Kenza eBookz
Cover art for L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 46

Post

L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 46

..... the weight of the cancer brought her down, she slowly lowered her eyes. Her question has no answer.....because she can't say anything. She still doesn't know, did she steal him or did he steal her? None of them did a great job. She can directly say that it is the sultan's job..... it is the sultan who has prepared everything, not her... as her first suspicion is that the silar of preparing everything has already taken her away from her soul. "But is he the one who started it?..... I know his behavior... he has some kind of secret that I have never seen in anyone's place but my cousin" She said again lowering her voice with a different style of teasing. The way she talks like it's a secret makes her laugh. What kind of people are these?, she looks very royal with them in a certain style... but also a gentle attitude and dealing with them to that extent?. Her eyes widened as she listened to Khansaa giving brief information about the haisam. The data reached her ears and went deeper to listen to them, and they kept opening a thin door for her, but the door didn't open... and it didn't lead directly to where she wanted to go. "Alhamdulillah, we are here" Taji hasna was saying, ju

Standalone post1,819 words

💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 46*

Sake gyara zamanta hasnaaa tayi,tana gyara lullubin tattausar laffayar jikinta.

"Allah yasa kada na dameki.....bana iya zama banyi hirara qanina ba" Ta fada da murmushi. Maganan daya dauke idanun akhnan daga kan hanya,ya maida kan hasnaa irin kallon da baya sauka kai tsaye cikin fuskar mutum.

"Ba don yana qanina bane.....amma shi din na dabanne. Inda Allah ya halatta aure tsakanin yaaya da qaninta,inajin da bazan bari ki samu Captain obbo ba" Ta fada da murmushi me sauti. Maganan ya sanya akhnan duban hasnaa kadan,fuskarta da idanuwanta dukka sun nuna mata da gaske take,abinda take fada daga zuciyarta ne. Saita gyada mata kai.

"Eh,bani kadai ba,na tabbata dukka qannen haisam idan da zaki tambayesu zasu gaya miki haka.....amma tsaya.....meye sirrin?,wannan zuciyar......ya akayi kika samu muqullin budeta?" Tayi tambayar da sigar tsokana da dariya sosai akan fuskarta. Murmushi kadan akhnan ta saki,haka kawai takejin wani nauyin khansaa ya saukar mata,tayi qasa da idanunta a hankali.

Tambayarta bata da amsa.....don bazata iya cewa komai ba. Har yanzu bata sani ba,ita ta saceshi ko shine ya saceta?,a cikin su batasan waye yayi wani aiki gagarumi ba. Kai tsaye ma tana iya cewa aikin na sultane ne.....sultane ne ya shirya komai,ba ita bace......kaman yadda zarginta na farko akan shine silar shirya komai tuni ya tsiyaye tas daga ranta.

"Kodai shine ya soma?.....nasan halinsa......yana da wani irin sirri da ban taba ganin gurin kowa ba sai qanina" Ta sake fada tana yin qasa da muryarta da wani salon tsokanar na daban.

Yadda take maganan kamar sirri sukeyi yaso bawa akhnan dariya. Wanne irin mutane ne wadannan?,tana hangen izzar sarauta sosai tare dasu da wani irin salo......amma kuma wani sassauqan hali da mu'amala garesu har haka?.

Idanunta ta lumshe tana sauraren yadda Khansaa ke bata taqaitattun bayanai akan haisam din. Bayanan data samu kunnuwanta da zurfafa gurin saurararsu,suka kuma dinga buda mata wata siririyar qofa game dashi,saidai qofar batayi fadi ba......bata kuma kaita zuwa inda takeson zuwa kai tsaye ba.

"Alhamdulillah mun qaraso" Taji hasnaa tana fadi,daidai sanda wayarta ta dauki qara. Kusan a tare suka maida dubansu kan wayar,ta dago fuskarta fal murmushi.

"Nanay ce.....anya nanay zata iya bacci yau?,matar sheikh a jimma kusa da ita?". Ta fadi wani kykkyawan murmushi yana mamaye fuskarta,sannan ta soma qoqarin daga wayar tana barin akhnan da zarcewa duniyar tunani.

"Nanay......khansaa.....hasnaaa......obbo......" Komai nasu wani iri yake mata,dukka sunayen baqi ne a kunnenta.

Cikakkiyar sallamar data burge akhnan taji hasnaaa din tayi cikin qaramar dariya.

"Nanay.....karki damu,matar captain tana cikin aminci......tana tare dani"

"Alhamdulillah.......alhamdulillah,karku barta cikin kadaici........abar mata duk wanda takeson kasancewa dashi,idan kun shiga ciki kun kammala komai ki kirani ki hadani da ita". Nanay dake tsaye gaban mirror dinta ta fada tana jin wani sanyi da nutsuwa yana saukar mata.

"Da wuri haka nanay?,babu kara ko kadan?" Qaramin murmushi Nanay din ta saki. Komai da takeyi kaara kawai take saboda dattijai dake cikin tafiyar,banda haka.....abinda zatafiso shine,taje da kanta ta tarbo matar muhammad dinta.....ta taka da kanta ta riqo hannunta,ta kaita palace learning residence. Itace mace ta farko da zata fara shiga gidan,wanda an ginashi ne kawai saboda ita. Suruka ta farko ga family din moti ibraheem aba jifar,amma tayi dukkan kawaici ta dauke kai ta barwa masu yi sukayi,hakan bai isa ba?.

"Hasnaaa....kiyi yadda yadda nace"

"An gama nanay" Ta fada da murmushi tana gimtse kiran,daidai sanda dukkanin motocin suka karkata akalarsu zuwa katafaren gate din me fadi da tsaho.

Wata irin qofa Dark carved hardwood me adon gold details,wata irin qofa ce da aka qerata da wani nau'in katako me duhu,katako ke daraja katako ba irin qofar qarfe da aka saba gani ba a dukka main entrance na gidaje. Da wani nau'in gold aka sassaqa zane a jikinta,zanen dake nuna symbol na sarauta da heritage dake nuna qarfin iko.

Lokacin da motocin ke qoqarin wucewa ta cikin qofar sai taji kamar sun qanqance saboda fadi da tsahon qofar. Idanunta ta sake saukewa a hankali akan murafun qofar guda biyu,tarihi take tunanawa da al'ada......amma ga duk wanda ya fita a gidan sarauta zai fahimci akwai alfahari wajen sassaqa qofar da kuma narkar da maquden kudade.

Zanen zaki ne a jiki,garkuwa da kuma wani irin crown da yasha banban da yanayin wanda ta taba gani. Idanunta ta maida kan mutum biyun da suka bude qofofin don bawa dukkanin motocin damar shigewa.

Wasu irin bayi ne manya,masu tsaho kauri da qiba,sama da yadda take ganin girma da cika idanun tamim da kusan yafi kowa cikin masarautar agadez irin wannan qirar. Sanye suke da wasu irin uniform dake nuna cikakakkun ma'aikatan da rayuwarsu ke cikin tsari.....uniform din da zai gaya maka an tsamosu ne daga wata masarauta me cikar izza da iko.

Wani irin parking lot ne dake tsare da wasu irin grass carpet na alfarma da wata irin rumfa dake bada yanayin ajiya me kyau,dukkanin motocin,duk yawansu a nan suka samu guri,kafin qofofinsu su fara budewa,saidai tasu motar bataga koda hasnaaa ta bude ba,sai murmushi data sauke mata.

"Wannan mutumin....kowa ma sai ya koya masa tsarinsa?,su waye mutanen nan?" Ta tambayi kanta da zuciyarta dake bugawa idanunta suna hangen hadimai da guards da sukayi sahu sahu kamar ba rai a jikinsu tsabar biyayya wa umarnin da bataji wanda yace musu ko kalma daya akan ga yadda zasu tsaya ko kuma ga yadda zasu tsara ba.....tsabar horo.....tsabar iyawa da tsananin qwarewa data zamewa kowanne hadimi ruwan jikinsa sakamakon jagorancin fasihin shugaba yarima me jiran gadon sheikh muhammad haisam. Sai ya zamana kamar kowa yasan kansa,kamar kowa yasan aikinsa.....kamar kowa yasan darajar kansa da muhimmancin lokaci,kamar kowa yasan abinda ya dace yayi a sanda ya dace ba tare da an bata lokacin yin magana da kowa ba.

A hankali qofofin motar suka bude da kansu ba tare da kowa ya budesu ba. Wani abu ya tsarga mata tare da sake nauyaya cikin kanta. Ta sani,akwai motocin dake da voice assistance.....akwai masu automatic doors.....amma bata taba tsammaninsu tattare da haisam ba.

Ta daya side din hasnaaa ta zagayo,ta miqawa akhnan hannunta tana fadin.

"Ki fito da addu'a....Rabbi anzilni munzalan mubarakan wa'anta khairul munzileen.....rabbi adkilni mudkala sidqeen,wa'akhrijni mukhraja sidqeen,waj'alni minladunka suld'anann naseera(addu'o'i ne masu kyau ga amaren da zasu sanya qafafunsu gidajensu na aure,sai a daure kuma a saka niyyar aiki da kykkyawan addu'a da fatan dake cikin ayoyin)". Lokaci daya dukkan ayoyin suka zauna mata a kai,ta maimaitasu kaman yadda taji hasnaaa tayi,sannan ta taimaka mata ta tattare mata rigar don kada ta taketa.

Maimakon grass carpet ko interlock ko marbles da take sanya ran gani a qasan,aah....wannan din wani shimfidadden velvet carpet ne me duhu da aka yiwa ado da zaren gold,iyakar ganinta.....ganin daya kai idanunta har hallway din.

Babban hallway take iya hanga daga gabansu.....wani irin hallway da aka tsarashi da wasu irin fitilu masu girma da tsaho da suke bada wadataccen hasken daya hana rana fitar da haskenta yadda ya kamata saboda hadarin dake kwance luf cikin sararin samaniyar jimma Ethiopia.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A hankali hasnaaa ta saita mata qafafunta zuwa bakin hallway din,ta tsaya cak tana fuskantarsa,daidai sanda siririyar daddadar busar sarewar ta soma tashi,sai tsaiwar ta mata kama irin tsaiwar da wani babban mutum keyi don ayi masa parade na girmamawa.

Cikin kintsi da nutsuwa gurin yake,kowa yana tsaye a nutse,yawansu bai sanya komai ya hargitse ba,iya yanayin kawai zai gaya maka harka ce ta mutane masu cike da addini da nutsuwa,wadanda suka samu tarbiyya da horo daga hannun daya dace.

Kyakkyawar dattijuwa ce,wankan tarwada dake da matsakaicin tsaho da kuma jiki take takowa ta saman wannan velvet din tana doso akhnan dake tsaye kanta a qasa. Daga bayan matar wasu matasan 'yammata ne guda shida,sanye da tufafi iri daya da suma sukafi kama da tufafin masarauta. Dukkanin su hannayensu dauke suke da wasu irin qawatattun Ornate wooden chests. Kallo daya zaka yiwa abubuwan masu kama da akwati me four corner kasan cewa zallar tarihi da al'ada me nuni da mulki da isa ke tattare dasu,duk kuwa da cewa suna lullube ne da wasu qawatattun yanki deep red silk material Amman hakan bai hana bayyanar qyallinsu ba,da adon gold dake jikin kowannensu. Mutum biyar ne a jere daya a bayan daya cikin Wani irin tsarin da zai nuna maka gogewa da qwarewa gami da sanin makamar aiki ga hadiman.

Duk inda aka gifta dasu wani daddadan qamshin turaren amber suke fiddawa dake sake nuna zallar isa da iko. Saman kowanne akwati akai emblem dake nuna kyautar ta musamman ce,ba ordinary kyauta bace.

Cikin girmamawa suka qaraso suka kuma rusuna kowanne yana ajiye na hannunsa sannan suka rusuna da wani salon gaisuwa ba tare da sunce komai da ita ba,sannan kuma cikin salon taku suka janye baya daga gabanta.

Murmushi dattijuwar tayi,tana matsowa gaban akhnan kadan. Hannunta ta miqa ta kamo hannayen akhnan din ta saka cikin nata.

"Muna miki maraba da shigowa ahalin ABA JIFAR.....muna miki maraba da shigowa masarautar Ethiopia jimma......" Wani abu taji me nauyi yana sauka cikin tunaninta da kwanyarta.

"Muna miki maraba da shigowa masarautar Ethiopia jimma" Kalmarta ta qarshe data gaza ganeta.

Su al'ummar qasar habasha suna yiwa duk wani baqo maraba da shigowa cikin qasar da wannan kalmar ne?,ko tana nufin ita din ta qulla alaqa da wani da yake da mu'amala da masarautar Ethiopia din?. Amsar data maqale cikin iska tana yawo tsakanin kwanyarta da tunaninta,bata kuma samu miqawa sosai ga tunaninta ba sautin matar ya sake katseta.

"Wadannan kyaututtuka ne na maraba......." Saita dakata da salon dake nuna mulkin dake jikinta itama.

"Domin nuna girmamawa ga matar sheikh dinmu,muhammad haisam.....sannan domin nuna karbuwa da kika samu.......saboda komai da zai fito daga hannun sheikh dinmu yana da daraja kima da martaba me yawan gaske".

" Na gode" Ta samu labbanta da maidawa matar da amsa da labbanta da takeji sun mata wani irin nauyi. Abinda takeji baya misaltuwa,a yanxun da suka shiga babban parlor na farko na gidan......tarin mutanen da suke jiran dakon isowarta suka fara miqa kyaututtukansu a gareta cikin wani yanayi na tsananin girma.....wani yanayi na nutsuwa da ba hayaniya,saika dauka duka duka mutanen dake gurin basu haura mutum biyar ba....wani yanayin gabatarwa dake nuna asalin izza da rashin daukan dukiya a wani abu me darajar da za'a kasa kyautar bajinta da ita.....sai takejin kamar wannan gangar jikin bata akhnan bace.....wannan ruhin an musanyashi da wani......wannan ba kyauta bace kawai.....daukaka darajarta kawai akeyi......wannan ba rayuwar zahiri bace gaba daya.....mafarki takeyi.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261

*SHAIDAR BIYA* 08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽