Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 34

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 34

.....orsa again. "May God have mercy on her" "Ameen amee" Ahmad and the sultan agreed to answer. "Is the body strong?" She asked him again, "We thank God." The way he spoke, she felt her heart break in the morning. That's how Safeena tells her every day until the day she leaves the world. "May God give you eternal health and the rest of the sick" "Amen" They all answered including my mother this time who coming to the place made her feel like she was a stranger, like she was isolated. "Our prince" Mammina said smiling. In a deep breath, Ahmad turned and looked at her. "When did he know all these things?" She asked herself. "When you fight, it's like you're putting a heavy weight on your heart, when you're patient with expressing your feelings about one thing". He spoke in the Oromo language to make sure that no one understood what he said, because even Morsa Safifyya understood that it was not the language of every part of her, that she had left the country and she had forgotten many things. She just smiled at him like she used to, until today she never uttered a single word to him, but he also knows, that doesn't mean anything is okay. The front of the sultan is full.....

Standalone post1,733 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 34*

"Allah ya tsinewa safeena da kabarinta dama dukkan abinda ya fito ta tsatsonta dama ahalinta gaba daya" Mammina ta fada har bakinta yana motsawa,wani abu me masifar nauyi takeji yana sauka saman zuciyarta. Ta tsanu safeena tsana mafi girma,tsanar da ko a lahira batajin zata daina mata wato bayan an mutu an gama kwanciyar kabari an tashi,dukkansu basu kai su goge wannan tsanar ba.

Ba wani dan adam a duniya daya taba kawo ma komai nata cikas sai ita.....ba wani wanda ta taba saka plan a gabanta ya zama silar wargajewarsa bayan baqar wahala datasha akai irinta. Daga ita sai IBRAHEEM,sauqinta daya.....IBRAHEEM har yanzu yana cin darajar taba sonshi da zuciyarta tayi,amma duk da haka shima saida ta barwa rayuwarsa tabo ta hanyar daukar rayuwa d'a na farki daya soma haifa a rayuwarsa.

Taimakonta daya sautin maganan da tayi baikai ga fita ba,saidai ahmad da idanunsa suke kanta ya tabbatar akwai wani abu data fada. Murmushi morsa ta sake.

"Allah yayi mata rahama"

"Ameen amee" Ahmad da sultane suka hada baki gurin amsawa.

"Ya qarfin jikin?" Ta sake tambayarsa

"Mun godewa Allah dai" Yadda yayi maganan sai morsa safiyya taji zuciyarta ta tsinke. Yanayin yadda safeena ke gaya mata kenan a kullum rana har ranar data bar duniya.

"Allah ya baka lafiya madawwamiya kai da sauran marasa lafiya"

"Ameen" Dukkansu suka amsa harda mammina a wannan karon wadda zuwansu gurin ya sanya taji kaman ta zama bare,kaman an wareta.

"Yarimanmu" Mammina ta fada tana murmushi. A nutse ahmad din ya juya yana dubanta,ya aje mata wani kallo da yanayin izzar data taba mammina din sosai.

"Wai duka yaushe ya iya wadannan abubuwan gaba daya?" Ta tambayi kanta da kanta.

"Idan kina fada,kaman kina qarawa zuciyarki nauyi ne,inda kin haqura da furtawar kiji da abu daya". Ya fada da yaren oromo daya tabbatar ba wanda zaiji abinda yace,don ko morsa safiyya ya fahimci ba yaren kowanne bangaren takeji ba,tsahon barinta qasar kuma yasa ta manta wasu abubuwa da yawa.

Murmushi kawai ta maida masa kaman yadda ta saba,har yau ko kalma daya bata taba furta masa ba,amma kuma shi ya sani,hakan ba yana nufin komai lafiya ba.

Gaban sultane ya qarasa cikin girmamawa ya tsugunna.

"Muna da baqi ranka ya dade cikin gidannan"

"Baqi?,wadanne iri?" Sultane ya fadi,don yadda yakejin jikinsa a yanzun bacci kawai yake da buqata.

"Eh baqi.....amma kamar ba gurinka kai tsaye sukazo ba.....daga babbar hukuma,alhaji nasiruddeen bahago" Jin sunan kawai ya sanya sultane tashi ya zauna sosai.

"Ba baqi bane ahmad....akwai sanayya me girma,duk sanda kuma kaga sunxo babban dalili ne ya kawosu,a shigo dasu" Ya fada yana duban Ahmad din. Kai ya jinjina a nutse,ya miqe wani sirrintaccen murmushi yana fita daga fuskarsa......ya taka a hankali xuwa qofa don bawa me wada umarni.

Tunda suka shigo gurin idanun mammina yake kansu. Haka kawai takejin akwai wani baqon al'amari a tattare dasu. Yadda suke dan kallonta daya bayan daya lokaci taji bata nutsu dasu ba. Bata duba yadda morsa safiyya ta kame daga gefe ba,suka gaisa cike da kima da dattako,suka kuma duba jikin sultane sannan suka mata barka da dawowar Ahmad ba tace.

"Kaman buqatar kwanciya sultane yake....don Allah idan ba matsala,ko zaku iya gama komai da wuri ya samu ya huta" Ta fada tana miqewa.

"Zaki zauna ne ai hajja zaituna,zuwan naki ne" Alhaji nasiruddeen ya fada a girmame.

Cak ta dakata tana dubansa,saidai kafin tace komai ya maida dubansa ga sultane.

"Allah ya baki yawan rai,ayimin afuwa nayi magana da iyali kai tsaye ba tare dana nema izini ba" Murmushi kadan sultane yayi,ba jiya ba yau ba,shekaru masu dama ne suka bada sanayyarsa da sabonsa da Alhaji nasiruddeen da kuma yanayin aikinsu.

"Ba komai......zaituna....zauna" Ya fadi yana dubanta.

Murmushinnan ta qaqalo,sannan ta koma tana zama din,a qasan ranta tana fatan wani abu ne ya taso wanda zai kuma daga darajarta.

"A daren shekaran jiya hukumarmu ta kama wasu mutane......wanda nasan labarin ya iso gareka?" Kai sultane ya gyada a nutse.

"Ma sha Allah.....munyi magana dasu,mu tuhumesu,mun kuma matsi bayanai muhimmai daga gurinsu,saidai ba yadda muka iya.....duk yadda mukaso mu kauce sunan iyalinka ya fito a ciki". Magana tasa ta qare da wani irin shuru......sannan kuma ta jona wani burkitaccen yanayi a zuciyar mammina da kwanyarta.

"Iyali waye a ciki kenan?" Tayi tambayar da sultane ya buda baki da zummar yi.

"Hajja zaituna,giwa". Ba wanda wuta bata daukewa a gurin ba,banda Ahmad da yake zaune abinsa yana gyarawa sultane rigar jikinsa.

" Ayi mana afuwa" Alhaji nasiruddeen ya fada yana sadda kansa qasa.

Shuru sultane ya sakeyi,mamaki kuma yana dan cikashi. Me ya hada iyalinsa dasu?,me ya hada zaituna kuma da Office Central de Répression du Trafic Illicite des Stupéfiants(hukumar hana fataucin miyagun qwayoyi).

Ajiyar zuciya ya sauke,yana maida idanunsa kan mammina.

"Kina da abinda zaki ce?". Kai ta juya kadan,tana qoqarin danne komai da komai da takeji. Ida aka ajiye komai ma.....ita giwa?....mace kamarta ace an shigo har masarauta bincike a kanta?.

" Bani da abinda zance.....kawai abinda zuciya da jikina suke gayamin shine......an shirya tozartani ne....ta yuwu an hada baki da abokan adawa don a bata sunanka dana masarautarmu gaba daya" Ta fadi tana fatan maganartata tayi tasiri a zuciyarsa.

"Ba haka bane Allah ya baki yawan rai...." Alhaji nasiruddeen ya fadi don kare zargin da takeson jifansu dashi,saidai kafin suce komai sultane ya dakatar dashi.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Duka wannan bata taso ba,basuce komai a kanki ba,hasalima basuce suna zargi ba,bincike kawai zasuyi don wankeki daga zargin da wadancan mutane suke jefa a kanki,so indai hakanne bana tunanin zai zama wata damuwa......."

"A shiga har gidana.....na aure da wasu garada....ayimin bincike har inda yake sirrina ne sannan na gaza damuwa?".

" Ba irin wannan binciken bane,amintattunmu ne guda hudu kawai " Alhaji nasiruddeen ya fadi da girmamawa.

Daga kanta tayi ta zube masa idanunta a kanshi. Taso ta ganeshi,koma tace ta ganeshi,kuma daga wannan aikin batajin zai sake gigin yin wani aiki daya shafi koda na qasanta ne ballantana ita.

"Na fahimta.....na fahimta da kyau,ba kuma laifi,kuna iyayi" Ta fada tana gyara zamanta sosai da yanayin saukar nutsuwa a zuciyarta.

"Mun gode" Shima ya fada yana rusunar da kansa.

"Zaki zabi da wanda zasu shiga cikin hadimanki?". Kai ta girgiza tana murmushi.

" Ba zabi.....suna iya shiga da duk wanda suka zaba".

"Ahmad......ka rakasu" Kiran sunan ahmad din kawai sai daya kada hantarta. Me yasa ahmad?,me yasa ba zaa saka wani ba ahmad ba?,ahmad daya rayu cikin wata rayuwa data bashi experience din da ko jami'an bata jin suna dashi?.

Da idanu ta bisu har suka kammala ficewa gaba dayansu,duk da wani sashe na zuciyarta yana cika da wani irin confidence.

Duk inda suka gilma cikin gidan sai idanu sun bisu. Baqon abune ganin ma'aikatan Office Central de Répression du Trafic Illicite des Stupéfiants tsakiyar masarautar haka suna tafiya kansu tsaye,tafiyar ma kuma bisa jagorancin yarima ahmad muhammad hammud. Ba wannan ba.......yadda suke dosar sashen mammina kai tsaye sai abun ya zama wani daban,abun kuma yaja hankulan duk wani hadimi dake kusa,wanda ke nesa ma labari ya fara tsalluwar masa.

Wasunsu suka fake da ayyukansu,wasu kuma suka nemi guraren da suke da tabbacin duk abinda ya faru zasu iya samu masaniya.

Duk da yawan securiy dake kula da kowacce qofa da zaka sanya qafarta ta sassan mammina,amma babu ta inda suka samu tuhuma tambaya ko kuma tsaiko saboda yarima ahmad dake tare dasu.

Alhaji nasiruddeen ya gyada kansa a hankali.

"Me yasa girma yawan adadin masu tsaro na sashen nan ya ninka na ko ina?" Yayi tambayar yana duban fuskar ahmad. Kafadarsa ya daga kadan

"Bazan ce ga dalili ba,don kusan nima har yanzu baqo ne cikin gidan" Ya bashi amsa akan salo da tsarin da aka dorashi tun farko yayin magana da baqin fuska.

A katafaren parlor dinta suka fara aikinsu,mutum hudun nan gaba daya Ahmad na biye dasu cikin qwarewa. Suka kammala da parlor din farko,suka wuce na gaba,daki bayan daki....parlor bayan parlor har suka dangane da dakin baccinta na qarshe wanda ya zama na musamman a gurinta.

Komai sai da suka bincike,suka kuma kara masa na'aura,saidai ba wani abu daya basu haske akan abinda suke tuhuma ko kuma nema.

"Muje kawai" Alhaji nasiruddeen ya fadi cikin sarewa da rashin qwarin gwiwa.

Taku biyu Ahmad yayi yana shirin sanya qafarsa waje idanunsa suka sauka kan wata waya data shigo ta window din dakin. Tsawa yayi cak yana qare mata kallo,wani abu daya taba faruwa a rayuwarsa ta baya yana dawo masa.

"Kai!....zo nan" Ya kira tamim,wanda shi ahamd ya zaba aka hadosu dashi. daurewa kawai yakeyi......amma kowanne sashe na jikin tamim rawa yake.

"Gani"

"Wannan wayar mece?"

"Ta panel ce...."

"Panel wanne iri?"

"Na Sola"

"Meye dalilin biyo da ita ta nan?" Ahmad yayi tambayar yana zubawa tamim idanu.

"Panel na solar din gidannan dukka a jimlace suke guri daya....baya ga haka ba wata waya da wani yake iya ganinta da idanu koda ta wuta ballantana solar.......meye dalilin sakawa daki guda daya wayar panel?" Ahmad ya qarashe tambayar yana duban Alhaji nasiruddeen wanda kiran da Ahmad ya yiwa tamim ya jawo hankulansu suka dawo dukkansu.

"Ku duba waccar wayar" Ahmad din ya fada yana ratsewa ya wucesu su da tamim din,saboda ganin wayar ya tuna masa wata rayuwa da yayi a baya,hawaye ne cikin idanunsa kuma bayaso kowa ya gani. Yana kan koyarwar haisam koda yaushe.

"Namiji duk inda yake jarumi ne,jarumtarka tana ninkuwa sama data saura a sanda aka haifeka shugaba....kuma a gidan sarauta....ko sau daya hawaye bai kamata ya fita a idanun NAMIJIN DUNIYA BA,idan ma ya kama zasu fita din ba'a kan idanun kowa ba". Wannan maganar ya riqe,kuma ta dasa jarumta da yawa cikin ransa.

*_Tabdijan.......rugiji gabji.....AIKE NE DAGA ME GAYYA ME AIKI ko kuma ARASHI NE?.....SHIN ME SUKE NEMA?,zasuci nasara su kama abun harinsu?,ko GIWA zatayi nata aikin na tabbatar da faduwarsu?_*

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽