
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 43
..... uk adults and elders that we have, will Ahmad the little boy be given the throne?, this is not in the legal system, when will he come back to memorize the royal system and lead?" Mammina said in anger. Just as the haisam was quiet in peace, the hall became silent, the silence was silent and she scolded herself because she started to look like everyone's eyes were on her. "You won't say anything?" "Thank you very much, Sheikh Haisam. We will not embarrass you. We will cook for him until he reaches the end, because he is more than us. Thank you very much for your understanding," Haisam said respectfully Morsa Safiyya dropped her stick and everyone signed the approval of Ahmad's rule. She respected God's decision to turn things the way He saw fit. Who ever thought that Ahmad would be alive again?
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 43*
Idonta ta lumshe sanda muryarsa ta cika Hall din cikin cikakkiyar sallamar data sanya kowa ya nutsu sosai tamkar yana gabansu. Cikin girmamawa suka gaisa da wazeer,sannan ya gabatar masa da dalilin kiran.
Boyayyen murmushi ya saki,ya soma miqa gaisuwa ga dukka wani babba da yake hasashen yana gurin.
"Ra'ayinka mukeso muji". Cikin nutsuwar nan tasa ya soma bayani.
"Allah S W T daya sanya mana 'ya'ya cikin hikimar bamu su shine,saboda mudin gajiyayyu ne,'ya'yanmu sune makwafinmu,sune qarfinmu,sune hotonmu....sune kuma masu iya dorawa daga inda qarfinmu ya tsaya......a yanzu alhamdulillah sultane yana da magajin da na gamsu zai iya riqe agadez.....zai iya kwatanta abinda sultane yakeyi bisa jagorancinku shawarwarinku da dafawarku.......bisa shawarata da hangena.....ahmad shine yafi cancanta yahau wannan kujera"
"Saboda ka raina furfura da shekaru na mutanen da suke gaba da ahmad din wajen gogewa da iya sarauta?,ta yaya duk manya da dattijai da muke dasu ace ahmad qaramin yaro zaa bawa sarauta?,wannan baya cikin tsarin doka ma,yaushe duka duka ya dawo da zai haddace tsarin sarauta har yayi jagoranci?" Mammina ta furta cikin harzuqa.
Kaman yadda haisam din yayi shuru cikin nutsuwa,haka hall din ya dauki shuru,shurun daya sakata ta tsargi kanta da kanta saboda gani data fara yi kaman kowa idanunsa yana kanta.
"Bazakuce komai dashi ba?" Ta fada cikin son danne tsarguwa da nauyin data ji.
Wazeer ne ya gyara zamansa sosai yana dora idanunsa a kanta.
"Mun gode sosai sheikh haisam.......shawararka ta karbu,kuma in sha Allah bazamu kunyata sultane ba,Ahmad ya dawo a daidai,zamu dafa masa har sai ya cimma gaci,saboda dukkaninmu ya fimu cancanta,alamun nutsuwarsa kawai tana bamu tabbacin zai iya"
"Na gode sosai.....na gode da fahimtata da akayi" Haisam.ya fada a girmame yana kashe kira.
Wani ajiyar zuciya morsa safiyya ta sauke hawaye yana sauko mata sanda kowa ke rattaba hannu gurin yarda da amincewar cancantar ahmad akan mulkin AGADEZ. Ta sake girmama hukuncin Allah me juya al'amura a yadda yaga dama. Wa ya taba tunanin sake samun ahmad a raye?,har wannan rana tazo da zai hau sarautar mahaifinsa koda kuwa riqon qwarya ne.
"Zakaran da Allah ya nufa da cara" Ta furta a hankali,saqon kuma yakai kunnen mammina,saqon da ta fadeshi ne kawai saboda lamarin ya mata kama da hakan,maganan kuma ya dauki hankalin mammina daga mummunan kallon da take saukewa wazeer. Yadda ya bata amsa a dazun kamar akwai wani qulli a ransa shima game da ita,me yasa bata tana sakashi cikin target dinta ba?.
"Yanzu ma bata baci ba,ban makara ba" Ta bawa kanta da kanta amsa,sai murmushi ya biyo baya ta jinjina kai.
"Kun sake sakashi a qabarinsa a karo na biyu.....qabari kuma duk wanda ya shigeshi sai ranar tashin qiyama shida fitowa" Ta fada can qasan ranta.
*ETHIOPIA*
*_ABA JIFAR INTERNATIONAL AIRPORT (JIMMA AIRPORT)_*
Cikin shigar da tayi daidai data 'yan uwanta,cikin yanayin da bai banbance matsayinta dana su Aanani ba take zaune cikinsu,cikin ayari ne musamman dake dakon isowar prince sheikh muhammad haisam aba jifar.
Tun daga ranar da labarin YAYI AURE ya shiga kunnenta,idan tace tayi cikakkiyar lafiya ta zuci data gangar jiki to tabbas tayi qarya. Daga wannan rana BACCI ya zame mata wani abu me wahalar samuwa ga idanuwanta.....daga wannan rana suka qulla abota da kukan zuci....daga wannan rana ya zamana ba wata rana da zata fito ta fadi bata tsaya gaban madubi ba.....bata kalli kanta ta tambayi kanta da kanta.
"ME KIKA RASA SAAMEE?.....MEYE BAKI DASHI DA KIKA GAZA FARAUTO SOYAYYAR CAPTAIN SHEIKH?" Wata tambaya guda daya data gagara samun amsarta.....sai kuma wani rashin tabbaci na
"Kin haqura?.....zaki yarda makamanki?,zaki tabbata mara nasara ta hanyar barwa wata shi?" Wannan tuhume tuhume ne da zuciyarta ke yawan yi mata su amma ta gaza bawa kanta da kanta amsa.
A daidai wannan lokacin sai takejin wani ciwo yana qulle mata a qirji. A duk inda ta ajiye idanunta zallar farinciki take gani a fuskar kowa na dawowarshi.....zumudi da walwala da fatan isowarshi cikin ahalin aba jifar da matar da zata yita amsa sunanta da nashi a maqale
"Matar shiekh muhammad haisam... Yarima me jiran gado" Ta lumshe idanunta muryarsu Aanani na mata amsa kuwwa. Ta kasa bude idanunta saboda ba abinda take kalla sai walwalar dake saman fuskokinsu.
Sanda qugun jirgin da yake bata tabbacin jirgin da suke dako ne ya iso.....a sannan ta bawa kanta da kanta amsar tambayarta..... Ba zata iya jurewa ba.....ba zata sallama haka da sauqi ba......ba kuma zata yarda tayi asarar abinda ta rayu shekaru kusan uku tana burin mallaka ba.
Saita samu kanta da miqewa tsam.....a sannu a sannu ta soma ja da gaya tana bacewa idanun duk wanda zai iya ganinta,tana barin dakin jira na musamman din da aka bawa iyalin me martaba ibraheem aba jifar don jiran isowar SHALELEN QASAR HABASHA......wanda airport din ta cika da manyan mutanen dake dakon isowar haziqin ma'akacinsu......sannan masarauta ke dakon isowar magajinta.
Ko ba'a gaya maka ba,koda kuma baqo ne kai cikin garin jimma idan ka kalli aba jifar international airport din zakasan cewa akwai babba kuma muhimmin abu da yake faruwa cikin airport din,saboda wasu irin lafiyayyun motoci dake jere bisa tsari masu kama d'aya dukkaninsu suna jiran isowar private jet din dake dauke da prince sheikh muhammad haisam aba jifar da matarsa.
Dukkanin mutanen dake airport din suna jiran isowarsun suma cikin tsari suke,fuskokinsu cike da walwala annashuwa da hira kadan kadan me nuna nutsuwar kowannensu.
HUSSAM kyakkyawan matashin mallakin qabilar oromo,kuma jini ga sheikh haisam din,kusan shine jagora kuma shugaba na tafiyar gaba daya. Kai kawo yake yana duba lokacin da yake a rubuce na saukar jirgin. Kamar ya matsu yaga isowar captain obbo......ya matsu idanunsa su sauka akan d'an uwan nasa da macen da tayi nasarar wuf dashi.
Cikin nutsuwa private jet din ke sauka da wani irin yanayi daya sauka saman zuciyar akhnan wadda ke zaune cikin kujerun alfarma da jirgin ya mallaka. Iya kujerun da su kadai sun isa su gaya maka luxury din dake cikin jirgin koda baka taka qafarka zuwa ko ina ba.
Yau jikinta yafi yin sanyi sama da ko yaushe....a yau da jirgin ke daukosu daga jidda zuwa jimma sai takejin komai yana kwance mata fiye da ko yaushe.
Wani irin royalty take gani.......wani irin yanayi na zallar girmamawa da wani irin respect. High luxury na rayuwa daya sake damalmala mata lissafin data fara qullawa kan WANENE HAISAM DIN.
Tafiyar awa shida ce.....amma banda sallah da yace tayi ta shiga toilet ta fito tazo tayi sallar bata sake motsawa ko ina ba. Hasalima yau da suke zaune guri daya na awanni masu yawa ya zame mata kamar wani surukinta. Tun shekaran jiyan da wannan abun ya gilma.....tun ranar bata sake bari idanunta sun shiga cikin nasa ba. Haka kuma takejin nauyin yana sake daduwa a kowacce rana,da mamakin yadda yake komai kanshi tsaye ba wan kwana kwana kamar komai ma bai taba faruwa ba.
Lumsassun idanunta ya soma budewa a hankali bayan ta tabbatar jirgin ya isa ga qasa......qasar da takeji a ranta a nan zata rayu?......na tsahon wanne lokaci ne?,wacce kalar rayuwa zatayi?,dawa dawa kuma zata rayu din?. Tambayoyin da suke sanyayar mata da dukka gabbanta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Falaak take tunawa taji sanyi da nauyin dake qirjinta ya ragu,saidai sam ba zatace taga falaak sau biyar cikakke ba tun daga barinsu agadez zuwa yanzun da suke sauka a jimma cikin jirgin da iya ita dashi ya dauko kamar dai wadancan jiragen. Akwai banbanci me yawan gaske na zahiri tsakanin wadancan jiragen da wannan.....nisan tazarar daya sake luluqa tunaninta a kanshi.
Idanunta duka ta qarasa warewa jin jirgin ya tsaya. Bata tsammaceshi a kusa da ita haka ba,don haka kanta tsaye ta ware idanun nata fes sukayi kyakkyawan matsugunni cikin nasa kuwa.
Zaune yake sosai a kujerar da take facing tata kujerar.......da wannan kayan da tunda ya fito daga dakin hotel dinsu na raffles makkah ya dauki idanunta da hankalinta,saidai a yanzun takatsantsan take da komai daya shafeshi a yanzun,bata yarda wani dogon kallo ya hadasu ballantana ya kama idanunta.
Ya zuwa yanzu ta gama sallama.....idanunsa ba.....burgeta suke,wani irin burgeta sukeyi,tana jin kamar a duniya sune idanu mafiya kyawu na farko data taba gani. Bata yarda ta kalleshi kai tsaye ba,saita sauke idanunta akan dogayen yatsunta farare tas da har yanzu sauran lallen jiki bai fita ba.
Shuru ya ratsa tsakaninsu,wani irin shuru da batasan me hakan yake nufi ba.
"A jirginma.....a qasarsa ma sai ya nuna izzar?" Ta fada can qasan ranta tana jin alamun idanunshi a kanta.
Da gaske ita yake kalla,zara zaran yatsunta da take murzawa a hankali. A duk sanda zai kalli hannuwanta sai tuna yadda yatsunsa suke narkewa cikin nata duk sanda zai kamasu. A duk sanda ya kallesun sai yaji kaman ya kamasu ya maqalesu cikin nasa. Taushi da dumin da yakeji a jikinsu na dabanne. Rigar jikinta wata irin luxury abaya ne da aka sanya dollars masu nauyi aka siyeta cikin haramin makka. Sun mata wani irin kyau.....wani irin black color me daukan idanu. Yana jin bazai iya barinta ta fita a haka ba......yana jin kamar duk mutanen jimma suna bakin qofar jirginne suna son ganin fuskarta.
Idanunshi ya zare yana jin wani numfashi me nauyi yana subuce masa. Ya saka hannunsa yana yaye labulen window din jirgin don ganin yanayin da farfajiyar ajiyar jiragen take ciki.
A kanta idanunsa suka sauka......Khansaa Moti ibraheem aba jifar. Jinin sheikh muhammad haisam,kyakkyawa macace 'yar qabilar oromo na asali,diya ta farko daga tsatson ibraheem aba jifar da khadeeja yunnus jallata.
Sanye take da wata tattausar lafaya wine color,wadda aka yiwa ado da olive green me wani irin nau'i me daukan hankali. Kyakkyawa ce ta gaske......wadda jinin moti aba jifar ke gwada kansa sosai a jikinta. Da kallo daya kawai idan kayi mata zaka tabbatar da cewa basarakiya ce.....akwai sarauta da mulki dake zagayawa cikin jininta.
Ita kadai yake hangowa tana takowa da kan matattakalar jirgin. Kallo daya ya yiwa fuskar 'yar uwartasa ya hangi wani irin murmushi kwance saman fuskarta dake kama data moti sak da sak.
Daga matakalar qarshe ta dakata,cikin izzar nan data zame musu natural a halittarsu,ta miqa dogon hannunta dake shirye da wasu irin awarware na iko tana karbar kyakkyawan qaraman luggage din dake hannun hadimarta,wadda ke ajiye qafarta duk inda khansaaa ta ajiye.
"Ki koma qasa,zamu fito yanzu" Tayi maganan da iko sosai cikin muryarta. Rusunawa tayi ta miqa mata akwatin,sannan ta soma sauka da stairs na jirgin tana komawa inda sauran mutanen ke tsaye jikin matakalar cikin jerin sahu guda biyu hagu da dama.
Murmushi ta sake saki sanda crew din ke bude mata qofar tana mata nuni da inda su haisam din suke cikin girmamawa,ta jinjina kai kadan sannan ta fara takawa a nutse fuskarta shimfide da wata tattausar fara'a tana nufar gurin.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽