
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 40
..... her words are not even in her soul. You know me, Ramlah. Anty is yours. I love you as much as I love you. By God, I always dream of seeing you happy. But be civilized. Life is not just about measurement. From the beginning until now, I am standing by your side. You know that right? I nodded, but I still couldn't figure out what she was saying. Then she begged. Let's say that Khalil is cured... are you ready to live with his family? Are you ready to live in a family that doesn't love you and how they abuse you? Do you care about that? My heart is broken. Her question was like throwing me into the river. But before I can give an answer... The sound of running and the sound of a horn broke the corridor. Doctor! Doctor, please come quickly! His body has worsened! Yaya Mujittapha's voice. After that, Babar Khalil came running, crying as if she was going to stop breathing. Doctor come and help him! It falls like a shure! Two doctors came out quickly, one with a tray of doses, and the other with oxygen. They went to the emergency room. I stood up. My eyes stopped shedding tears. My body is broken like a tree that has been cut down. I looked at the fight between them and Khalil. Anty
Ina tsaye har yanzu a bakin ?ofar dakin jinya, jikina ya mutu da hawaye, zuciyata cike da fargaba. Cikin wannan halin, sai naji an dafa kafadata.
Ramlah... wata murya ta kira ni.
Na juyo. Anty Luba ce. Anty ?ina. Tana sanye da zani mai launin shu?i, mayafinta na rufe daidai habarta. Fuskarta a cike da murmushi na tausayi, kamar yadda take kullum idan tana son ta sa ni yin abinda take so.
Ta matsa kusa, ta ?ora hannunta a kaina. Ina kika shiga ne? Kina kuka haka kamar yarinya? Na kalleta kawai dan ni yanzu naganeta nagane makiyata ce wacce bata ?aunata ko ?adan.
Na share hawayena da gefen hijabina. Anty Khalil ne. Maganarsa da yadda nake ganinsa ya firgitani. Yana fa?in kamar bazai rayuba...
Ta ja numfashi, ta zauna kusa dani a kujerar bakin corridor. Sai ta kama hannuna da taushi. Ki kwantar da hankalinki mana, Ramlah. Idan har Allah ya ?addara ki da shi, zai dawo. Amma ki sani a rayuwa ba komai ke zuwa yadda muke so ba.
Na kalle ta da mamaki, zuciyata ta ?an harzuka. Saboda nasan maganarta ba har cikin rai take ba. Kin san ni, Ramlah. Anty ?inki ce. Ina sonki kamar yadda nake son ?ana. Wallahi ni a kullum ina mafarkin ganin ki kin samu farin ciki. Amma ki ?ara wayewa. Rayuwa bata tsaya kan ?auna kawai ba. Daga farko har yanzu, ni ke tsaye a gefenki. Kin san haka ko?
Na gyada kai, amma har yanzu na kasa gano inda kalmarta ke nufi. Sai ta ?ora
Bari muce ma Khalil ya warke... shin ke kin shirya zama da danginsa? Kin shirya jure zaman cikin iyalin da basa sonki kinsan yadda suke zaginki kuwa? Ko kin damu da hakan?
Zuciyata ta tsinke. Tambayarta kamar jefa ni tayi cikin kogi. Amma kafin in ba da amsa...
Sautin gudu da ?ara suka fasa corridor ?in. Likita! Likita don Allah kuzo da gaggawa! Jikinsa ya tsananta! Muryar Yaya Mujittapha ce.
Bayan sa kuwa sai Babar Khalil ta shigo da gudu, tana kuka kamar za ta yanke numfashi. Likita kuzo ku taimake shi! Yana faduwa kamar mai shure!
Likitoci biyu suka fito da sauri, ?aya da tray ?in allurai, ?aya kuma da oxygen. Suka nufi cikin ?akin jinya da gaggawa.
Na mi?e tsaye. Idanuna sun ?i daina zubar da hawaye. Jikina ya kakkarye kamar bishiyar da aka sare. Na kalli ?ofar ?akin da suka shiga da Khalil.
Anty Luba ta dafa bayana, amma wannan karon ba ta ce komai ba. Sai kallon da ta jefa min. Kallon da ba kowanne kallon kulawa ne ke da shi. Wata siririyar dariya ta bayyana a fuskar ta. Maman khalil ganin halin danake ciki tasanya yaua Mujittapha yace natafi gida duba da yadda dare yaja sosai.Tunda na fice daga asibiti, hankalina ya bace. Zuciyata gaba ?aya ba ta cikin jikina zuciyata a cikin dakin jinyar Khalil.
Na nemi hanyar makaranta, amma ba don nasan inda nake ba.Sai kuma na tuna makarantar da ake tashinmu karfe biyar na yamma. Sai kawai na farga cewa... lokaci ya kure. Na duba agogon da ke jikin bango 9 na dare.
Na dafe ?irji. Zuciyata tayi shiru. Ba ta dukan tsoro, ba ta harbin fargaba. Amma na san akwai abu a cikinta fatan cewa Khalil zai rayu. Wannan ne ka?ai burinta yanzu.
Na zauna a ?aramin benci a jikin harabar Asubutin. Na kasa motsi, kamar wata dutse. Tunani ya mamaye ni, na rasa inda zan sa kaina. Sai wata murya a cikin raina ta soma magana... Ramlah, kina ?aunar Khalil ne?
Na lumshe idona. Ban da amsar hakan.A'a... ba kawai Khalil nake so ba. Ina kaunar wanda zai kulani. Wanda zai ji damuwata. Zuciyata tana jin da?in rarrashi. Tana bu?atar murya mai sanyi da hannu mai taushi duk abin da ban samu a rayuwa ba, sai yanzu na fara ganinsa.
Na bu?e jakata. Na duba ciki. Ko sisi babu. Gabana ya fa?i. Idanuna suka sauka ?asa, na rasa me nake ciki. Masu mota sai hucewa suke yi a hanya, kowa cikin gaggawa.
Na tsaya a gefen titi, zuciyata a hargitse, jikina a sanyaye.
Can sai wani napeep ya tsaya. Direban ya le?o yana dariya kadan. Hajiya... bakiga ruwan da ke sauka yana dukanki ba ne?
Na ?an dubesa da ?yalli. Ni banda kudin mota ne shiyasa.
Sai ya girgiza kai yana murmushi. To shiga, zan kaiki gida. Ba komai.
Na yi masa godiya da murmushi mai rauni. Na shiga cikin napeep ?in. Shiru ne ya rufe tafiyarmu, amma zuciyata na tafe da ro?o da addu a. Na kalle shi da tausayawa. Kamar akwai sauran mutanen kirki... ba kowa ne mugu ba.
Da muka isa kofar gida, na sauka. Na gode masa sosai. Allah ya saka da alheri.
Na tura ?ofar gidan cikin sanyin rai. Na shiga ciki da takun mutumin da ya dawo daga yaki ba tare da nasara ba. Zuciyata cike da tambaya ?aya Shin Khalil zai wayi gari?
Haka na tura ?ofar gida, na shige cikin falon mu. Da ?yar na iya furta
Assalamu alaikum
Sai na tsaya. Momy na zaune a gaban kujera tana waya, tana dariya kadan, tana kuma girgiza ?afarta kamar ba komai ya dame ta.
Ya Billy, tana zaune a ?aya gefen palon tana kallon TV, amma duk da haka sai ta zuba min ido kamar tana jiran wani abu ya faru.
Ni kuwa ban karaso ba, ban kai kujerar ma ba... cikin minti ?aya kawai, sai naji an finciko ni daga hannu.
Ramlah!!! Abba ne!
Na juya cikin razana, amma kafin in iya cewa komai, hannunsa ya sauka a bayana da ?arfi. Na fadi kasa da huci, idona suka cika da hawaye.
Shin sai dare haka kike dawowa gida?! Kina yawo kamar wata 'yar iska! Ke wacece a wannan gidan da zaki kai dare har yanzu? Daman da gaske zainab take datacemun kin fara yawo ko?!
Na yi shiru. Banza na masa. Zuciyata cike da wahala da gajiya. Na kasa magana, saboda na san komai zan ce ba zai kare ni ba.
Momy ta katse wayarta, ta dafa cinyarta kamar mai ba da shawara.
Ka duba fa! Wannan ba karamin rainin hankali bane. Yau gaba da karfe tara ta dawo daga makaranta! Duk macen kirki da tarbiyya zata dau lokaci haka tana yawo? Waye ya dauke ta? ina ta je?
Abba ya karaso,Ya daka min tsawa. Kindaina jin magana saboda kina jin ke cikakkiyar budurwa ce yanzu? Ai sai na nuna miki cewa ni ne uban gidan nan!
Ya dauki wayar ji?in tv yazubamun,Na rike cikina, saboda yadda bugun hannunsa ya ratsa ?asata kamar wutar lantarki. Na ji nauyin jiki.
Na ?ago kaina, cikin hawaye nace Na je asibiti ne... Khalil ne, yana fama da ciwo sosai...
Abba ya girgiza kai, yana ci gaba da masifa. Kina shashanci da wani banza da ba ni na zaba miki ba! Wato sai kinyi abin da kike so? To wallahi sai na saka a daina barin ki fita makaranta! Gaba daya.!
Kalmar nan ta ?arshe ce ta karyani. Idona sun cika da hawaye, amma zuciyata ta ?auki dumi. Wannan dumin ba na ?auna bane na ?orafi ne, na ?acin rai ne, na daci ne da aka watsa a zuciyata.
Sai kawai ya kai hannu ya ciro wayarsa daga gefen TV, ya kunna. Ya matsa manhajar hoto, ya nuna wasu hotonw. Sai ya juyo gare ni da ?arfi.
Wannan hoton...! Wannan hoton fa?! Dan ubanki wannan wani irin iskanci ne?! A jikin sa kike kwanciya? Haka kika bar gida kije kina rungumar namiji?!
Na zaro ido, jikina ya rika rawa. Ban san lokacin da nayi baya ba. Wanene ya daukemu? Innalilahi. Yanzu fa sai yakasance anty luba ko? Na fara hawaye.
Wayar ya daga sama ya bugeni da ita a kafa?a. Na fadi ?asa, kuka ya ?wace min.
Wato ke yanzu kina da saurayi ko?! Khalil ?in nan shi ne zakiyi wa biyayya fiye da iyayenki? Kin manta da sunan gidan da kika fito?.
Na rarrafa a kasa, jikina na ciwo. Amma zuciyata ita tafi ciwo. Muryar sa na dukan kai na kamar ?aho. Sai ya dakan tsawa
Babu ke! Babu Khalil! Wallahi idan kika ?ara zuwa inda yake, idan kika ?ara ha?a kanki da shi... Allah ya isa ban yafemiki ba!
Na kalli Mumy, cikin hawaye da ?as?antar da kai. Momy... wallahi ba haka bane. Khalil yana jinya ban je wajen banzanci ba.
Ta yi dariya mai zafi. Jinya ko? To sai me? Sai ki kwanta a kirjin marar lafiya a asibiti?! Wannan wace irin tarbiyya ce?!
Na sunkuyar da kai. Wani irin kunci ya mamaye zuciyata. Ina cikin iyayena... amma kamar bana gida.
Allah ka gani... ban aikata ba. Ban tozarta kaina ba. Amma yau guri da ya kamata na samu ?auna, sai na samu wula?anci.
Sai na rasa numfashi. Hawaye na gangara ba tare da izini ba. Kalmar Abba tana dukan zuciyata
Babu ke! Babu Khalil!
Nana hadiza 09030569336?ADDARAR RAMLAH
SHAFI NA ARBA'IN DA DAYA
Wannan littafin ku?i ne, ba kyauta ba! Biya Naira 700 kacal ki karanta cikin salama! Domin biyan ku?i: Acc Name: Bilkisu Sani Kaura Acc Number: 7040402435 (OPAY)
Tura shaidar biya zuwa WhatsApp: 09030569336 ko 07040402435
Masu son vip ??Sai ku bibiyeni a Arewabook @nanadiso10 https://www.arewabooks.com/book?id=6813670d91815df57bc25693
********