Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 38

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 38

.....facing. A girl's side! Because of her, our friendship has faded. What do you think now? She was crying for lovers. Alhamdulillah Yaya Malam prevented the marriage. She is better off marrying a poor man. This time, my breathing was a little slow and I stood still, my legs were as if they were planted on the ground. Anti Luba? Who do I think is the mother of wisdom? Is she the one saying these things about me? Is she my enemy? With a heart like that? Thank God for my mother. My eyes filled with tears that I forced them not to fall. I adjusted my voice and said Anty Luba... hello and wait. I stopped for a while... She quickly spoke, as if she didn't know I was listening to her words. Then she changed her voice and made a lie in persuasion. By God, there is no way I know why I told you to come. Banson Zainab came to tell you something bad. Anyone with a heart of faith will want you to stand up and defend yourself. I smiled. A smile that hurts more than tears. The smile that contains the darkness of life, and the fatigue that the heart is facing. I didn't say anything. I opened the car door and entered in silence. On the way no one spoke. But in my heart, there is a noise of the t

Standalone post1,443 words

A hankali na karaso bakin motar Anty Luba. Hannuna na kadawa kadan, zuciyata na bugawa da irin fatan da ba a iya furtawa fatan ganin fuskar da a da nake ?auka kamar mafaka, fatan jin muryar da nake kallo a matsayin ta uwa... ba wai uwa ta jini ba, amma uwa ta tausayi. Sai dai kafin na isa kofar motar, sai ga sautinta ya doki kunnuwana kamar wuka mai kaifi. Muryarta tana fitowa daga wayarta, ba tare da ta san ina kusa ba. Kalamanta sun yanke min numfashi kamar ruwa mai sanyi a dare babu dumi, babu sanyi sai radadi.

Ai wallahi sai ka ga yadda ya haukata kansa akan wannan diyar mahaukatan Ramlatu. Ya lallace! Ni fa gani nake kamar ba zai tashi ba. Har matar baban ta ce wai lalata suke yi da Khalil din! Bata ma da tabbacin tanada budurcinta. Gabana ya fadi. Na kasa motsawa. Hawaye suka tsaya a tsakiyar idona.

Tayi dariya. Dariyar da ba dariya ba bace dariyar mugunta ce, dariyar zuciyar da ta ?i jin tausayi. Sannan tace da wani salo mai zafi Ai ni Zainabu Taimun dai dai da take cin ubanta. Shegiyar yarinya! Saboda ita ne zumuncin mu ya dusashe. Kaga yanzu? Kuka take yi wai masoya. Alhamdulillah da Yaya Malam ya hana auren. Ta fi dacewa ta auri wani talaka.

Wannan karon, numfashi ya dan tsay da fita daidai Na tsaya cak, kafafuna sun kafe kamar an shuka su a ?asa. Anty Luba? Wacce nake dauka uwar hankali? Ita ce ke furtan wannan kalamai akaina? Ita ce makiyata? Da zuciya iri haka? Innalillahi wa inna ilaihi raji un.Da kyar na iya jan numfashi, sai na karasa kofar motar da jiki a raunane. Idanuna sun cika da hawayen da na rin?a tilasta su kar su zubo. Sai na daidaita murya nace Anty Luba... sannu da jira. Na dan tsaya ne... Da sauri ta jiyo, kamar wadda bata san ina jiyo maganganunta ba. Sai ta canza murya, ta sanya wata ?arya cikin lallashi Wallahi babu yadda zanyi ne shiyasa nace ki zo. Banson Zainabu taje tayimiki wani sharri. Duk mai zuciyar imani ai zai so ki tsaya ki kare kanki. Na yi murmushi. Murmushin da ya fi kuka zafi. Murmushin da ke kunshe da ?aryar rayuwa, da gajiyar da zuciya ke fuskanta. Ban ce komai ba. Na bude ?ofar mota, na shiga cikin shiru. A hanya ba wanda yayi magana. Amma cikin zuciyata, akwai hayaniya hayaniyar gaskiyar da ta fara haskakawa. Ita ce Anty Luba gatana, uwar ?arya. Ita ce ta jefa ni cikin rudani, ta lakume amana kamar abincin dare.

Da na karasa cikin gida, na tarar da Abba ya dawo. Yana zaune a falo, kamar yadda ya saba idan ya gaji daga aiki. Da nutsuwa na karasa kusa da shi, na sunkuya kadan cikin ladabi nace Abba, sannu da dawowa. Ya dube ni da idanu masu taushin hali, ya amsa Yauwa Ramlatu. Yaya hanya? Na dan gyara zama, na mikawa Mumy ledar da Anty Luba ta bani. Ban ce komai ba. Na bar kaya suka yi magana da kansu. Sai na lura... fuskar Abba tana ?auke da wani irin nauyi. Fuskar wanda zuciyarsa ke daure da tunani. Shi mutum ne mai tausayawa, mai ?aunar dangi da zumunci, amma yanzu kamar an ?aure masa zuciya da sarka. Ina ganin haka na fahimta... Mumy ce ta mamaye tunaninsa. Gaba ?aya hankalinsa yanzu, bata bar wa kowa sarari ba. Na mike da nufin barin falon, sai na ji ya kira sunana Ramlatu... Na juyo a hankali. Ya dube ni, Malamin islamiyyarki ya kira. Gobe ki shirya, zaki je. Na ?aga kai kadan, nace To Abba. Na nufi ?akina a kasalance. Da zarar na shiga, na cire kayana cikin gajiya. Jikina duk yayi sanyi, ba don sanyi na waje ba amma don gajiyar tunani, da radadin cikin zuciya.

Na shiga wanka, amma kurajen da ke jikina, musamman a gabana, sun kasa mutuwa har yanzu. Su na ci gaba da bata min kwanciyar hankali. Duk wani motsi sai in ji zafi. Wannan zafin jiki ya ?ara haddasa ni?a-ni?a a zuciyata domin ya tabbatar min da cewa ni ce kawai nake fama da wannan tashin hankali, babu wanda yake damuwa da jin ko ina lafiya ko a a. Na bude kasan kayana, na ?auko Maclean daga wanda na tatso agurin Mumy. Na wanke bakina da shi,Sai na zauna, na tsefe kaina jiki a raunane, zuciya a gajiye. Na kwanta. Amma kwanciya ce ta jiki, ba ta rai ba. Idanuna suna kallon sama, zuciyata na tambaya Ina Khalil? Ko wanne hali yake ciki kuwa? Wannan itace tambayar danake taxiway kaina. Inama ina da waya. Inama zan iya tambayarsa, in ji muryarsa, in san halin da yake ciki. Amma babu.Na juya gefe daya. Hawayen da suka kasa fitowa tun dazu sun gangaro a hankali. Na lullu?e kaina da bargo

Sai da dare yaraba Na farka da ihu. Wallahi na rantse, ban taba jin tsoro irin wannan ba a rayuwata. Jikina duk gumi, zuciyata kamar zata fado kasa. Har yanzu ina jin kamar ina ciki... ciki na wancan mummunan mafarkin.

A mafarkin, na tsinci kaina a cikin wani daji mai duhu. Komai ya narke da duhu, kamar rana ta ?i fito wa duniya. Sai iska mai sanyi tana kadawa, tana shigowa ta cikin fata ta har jijiya. Duk inda na kalla, babu rai, babu tsuntsu, babu sautuka shiru ne kawai da wani nauyi a zuciyata. Na fara tafiya... amma ban san ina nufa ba. Cikin duhun nan, sai na fara jin ?amshi ba mai dadi ba, ba kuma mai muni ba. Wani ?amshi ne da ke tuna min da kabari. Sai na ji gabana ya fa?i.Kafin na ankara, sai wata mata ta bayyana a gabana ba zata fi tazarar taku biyu da ni ba. Gashinta ja-jayi, tsawo kamar zobe, tana kallona da idanu marasa rai. Hannunta na ri?e da wata wuka mai kaifi wadda ke ?auke da jini mafarkin jinin ne? Ban sani ba. Ta fara dariya... wata dariya mai cike da mugunta. Kamar daga wata duniya daban. Ta ce min da murya mai ?yarar kunne Ke ce! Na jira wannan rana... yanzu zaki biya! Na juya da gudu amma ?afafuna sun ki motsi. Na yi ?o?arin yin ihu, amma muryata ta makale kamar an ?aure min makogwaro. Ina kallo, tana matsowa kusa da ni. Sai ta daga wukar sama... ta sauke ta da ?arfi! Na farka nan take. Ban san yadda na tashi ba, amma na san ihu nayi sai dai har yanzu zuciyata tana rawar jiki. Kamar mafarkin bai ?are ba.

Washegari da safe, duk da cewa jikina har yanzu bai gama dawowa daidai ba daga wancan mafarkin, na tashi da niyyar mantawa da shi. Na nufi aikin yau kamar yadda na saba tsaftace falo, gyara curtains, da share-share. Duk abinda nake yi, zuciyata tana cikin tunani. Sai na ji muryar Mumy da Yaa Billy daga ?akin falo. Suna magana, amma muryoyinsu cike da damuwa. Na dan matsa kusa kadan, ba don le?a ba, sai don ji idan wani abu nake bukata na gyara.Abin da na ji ya tsaya min a zuciya.Yaa Billy ta fara da murya mai sanyi, kamar wadda ta sha kuka

"Ina sonsa Mumy... Wallahi. Ina masa mahaukacin so. Kuma ni zan iya da ita." Bansan waye wannan da ake magana akai ba. Amma kalmarta "da ita" ta janyo hankalina. Kamar ana magana ne akan wata mace, wata kishiya ko wadda ke tsakani da Yaa Billy da wanda take so. Amma ina, ni dai ban ce komai ba. Sai na cigaba da sauraron yadda Mumy ta mayar da martani cike da hushi da takaici. "Ke wai baki da hankali ne? Matar da kika zauna a gidanta, har kika gama jami a? Kuma kinsan halinta! Ita zakice kina son mijinta?" Na tsaya cak.

Na gane yanzu, ana magana akan abokin abba wannan attajirin. Sai Mumy tace "Kingani Bilkisu, kar ki jawo min magana. Ki kalli yadda mijin ke rike hannunta a hoton da kika gani shine kikeso ki sa kanki a tsakaninsu? To! Ahir! Wallahi kar na kuma jin wannan batu a bakinki. Kada ki jawo min masifa. In banda ke da fitinarki, ina ke ina Alhaji As ad? Masu kudin ?asa! Ga mulki, ga kudi! Ki bar wannan batun!" sai na ji shesshekar kuka. Yaa Billy ta sa kuka ta fice daga falon da sauri, ba tare da ta ce komai ba.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH

SHAFI NA TALATIN DA TARA

Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435

Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********