Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 40

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 40

.....she feels a kind of cold. Deeply, he looked at her eyes and put a rose in it, and he put his thumb slowly and gently rubbed the skin of her hand. "Calm down...uhnnnn.....I won't hurt you, take a deep breath and let it out slowly.....I promise you, before you finish letting it out it will be completed.....do you trust me?". Slowly, as if she had a neck pain, she raised her head. "Alright.....keep looking at me.....don't take your eyes off, I will know if you are serious" He said, closing his eyes deeply and opening them to her. She felt the needle slowly go through her skin, but it was a situation she had never experienced before. There is nothing that she is afraid of when she is going to be injected like that, seeing how he is giving her some things directly from his big white eyes to her eyes when the needle is inserted into her body. "Finished" He said slowly, pushing his chair back and letting out another breath. For the first time he felt something different.....the first time he ever felt some eyes carrying some heavy things....The weight that they kept on him some heavy things and killing the body. She looked down with her eyes and was feeling ashamed. "From injecting?

Standalone post1,911 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 40*

"Oya.." Ya fada yana sake bata hannunsa. Kaman zata tashi ta zura da gudu haka ta miqa masa hannun,ya riqe tsakiyar tafin hannunsa yana kallon tattausan farar fatar dake shimfide a singalilin hannun nata.

"Wayyo bappi....." Ta fada a raunane sanda yaje da allurar dab da fatarta. Tsaiwa yayi cak yana dubanta,ta cure sosai tana rawar sanyi,tausayinta yaji ya sake kamashi a karo na biyu,sai yake jin kaman zaiyi wani abu ba daidai ba,sai yake jin kaman zai taba amanar da aka bashi ne.

A hankali ya maida allurar ya ajiye,a can cikin zuciyarta tayi sak tana jiran taji tsinin allurar amma sai taji shuru,a maimakon hakan,sai wannan husky voice din nasa daya mamayi kunnuwanta da haruffan sunanta da taji suna ratsa qasusuwanta.

"Aakhnaaan" Sassanyan numfashi taja a boye tana saukeshi,ya sake maimaita kiran nata yana dorawa da

"Kallo nan" Bata musa ba.....don bugun da zuciyarta keyi....ya gauraya da kiran sunanta da yayi ya qara mata jin wani irin sanyi.

A nutse ya lalubo qwayar idanunta ya saka tashi a ciki,ya sanya babban dan yatsansa a hankali yana murza fatar hannunta.

"Ki nutsu....uhnnnn.....bazan miki da zafi ba,kija numfashi sosai ki fitar a hankali.....na miki alqawari,kafin ki gama fitar dashi an kammala.....do you trust me?". A hankali kamar me ciwon wuya ta daga kanta.

"Alright.....ci gaba da kallona.....karki dauke idanunki,zan gane idan da gaske kike" Ya fadi yana lumshe idanunsa a nutse sannan ya budesu a kanta.

Tana jin sanda allurar ke ratsa fatarta a hankali,saidai wani yanayi ne da bata taba kawowa zata jishi ba. Ba wani abu da takeji na tsoro ko firgici a duk sanda za'a mata allura irin haka,tafijin yadda yake sake mata wasu abubuwa kai tsaye daga manyan fararen idanunsa zuwa nata idanun akan shigar allurar jikinta.

"Finished" Ya fada a hankali yana tura kujerarsa baya yana sakin wani numfashi can qasa.

A karon farko yaji wani abu na daban.....lokaci na farko daya taba jin wasu idanu suna dauke da wasu abubuwa masu nauyi.... Nauyin da suka dinga ajiye masa wasu abubuwa masu nauyi da kashe jiki.

Qasa tayi da idanunta tana jin wata kunya tana kamata.

"Daga yin allura?,saiki saki idanu da baki kina kallonsa?.....kamar ma dai......" Da sauri ta katse zuciyarta ta hanyar takurewa gaba daya cikin duvet dinta.

"Zaki iya kwanciya don allurar yabi jikinki?,zai iya daukan awa daya zuwa da rabi saboda bana jijiya bane,yana kuma aiki ne a hankali" Ya fada sanda yake tattare kwalaben yana adanawa cikin dust bin. Kai ta gyada masa,sai ya taka a hankali ya sake gyara mata gadon.

"Getup" Ya fada a tausashe yana kallonta duk da ta boye dukka fuskarta cikin duvet din. Kai ta girgiza

"Zan tashi da kaina....zan iya" Hannunsa dake nade a qirjinsa ya sauke,ya juya ya soma takawa yana barin dakin ba tare da yace da ita komai ba.

Haka kawai sai ya gaza nutsuwa bayan ya koma dakin. Sundan qara waya da omar yace masa batajin dadi,ya bari zuwa gobe saisu qarasa aikin.

"Allah ya bata lafiya......amma dai a dinga sassautawa farin shigar nan" Bai wani yi nauyin fahimtar abinda omar ke nufi ba,don ba qanqanin yaro bane shi.

"Omar.....omar" Ya kira sunansa har sau biyu yana rasa me mai zaice masa. Wannan din ya sanya omar dariya sosai. Ba kasafai haisam ke denying abubuwa ba,idan ka fada yana barinka ne da fahimtarka kawai,amma yau din yadda yake qoqarin cewa wani abu sai ya bashi dariya.

"Nidai bance komai ba......asuba ta gari Mr lowering gaze" Shuru haisam din yayi na sakanni kafin ya sauke wayar yana dan qaramin murmushi,jikinsa ya bashi da alama gulmarsa kawai akeyi tsakanin su shidan,amma ko meye zasu hadu a Ethiopia,kowanne a cikinsu ai yasan halinsa.

Ya kammala komai ya kwanta,amma haka kawai sai zuciyarsa ta kasa nutsuwa.

"Amana ce.....amana ce a hannunka" Wannan kalmar ta sakashi sauke qafafunsa qasa,ya dauki wayarsa ba tare daya damu da sanya slipper dinsa ba ya bude qofar ya fito.

Yana tura qofar dakin yaji yunqurin amanta tun daga toilet

"Ya salam" Ya fada a rude yana qara hanzarinsa da kuzarinsa ya isketa cikin toilet din.

Dafe take da sink amma qafafunta da sukayi laushi saita kasa tsaiwa sosai,ga yunqurin aman dake sake jigatata. Wani irin riqo yayi mata cikin jikinsa yana supporting nata sosai,riqon da yazo mata a sanda take buqatar hakan,sai kawai ta sake sallama tana bar masa daman riqetan da yakeso yayi,aman ma kaman jiransa yakeyi sai gashi ta farar da amayar da tea din dukka da tasha dazun harda guntun dabinon da taci a salman alfarisi date farm.

Sosai ta amayar da komai,tanata qoqarin sakarwa aman ruwa don kada ya gani amma sai ya riqe hannayenta gaba daya cikin nasa. Ta daga blue eyes dinta da suka jigata sosai suka hada idanu,sai taji wani nauyinsa yana saukar mata. Yaga qazantarta sosai,ta dauka zataga sauyi ne a fuskarsa,amma sai take hangen wani tausayi shimfide saman kyakkyawar fuskarsa.

"Kin kammala ne?" Sadda kanta tayi qasa,a duniya bata dauka akwai wanda zai mata irin yadda sultane yake mata ba. Yana tsaye dab da qazantar amanta amma kuma kulawa kawai da damuwa take gani akan fuskarsa ba qyama ba.

"Eh". Ruwa ya dinga zuba mata tana wanke fuskarta da bakinta. Yabi hannuwanta da kallo yadda suke kakkarwa,ta kammala ya jawo qaramin towel ya damqa mata. Ta dauka iyaka kenan,sai taga ya riqe tsintsiyar hannunta,bai kuma saketa ba sai daya tabbatar ta kwanta sosai ya maida duvet din ya rufeta.

Idanunta a lumshe numfashinta yana sauka a hankali,tana jin qarar ruwa a toilet din,tana jin alamun wanke sink din dama duk gurin data bata da qaramin brush.

Slippers din ya zare daga bakin toilet din,ya tako a nutse har zuwa bakin gadon. Tana jin tsaiwarsa amma ta kasa bude idanunta saboda sanyin dake nuqurqusarta.

*_Assalamu alaikum warahmatullah_*

*_Akwai pyjamas/home wear/lounge wear tsala tsala masu dadin zaman gida da bacci_*

*_Sabbi kar a mutunce cikin jakarsu,a affordable price_*

*NA IYAYE DA YARANSU*

*_kina kasuwancinsu?,Maza zoki gwada wadannan dana kawosu......quality dinsu ya girmi farashin_*

*_ki siga ki siyawa yara.....masu dadin sawa a zafinnan.....ga taushi ga ba nauyi_*

*_maza tuntubi huguma ta nan don ki ganewa idanunki_*

08187255862

Idanunsa ya zube fes a kanta,sai ya lura da yadda haqoranta suke haduwa guri daya amma tana qoqarin hana hakan faruwa. Aman da tayi relief ne yasan zata samu.....amma baisan me yasa har yanzu sanyin da takeji yaqi raguwa ba,da alama jininta yana da qarfi sosai. Har qasan ransa yaji bazai iya tafiya ya barta a haka ba,sai ya juya a nutse ya fara bude windows na dakin tunda ba fanka ko Ac,dole su baqaci fresh air komai qanqantarta.

Ta cikin rufaffun idanunta take iya ganin duhun daya mamaye dakin. Ta cikin rufaffun idanunta take iya jin motsin haurowarsa gadon,hakanan ta cikin rufaffun idanunta takejin sanda ya janye duvet din,saidai abinda ya bata mamaki lokacin da taji ya hauro daya side din ta samanta,ya kuma fara laluben zip na sleepwear din jikinta.

Duk wata tsiga ta jikinsa saida ta zuba saboda wrong position daya dora hannunsa. Maimakon ya kama zip sai hannuwansa suka tafi wani guri na daban. Kamar an jona masa wutar lantarki a jikinsa haka yaji wani irin shock daya harba tare da harbawar jinin da zuciyarsa take aikewa a kowanne second zuwa sassan jikinsa.

Abun yazo mata a bazata....wannan ya sanya numfashinta ya dauke na wucin gadi ta kuma kaiwa hannunsa cafka ta riqe sosai zuciyarta na dokawa da matsanancin qarfi.

"Ka......kkkaaaaa" Sai kuma ta kasa fada,ta kasa hada haruffan saboda bugun da zuciyarta keyi din ya hana daidaituwar kalaman saman harshenta har sukai ga fita.

Yasan me takeson fadi,sai kawai ya sauqaqe mata,ya saukar da kanshi daidai kafadarta,da wani irin sauti da yayi ma kunnuwanta laushi da yawa,sautin da yafi kama da rad'a yace.

"I'm.....I'm sorry.....“That wasn’t my intention.” ya fada yana dakatawa kamar wanda ke zaben kalmomin da zaiyi magana dasu

"......yi directing dina zuwa zip..........sanyin da kikeji yayi yawa" Ya fada yana jin kalaman kamar zasu qwace daga bakinsa,don abinda yakeji a yanzun cikin jikinsa kamar zai wuce ne da numfashinsa.

Duk magananshi da harshen France yana sake sawa komai yana qwace mata ne....muddin zai bude wannan husky voice nashi ya yara mata french to yana sanyata tajita kaman ZERO,yana sanyata tana jin kaman bata iya komai a yaren ba....kaman bata iya pronouncing na yaren yadda ya dace ba....ballantana yanzu. Muryar dayake mata magana dashi wata murya ce ta daban,wata murya ce ba kalar wadda ta saba ji daga gareshi ba.

"Nooo..." Ta fadi tana dan jan kalmar da dan tsaho. Akwai kafiya cikin muryarta,shi kuma ba wannan yake buqata ba a yanzu. Koda wanne lokaci zata iya loosing yanayinta inde bai samar mata da abinda zai bata dumi sosai ba.....ba kuma abinda zai wannan aikin nan da nan sai skin to skin.

A hasashensa cikin duhun ya sake kai hannunsa jikinta,cikin sa'a ya dora hannunsa akai,saidai akwai alamun nata hannun yana gurin. Ture hannun gefe yayi,ta buda baki da niyyan magana tana son maida hannunta gurin,saidai hannun nata a ainihin fatarta ya sauka don tuni yakai zip din qasa.

A nutse ya soma sabule mata rigar daga kafadarta zuwa daya kafadar,dukkanin labbanta rawa suke,magana takeson tayi amma bata da wannan energy din.

Wani irin yanayi ne me wahalar fassara a gareshi.....bashi kadai ba,ga duk wani kamammen namiji daya adana samartakarsa hakance zata kasance dashi. Dukka hannuwansa rawa suke lokacin da yayi mata kyakkyawan masauki cikin faffadan qirjinsa,ya maida hannuwansa dukka biyun ya mata kyakkyawar runguma. Fatarsa ta manne da tata,yalwataccen gargasar nan me santsi dake lullube da qirjinsa ta sauka gefan kuncinta......fuskarta ta nutse tana samun kyakkyawan masauki cikin qirjinsa. Karo na farko a rayuwarta da wani d'a namiji ya kusanceta irin haka.....kamar yadda ya zama karo na farko da wata diya mace ta kusanci gangar jikinsa har haka......sannan yaji kaman kusancin yanason kutsawa tare da danna kai ya zarce iya skin nasa kawai. Kamar akwai wani abu dake qoqarin bonding nasu da wani irin zafi da sauri me kama da walqiya.

Sake boyeta yayi sosai cikin qirjinsa yana jinsa a hankali yana fita daga ainihin wannan duniyar zuwa wata duniyar ta daban,hancinsa yana zuqo mata daddadan qamshin da lallausar sumarta da fuskarsa ta shige ciki tayi mayafi da ita. numfashin da yake zuqa a yanzu cikin hancinsa yana jin cewa ba ainihin numfashinsa da yake shaqa bane a kowacce rana. Bugun da zuciyarsa takeyi a yanzu yana jin ba ainihin wannan zuciyar bace a qirjinsa a yanzu.....duniyar da yake ciki.....mintunan dama awannin dukkaninsu ba irin sauran awannin da yayi a shekarun rayuwarsa gaba daya bane.

*_Assalamu alaikum warahmatullah_*

*_Akwai pyjamas/home wear/lounge wear tsala tsala masu dadin zaman gida da bacci_*

*_Sabbi kar a mutunce cikin jakarsu,a affordable price_*

*NA IYAYE DA YARANSU*

*_kina kasuwancinsu?,Maza zoki gwada wadannan dana kawosu......quality dinsu ya girmi farashin_*

*_ki siga ki siyawa yara.....masu dadin sawa a zafinnan.....ga taushi ga ba nauyi_*

*_maza tuntubi huguma ta nan don ki ganewa idanunki_*

08187255862

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽