
Post
KADDARAR RAMLAH BOOK 1 PAGE 45
..... This is not only from the body, it is from the heart. He stood up with difficulty, and lay down next to her. She didn't stop waiting, she lay down on his body, and rested her head on his chest, listening to his heartbeat. She put her hand on his hand. She kissed his neck with warm kisses. She said in a low voice, like a prayer to God to give you peace. God brought everything back. I don't need strength if you are not there. As ad he looked into the eyes. Then he said, "This care, Ayshatu, let's say I found you first." I would not let any woman into my life. By God, that is the house I don't want to leave. Ayshatu lay on his body, caressing his back like a baby. She tells him the words that not every woman can say to her husband. You are stronger than pain, you are stronger than evil. You are more than tired. You are better than anyone else. You are As ad ?ina. (A woman should not allow her husband to be tired of life. She should not let him understand that there are women who show love. ??? Sit next to your husband, whether he is tired, or falls, or eats. ???? Pray for him, but cup his hand warmly, embrace him with love, wipe the sweat from his body with care.
Ayshatu ta zame daga cinyarsa a hankali, ta sauka ta dur?usa a gabansa kamar wata baiwa, Wani irin farin cikin kai ne, mace mai daraja ta iya zubewa a ?asa domin mijinta? A irin wannan lokaci ne kulawa ke canzawa zuwa ruhi ?auna ta zama jinya, kuma soyayya ta koma magani. Hannunta a kansa, tana shafewa a hankali kamar tana ro?on ciwo ya fice. Ta ce da ?asa da murya mai ra?a?i
Ka daina jin kamar kai ka?ai ne. Ka daina jin kamar ka kasa. Ni ina nan tare da kai. Idan baka jin ?arfi, zan kasance ?arfinka. Idan ba ka jin ?auna, zan zama ?aunarka.
As ad ya tsareta da idonsa. Ba zai iya misalta irin salonta ba ba mace bace da ke da iyaka. A rayuwarsa duka, babu wadda ta tsaya masa kamar Ayshatu.
Ta mi?e tsaye cikin salo, doguwar rigarta na bin jikinta kamar ruwa. Kafarta ta dan sau?a da sau?i, ta nufi gado cikin natsuwa. Ta zauna a tsakiyar gado tana kiran sa da murya mai salo Zo mana. Kar ka bari ciwon zuciya ya cinye zuciyar ?auna. Zo ka kwanta. Ko baka da ?arfi.
As ad bai iya ?in ta ba. Wannan ba daga jiki kawai ba ne daga zuciya ce. Ya mike da kyar, ya karaso ya kwanta a gefenta. Bata tsaya jira ba, ta kwanta jikinsa, ta ?ora kanta a kirjinsa, tana jin yadda bugun zuciyarsa. Ta ?ora hannunta a kan hannunsa. Ta sumbace wuyansa da la??a masu dumi.Ta furta da ?asa da murya, kamar addu a Allah ya baka lafiya. Allah ya dawo da komai. Ni ba na bu?atar ?arfi idan ba kai.
As ad ya kalleta cikin idanu. Sai ya furta Wannan kulawar, Ayshatu sai dai a ce na same ki da farko. Da ba zan bar kowacce mace ta shiga rayuwata ba. Wallahi ke ce gidan da ba zan so barin sa ba.
Ayshatu ta kwanta a jikinsa, tana shafa bayansa kamar jariri. Tana fa?a masa kalmomin da ba kowacce mace ke iya furta wa mijinta ba. Ka fi ?arfin ciwo, ka fi ?arfin sharri. Ka fi ?arfin gajiya. Ka fi kowa. Kai ne As ad ?ina.
(Kada mace ta bar mijinta ya gaji da rayuwa. Kada ta barshi ya bar fahimtar cewa akwai mata masu nuna kauna.
??? Ki zauna kusa da mijinki, ko ya gaji, ko ya fadi, ko ya ?aci. ???? Ki yi masa addu a, amma ki dafa hannunsa da dumi, ki rungume shi da ?auna, ki goge gumin jikinsa da shagwaba.)
(Ba a girma da aure. Ba a tsufa da soyayya. Ba a yawan shekaru a gado, sai yawan ?arfin zuciyar mace. Kuma mace ce ta fi kowa sanin jinyar mijinta, idan ta damu.)
(Ayshatu ta san irin kalmomin da As ad ke bukata, ba don ya fa?a ba, sai don tana jin shi. Tana masa magana kamar zuciyarsa ce ke magana da kanta. Tana sumbatarsa kamar magani ke fita daga la??anta. Kuma wannan daren, daren da wata mata za ta bar miji a duhu, Ayshatu ta canza shi zuwa haske da ?auna.)
********* ****************
Yau muna da ba?uwa agidan mu kanwar mumyce , Yakaka. Ni da ita fa, tun ina ?arama, babu wata soyayya tsakaninmu. Tunda ban ma san kiyayya ba, na riga na fara jin ?iyayyarta. yau da nagama aiki da girki dayake lecture ?in yamma ce, ban sami damar hutawa ba.
Na fito daga da?ina, jaka a hannu, sanye da abaya wacce na sanya yanzu haka ba ta ?oyewa halittata ba. Sai wata irin kallon tsana Yakaka ta jefani da shi, Ni da ake kira da kwaila yau nice make sanya breziya har size 39, idan kuga yadda nayi kyau sai kunyi mamaki shiyasa mumy kullum maganarta maganin kiba nakesha.
Na karasa cikin palon Na fa?i wa Mumy zan tafi makaranta. Batace uffan ba. Sai kawai muryar Yakaka ta cika parlour, tana cewa
Ai na fa gaya miki! Sai ta zama miki ?adagaren bakin tulo. Gobe sai kiyi kuka da idonki akan wannan diyar Larabawan kauyen da kika ?i ba kakarta!
Wannan magana kamar ta fantsama kai tsaye cikin zuciyata, duk da ban ce komai ba. Amma Mumy ta ce da ?an murya
Yakaka tana shan abun kara kiba ne fa.
Yakaka kuwa ta barke da dariya Ke mahaukaciya ce wallahi! Kin manta yadda mahaifiyarta take? Kin manta yadda mijinki yazama bawanta? Mu da har tausayi muke ji miki, Ai ba sai angagamiki ba wannan yarinyar sai tafi mahaifiyarta kyau wallahi ko tasha magani ko batasha ba .
A nan ne zuciyata ta soma bugawa tamkar ana buga ganguna. Kafafuna sunyi nauyi. Ban ce musu uffan ba. Na juya kawai, na nufi makaranta. Sai na ga Malam Idi a ?ofar motar, na gaida shi. Haba, ina da lecture amma hankalina bai nan . Maganganunsu Yakaka da Mumy suna yawo a kwakwalwata kamar ?udaje.
**** Zaki tsaya kina kallonta ne, Zainabu? Yanzu fa tasoni kika yi. Kikace bakin cikin yarinyar nan zai kashe ki, ko? tunda yanzu, ko kin yi kissa, kin shirya makirci, bayan kwana biyu uban ta zai dawo da kulawa gare ta kamar ba a taba ba.
To, banda ke da abunki irin soyayyar da mahaifinta ke nuna mata zaki iya yakar ta da makirci kuwa? Ki gode wa Allah da bai gane ki a wancan lokacin ba. Wannan lokaci ne da za mu sake bude masa ido da kwankwasa zuciyarsa.
Mumy ce ta share hawayenta, ta ce, Yakaka, masifar da nake ciki ta fi karfin bayani. Kinsan Bilkisu bin maza take yi. Mumy ta fada cikin kuka mai karfi.
Ke, banson karya, Bilkisun taki? Inji Yakaka. Wallahi gaskiya nake fada. A haka ma na ci ubanta, amma abun bai sauka ba. Aikin ma bata zuwa sha awarta ce kawai take bi. Yakaka, har shaye-shaye Bilkisu take yi fa. Ni na gani da idona!
Idan mahaifinta ya gane haka, wallahi sai ya raba ta da kowa sannan ya yi mata aure cikin hanzari. Zai iya rabuwa da Bilkisu har abada. Kinsan ta fara haddasa fitina tun lokacin da aka kai ta gidan abokinsa. Shine ta nutsu, amma yanzu abun ya koma kazanta.
Shiyasa nace miki kizo ita wannan yarinyar da na dinga dorawa akan bin mazan da shaye-shayen wallahi bata aikata ba. Bata lalace ba sai tawa. Yakaka, ya zan yi? Dan Allah zuciyata na yi min zafi fiye da yadda zan iya dauka.
To yanzu dai, shawara guda ?aya ce zan baki, inji Yakaka. Ki san yadda zakiyi, kiyi wa Bilkisu aure. Ki samo wani babban mutum, a aura mata. Daga nan kuma a shiga malamai, a kulle mata kafafu gaba ?aya.
Zainabu ta kalli Yakaka, ta ce Ramlah fa, Yakaka? Ina son ta haukace da bakin ciki. Bana so ta gama karatun nan nata. Ina so ta mutu da bakin ciki kamar uwarta.
Yakaka ta yi dariya, sai ta ce, Wannan kuwa abu ne mai sau?i, Zainabu. Abu na farko aikin fili. A ha?ata da wata larura har ta zama sanadiyar rashin lafiya. Idan da ciwo, ai karatun bazai yuwu ba, ko?
Abu na biyu, inji Yakaka, ki samo a aura mata Bashari. Indai kina so ta lalace, to wallahi zata lalace. Ki dubi Bashari dan shaye-shaye ne, dan iska ne, dan bangar siyasa ne, sannan kuma azzalumi ne. Babu mutunci, kuma dan fashi ne cikakke. Rayuwa a kauye zai killace ta. Zai mata ciki da ciki, har ta rude. Kinga, babu rabuwa kuma rayuwarta zata rufta tun daga nan.
Zainabu ta dafe kirjinta cikin jin da?i, ta ce Na yarda, Yakaka. To yanzu me za mu fara yi?
Wannan ba matsala ba ce, Yakaka ta amsa. Ni zan daidaita mahaifinta. Sai dai a ?an buga kansa sau ?aya kawai dan kada ya mana cikas.
Mumy ta fashe da dariya, tana fadin Allah ya bar min ke, Uwata! Shiyasa nake ?aunarki.