
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 32
.....n her mode was changed or something related to her between the minutes that separated. His eyes were fixed on her face, both his hands were in the pockets of his body, but once she was willing to look at the part he was leaving himself. Her heart is still beating, she is afraid of him, he is entering her, she is looking at him differently now. "Is that the case too?" That's the only thing she keeps repeating in her mind, so she chooses to move forward even though she feels all his eyes on her body. The side of her veil was held, and she was pulled back a little, she stood still, her chest continued to beat, but she agreed and looked back. "Wait for me" He said in a soft tone and walked to the front of the fridge and took out a glass of cold water and filled the cup and drank it. He doesn't know why, just by looking at her, he feels that his throat is getting dry, and his breathing is getting a little heavy. "Let's go" He said standing behind her as if he was given the task of monitoring her every movement and her breathing. I don't know how many times he changes sides from her left to her right. He was on her left, and she found him on her right, as if he felt the protection h
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 32*
Kaiwa nan gurin a tunaninsa ya tilasta masa kai tafin hannunsa saman sumarsa ya shafeta a hankali wani murmushin yana sake qwace masa,daya duba lokaci kuma sai yayi gaggawar watsar da tunanin ya jawo lotion dinsa ya fara shafawa. Yanajin wani sakayau cikin zuciyarsa da ruhinsa har ma da gangar jikinsa.
Moroccan jallabiyya ya saka fara qal da aka yiwa adon golden zare. Zaka rantse da Allah wani ado na musamman yayi saboda yadda rigar ta zauna masa ajiki ta haskashi ta masa wani irin kyau. Da sassanyan qamshin nan nasa ya zura wasu fararen flip flops sannan ya maida wayarsa aljihu ya fito a nutse.
Yana rufe qofan dakin tana fitowa daga cikin dakin itama. Kaman hadin baki ko ra'ayinsu ne yazo daya?. Farar abaya ce a jikinta,ta nade kanta tsaf da mayafin abayan daya kasance yalwatacce ne. Kasancewar abayar fara bai rage koda digo daya na kyan data mata ba,duk da bame duhun kala bace. Fuskarta tayi wani fayau da haske,kaman an sauya mode nata ko wani abu dake tattare da ita tsakanin mintunan da suka rabu kadai.
Idanunsa zube akan fuskarta,duka hannayensa suna cikin aljihun jallabiyyan jikinsa,saidai ko sau daya taqi yarda ta kalli ko sashen da yake ma bareshi kanshi. Zuciyarta har yanzu bugawa takeyi,wani tsoronsa takeji yana shigarta,wani kallo na daban take masa yanzu.
"Shima ashe haka yake?" Abinda kawai take nanatawa kenan a ranta,don haka ta zabi fara yin gaba duk da tana jin dukkanin idanunsa akan jikinta.
Gefan mayafinta taji an riqe,an kuma jawota baya kadan,ta tsaya cak qirjinta yana ci gaba da bugawa,saidai taqi yarda ta waiwaya.
"Ki jirani" Ya fada da wani soft tone sannan ya taka zuwa gaban fridge ya ciro gorar ruwa mara sanyi ya cika cup ya shanye. Baisan me yasa da kallonta kawai sai yaji maqoshinsa yana bushewa ba,numfashinsa kuma yana nauyi kadan kadan ba.
"Muje" Ya fada yana tsaye daga bayanta kamar wanda aka bawa aikin kula da duk wani motsinta dama fitar numfashinta.
Batasan sau nawa yake canza side daga hagunta zuwa damanta ba. Yana hagunta sai ta tsinceshi a damanta,kamar wanda yakejin kariyar da yake bata tayi kadan.
Haka kawai yakejin kamar kowa ma kallonta yakeyi,kamar kowa idanunsa yana kanta. Baisan me ya sanya wannan kishin ya qaru a qirjinsa ba,kawai tsaiwarsa a bangare guda yana jin bata gamsar dashi ba.
Kamar kowanne lokaci,yanayin na dabanne...... Kusan ko ina ba wani baqon abu bane masoya ne riqe da hannun juna suka kai kawo. Shuru ya ratsa tsakaninsu,shurun daya musu jagora,ya sanya zukatansu tunani mabanbanta. Wani nauyi takeji sosai duk sanda zasu daga taku su sauke tare,wani iri takeji duk sanda taga ya juya ya kalleta sannna ya kauda kai. KUNYA......a yau tasan ainihin zahirin ma'anarta......haka kunya take da nauyi?,duk yadda kallonsa ya zame mata kusan dabi'a a yau dai ba zata iya hada idanu dashi ba. To amma shi daga mode dinsa kansa tsaye yake takunsa kamar komai bai faru ba.
Idan ta tuna yadda ya ganta tana jin kamar ta nutse a qasa......tana jin me yasa ta fito?. Idan yadda ya sakata a jikinta ya dawo mata sai taji wani qaramin spark yana tashi cikin jiki da kwanyarta. A tsorace take,mugun tsoron da ba komai take ganewa ba,amma a sanda ya sanyata tsakiyar wannan qirjin.....faffadan kafadar da ta dade da sanin qarfinta......ta kuma dade da zame mata garkuwa game da abubuwa da dama sai da aka sanar da ita shigarta cikin wani sabuwar GARKUWA da bata taba shiga ba a rayuwarta.
Swissotel suka isa,sai a sannan ta tuna da iffah. Ta kirata bayan nan har sau biyu sun gaisa,amma basu sake haduwa ba. Batasan me ya faru ba,itadai taji ya cusa zaratan dogayen yatsun nan nasa cikin siraran yatsunta ya kuma hade tafin hannunsu guri daya.
"Welcome sir" Abinda ta dinga ji kenan daga bakin ma'aikatan hotel din,tun daga reception har suka kai qofar dakin data shima daya daga cikin manyan suits ne irin nasu,saboda tsarin gurin da komai na dabanne.
"Welcome sir" Kalman ya sake maimaituwa a kanta. Wani tsananin mamakin yana sake ninketa. Wato tayi kuskure......tayi kuma underestimating matsayinsa kenan?.....tunda tunaninta ma ya tsaya ne kawai a raffles makkah palace kadai yake da wannan girmamawar?,abun har swissotel ma?.....abun har askar na bakin haram.....WAYE SHI WANNAN MUTUMIN? Ta sake tambayar kanta daidai sanda taji tsoronsa yana sake shigarta,saita yanke zame hannunta cikin nasa tana daga idanunta tare da masa duban rashin yarda.
Sake matse hannun nata yayi,sannan ya daga idanunsa a hankali ya zube mata,qwayar idanunsu suka gauraya guri daya.
"Waye kai" Ta motsa labbanta zuciyarta na bugawa ta jefa masa tambayar. Ido kawai ya zuba mata kamar baya fahimtar yaren da take magana dashi,sai kuma wannan murmushin da yake narkar da kowacce jijiya dake riqe da zuciyarta ya subuce masa,sannan ya kauda kansa a hankali daidai sanda maleek ke bude qofan dakin.
Dole ta janye dubanta ta maida kan maleek din,sai taga yaqi kallonta,idonsa akan haisam.
"Fito" Haisam ya furta a nutse yana watsawa maleek idanunsa. Yayi kuma maganar ne ba tare da yabar maleek yace komai ba
"Am....amma tana ciki....."
"Muna iya komawa ni da ita?" Ya fada yana nuna akhnan da yatsarsa.
Sosai ya fahimci abinda haisam ke magana akai,kishi.....kishi ne da bazai barshi ya shiga ciki ba,shima kuma bai yarda ya koma ba duk da matarsa tana ciki. Dole kuma yana buqatar wani,wanin da zai lallasar masa falaak din ya kuma bata taimako bayan wanda yayi iya yinsa.
Matsawa akhnan hanya maleek yayi yana fitowa,saidai bai yarda sun hada idanu ba,sai wani gaisuwar babbar yaya da yake mata.
"Barka da warhaka tanti.....ina fata kina lafiya" Ita bata ma fahimci wannan abun nasa ba,hankalinta dari bisa dari yana kan falaak,bata taba zaton ta damu da ita ba sai yau,yau din da taji batun kisa. Mamaki kuma ya kamata ganin maleek ya fito gabansu,ba alamun jini ko wani abu na kisa a tattare dashi,kawai tunda taji alamar haisam ya sake mata hannu saita zame da sauri ta wuce ciki.
"Fito munafuki" Haisam ya sake maimaitawa yana zubewa maleek idanu. Murmushi kawai maleek ya saki suna takawa zuwa lobby din dake daura da gurin,wanda aka qawatashi da kujerun zama daidai da yadda masu zama a gurin zasuji dadin zamansu.
Kai kawai maleek ke girgizawa,ya gaza amsawa haisam kalman munafukin daya kirashi.
"Kayyasa......wallahi mun dade a matsayin buhunhuna kuma bahuna......ashe naseeb ya fimu wayo?,me yasa duka shekarun nan muke zaune bamuyi aure ba?" Shuru kawai haisam yayi,da wannan kalar cikakkiyar nutsuwar tasa yake kallon maleek. Yanason gano abinda yaji ba'a kalamansa ba,a yanayinsa da yadda maganan ke fita daga can qasan zuciyarsa. Bazai qaryatashi ba,idan ya gwada da abinda ya faru dazu dashi baisan me ya sanya maleek wannan sambatun ba. Bayason jin komai,kamar yadda yasan maleek din shima ba fada zai ba,amma sambatun da yake masa yayi yawa,yana tsoron kuma amanar sultane a hannunsu,kada yaci gaba da tafi da falaak din a haka,shi yasan illar da irin hakan yake haifarwa a matakin farko tsakanin ma'aurata.
"Wanne irin rashin imani ka gwadawa d'iyar mutane?,kanason taci gaba da gudunka?" Sakin baki maleek yayi ya zubawa haisam ido.
"Captain......anya kuwa kaje inda naje?" Tambayar ta dan zowa haisam da nauyi,sai kawai ya lumshe idonsa ya budesu duka akan maleek,don ya sani,idan bai sauke masa nauyi me yawa ba daga cikin idanunsa ba yanzun sai ya sauka daga kan layi ko shi ya saukeshi.
"Ba wannan na tambayeka ko nace ka tambayeni ba.....ba huruminka bane" Idanun sunma maleek nauyi yadda aka saba,ya dauke kansa zuwa gefe saboda a yau dai yana jin bazai fasa yiwa haisam tsiya ba ko bata da yawa
"Allah ya sani ni bada niyya bane,bansan ma yadda akayi komai yazo a haka ba.....amma dai yadda kamin tambayar nan ne captain sai ake gayamin bakaje ko ina ba shi yasa ka tuhumeni,inda ka bude littafin kayi karatunsa da kyau Allah ba zaka tuhumeni ba,saboda kaima......" Saukar wani irin duka a gadon bayansa ya dakatar da jawabinsa,koda ya waiwayo sai yaga haisam ne,kuma sake mulmule hannunsa yakeyi,ba shiri ya matsa zuwa mazaunin gaba
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Fisabilillahi ina kan sharafina zaka tsugunnar dani....."
"Gwara ka tsugunna din ai......kaga sai kuyi jinyar,tare mara imani" Dariya maleek ya fashe sosai dashi
"Um....um fa captain.....kada lokaci yayi muzo muna wasan 'yar buya fa?".
"Wasan 'yar bacewa zamuyi" Ya fada yana danna masa harara,dole maleek ya sake sakin dariya sosai yana duban haisam.
Qafafunta har rawa suke sanda ta isa bakin gadon dake a yamutse kamar na 'yan dambe.
"Falaak" Ta kira sunanta muryarta tana rawa ta kuma haura gadon da sauri tana rarumar falaak din.
Rungumeta tayi sosai a jikinta,ita kuma falaak din ta saki kuka sosai tana riqe akhnan din itama.
"Me yayi miki falaak.....me yayi miki?" Tambayar kawai da akhnan din ke iya maimaitawa kenan a rude tana sake riqe falaak sosai cikin jikinta. Idanunta akan fuskarta da taga ta wani rame lokaci daya ta fada sosai.
"Ba komai" Amsar da falaak ta iya bata kenan. Batasan yadda zata mata bayani ba,batasan me zatace mata ba,saida tazo sannan takejin wata kunyarta tana danneta,damuwa da rudewar kuma data gani tattare da akhnan din saita qara mata qaunarta sosai.
Tambayar duniya amma amsar falaak itace ba komai,dole akhnan ta saketa a hankali tana fadin.
"Na baki ruwa?,bakinki kaman ya bushe....jikinki da zazzabi sosai".
"Wanka nakeso na sakeyi,ruwan dumi nakeso sosai" Kai akhnan ta daga mata jikinta har yanzu rawa yake,don bata gamsu da abinda falaak ta fadinba,bata taba ganinta cikin wannan yanayin ba duk da ba wata doguwar alaqa bace a tsakaninsu.
Hannunta ta dauke da dan sauri jin ta dorashi saman wani danshi danshi..
"Jini?!" Ta fada a rude tana duban falaak,saita sake maida idanunta akan bedsheet din. Nan gurinne kawai keda jinin,amma akwai wasu gurare da ya danyi staining kadan kadan.
"Falaak......ki fadamin ne yayi miki....jini fa nake gani,ki fadamin ko na kira sultane yanzun nan"
"Ba komai.....ba komai tanti" Falaak ta fadi idanunta suna rau rau da hawaye. Ido ta zubawa falaak ranta yana baci,da alama yarinyar soyayya ta rufe mata idanu ne har bata ganin laifinsa,ita kuwa ba zata bari ba.....ba zata bari kowa a cikin su ya cutar dasu ba don suna ganin ba qasarsu suke ba,kawai saita sauka daga saman gadon da hanzarinta,don ta tuna wayar haisam din ya zameta a hannunta sanda zasu shiga elevator.
A nutse ya daga idonsa daga kan waya ya maida kanta sanda take fitowa daga dakin,ya zuba mata idanu ganin tana waige waige. Miqewa yayi tsam,don shi kadai ne a gurin,maleek ya sauka can first reception zaya karbi saqo.
"Wayata zaka bani" Ta fada tana miqa masa hannunta. Hannun yabi da kallo,gefan hannun rigar tata ya danyi stain na jini kadan. A nutse ya sauke kallonsa cikin qwayar idanunta. Yana karantar wani fushi da zafi sosai cikin idanunta
"Kiyi me da ita?" Ya tambaya calmly.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽