
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 45
..... that's enough for her to join her soul. The word entered the third day and she started to let go of what she was holding and turned her head to Aanani, she was looking at the stairs of the plane, this made her focus on Aanani's frustration. When it comes to data fetching and downloading, Aanani does his own thing. She only makes tasbihi, which causes many people in the place to faint what is in their hearts and souls. "This man......does he know what he has saved?, is he able to look at women?, is he able to choose where his eyes are?" Rumaisa said while holding Aanani's hand, Aananin with all her composure moved, her only wish was for them to reach the place, she hugged Akhnan and made sure what her eyes were seeing was real?. Her heart is just melting in a certain state. The welcome they received from the last staircase in the words of respect coming out of the mouths of the people who confirmed that they were close to him. Are those close to him? Where do I see the other common people?. It is a red carpet that contains big words of welcome in a short text to make sure that it is not woven from useless threads, the carpet is designed to the extent that she thinks its height
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 45*
"Na shiga uku!" Aanani dake tsaye kusa da rumaisa cikin wani irin yanayi na bala'in qagauta ci da zuci da jin kamar ta tattaka matakalar jirgin ta qarasa shiga ciki ta taddosu.
"Yaa Khansaaa ta dade.....me sukeyi ne a ciki?,don Allah da kalli kusan mintinan mu nawa?......anya ba ramawa yaa Khansaaa zatayi ba?" Maganganun data dinga fadi kenan tana takurawa rumaisa wadda ke cikin Instagram tana duba masu deco din gurin event da Khansaaa tace ta duba musu.
"Ya isheni haka mana Aanani?.....idan ba zaki iya jira ba,me zai hana ki shiga ki gayawa Capt obbo din ya dade?" Idanu ta fiddo,ta sani gatsali take mata kawai,don ko giyar wake tasha ina ita ina wannan aikin.
"Komai sai kice naje na gani ko na tambaya?.....ba obbo hussam bafa ake magana?,CAPTAIN OBBO nace miki".
" Aanani" Rumaisa ta fada wadda maganan Aanani ya tilasta mata sauke ipad din da take kalla ba ta zubewa Aanani din su.
"Nayi shuru" Ta fada ganin yadda rumaisa din ta hade rai.
Kalmar na shiga ukun data fada ita ta saka rumaisa sakin abinda take ta maida kanta ga Aanani din,saita lura stairs na jirgin take kalla,wannan ya sanyata maida hankalinta gurin cikin takaicin Aanani. Saidai fit duk wani fada data debo zata saukewa Aanani yayi nasa guri.
Tasbihi kawai takeyi,wanda tasan yawa yawan mutanen dake gurin suma abinda ke cikin zukatansu da rayukansu.
"Man dinnan......ashe yasan wanne tanadi yayi?,ashe ya iya kallon mata?,ashe ya iya zabe ras idanunsa suke?" Rumaisa ta fada tana damqe hannun Aanani,Aananin da nutsuwarta dukka tayi qaura,nata burin kawai su iso gurin,ta rungumi akhnan ta tabbatar da abinda iidanunta suke gani da gaske ne?.
Wani irin narkewa kawai zuciyarta keyi cikin wani irin yanayi. Tarbar da suka fara samu tun daga matakalar qarshe cikin kalmomin girmamawar da taji suna fita daga bakin mutanen data tabbatar makusanta ne a gurinsa. Makusantansa ma kenan?,ina ga sauran mutanen gama gari?.
Shinfidadden red carpet ne dake dauke da manyan kalmomin welcome cikin wani qasaitaccen rubutun data tabbatar ba daga zaren banza aka saqashi ba,carpet dinne shimfide iyakar ganin da take kyautata zaton tsahonsa yakai har inda zasu qarasa ga motocin da isa da iko yasa aka barsu suka shigo sansanin saukar jiragen daga bangaren da tsaiwarsu bazai bada matsala ba.
"English kawai" Khansaaa ke fadiwa su rumaisa tana duban idanunsu.
"Duk wanda kika gani anan yana da kusanci dani ta kusa sosai.....qanne....yayye....aunties da uncles dina" Ya fadi qasa qasa da tataccen French dinnan nasa dake sake qone mata ruwan kai da kuma goge mata hadda. Wani abu ta hadiye tana lumshe idanunta,sannan ta gyada masa kanta a hankali. Wani irin sanyi jikinta yakeyi,ya matsa hannunta a hankali yana sake cewa.
"Akwai girmamawa sosai a al'adarmu ga dukka wanda ya girmeka,gaisuwa dole ce....a yanzun za'a dauke miki na sani saboda banbancin harshe da yare dake tsakaninmu.....amma zaki san hakaa gaba,zaki koyi hakan....." Ya sake fada softly,daidai sanda Aanani ta gaza jurewa ta tako ta ruskesu.
"Ina jin kamar na zama tsuntsuwa na riskeki tun kafin ki fito......barka da zuwa yayarmu" Aanani ta fada tana rungume akhnan Kai tsaye cikin jikinta.
Batasan me ya jefa murmushi saman fuskarta ba,amma ta samu kanta da maidawa Aanani martanin rungumartata.
"Na gode" Tace da Aanani din,wanda kwarjinin haisam kawai ya sanyata janyewa da baya tana bawa sauran guri.
"Muryarta dadi.....wani qamshi takeyi me dadi yaaa rumaisa" Aanani ta fada tana kasa tsaiwa guri daya tsabar zumudi.
Tun daga gaisuwar musabaha data fara binsu daya bayan daya sunayi ta soma ganin wani irin kalar karamci. Duk da ba kowa take iya jin abinda yake fada ba,amma yanayin fuskar duk wanda yake gurin tana iya hangen zallar kulawa da girmamawa me tarin yawa a tare da ita.
"Saura nan bangaren" Aanani ta fada tana nuna sashen da cousin dinsu maza ke tsaye,saidai ta kasa qarasawa saboda wani kallo da haisam ya aje mata.
Daga bayansa ya ajeta,suka qarasa suna gaisawa da masu shekarun ciki. Tana daga bayan nasu take qoqarin gaidasu da harshen English,gaisuwar da bai bari tayi nisa ba ya juya suka soma bin carpet din daya karkata shiyyar da motocinsu ke tsaye suna jira,saidai ko taku uku cikakke basuyi ba wata inuwa ta mamayi saman kansu da wata irin lema ta alfarma,kaman qiftawa da bismillah kuma hadimai suka rufe hagunsu da damansu su da duk wanda yake takawa ta bayansu.....gaba kadan kuma wasu qosassun mutane ne sanye da baqaqen suit da farar 'yar ciki. Komai nasu iri daya ne,hatta da takalman qafarsu kuwa,bata kuma lura dasu ba sai da sukazo dab da inda motocin suka jera kansu.
Gaba daya jinin jikinta ne yaso daskarewa na wasu daqiqu,lafiyayyun Rolls Royce ne da adadinsu ya kusa guda goma zalla,sannan wasu BMW din da suka adadinsu ya kusa guda goma din.
Biyar daga cikin Rolls Royce din sunfi duk wata mota dake gurin tsada,motocine dake nuna tambari na SARAUTA da masarautar data amsa sunanta wajen cikka izza qasaita da isa. Qirarsu ta daban ce.....sabuwar qirar da sai shekara me zuwa kamfanin zai fiddasu.
"Me yasa komai irin wanda jama'a ke jira shekara ta gaba a fitar musu ne?,ya akayi shi yake dasu?" Ta tambayi kanta a rikice idanunta na sauka zuwa qarshen red carpet din. Ddaga inda zai qare kaman qiftawar idanu,ba tare da taga anyi wani motsi na bada umarni ba aka maye gurbin qasar gurin da wani hand Embroidered royal carpet wanda yake bada cultural da royal identity. Wani irin qawataccen zane ne na sarauta.....sarautar gidan ibraheem aba jifar,masarauta mafi girman iko isa da qasaita cikin qasar habasha.
Kallon carpet din kawai take tana Takashi a hankali tana qididdige irin kudin da aka zuba wajen saqashi. Wata irin saqar hannu ce dake nuni da zallar iko da isa.
A wannan ranar.....bashi ke bude mata qofa ba,kaman yadda bashi yake budewa kansa qofa ba,qofar da kanta tasan da isowarsa,cikin girmamawa kuma akayi wata qaramar magana data zauna da girma sosai a zuciyarta kafin ta bude qofar a hankali.
"Welcome sir" Shine abinda qofar kawai ta fadi.
Batasan wanne adadin abubuwa take buqata ba kafin ta samu nutsuwar data kamata....shigarta motar sai ya zamana kamar an cireta cak daga wata duniyar ne zuwa wata duniyar ta daban. Ba mota take gani ba itakam,ba wani alamun mota tattare da inda take zaune a yanzu tana kallon yadda hadimai da qwararrun masu tsaron lafiya ke kaffa kaffa dashi cikin wani yanayi na tsantsar qwarewa da tattali,tamkar wata kadara guda daya kenan da suka taba mallaka a rayuwarsu mafi girman daraja da tsada a duniya.
"Don Allah kibar motarmu ta bisu.....ban gaji da ganinta ba yaa Khansaaa"
"Ba yanzu ba Aanani,ba yanzu ba,baquwace har yanzu batasan komai ba,sannan kin sani ba masarauta za'a wuce da ita kai tsaye ba,al'ada bata bawa kowa da kowa daman ganinta ba,me kikeci na baka na zuba?,taku ce fa,surukar nanay ce" Khansaaa tace da Aanani data so taqi shiga nasu motar da zai maidasu gida.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Amma dai wannan.....an lasa mana zuma ne a baki fa"
"Kiyi haquri....karkisa captain yayi magana" Kiran sunan haisam kawai ya sanya Aanani dole ta haqura,ta shiga wata motar daban.
Tana jin sanda aka gama busa wani sarewa data tabbatar algaita ce.....amma ba irin algaitarsu sak da sak ba suke ji tsakanin nigeria da niger ba. Wani busa da a kowanne fita da sautin zaiyi GIRMAN IZZA YAKE NUNAWA....suka kammala,convoy na motocin suka soma jera kansu da wani irin tsari da zai gaya maka kowanne driver dake riqe da steering motar tabbas yasan me ake kira mota.
Wani shuru ya wanzu cikin motar,shurun daya qara shakka kokwanto da taraddadi me yawa a zuciyarta. Zuciyarta ta qara wani nauyi tare da matsanta mata son sanin amsa guda daya tak da ta nanatawa kanta tambayar WAYESHI har batasan adadi ba.
Blue eyes dinta ta daga zuwa gareshi,idanunsa suna kan titi kaman me son gane dame dame qasarsa da yankinsa suka rasa bayan baya nan?. A yau da take kallonsa da shudayen idanunta.....inda ya kula.....inda zai iya daga ido ya kalleta ba abinda zai gane face ROQO DA FATA nason sanin wayeshi da gasken gaske. Saidai a yau din ba zata iya buda bakinta ta tambayeshi kaman yadda ta saba yi a baya ba.
Bata kammala wannan tunanin ba taji driver dake jagorancin motar yana isar masa da saqon zasu sauka don tsaiwa su karbi tarba daga shugaban qasa.
"Okay" Kawai ya fada da wannan nutsuwar tasa data saukar da wani tasiri a zuciyarta.
"Nutsuwa da haiba" Zuciyarta ta fada mata a hankali,abinda ya sanyata dauke kanta zuwa wani sashe na daban tana jin kamar zuciyarta zata narke.
Wanne irin duhu yaketa sanyata haka?,me yasa bazai taimaki ruhinta ya taqaita mata wahala da ragaita da tunaninta yakeyi tsakanin tsoro shakka da kokwanto?.
Ta daga idanunta a nutse tana maidasu ga window ta cikin baqin gilashin da zai baka daman ganin na waje ba tare da shi ya ganka ba.
Shine....mr President na Ethiopia gaba daya Taye atske selassie,tare da prime minister abiy ahmed.
Dukkaninsu ta sansu,saboda tafiye tafiye na seminar data tana hadasu a gurare har biyu.
"Afwan......khansaa zata kasance da ke,zan sameku a gida in sha Allah......you are safe" Ya fada softly yana bata tabbaci da qwayar idanunsa.
Kamata yayi taji bata gamsu ba......kamata yayi taji ta qaryatashi da dukkan ruhinta da gangar jikinta,amma abun takaicin sai taji zuciyarta ba wani d'ar shakka ko kokwanto akan maganarshi.
Da idanu ta bishi sanda yake sauka a motar,da dukka nutsuwarsa yake takawa zuwa garesu,ba wani yanayi da zai nuna maka farin shigar haduwa dasu ne,dukkan takunsa da motsinsa yana nuna maka mutumin da aka haifa cikin mulki da iko ne.
Idanunta ta janye gabanta na bugawa da qarfin gaske sanda taga yana basu hannu kai tsaye suna musabaha,fuskar nan tasa da madaidaiciyar fara'ar dake qara fidda kyansa da kwarjininsa,daidai sanda khansaa ke shigowa cikin motar.
"Sai kinwa angonkin nan uzuri,jama'arsa yawa ne dasu,kowa zai buqaci ganinsa na sani a dawowar nan,zai iya zama busy na wasu lokuta.....amma idan komai ya daidaita....." Saita dakata tana sanin murmushi.
"Zaki bada shaidar ba macen data kaiki dacen miji" Ta qarasa fada sanda motar ta fara motsawa a hankali da sauran ayarin motocinsu da suka fita daga cikin nasu prime minister da mr President.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽