face rigar jikinta zallah
"Bappi" Ta sake fadi a hankali idanunta suna tara ruwan hawaye. Sosai ta qanqame pillow din tana cusa kanta a tsakiyarsu. Kewar sultane take.....amma sai takejin akwai wani abu daban data rasa.....akwai wani gurbi daban daba na sultane ba.....akwai wani abu daban da take kewa sama da kewar sultane.
Idanunta ta lumshe,hoton fuskarsa ya gilma mata,kafin ta iyayin komai kuma sai wata irin mahaukaciyar kewarsa ta lullube ruhi da zuciyarta gaba daya ba tare data bar mata gurbi komai qanqantarsa ba.
"Aah" Ta fada tana girgiza kanta duk da nauyin da yayi mata. Batason ta yarda ko ta aminta da abinda zuciyarta keson gaya mata. Ba haka bane.....tanajin wani kusanci ne kawai ya jawo haka wanda zayazo ya wuce.
Hankali kwance omar ke bashi dukka bayanai akan kamun mammina. Yayi relaxing sosai yana saurarensa,bayan ya gama ji din kuma ya gyara zamanshi da kyau.
"Sati daya.....sati daya nakeso su riqeta a gurinsu.....kafin satin na kammala da issue din company din,inaso komai ya gama fits lokaci daya".
"An gama......amma kamar a wayar uwargida za'a samu phone number nata?,ina buqata zan qarasa wancan binciken daka bani" Kai ya jinjina a hankali.
"Alright.....ka riqe wayar ina zuwa" A nutse ya miqe yana zare towel din jikinsa bayan ya saka boxers da moroccon jubah fara tas,jikinsa na fidda qamshin cream perfume dinsa me wani irin qamshi laushi da kwantar da zuciya ya soma takawa zuwa qofar fita ba tare daya saks bedroom slippers dinsa ba.
Numfashi ta sake ja sosai tana jin kamar yana neman yayi mata kadan,tana kuma sake cusa kanta cikin pillows din,abinda yake qara mata qarancin iskar da take shaqa.
Ya tura qofar ya bude a nutse idanunsa na sauka saman gadon dake nuna alamun akwai mutum kwance akai. Haka kawai yaji wani abu ya fusgi hankalinsa,kai tsaye ya soma takawa zuwa saitin gadon bayan ya biya ya qara hasken dakin ta hanyar kunna qwai guda daya. Saidai yana qara taku daya qafarsa ta taka wani abu,sai ya danja baya da sauri tsigar jikinsa na tashi. Brazier dinta ce fara qal yashe a qasa,sai rigar data fita da ita da under wear dinta data suma a wani gefe na daban. Idanunsa ya zare a hankali daga kan bra din,tuna tuna masa da wancan ranar.......tana tuna masa da wancan yanayin,tunin daya sanya tsigar jikinsa zubawa gaba daya,cikin second biyu kwanyarsa ta harba saqo zuwa ga gangar jikinsa. Zuciyarsa ta motsa kadan daga inda take zaune,cikin kokwanton da shakkar maimaituwar faruwar abinda ya faru a wancan ranar yaci gaba da sanyo kai cikin dakin
A nutse ya qarasa gaban gadon idanunsa a kanta,yanayin kwanciyarta,a qudundune cikin duvet ko kanta baka iya gani yasa yaji bai gamsu da yanayin ba. Hannu ya miqa a nutse yana qoqarin janyewa gami da kiran sunanta da wani irin yanayin daya ratsa har kwanyarta,kiran daya sanyata jan wani irin dogon numfashi daidai sanda yake yaye duvet din daga fuskarta zuwa saman wuyanta.
Ajiye numfashin tayi tana qoqarin sake jan wani.
"Subhanallah......me ya sameki?" Ya furta a rude yana haurawa saman gadon da gaggawa fuskarsa da muryarsa duka suna nuna tsananin rudewarsa,saidai hannunsa kadai daya dora saman sassalkar sumarta data warwatsu tsakanin pillows din dake kan gadon dama fuskarta da tayi wani fayau ya bashi amsa.
"Ya salaaaaammm" Ya fada da wani irin yanayi yana qarasa haurawa gadon gaba daya tare da qoqarin dagota gaba daya zuwa jikinsa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽