Kenza eBookz
Cover art for KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 39

Post

KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 39

.....or will the father wash? I looked in surprise and said, what about Pant? Oh Billy, I won't even look at yours, let alone wash Kasa, and then mummy will wash me with a slap. Are you going to talk back to her? Okay, go and wash her! Just stupid. That's how I washed. My heart is full of anger. If I am to be honest, my money is ?2,000 left from the money I took for Mumy. I didn't think it would be enough for me until I came back, but I just put it in my Islamic bag. I took a shower and went to bed. I woke up around three o'clock. I got ready in hijab for school. Abba said that I returned to this word and his words calmed my soul. By God, we have not been living in this house for a while. I took my bag, said goodbye to Mumy, and left. When I came out on the street, the sun covered the sky as if it was going to mix with fog. My hijab was walking with a little wind, a new hybrid car, shiny, I saw behind me. I was walking slowly, and I noticed that the car was following me. Inside the car, a handsome young man was sitting, looking at me through the glass. There is nothing but a smile, the kind that captures attention but makes a woman's heart hard to wake up. I looked to my side, and

Standalone post1,867 words

Matsa munafuka! Kibani waje shegiyar jinin munafukai da mayu. Wato la?e kike mana ajikin ?ofa? To dan uwarki, ba As ad ba, ko Malam Idi direba, ba zaki aura irin su ba sai dai can wani talakan.

Na zuba wa Mumy ido, amma shiru nayi, saboda wallahi banga laifi na ba. Ina gefe ina goge TV, sai kawai ta fito ta karemin zagi. Tsaki nayi a raina, dan abunsu yana isata. Wannan hantara babu inda zanji sanyi araina kowannen su baya ?aunata.

Ban gama zancen zuciyata ba, sai ji nayi an finciko rigata ana jan ta. Ina dagowa, sai naga Yaya Billy ce. Nace da ita, Menayi miki?

Me isa kike tabamin ku?ina, dan ubanki? Nagaya miki fiye da sau ?aya why are you stealing from me?

Na firgita nace, Wallahi nifa ban ta?a ?aukar miki ku?i ba. Gyaran ?akinki kawai nake yi... ban ?auka ba!

Can sai naji muryar Mumy Nima wannan satar nan ta dameni. Ana mun ?auke-?auke! Wacce irin shigiyar yarinya ce ke? Kin zama mana annoba.

Sai kuma Billy ta bu?e baki da wani ?yama Mumy, kina gani fa? Pant ?ina bata wanke ba, ko ubanwa zai wanke?

Na kalleta cikin mamaki nace, Pant kuma? Ya Billy, ai bazan ma kalli naki ba, balle har in wanke

Kasa na karasa sai mumy ta wankeni da mari. Sa arki ce da zaki mayarmata da magana? Dallah, ?auka ki wanke mata! Mara hankali kawai.

Haka na wanke. Zuciyata cike da ?yama. Idan zan fa?i gaskiya, kudin hannuna saura ?2,000 daga kudin da na ?auka na Mumy. Ban jin zai isheni har naje na dawo, amma dai sai nasaka a jakar Islamiyya ta. Nayi wanka, na kwanta.

Wajen ?arfe uku na tashi. Na shirya cikin hijabin makaranta. Abba yace na koma wannan kalmar tasa ta sanyaya raina. Wallahi zaman gidan nan bai yi mun da?i ko kadan.

Na ?auki jakata, nayi wa Mumy sallama, na fita.

Da na fito bakin titi, rana na lullu?e sararin sama kamar zata ha?a da hazo. Hijjab ?ina yana tafe da iska kadan,wata hadaddiyar mota, sabuwa, mai she?i Na hangota bayana. Ina tafiya a hankali, na lura motar tana binai. Cikin motar, wani kyakyawan matashi ke zaune, yana le?ena ta gefen gilashi. Baki ?aya sai murmushi yake, irin wanda ke ?aukar hankali amma ke sa zuciyar mace ta farka da kyar.

Na ?an waige gefe na, sai na maida kaina gaba kamar ban lura da shi ba.

Ina gab da fita babban titin unguwarmu, kawai sai naga ya faka motar gefe. Yayi saurin fitowa, ya nufo ni da tafiya mai sauri. Sai da yazo kusa da ni sosai, sannan ya ce

"Yammata... yammata! Dan girman Allah ki tsaya mana, da gaske nake!"

Na juyo kadan, na kalleshi da wani irin kallon raini, wanda ya kamata ya fahimci ba irin yammatan nan baniba marasa kamun kai. A raina nace Wannan kuwa, ko ba a fada ba, mai kudi ne ko yaron wani mai kudi da bai san wahala ba. Ya matsa gaba kadan, yana kara ce mun DanAllah ki saurareni mana. na zuba masa idanuwana sannan nace Kayi hakuri. Ni matar aure ce.

Atake ya tsaya cak. Baki bu?e kamar wani yaro da aka kama da laifi. Sai ya ce Afuwan, sis. Wallahi banyi zaton haka ba. Ki gafarceni. Ya juya a hankali, ya koma motarsa da dan kunyarsa, har ya rufe kofar da ?an sake numfashi.

Ni kuma na karyar da kaina gefe, na tsallaka titi da sauri na samu abun hawa. Motar keke-napep kawai na iya bi yanzu. A da kuwa, Malam Idi ke kaini ko ina mutumin kirki, mai hakuri, mai daraja. Shi ne driver ?in gidanmu. Amma yanzu, babu komai. Shi kansa Malam Idi ya daina zuwa tun da mumy ta yi duk wani abu da zata iya, ta sa an kore shi saboda ni. Abba kuwa, bai ta?a siya min mota ba kamar yadda ya siwa yaya Billy da mumy.

Isata asibitin ke da wuya, na nuna wa napeep inda zai ajiyeni. Ya ce min ?500 ne kudin. Na cire na ba shi, cikin rashin natsuwa.

Na tsallaka cikin Asubutin u^-?in, ina waige-waige. Bana son na ha?u da kowamusamman wanda na sani. A yanzu, na daina yarda da kowa. Makiyana sune ke yawan nuna mini ?auna ta boye, suna murmushi a gaba, amma zuciyarsu tamkar wuta.

Ina shiga corridor ?in, na hango yayan Khalil ya rungume shi sosai. Khalil yana dan takawa da ?yar, alamu sun nuna cewa ko likita ya bada umarnin hakan ne. Ko ina ya kumbura saboda ruwan da ke taruwa a jikinsa. Fuskar sa cike da rauni da ciwo. Na karasa da ?an hanzari, cikin tashin hankali nace sannu! Yaya Mujittapha, ina wuni? Ya mai jiki?

Ya amsa cikin gajiya, yana murmushi da ladabi Likita yace a dan sakashi ya dinga takawa. Muka gama yanzu, muna shirin komawa daki.

Khalil ya ?ago kai yana kallona. Ya washe baki da ?yar, amma har yanzu idanunsa sun cika da kauna. Fuskarsa tayi duhu, tayi baki sosai, jikin sa babu kuzari ko kadan. Na kalle shi, zuciyata na karaya.

Khalil, ya jiki? Allah ya baka lafiya. Ya yayemaka, na fa?a da tausayi.

Yaya Mujittapha ya ce, Za a ajiye shi nan kusa da da?in, yana nuna kujerun bakin corridor.

Khalil ya ?aga kai, murya cike da rashin kuzari amma mai tsantsar shau?i da so, ya ce Ramlahhhh

Na daga masa kai. Sai ya ce Zo ki zauna nan. Inason muyi magana.

Na amsa masa da shiru, zuciyata na bugawa kamar ana buga gangi. Na karaso da sauri, na zauna a gefensa. Idanunsa ya zubamun, suna narkar da zuciyata. Na juya gefe kadan domin boye hawayen da suka fito da kansu. Na share su da sauri, amma har yanzu idanuwansa na kaina.

Ya ri?o hannuna da sauri, kamar wanda ke neman ya ?auki numfashinsa na ?arshe. A take, naji wani irin zafi ya ratsani zafi.Na ?ago kai da sauri, idanuna sun cika da mamaki da tsoro. Khalil Na fa?a a hankali. Jikinka zafi sosai. Sai ya murmusa. Murmushi mai rauni,Ya ce, Ramlah Yadda ya furta sunana ya sakani jin wani abu ya girgiza ni daga ?asa har zuciyata. Murya ce mai nauyin da ba zata manta ba.

Nan take hawaye suka zubo min. Na runtse idona, ina ?o?arin jure kukan da ke tasowa daga ?asan zuciyata.

Inaji a jikina kamar bazan rayuba... kamar rayuwata ta ?are, yace da ?yar, kamar numfashi yana gujewa bakinsa. Na zaro ido, na ?aga hannuna cikin sauri na danna kan bakinsa. Khalil, don Allah ka daina fa?in haka! Ka daina wallahi... Kada ka kara fa?a. Muryata ta katse kamar ta mai ta motsi, zuciyata na ci gaba da bugawa da karfi.

Ya ?auke hannuna da sauri, ya kalle ni da idanuwansa masu kumburi. Ya ce cikin wata murya mai rauni amma cike da ?auna Bazaki fahimta ba, Ramlah Na soki tun kafin mamanki ta rasu. Tun lokacin da kike Primary 5. Na rayu da soyayyarki a cikin zuciyata, kullum ina mafarkin ki zama tawa.

Ya sauke ajiyar zuciya, yana ci gaba da kallona. Naso a auramin ke, amma abbanki ya hana. Bayan kin kammala makaranta, shima ya ?i amincewa. Amma har yanzu ina jin cewa ni ba mijinki baniba, amma ina so ki sani Ina ?aunarki.

Ya girgiza kai, yana goge hawayen da suka gangaro a fuskarsa. Bansan me nake ji akanki ba, Ramlah. Amma na tabbata ni inason ki. Duk wahala, duk rintsi, duk ?unci da dare ya sauka, ina ro?onki ki dage da karatu. Karatun da zai maki amfani sosai.

Ya matsa kusa da ni, ya dafa kafadata da hannun da ke rawar sanyi. Ki tsaya da kafafuwanki, kinji? Ki tsaya da ?arfi. Ki dage da addu a. Tana iya zama kawarki, uwa, babanki, yayarki duk a lokaci guda.

Sai ya kalli idona sosai. Ki kula da kanki, Ramlah. Komai tsanani, komai wuya, komai ka?uwa, karki manta ke kanki kike da farko kafin kowa.

Fashe masa da kuka nayi. Hawaye na gangarowa. Na dafa kafadarsa, zuciyata kamar za ta fasa ?irjina. Dan Allah ka yi shiru, Khalil. Dan Allah ka daina. Ban so ba zaka mutu ba! Wallahi ba zaka mutu ba... Kai zaka rayu, ka gan ni na cika buri na!

Na kwantar da kaina a kafa?arsa, numfashinsa yana busa a kunne na. Wani irin sanyi mai ?aci ya ratsa zuciyata. Lokaci ya tsaya cak. Na daina jin motsin duniya duk da hayaniyar corridor, likitoci na wucewa, marasa lafiya na gunaguni a cikin kunnuwana, abinda nake ji kawai shine numfashin Khalil da bugun zuciyata.

Ramlah ya kira sunana da wani irin sanyi mai narkar da rai. Idan har bana nan gobe

Nace ka daina fa?a hakan! na katse shi da kuka mai ?arfi. Kayi shiru Khalil, banaso! Ka gaya min cewa zaka rayu! Ka gaya min za mu yi aure, ka gaya min

Na kasa karasawa. Kalma ta tsaya a ?irjina, ba ta iya fita ba. Kamar wata ?ura ce ta toshe ma bakina mafita. Na ?ara rushewa da kuka.

Ya ?ago hannunsa da ?yar, ya dafa kaina, yana shafa kan kamar zai tuna wani abu da ya dade da ?ace masa. Ina son ki, Ramlah. Wannan ne gaskiya. Ko da ba zan kasance a kusa dake ba, zan kasance cikin zuciyarki har abada.

Sai muka ji ?ofar corridor ?in ta bude da ?arfi. Yaya Mujittapha ya dawo da likita. Fuskarsa a cike da damuwa, hannunsa na nuna yadda lokaci ke kurewa.

Bai kamata ya zauna haka ba, likitan ya ce da sautin lallashi. Jikin sa na bukatar hutawa, kuma dole a ba shi magani yanzu.

Na mi?e da sauri, na share hawayena. Khalil ya kalleni da murmushi murmushi da ya fi magani, ya fi soyayya da kanta.

Na ?ago hannunsa na sumbaci tafin sa. Na ce, Khalil... wallahi zan dage da karatu. Zan zauna da kafafuwana. Zan ro?i Allah kullum saboda kai. Ka yi min alkawari zaka cigaba da fafutuka. Kayi min alkawari zaka tsaya tsayin daka, ka tashi daga wannan jinya.

Ya zuba min ido, da karfin hali ya daga yatsansa daya. Na yi miki alkawari... Amma ki yi min wani al?awari ma. Ina jinki, na ce cikin sanyi.

Ki zauna da zuciyarki. Kada ki bari duniya ta karya ki. Kuma idan wani ya so ki... a nan gaba, idan ni ban samu na dawo ba, ki bari soyayya ta shigo zuciyarki. Kar ki zauna da ciwo saboda ni.

Na ri?e hannunsa da ?arfin da na iya. Na ce Khalil... bazan iya manta da kai ba. Kai ne farkon ?aunata, kai ne tarihin zuciyata.

Likita ya gya?a kai, ya ce Yakamata ki bashi lokaci ya huta.

Na ?aga masa kai cikin ?aci, sannan na matsa gefe kadan, amma idanuna na kan Khalil har likita ya ja gadon da aka shimfi?a shi, ya mayar da shi cikin dakin jinya.

Na tsaya a bakin ?ofa, zuciyata na rawa. Da idona nake masa kallon da ya ?unshi duk wani abu da baki ba zai iya fa?a ba.

Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH

SHAFI NA ARBA'IN

Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)

Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435

Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693

********