Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 34

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 34

..... open the door for me. I went down slowly, my body did not smell. I went to the gate and knocked. The guards opened the door for me. I entered the house slowly, my heart seemed to break my chest. I pushed the door open... my eyes met hers. Mumy is walking around in the middle of the hall, walking as if she is waiting. When she saw me, she stopped. She stared at me. I said in a calm voice: "Mummy, hello and home..." She didn't say a word, she just got up quickly tuuah! Two hits in a row! I had to kneel on the ground because of their power. My eyes filled with tears, and my heart seemed to burst. She said in a voice full of hatred, "Whose father's house did you go to? It seems that since your father left, you went on a vain trip! Or Islamiyya, you will return at nine o'clock? You are a whore! Shegiya... a slut like your mother. Where are you going to start following a path like her?" Terrified and agitated, I looked... I couldn't speak. I opened my mouth and wanted to say something but _praah!_ Then she beat me and insulted me with hot words. "Did you go to Dubiya? Or hotel Dubiya? You just have to wait for your father to come back... by the way, I'll tell him everything!" I fro

Standalone post1,621 words

Bayan na fita daga asibitin, zuciyata kamar an daura min dutse. Kowanne mataki da nake ?auka, kamar nauyi nake ja.

Tunani na Khalil. Tunani na Mama. Tunani na yayyensa da suka ?i kallona. Tunani... akan me yasa rayuwa ke canzawa a hakan?

Na kai hannu na bisa kaina, na dafe, sai hawaye suka gangaro a hankali. Duk da ina ?o?arin ?oyewa, sai da wasu biyu suka zubo har ?asan habata.

Na share su da sauri, amma zuciyata na bugawa kamar ana dukan ?ofa a cikinta. Wani irin damuwa ne da kalmomi ba za su iya bayyana ba.

Sai da muka hau hanya zuwa gida, zuciyata ta fara bugawa da ?arfi. Na kalli agogon motar, naga ?arfe tara saura. Magriba ma ban yi ba, balle isha i. Na dafe kirjina. Na sauke ajiyar zuciya. Nasan halin Mumy... kuma wallahi, yau sai ta kusan karyani.

Ban san irin karyar da zan gaya mata ba. Sai kawai na saka kaina a jikin tagar mota, na hau kuka cikin shiru. Ban ce wa driver komai ba, shi ma shiru yayi kamar ya fahimci damuwata.

Da muka ?arasa kofar gida, sai driver ?in ya fito ya bu?e min ?ofa. Na sauka a hankali, jikina babu ?wari. Na nufi kofar get ?in, nayi knocking. Masu gadi suka bu?e min.

Na shiga cikin gidan a hankali, zuciyata kamar zata fasa ?irjina.

Na tura ?ofar palo... idona ya ha?u da nata.

Mumy na zagaye a tsakiyar palon, tana tafiya kamar wadda ke jira. Da ta ganni, ta tsaya cak. Ta zubamin ido. Na ce cikin sanyin murya:

"Mumy sannu da gida..."

Bata ce uffan ba, kawai ta taso da sauri tuuah!

Mari biyu a jere! Sai da na dur?usa a ?asa saboda ?arfinsu. Idanuna suka cika da hawaye, zuciyata kuma kamar zata fashi.

Tace da wata murya mai cike da ?iyayya

"Gidan uban wa kika je? Wai tun da mahaifinki yayi tafiya kin koma yawon banza! Ko Islamiyya sai ?arfe tara zaki dawo? Ke karuwa ce! Shegiya... yar iska kamar uwarki. Inaga zaki fara bin hanya irin tata ko?"

Cikin firgita da tashin hankali, na kalleta... ban iya magana ba. Na ?an bu?e baki ina son na fadi wani bayani sai kawai _praah!_ Sai da ta ?ara min duka tana zagina da maganganu masu zafi.

"Wai dubiya kika je? Ko dubiyar hotel? Sai dai ki jira uban naki ya dawo... wallahi sai na gaya masa komai!"

Na daure, na girgiza kai cikin hawaye. Nace da ita cikin rawar murya

Mumy wallahi... Allah ya sani asubuti naje dubiya.

"Allah sai na i gaya masa Idan ubanki ya dawo, sai ki gaya masa! Dallah ki tashi kije kitchen ki dafa jallop din taliya. Ga bereziyata can kije ki wanke. Kazama kawai!"

Na ?an dakata, nace

"Mumy... bari nayi sallah, please."

"Sallar uwarki! Dallah shige ki yi min abincina kafin na karya ki. Ke fa banza ce, kazama! Wuce kije kitchen!"

Na juya da jiki mai nauyi, zuciyata cike da ra?a?i da ?acin rai. Na shige cikin daki ina kuka, amma na ce zan daure... Allah na nan, kuma zai kawo min mafita.

Cikin tsananin damuwa na dora mata jallop ?in taliya a kan sin ?in kitchen. Na sauke numfashi inayin shiru kamar mai jiran sakon da bai zo ba. Daga nan na ?auro alwala a hankali, zuciyata tana tafasa da tunani, hankalina yana can wajen Khalil.

Na tsaya yin salla a kitchen saboda tsoro ya hana ni shiga ?aki. Gabaki ?aya tunanina ya tattaru ne a kansa. Kai! Duniya abun tsoro ce...

Ni da kaina ban ta?a tunanin akwai irin soyayyar da Khalil ke yi min ba soyayyar da nake jin kamar zan narke saboda nauyinta da gaske.

Ban gama komai ba sai wajen ?arfe goma da rabi. Na tashi na ?akko bra da pant na Mumy, na wanke su da kyau, na shanya. Da kyar na tafi dakina.

Da na shiga, gabana ya ?ara ?aukar zafi. Kurajen dake min ?unci sun dan lafa, amma susar su sai gaba take da karfi. Wallahi ina jin zafi, amma ina jimrewa, domin tsarki da ruwan gishiri yana bani sau?i ko da kuwa yana ?ona jikina.

Sai na ha?a ruwan zafi da gishiri, na wanke gabana da niyyar samun sau?i. Amma ba zan iya fa?a wa Mumy ba nasan idan na bu?e baki ta ce, To ba yawon banza ne ke kawo hakan ba? Tunda yanzu, kalmarta ?aya ne Karuwanci.

Wani zafaffen hawaye ya gangaro kan fuskata. Wallahi maraicin uwa radadi ne. Radadin da idan kana ciki, baka da mafita sai Allah.

Wani lokaci ina mamaki... me nayi wa Mumy haka? Ita ce Mumy ?ina da a da take sona har fiye da kowa. Ita ce ke kawo min abinda nake so, kullum tana tare da ni. Amma yanzu ita ce babbar makiyata.

Na fashe da kuka... kuka mai ciwo daga can ?asan zuciyata. Har cikin ?ashi nake jin dumin wannan kukan.

Ahaka na tashi, na nufi daddumata Na hau yin sallah, na yi nafila cikin kwanciyar zuciya, ina maimaita

"Ya Allah, Ka ba Khalil lafiya... Ka ba ni hakuri da kwanciyar hankali... Ka ba ni mafita daga wannan rayuwa..."

Zuciyata tana kuka... idanuna ma haka... amma zuciyata ta fi kukan da ya fito da ido.

**********

Cikin kwanakin nan, damuwa ta mamaye rayuwata. Wallahi ko kofar gida bana fitowa, sai dai na zauna a daki na shiga kuka. Tun ranar da na kai karfe tara a waje, Mumy ta kira Abba, ta gayamasa. Shi kuma nan take ya bukaci a bamu waya. Fa?a ya shiga yi min cikin ?acin rai, ya hana ni fita har zuwa Islamiyya. Wannan yasa hankalina ya ?ara tashi.

Yanzu haka, bayan na gama duk aikin gida, ban da wani abin yi. Sai kawai na kwanta ina kishingi?e, zuciyata cike da nauyi. A cikin bacci na, na fara mafarki mai firgitarwa. Wata ba?ar mace ce ke bina da wu?a tana ?o?arin kashe ni. Ina ta gudu, amma kamar ?afafuna sun ?ulle. Sai kuma wani bak in halitta ya rikeni yana neman sha jinina.

Ban san yadda akayi ba, sai kawai na farka cikin razana. Na tarar da Mumy na kwarara min ruwa a fuska tana masifa. Cikin tsoro na kalleta, na rasa ma bakin magana.

Ta ce, Ban ce miki yau Abba zai dawo ba? Bazaki tashi ki masa girki ba? Kina nan kina surutai cikin bacci kamar mai aljanu!

Na yi shiru, ban ce komai ba. Sai da ta fita sannan na soma karanta addu o i. Na tashi jikina ba kwari, amma na daura alwala na shiga kitchen domin fara girki.

Ina tsakiyar girkin ne sai na ji sallamar ?annin Abba naji wani sanyi ya shige ni. Anty Luba ce da wasu daga cikin dangin Abba. Tuni na san za ta taimaka min in samu damar ganin Khalil, tunda ta fi kowa sanin irin halin da muke ciki, kuma ita mutuniyar Mumy ce.

Na fito da fara a na gaishe su. Kowacce ta zuba min ido tana cewa, Ramlah ce? Kai! Kinyi kyau, kin yi kiba sosai!

Mumy da sauri ta ce, Ai maganin kiba ta fara sha sai kibar ke shigarta.

Anty Luba ta yi dariya, ta ce, A a Mumy, ai Ramlah daman ji?in kiba ne da'ita, kuma kina kula da'ita sosai shiyasa.

Na kai musu abinci da ruwa da lemo, sannan na koma ciki nayi wanka. Su Hafsa kannen Abba ba sa sona tun asali ma dan ba su son mahaifiyata. Shiyasa ni ma bana kulasu tsakanina dasu gaisuwa.

Na fito daga bandaki sai naga Anty Luba tana salla. Na tsaya, ina kallonta komai nata dagwas dagwas abunta da zarar ta idar sai ta janyo ni kusa da ita. Ta kalli fuskata tana murmushi, tace "Ramlah, mashaa Allah! Kin yi kyau. Wallahi kin koma kama da mamanki. Mamanki fa kamar balarabiya ce. Ko ince, itace kam da Kakarki Mama. Kawai haske zasu nuna miki. Allah ya jikinta."

Na ce: "Ameen." Sai ta kalleni sosai, tace

"Ramlah me ke faruwa tsakaninki da Zainab ne? Na lura komai naki sai ta gwasale. dazu Har zaginki naga datayi.

Baki na na bu?e nace "Wallahi yanzu ba ta ?aunata ko ka?an. Ba kamar da ba."

Ta girgiza kai, tana murmushi mai tausayi.

"To ai na sani. Kiyi hakuri, Ramlah. Wannan itace taki kaddarar ki kar?eta da zuciya ?aya. Ko da Abba ya hana Khalil aurenki, wallahi ni ba ji da?i ba ace mutum tun kana ?arami yake sonka kuma anyi masa alkawarinki sai yanzu a hanasa. Duk da nasan zugar momy ce. Amma kinga fa yadda ya koma yanzu..."

Wani zafaffen hawaye ne ya zubo min, nace

"Anty Luba, dan Allah ki taimaka min ki kai ni naga Khalil. Wallahi kullum cikin tunaninsa nake."

"Kar ki damu, abinda ya kawoni kenan. Hajiyarsu ta aiko ni. Nazo domin mu shirya, muje tare.

Ko da zata fita, ta tambayi Mumy

"Mumyn Ramlah, ina Bilkisu take ne?"

Mumy tace "Ai tafara zuwa aiki."

Anty Luba ta ce "Kai, mashaa Allah! To kinga zanje kasuwa wa zai rakani ya rike mun ledoji?"

Sai Mumy ta ce "Ga Ramlah nan, uban me take yi da bazata rakaki ba?"

Anty Luba tace "Nagode. Ramlah, sa hijjab dinki, ki rakani kasuwa."

Na amsa da murmushi, na shige ciki na ?auko hijjab. Doya da kwan da nayi na zuba a flask, fura na kuma na zuba acikin jug nasa fridge.

Na kalli Mumy, nace "Mumy, sai mun dawo."

Su anty Hafsa ma na yi musu sallama, suka amsa amma daga ciki.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH

SHAFI NA TALATIN DA BIYAR

Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435

Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********