
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 42
... She put her hands on her neck... Her ears, her breasts, her thighs right behind her. Wherever she goes, she remembers what kind of situation the hand landed on, she lowers her eyes and clutches the pillow she is holding. But now she is feeling that same feeling that she should have felt so much that she was afraid to stop it. "Biftuuuuuuu" A part of her heart called out to her with a loud voice. Hasn't she started going crazy?.....hasn't she started having brain problems?. Why does everything around her change? Why does everything about her change itself? Where is this idea of hers?... where have all her rules and regulations gone? What about this teacher? This teacher is just like other teachers. "I'm not like other teachers, akhnan.....not like the others" A part of her heart came to tell her slowly. She was not quick to deny it, she got herself to talk about it again. The first day I saw him...... how amazing he was. How he does not accept humiliation, lowliness or distance. The great position of her father and all her beauty did not even once make him join the ranks of the men who wanted to enter her life, until now..... until now, when the marriage tie was broken.....
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 42*
Duk abun daya ne,amma saboda Allah ya karrama dan adam ya sanyashi ya zama ta halastacciyar hanya. Cikin girma mutunci da karamci da amincewar iyaye,bayan ka biya wani abu cikin kalmomin Allah da sunnar manzonsa S A W.
Yana jin sanda ta fito,ta dade tana lallabowa gami da takawa a hankali tanason saka kayanta. Bata lokaci yayi,yayi kaman bayan gurin,bai juyo ba ya barta ta shirya duk da tsorace take,sai daya tabbatar ta hau gadon sannan yabar bakin gurin,ya tako a hankali da wani irin sanyi da nutsuwa yaja duvet din ya lullubeta.
Samun kansa yayi da sunkuyawa daidai goshinta. Lite kiss ya ajiye mata,ya taka da baya da baya a hankali ya kashe duk wutar dakin,sannan ya juya yana barin dakin da wani abu daya soma nauyi da girma a qirjinsa,wani abu da baisan meye shi ba.
Duk da taji fitarsa amma ta kasa motsi tun bayan da kiss dinsa ya zauna mata daram a goshinta. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana tuna komai daki daki. Takai hannunta saman wuyanta... Kunnuwanta,qirjinta,cinyoyinta dama bayanta. Duk inda takai hannun saita tuna da wanne irin yanayi nasa hannun ya sauka a gurin,saita runtse ido sosai tana damqe pillow din da take kai. Sai a yanzun takejin wancan feeling din daya kamata ta jishi a dazu sosai tsoro ya hana.
"Biftuuuuuuu" Taji wani sashe na zuciyarta ya kirata da qarfi,saita cusa kanta cikin pillow tana rasa me zatayi?.
Anya bata fara hauka ba?.....bata fara samun matsalar kwanya ba?. Me yasa komai dake tattare da ita yake sauyawa?,me yasa komai nata yake sauya kanshi?. Ina wannan ra'ayin nata?....ina dukka dokokinta da tsarinta suka tafi? Wannan malaminne fa?,wannan malaminne fa kamar dai sauran malamai data sani.
"Ba kamar sauran malamai ba akhnan.....ba kamar sauran ba" Wani sashe na zuciyarta ya shiga gaya mata a hankali. Batayi saurin qaryatawa ba,samu kanta tayi da sake tariyo komai nasa. Ranar farko data fara ganinsa......yadda izzarsa bata bari a takashi. Yadda bai yarda da wulaqanci qansqanci ko tazarci ba. Girman muqami na mahaifinta da dukka kyanta bai sanya ko sau daya ya shiga sahun mazan dake nacin shiga Rayuwarta ba,sai yanzu.....sai yanzu da igiyar aure ta qullesu guri daya.
Saka dukkan qarfinta tayi tanason wancakali da tunanin ko zata samu bacci,saidai duk inda ta motsa.....duk yadda ta juya ba abinda hancinta yake shaqo mata sai wannan qamshin nasa. Wannna qamshin dai.....qamshin da tasake ji a ranta ko yaya ne zatayi ta mallaki wannan turaren.
"Ta yaya biftu?" Ta tambayi kanta da kanta tana tsaiwa cak. Ba abinda yake dawo mata a kai sai tafiyarsu....wannan tafiyar tasu.
"Waye shi?" Ta sake tambayar kanta. Iko da take gani tattare da komai nasa yana sake jefata a tunani tarin zaquwa da son sanin WAYESHI?. Baya bayyana iko da kansa.....amma ikonsa ne yake magana da kansa ba tare da haisam din ya furta komai ko ya nuna komai ba.
Wani abu ya sake ratsa zuciyarta sanda ta kwantar da kanta saman tafin hannunta. Daidai da tafin hannunta qamshinsa yake. Kowacce gaba ta jikinta tuna mata dashi take. Tana iya jin hannuwansa ako ina na jikinta tamkar a yanzunne yake yin komai.
"Ya salam,ya Allah" Ta fada a hankali tana lumshe idanunta,tana kuma jin yadda bugun zuciyarta yake sauyawa da wani irin sauri.
Da gaske bacci ya qauracewa idanunta,duk inda ta juya qamshin da batasan haka yake ba sai a yau din. Bedsheet dinta.....duvet dinta....pillows din dake kan gadon gaba daya,uwa uba jikinta da batasan me ya zaunar da qamshin ba bayan wankan duk da tayi,saita yanke ta sake wani wankan ta kuma canza muhalli ko zai ragu.
Wankan ta sake,ta kuma hado da alwala ta sauya wasu kayan,saidai still ba abinda ya sauya wannan,sai kawai ta dauki abun sallah,ta koma bakin haram view ta shimfida ta tayar da sallah nafila.
Raka'a hudu kawai idanunta suka fara nauyi,ta zauna a gurin a hankali. Dabi'arsa ce istigfari,sau tari zata jishi yana yinsa can qasan maqoshinsa,a hankali sai taji bakinta ya kama....daga wannan yanayin daga wannan lokacin daddadan bacci me cike da mafarkansa a wancan yanayin na awannin dazu ya sureta.
★★Kwata kwata bata taba kawowa zai sake iya hada idanu da ita ko tunkararta ba. Sai gashi gata cikin wani irin yanayi na nutsuwa gaban ka'aba suna dawafin ban kwana(ba wajibi bane a umra,ya zab'ar musu suyi dawafinne kawai).
Wani irin nutsuwa ta dinga shigarta,wani irin yanayi,saita samu kanta tana koyi da yadda yake aiwatar da dukka motsinsa na ibada tana qoqarin kwaikwaya.
Duk sanda ta daga idanu ta kalleshi abun jiya yake fado mata,wani irin satar kallo take masa don tasan muddin ta bari ya kamata tana kallonsa qila kunya ce ajalinta.
A yanzun daya nutsu yake zaune yana addu'o'insa sai take satar kallonsa. Wani iri kamala tana sake lullubeshi,ta dauka wannan kwarjinin da yake mata.....wannan cika idanun da wannan haibar da take cika mata idanu zasu zagwanye daga abinda ya faru a jiya,amma sai taji babu ko daya data girgiza,babu ko daya data tabu,saidai mamakinsa kawai da takeji cikin zuciyarta.
Wani abu d'aya data lura dashi.....wanda har sai daya sanya taji kanta ya wani kumbura. Kaffa kaffan da yakeyi da ita wanda ya ninka farkon shigowarsu makka. Hannayensa yake sanyawa hagu da damanta ya kakkangeta daga kowanne namiji da zai matso kusa da ita. Har sukayi dawafin nan bakwai bataza ce iya cewa ta hada kafada da wani namiji guda daya ba.
Koda zamzam da zata sha yana tsaye bisa kanta bayan ya matso ya bata da kanshi,hakanan a yanzu da suke gaban ka'aba daga dan nesa inda kowa ke zaune yana gabatar da addu'o'insa.
*AGADEZ*
*_SULTANE PALACE_*
K'arfe takwas na dare ne,wanda yayi daidai da qarfe goma na dare agogon saudiyya.
Masarautar tayi wani irin shuru,shurun da kana jinsa zakasan ba shuru bane na al'ada,ba kuma shuru bane dake nuni da lumana da nutsuwar duk wani d'an masarautar.
Kusan ba cikin masarautar kawai ba,AGADEZ gaba daya cike take da alhini lalurar data kwantar da sarkinsu me adalci.....sarkin da suke mata wata tsaftatacciyar soyayya saboda kulawa da damuwa da yayi da matsalolinsu SULTANE MUHAMMAD HAMMUD na biyu.
A daidai wannan lokacin take takawa cikin izzar da har yanzu takejin ba wani abu da zata bari ya taba wannan izzar......duk da kuwa har yanzu ta gaza gamsuwa da kallo da gaisuwa dama tarbar da hadiman gidan sukayi mata.
Kwanaki bakwai kenan.....kwanaki bakwai din data yisu a hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun qwayoyi. Kwanaki bakwai din da suka zame mata daidai da shekaru dubu bakwai wajen tsaho da ganin baqinsu.
Ba'a ci zarafinta ba,ba'a hanata muhalli da abinci me kyau ba......amma tashin hankali da masifar data shiga na kula da yaduwa da labarin kamata da tsareta da yayi cikin niger gaba daya yafi komai zame mata barazana.
Da kowanne motsi na ma'aikatan hukumar take fahimtar komai. An shirya komai ne kawai don a kawota nan a b'ata sunanta.......to amma babban abun mamakin......ya akayi birnannen sirrinta?,boyayyar harqallarta?,tsohuwar sana'arta da tafi kowacce mallaka mata baqaqen kudade lullubin sirrinta ya yaye?.
"Sheikh muhammad haisam......alsaamit" Sunan daya dinga maimaituwa a cikin kanta kenan. Ta sake gasgata hakan sanda aka saketa bayan kwanaki bakwai da sunan an mata alfarma,zasuci gaba kuma da bibiyar case din.
Kenan sun mata kisan mummuqe kenan?,sun bankado komai don su tona asirinta su zubda kimarta a idanun duniya bawai don su kamata ba?.
"Me yake shiryawa?" Tambayar data kwana tana zirga zirga kenan a kanta bayan ta dawo dakinta ta kuma gagara samun amsar,wanda daga qarshen dare kwanyarta ke gaya mata.
"Ki shirya yadda zaizo hannunki......yadda zaki mallaki qudurinki na qarshe.....ki cinnawa burinsa da dukkan ikonsa wuta.....wutar da bazasu iya kasheta ba har qarshen rayuwarsu". Wannan shine shawarar da zuciyarta ta bata. Shawarar data rasa ta inda zata kamota sai a yanzu da take kan hanyar amsa zaman tattaunawa akan makomar masarautar game da lalurar sultane.
Wani murmushi ta saki me sauti,har sai da hadiman dake take mata baya suka kalli juna.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Kwanciyar sultane......itace zata zame min hanya mafi sauqi da zan kammala komai......ya kamata YA MUTU ya qarasa mutuwa" Ta fadawa kanta tana jinjina kai da jin gamsuwa da wannan shawarar.
Da izzar da a yau takejin kamar ta raunana take takawa cikin dogon dakin tattaunawar dake dauke da kujeru na zama iya adadin 'yan majalisar sarki da sauran spare kujeru koda za'a buqaci zama da wasu mutane na daban,kaman yadda a wannan zaman aka buqaci zuwan yakumbo,nannie.....morsa safiyya,da mammina din,sai tsoho me ran qarfi kaka ga morsa safiyya daya zama kamar d'an gida.
Kallon da take gani a idanun wadannan mutanen,kallo ne daya sanyata jin wata siririyar muzanta ta fara saukar mata,amma daga baya taji ta ware bayan kawo gaisuwa da wazeer da sauran manyan fada sukayi kaman yadda aka saba.
Wani kallo ta ajewa morsa safiyya,tayi sanyi sosai yanayinta ya nuna hakan. Ba qaramin tabata ciwon sultane yayi ba,wani irin ciwo daba wanda ya gaya musu me yake damunsa?.
Yanzun nan kuna magan dashi,bayan awanni sai ace babu shi ya shiga coma. Wata irin coma da duk bayan awanni yakan iya tashi,ya sake komawa bayan awanni.
"Ya Allah,idan har wannan itace qaddarata a rayuwa,Allah ka bani ikon cinye wannan jarrabawar.....ba khadeeja......ba safeena.....yanzu kuma sultane?" Iya tuna wannan kawai ya sanya hawaye zarto mata,hawayen daya sauka a idanun mammina.
Wani irin dadi taji yana mamayarta,ta sauke murmushin nasara. RAUNI wani abu data jima tanason jefawa hade da tsoro a zuciyar safiyya amma bataci nasara ba saboda kalar zuciyar dake qirjinta,saidai yanzu gashi cikin ruwan sanyi komai yana zuwa daki daki,da alama wannan karon duk da aikin na qarshe ne ya kamata yazo da zafi zaizo mata a sauqaqe.
Dogon maganganu da tattaunawa akayi,kafin daga bisani aka gangaro kan ainihin dalilin haduwarsu.
"Ya za'ayi da riqon qwarya na sarautar AGADEZ?" Wani abu ya harba a zuciyar mammina. A irin wannan lokacin karon farko taji inama ace ta haihu?,inama ace tana da d'a?,koda wannan d'an bana sultane bane ta mallakawa sultane shi,da tuni yanzu wannan damar cikakkiya tata ce. Tsanar safeena ta sake cika mata zuciya da ruhinta gaba daya. Safeena ce sila.....Ahmad tabbas inda ba safeena d'anta ne....rabonta ne,ita zata haifeshi,tsinanniya safeena ta qwace mata wannan damar.
"Ina ganin a wannan lokacin muna buqatar muji ta bakin sheikh haisam,don shima a matsayin d'a yake a gurin sultane" Nannie ta fadi,maganan kuma ya zaunawa kowa,take kuma wazeer ya soma lalubar haisam din
Wani makirin murmushi ta saki tana sake gyara zamanta hankalinta kwance. Akwai mutane da yawa da take hasashen su za'a bawa,inde hakanne sama da mutum goma a cikinsu data lissafa kowa a cikinsu tana da yadda zatayi dashi.
Manyan idanunsa dake lumshe ya bude a hankali jin alamun wayarsa dake jikinsa. Ya zarota yana duba me kiran,sai ya miqe a nutse a hankali yana fadin
"Kiyi addu'a,ki roqi Allah dukkan alkhairi na duniya dana lahira.....ina zuwa" Ya fadi a nutse yana danyin nesa kadan da ka'abar saidai bai gaza hangota ba daga nan inda yake tsaye.
Shuru tayi maganansa tana mata yawo cikin kunnuwa. Tana lissafa iya adadin abinda ta roqa daga zuwansu garin zuwa yau da suke shirye shiryen fita daga qasar.
"Shine kawai ya rage.....baki bawa Allah zabi ba.....baki roqi Allah komai a kansa....baki magana a kansa ba,bakice komai wa Allah a kansa ba" Wani sashe can qasa ya yunquro daga zuciyarta yana rad'a mata..
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽