
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 35
.....which is like a dead body. You can only hear his breath. His face is dark, his eyes are closed, as if he has no life, except for the difficult breathing that comes out of his mouth. During this time, his sister turned to him in distress, "But Ramlah, don't you have a heart? Do you see how this boy is limping because of you? He has been calling your name for three days, every day, Ramlah... Ramlah even when he is sleeping, he mentions you. But you didn't come and look? I was filled with shame and worry. Tears started to fall from my eyes. I hardly had the chance to say "Anty... by God, it's not carelessness. There is no way to go out, by God, I always pray for him, and with the grace of God, he will get better." She looked at me and hugged me. But I didn't respond. I ended up standing on the edge of the bed and looking at him. Then I knelt on the floor and patted his hand gently. Then.. the cry that came out of my mouth was a cry from the heart, a cry that was full of pain and love and compassion. I just felt my hand being squeezed. It was strong. He is worried, like someone who is trying to find a way out of a deep hole. His voice is shaking, full of pain and anger.
Tunda muka fara tafiya, Anty Luba ke ta tayani hira iri-iri. Hira mai da?i, cike da fahimta da kulawa. Har tana cewa tana jin dai Abbana zai tura ni waje domin ci gaba da karatu. Nikam sai na kalli fuskarta na yi murmushin dole. A Zuciyata tamkar in ce mata "Anty, ai mumy ta hana abba turani Amma sai na ha?iye abun na yi shiru, na maida kallona waje.
Da muka karasa asibitin, muka shiga. A yau, dukkan yan uwan Abba suna nan. Kowannensu da wata irin fuskata bakin ciki, tamkar ana karanta matsalolin zuciyarsu daga cikin idanuwansu. Suka amsa gaisuwata, amma ba don suna so ba kallonsu ya nuna cewa zuciyarsu ba tare da ni take ba. Suna kallona kamar ni na janyo ciwon da Khalil ke fama da shi.
Na tura kofar dakin Khalil da sannu a hankali, zuciyata cike da fargaba. Na shigo da sallama. Hajiyarsa na zaune a gefen gado, ta rame sosai. Fuskarta ta kumbura, idanuwanta sun kumbura alamar kuka.
Shi kuwa Khalil... Subhanallah.
Khalil da na sani, mai kuzari, mai dariya da annuri... yanzu yana kwance kamar gawa. Sa Numfashinsa kawai kake ji. Fuskarsa tayi duhu, idanunsa sun rufta, kamar bashi da rai, sai numfashi me wahala da ke fitowa daga bakinsa.
Cikin wannan lokacin ne yayarsa ta juyo da masifa
"Amma Ramlah, anya kina da zuciya kuwa? Kin ga yadda yaron nan ya rame saboda ke? Kwanaki uku kenan yana kiran sunanki, kullum sai Ramlah... Ramlah ko yana bacci ma sai ya ambace ki. Amma kikasa zuwa ki dubasa ?
Na cika da kunya da damuwa. Hawaye suka fara gangarowa daga idanuna. Da kyar na samu damar cewa
"Anty... wallahi ba rashin kulawa bane. Babu halin fita ne, wallahi kullum ina yi masa addu a, kuma da yardar Allah zai samu sau?i."
Ta kalle ni, ta harare ni. Amma ni ban mayar da komai ba. Na karasa gefen gadon na tsaya ina kallonsa. Sannan na dur?usa a kasa, na dafa hannunsa a hankali. Sai.. kukan da ya fito daga bakina kuka ne daga zuciya, kuka da ke dauke da ciwo da ?auna da tausayawa.
Kawai naji an dam?i hannuna. Da ?arfi ya dam?e shi, kamar wanda ke kokarin kama mafita daga rami mai zurfi. Muryarsa na rawa, me cike da ciwo da ?unci
"Wallahi babu inda zakije... Ramlah ki tsaya... kar ki tafi ki barni... don Allah ki tsaya..."
Idanuwansa a rufe, amma hawaye suna kwarara daga su kamar wanda ke kuka a mafarki. Hajiyarsa ta dafa kafadarsa tana cewa
"Khalil... ka bude idonka, ga Ramlah nan fa... itace ta zo."
Cikin yanayi na tausayi, da rauni mai tsanani, ya bu?e idanunsa a hankali. Sai ya zuba min su idanuwansa sun bushe, sun kumbura. Ya dafe cikinsa kamar yana jin ciwo. Muryarsa na fita da ?yar kamar ana hura iska
"Ramlah... kina nan ko? Don Allah... kar ki ?i ni. Ki tsaya... Amma kada ki ?yale ni ki barni cikin wannan duhun da nake ciki..."
Zuciyata tayi wani irin nauyi. Kuka na cigaba da saukowa cikin tsantsar ra?adi.
Na kallesa nace
"Khalil... wallahi ina tare da kai. Wallahi bana ?in ka. Ka daina yi wa kanka haka... Don Allah... ka ci abinci..."
Hajiyarsa ta tafara magana ci?in damuwa
"Ramlatu, babu abinda yake yi sai ambaton sunanki. Dazun ma har da kuka yake cewa, Ramlah ta gudu ta barni Ramlah ta manta dani. Wallahi dai kin ga yadda ya rame... kamar an busar da shi."
Na lumshe idanuwa, na dafe kirji. Sai na ce cikin wani irin zazzafan hawaye
"Khalil... idan baka ci abinci ba.... ya kake so in ji? Ka ci abinci Khalil... don Allah..."
Ya dafe hannuna, hawaye na sauka daga idonsa. Muryarsa na rawa kamar wanda zai bar duniya
"Idan na mutu Ramlah... ki saka sunana a zuciyarki. Idan kin haifi yaro... ki sa masa sunana. Kada ki manta da ni... Kada ki hana yaronki sanina... Ki yi min addu a ko da na daina kasancewa a kusa da ke."
Na fashe da kuka mai ?arfi. Kuka da ban ta?a yi ba. Na dur?usa a gaban gadon, na jingina kaina a saman hannunsa, zuciyata na tafasa da zafi.
Cikin kuka da girgiza, sai ya dam?i hannuna kamar wanda ke neman mafita daga bala i. Ya ?an motsa jikinsa kamar yana ?o?arin tashi, amma sai ya saki ajiyar zuciya mai ra?a?i alamun ciwon ya hana shi ?arfi.
Kukansa ya ?ara karfi. Dakin ya cika da sautin kukan da ke tafasa zuciya. Nima ban iya jurewa ba, sai na fashe da kuka, zuciyata kamar za ta fashe da zafi.
A hankali, cikin murya da rauni, ya juya yana kiran Hajiyarsa
"Hajiya... danAllah ki ri?e Ramlah... ki ?oyemin ita... ki auramun ita... hajiya ki tsaremin ita kamar rai na...!"
Hajiyarsa ta dafe kirji, kuka ya ?wace mata. Kamar ba ita ba, ta fita daga dakin tana goge hawaye da hannunta. Ban ta?a ganinta cikin irin wannan yanayi ba.
Khalil kuwa ya shiga magana, kalmomi masu sosa zuciya, kalmomin da duk mai rai dole hawaye zai zubo masa. Ya ce:
"Ramlata... Ramlah danAllah... ki so ni... ki ?aunace ni kamar yadda nake ?aunarki... Kiyi min rai Ramlah... ke nake da ke... ke kadai...!"
Yayi shiru na ?an lokaci, sannan muryarsa mai ra?a?i ta dawo
"Wallahi ko da duniya zata ?i ki... ko da dukan dangina zasu ki ki... ni ba zan ta?a ?in ki ba... Ramlah... ke ce rayuwata."
Cikin rawar baki da hawaye, na dafa ?irjina da hannuna biyu. Zuciyata kamar za ta fashe. Naji tamkar kalmominsa suna ratsani kamar ?usa. Kuka ya?i tsayawa a bakina, sai motsin zuciya, da dukan kirji kamar ana harbina da ?aho.
Na bu?e baki cikin rawar murya, nace
"Khalil... ina tare da kai... wallahi bana ?in ka. Zan tsaya maka... zan so ka... zan zama tare da kai har karshen rayuwarka da yardar Allah!"
Yayi ajiyar zuciya mai nauyi, sannan ya runtse idanunsa. Daga gefensa, na cigaba da kallonsa ina share hawaye, zuciyata na tafasa da ?auna da tausayinsa.
Tunda Hajiyar Khalil ta bar ?akin, sai ta ciro wayarta tana kuka tana girgiza kai, ta kira Abba. Cikin rawar murya da ra?a?in zuciya ta ce
Don Allah Malam... ka dubi zumunci... ka duba yadda Khalil yake. Ka yarda ya auri Ramlah. Wallahi yaron nan zai mutu!
Sai naji muryar Abba a gefe.
Zan ro?e ki da ki bar wannan maganar. Na riga na zartar da hukunci babu Khalil, babu Ramlah, har abada. Ku je ku samo masa wata, amma ba ita ba!
Sai kukan Hajiyar ya ?ara fitowa. Ta hau masifa, zuciyarta a cunkushe, tana fa?i
Wallahi Allah, kai ba dan uwa ba ne. Ka raina zumunci. Ka manta ni ?ar uwarka ce! Abinda kayi min, Allah zai sakamin da zuriyarka. Wallahi sai ka ga sakamakon abinda kayi min, Malam!
Anty Luba da ke gefenta sai ta kar?i wayar da sauri, tana kuka itama, tana kwantar mata da hankali
Hajiya ki yi ha?uri, don Allah. Wannan ba kalmar da ya kamata mu fa?a ba. Yaya Malam ba haka yake ba, wata?ila zafin zuciya ne ke sa shi haka. Ki dan sauke rai hajiya...
Sai Hajiyar ta ri?e kanta da hannu biyu, hawaye na gangarowa daga idonta. Tana kallon Luba da wani irin ?acin rai ta ce
Luba... me zanyi? Kalli ?ana! Kalli yadda yaron da na haifa da jikina ya koma kamar mahaukaci saboda wata yarinya. Wallahi ko zan rasu sai Ramlah ta zama matarsa. dole sai da waliyyi? To, na riga na mallake auren nan! **
Ta fashe da wani irin kuka mai tsanani, tana girgiza kai, kamar wacce ta rasa komai a rayuwa.
Luba ta matsa kusa da ita tana shafa bayanta tana cewa
Ki kwantar da hankali hajiya. Komai zaiyi sauki Muna tare da ke. Allah zai kawo sau?i.
Bayan wasu 'yan mintuna, sai ga nurse ta shigo. Tayi masa allura, tana kallonsa da tausayawa. Anty Luba ta juya ta kalleni da murmushin tausayi a fuskarta tace
Ramlah, tashi mu tafi gida. Kalli fa, har takwas ya wuce.
Na zuba mata ido cikin shiru, zuciyata na wani irin karyewa. Na kalli Khalil dake kwance kamar wanda ba rai a jikinsa, sai hawaye suka gangaro saman fuskata. Cikin murya mai rauni nace
"Anty Luba... dan Allah, ki barni na kwana da shi. Zuciyata babu dadi wallahi. Idan yafarka bai ganni ba, zai kara shiga damuwa.
Hajiya ma ta saka baki, tana share hawayenta tace
Luba, ki bar ta dai. Tana da gaskiya. Zuciyar yaron nan tana a hannun yarinyar nan.
Sai Anty Luba ta girgiza kai, tace
Ramlatu, kinason ki jawo min masifa ne? Kinsan abbanki da yaji haka zai iya kulleni... ki rufamun rufamun asiri... don Allah muje.
Na juya na kalli Anty Luba cike da kuka, hawaye na gangarowa kamar ruwan sama. Na ri?e hannunta nace
Anty... zuciyata zafi takeyi. Wallahi bazan iya tafiya ba. Ki barni anan... ko abban kuwa yankani zai yi, zan dauka.
Ta zubamin ido, idonta cike da damuwa. Ta fita daga ?akin ba tare da ta ce komai ba. Na zauna gefe ina kallon fuskarsa, ina hawaye.
Bayan ?an mintuna sai ta dawo, murmushi a gefen le?enta, tace
Ramlatu... ki taimaka ki tashi muje. Gobe sai ki dawo. Abbanki ma ya kira, yace ina diyarsa?
Sai na fashe da kuka sosai, nace
Anty... bazan je ba. Wallahi bazan iya barin shi haka ba...
Dakyar... dakyar na mi?e, na fito daga ?akin ina jiyo zuciyata na fasa kamar za ta ?alle. Cikin kuka da ciwon rai na fice daga asibitin.
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH
SHAFI NA TALATIN DA SHIDA
Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435
Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********