
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 33
..... their faces are standing without a smile or a smile. On the other side, there are two other women, each wearing a veil, their faces are swollen from crying. The look they turned to me was full of anger, as if I was the cause of their worries. I squeezed my heart, my heart was beating fast. On the other side, I saw a curtain, which was slowly removed. My eyes landed on a man who was lying motionless, it was Khalil! I clutched my chest in panic, I said "Innalillahi wa inna ilahi raji un"... I came closer to the bed, my eyes were full of tears. Khalil is very limp, his skin has changed color. His face was covered in dark white, signs of serious illness. He didn't move very much, except for a voice that came out of his mouth in a loud voice. I heard him say, "Ramlah... if you give birth to a baby for me, name your mother... name your mother..." Tears took away my strength. I let out a kind of intense cry that came from the heart, which even if I didn't utter a word, the heart appeared. "Khalil! Is that you? I know you don't deserve this! God bless you... God bless you..." The room was filled with tears. His brothers and his mother all began to cry, they were praying. Or moving...
Tun cikin motar nake kallon yadda Maman Khalil ke kuka kukan da ke fita daga zuciya, wanda ba'a iya ?oyewa. Hannunta na goge idanu, amma hawaye na ci gaba da zuba. Ganin haka sai damuwa ta sake lullube ni. Zuciyata ta dinga bugawa da ?arfi.
Na kalleta cikin firgici, amma sai na ?auke kaina. Tambayoyi masu nauyi suka fara zagaye cikin zuciyata
Shin Khalil ne ya mutu? Ko Abba ya aiwatar da barazanar da ya yi masa? A wannan lokacin, bani da wanda zan tambaya. Bani da wanda zai bani amsa. Sai dai zuciyata na karanta mummunan abu.
Mun tsaya a gaban wani katafaren private hospital mai kyau da tsafta. Tsakar gidan cike da furanni masu kamshi, kofar shiga tana ?auke da sunan "Al-Ameen Specialist Centre."
Maman Khalil ta juyo gare ni da ido cike da ra?a?i, ta ce
Ramlah... fito.
Na sauka daga motar jikina duk a mace, numfashina ya rikice. Muka danyi tafiya ka?an cikin asibitin har muka ?arasa wani ?aki da aka kawata cikin salo fale-fale masu tsabta.
Da muka bu?e ?ofa muka shiga, sai ga maza biyu tsaye fuskokinsu babu annuri ko murmushi. Gefe guda kuma akwai wasu mata gufa biyu, kowacce tana sanye da mayafi, fuskokinsu sun kumbura da kuka. Kallon da suka juyo suka yi min ya cika da harara, kamar ni ce sanadin damuwar da suke ciki.
Na danne zuciyata, zuciya na harbawa da sauri. A gefe na ga wani labule, an yaye shi a hankali.
Idanuwana suka sauka kan wani mutum da ya kwanta ba tare da motsi ba Khalil ne!
Na dafe ?irjina cikin firgici, na furta Innalillahi wa inna ilaihi raji un...
Na matso kusa da gadon, idanuwa na cike da hawaye. Khalil ya rame sosai, fatar jikinsa ta sauya launi. Fuskar sa ta cika da fari mai duhu, alamun rashin lafiya mai tsanani. Baya motsi sosai, sai murya ?aya-?aya da ke fita daga bakinsa cikin surutu.
Na ji yana fa?in "Ramlah... idan kika haifa min baby, ki saka sunan mamarki... ki sakawa mamanki..." Hawaye suka kwace min da ?arfi. Na saki wani irin kuka mai tsanani kuka da ya fito daga zuciya, wanda ko ban furta kalma ba, sai zuciya ta bayyana.
"Khalil! Kai ne haka? Na san ba ka cancanci wannan ba! Allah ya kawo maka sau?i... Allah ya baka lafiya..."
Dakin ya cika da kuka. Yayansa da Mamansa duk suka fara hawaye, suna karanta addu a. Ko motsawa bai yi sosai .Dakin ya koma shiru. Sai sautin kuka da karanta istighfari ke tashi daga ko'ina. Na girgiza kaina cikin ba?in ciki, zuciyata kamar an caka mata ?usa mai zafi. A wannan lokaci, na fi kowa jin ?unci. Na fi kowa jin nauyin wannan halin da muke ciki.
Kamar ina mafarki... amma wallahi, ba mafarki ba ne wannan gaskiya ce, Khalil ne yake kwance babu lafiya dik wanda yagansa Sai yayi masa kuka.
Daga gefe na jiyo yayarsa da masifa, tana kuka tana fadin
"Ramlah! Wane irin asiri kika yiwa Khalil?!
Na juyo da ido cike da damuwa, zuciyata na harbawa kamar zata tsinke. Ita kuma ta ci gaba da masifa cikin kuka mai nauyi.
"Wacce irin soyayya ce haka? Tun ranar da mahaifinki ya raba ku, sai ya rikice! Ya zama kamar mahaukaci. Shaye-shaye ne kawai ke damunsa! Ki dubi yadda ya rame! Kina kallo kina kallon yadda yake lalacewa!"
Zuciyata ta kar?i kalmarta kamar an jefa mata ?aya. Na kasa motsi daga inda nake. Sai wani kuka ya ?wace min, na zube a kasa da ?arfi ina rera kuka mai ciwo.
Na kalle shi Khalil. Ya rame, ya bushe, kamar ba shi ba. Fuskarsa duk ta sauya, idanunsa sun rame, numfashinsa ba daidai ba. Na juyo na kalli Maman Khalil, fuskarta cike da hawaye. Kamar rai zai fita. Samarin yayyansa ma kuka suke tamkar yara.
A hankali na matso kusa da gadon, jikina na rawa. Na kama hannunsa cikin tausayawa, murya na rawa nace "Khalil dan Allah ka tashi."
Sai muka ji kamar daga can ?asa yana ?o?arin magana. Muryarsa da rauni sosai
"Ramlah ce?... Mama, Ramlah ce?"
A hankali ya bu?e idanunsa, yana kallona. Idanuwansa sun cika da ?auna, hawaye da ra?a?i. Ya ce da murya mai narkewa
"Ramlah... dan Allah ki aure ni. Ki gaya wa Abba kina sona. Kina kaunata ko?"
Cikin wani irin shauk i da tausayi, kuka ya ?wace min. Na kasa magana Sai dai na lumshe ido sannan nace da murya mai laushi
"Ka bar shan komai. Kada ka ?ata rayuwarka. Ina tare da kai... kullum."
Sai ya motsa kamar yana ?o?arin tashi, amma jikinsa ya gaza. Sai yayansa ya shigo da sauri, ya dagashi a hankali ya sa masa filo a bayansa. Na ji yana fa?a wa su Mama
"Su bamu wuri."
Kowa ya fice. Dakin yayi shiru. Sai ?amshi da karancin numfashin Khalil ke tashi.
Ya kalleni da ido masu ra?a?i. Yace "Ramlah kin san halin da nake ciki? Abba yace wallahi har abada ba zan auri ki ba. Wai wai zan lalata miki rayuwa."
Ya juyo da ido gare ni, yana fitar da numfashi a hankali "Amma ke kina sona ko?"
Na daga kai, idona cike da hawaye.
Ya lumshe ido cikin salama, sannan ya ce da wata kalma da ta tsayar min da numfashi
"Ke ce rayuwata. Idan na rasa ki kamar na rasa numfashina ne."
Na lumshe ido, zuciyata na bugawa da karfi. Na kasa magana. Zuciyata kamar an shake ta da igiya. Kamar numfashina yana tafiya da kowane kalmar da Khalil ke fa?i. Ya juyo yana kallona. Fuskar sa ba annuri, amma kalmarsa mai da?i da ciwo a lokaci guda.
"Ramlah..." ya kira sunana da wata murya mai taushi kamar numfashin ?arshe.
Na ?aga kai, idanuna cikin nashi, sai yace
"Idan na mutu Ramlah... idan Allah ya ?auke ni..."
Ya tsaya. Numfashinsa ya dan yanke. Sai ya ?ora hannu bisa fuskata a hankali.
"Ki saka sunana a zuciyar ki har abada. Koda kin auri wani, ki rikeni a cikin zuciyarki."
Hawaye suka fara zuba daga idona nace Kadaina fa?in haka Baza mutu ba.
Yakara fa?in "Idan kika haifi yara... ki fadi musu labarina. Kice musu akwai wani saurayi da ya ?aunaci maman su kamar numfashinsa... amma ba su da rabo."
Na fashe da kuka. Kuka mai tsanani wanda sai da ya girgiza duk jikina.
"Khalil ka daina fa?in haka... ka daina..." na ce cikin rawar murya.
Amma ya cigaba.
"Ramlah... ki yi min addu a idan na mutu. Koda duk duniya ta manta dani... kada ke ki manta."
Ya sauke numfashi, yana kallo na, sannan ya furta da ?arfi kadan
"Ni dai ina son ki Ramlah. Kuma idan na mutu... kauna ta bani daraja. Ki ce min... soyayya ta bata tafi a banza ba."
Hawaye suka ci gaba da gangarowa daga idanuwansa. Sai ya ce
Na saka kaina a ?asa, na fashe da kuka. Na ji kamar ana warware zuciyata ne a hankali. Kamar zan fita hayyaci na.
Wani irin tari ya taso masa kwatsam, har sai da na firgita. Yayi ?arfi sosai, kamar zai fitar masa da zuciya. Hankalin kowa ya tashi.
Cikin mintuna ka?an likita ya shigo da sauri. Amma maimakon fara dubashi, sai fa?a ya fara
"Me ya sa ba a ba shi abinci ba tukuna? Ta yaya ake tunanin mutum zai sha magani ba tare da komai a cikinsa ba?"
Mama ta daure fuska, cikin muryar damuwa tace
"Ai likita ba cin abincin yake yi ba. Koda ya ci, sai yamaida. Duk wani abu da ya ci, sai ya dawo da shi."
Likita ya jinjina kai yana girgiza, sannan yace
"Dole ne a daure a ba shi yanzu. Abincin ya fi magani muhimmanci a wannan lokaci."
Na juyo ina kallon Mama. Na ce da ita a hankali
"Mama, dan Allah ki bani abincin. Zan ba shi da kaina."
Ta dubeni na ?an lokaci, sai ta ?aga kai cikin natsuwa tace
"To Ramlah, nagode. Ga abincin nan."
Ta mi?o min farantin, na kar?a a hankali, zuciyata cike da tausayi. Na nufi gadon da yake kwance, na zauna a kusa da shi, ina kallon fuskarsa.
Wallahi idan ka gan shi a yanzu, sai ka sa kuka. Shi da yake namiji ne mai ?arfi da kuzari, yanzu ko jingina da kai ba zai iya ba.
Na ce a hankali
"Khalil, ka bu?e baki ka ci. Dan Allah..."
Ya ?an juyo yana kallona da idanunsa masu cike da rauni. Sai ya bu?e bakinsa ka?an. Na fara ba shi a hankali kamar yaro. Duk abincin ya cinye da ikon Allah. Bai ce komai ba, amma idanuwansa sun fa?i komai.
Na kalli agogo. Lokaci yana kusa da ?arfe bakwai na dare.
Nurse ta shigo, ta yi masa allura. Kafin minti talatin ya cika, bacci mai nauyi ya ?aukesa. Na sauke numfashi, na tashi na juyo na kalli Mama.
Na ce da ita cikin ladabi
"Mama, zanje gida yanzu."
Tayi shiru kamar bata jini ba. Sai da na maimaita sannan tace da dan sanyi
"To Ramlah, ga driver a waje zai kai ki."
Naji kamar kalamanta sun buge zuciyata, amma nayi shiru. Na mi?e da ladabi, na fita daga ?akin.
Yayyensa mata suna zaune, amma babu ko ?aya da ta kalle ni. Babu wacce ta ce min sai anjima bayan nayi musu sallama babu wacce ta yi magana. Sai zuciyata ta sake nauyi.
Na daure, na sauka har waje. Driver na jira na, na shiga mota cikin shiru. Har muka bar asibitin, babu wanda yayi magana..
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TALATIN DA HUDU
Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435
Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********