
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 33
..... he stood still and froze in place. Some kind of situation, what really burdened her, why didn't she stop and not pull back, a stick came near her, now he said some words to her and their weight made her feel like she couldn't lift her feet. "Uhmmm.....tell me....what will you say to the sultan if you don't call him, I'll help you call him." He said while pressing his phone as if to ask for the Sultan's number. As soon as her energy was taken away, her ideas disappeared. Why did I tell her so directly?, she just looked at him and her mouth was unable to say anything. Sanda raised his eyes and they met hers, raising both of his eyebrows. "You keep staring......uhmmm tell me what are you going to tell him?" Her eyes dropped with a kind of coldness, then she took three steps back in a tactful way, then she turned around with a cold feeling and disappeared into the room. When you look at her, how fast she is, he will tell you that there are things that compel her, and there are things that she avoids, but the speed does not match her character. He didn't smile at him, he bit his lower lip, he slowly moved back and sat down after putting the phone by his side. She stood for a long
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 33*
"Na kira sultane.....na fada masa jini har a kwancinta amma taqi gayamin abinda yayi mata....bayan dazun zai kasheta tacemin" Tayi maganan tana sauke numfashi da alamun fushi sosai a fuska da muryarta.
Wani irin kyau tayi masa.....wani irin kyau daya sanyashi lumshe idonsa sannan ya budesu dukka akan fuskarta. Bai taba ganin fushinta na gasken gaske ba sai yau.....wani irin kyau fuskar tayi yadda ta tsuketa.
"Ba zata gaya miki ba.....kema ba zaki kira sultane ba....kije ki taimaka mata kawai ya isa".
"Jini fa a jikinta?,sannan kace kada na kirashi?" Ta qarashe fada tana kallon yadda yake takowa inda take yana rage tazarar dake tsakaninsu. Bata matsa baya ba,saboda ranta a bace yake da gaske,wannan ya basu daman tsaiwa sosai gab da junan da cikakken motsi dayansu yayi yana iya cike gap din.
"Sun cika aurensu ne.....zaki fallasa sirrin first night din wasu ne?" Dummm taji kanta yayi mata,hannunta dake pointing wani guri ya tsaya cak ya qame a gurin. Wani irin yanayi me nauyin gaske ya saukar mata,shin me yasa ma ta tsaya bata ja baya ba sanda yazo dab da ita,gashi yanzu ya fada mata wasu kalmomi da nauyinsu ya sanya takejin kamar ba zata iya daga qafanta ba.
"Uhmmm.....tell me....me zakice da sultane din idan kin kirashi,I’ll help you call him." Ya fada yana latsa wayarsa kamar me nema mata number sultane din.
Kaf energy dinta aka kwashe,idea dinta kuma ta bace. Shi baida kunya fisabilillahi?,meye na gaya mata haka kai tsaye?,saita samu kanta da kallonsa kawai bakinta ya gaza cewa komai.
Sanda ya dago idanunsa sai suka hadu da nata,ya dage giransa dukka biyun.
"You keep staring......uhmmm tell me me zaki gaya masa?" Idanunta ta sauke da wani irin sanyi,sai tayi taku uku baya cikin dabara,sannan ta juya da wani zafin nama tana arcewa cikin dakin.
Da kallo yabi bayanta,yadda take saurin kawai zai gaya maka akwai abinda ya tilastata,akwai abinda kuma take gujewa,amma sam saurin baiyi matching character dinta ba.
Baisan ya akayi murmushi ya subuce masa ba,ya ciji gefan lips dinsa na qasa,ya koma da baya a hankali ya zauna bayan ya ajiye wayar a gefansa.
Ta dade tsaye tana kallon falaak sannan ta tattaka tana mata sannu. Tsoro sosai ya dinga mamayarta sanda taga falaak din na takawa da dabara zuwa toilet. Abinda bata taba ba,yau itace da yaye bedsheet da kanta,bedsheet din data ji qwalla da tsoro sun kamata da taga ragowar jinin da yayi staining a jiki.
"Maza basu da imani" Ta samu kanta da fadi itakam ta yaya ma zata bari akai wannan abun bare har ayi mata irin wannan aika aikar?.
"Kina da tabbaci?" Zuciyarta tayi mata tambayar data kusa tsayar da bugun numfashinta saboda tsoro.
Ita ta taimaka mata da iya abinda zata iya ta gasa jikinta,saidai ko gurin gyara gurin falaak din ta lallaba tayi. Koda akhnan batayi mata komai ba zuwanta ya bata relief sosai. Kallon falaak kawai take jikinta a sanyaye tsoro yana kamata,to amma sai take samun sassauci idan ta tuna ba wani soyayya bane a tsakaninsu da zai kaisu ga wannan,uwa uba ma daki daban daban suke kwana,ba kaman falaak ba data lura suna sharing daki daya ne.
"Ke kinsan haka yake,me ya kaikai sharing daki dashi?" Tambayar ta bawa falaak mamaki da dariya can qasan ranta,da gaske akhnan batasan haka abun hake yake ba?,inde haka ne kuwa akwai qura,sai ta yanke tayi mata gwari gwari kawai.
"Haka abun yake tanti....haka kowacce mace takeyi"
"Take uban me falaak?,kinsan me kike fada kuwa?" Ta fadi har batasan tayi spark ba saboda wani tsoro da falaak din ta qara mata. Qasa tayi da kanta dariya nason qwace mata amma tana dannewa. Da gaske koda akhnan tasan da wannan abun amma sam bata taba kawoshi a lissafinta ba sam a cikin aure.
"Da gaske nake....ki kira tanti hairaaan kiji"
"Akanme?.....ni bazai faru dani ba bare na nemi sani,kema Allah ya baki lafiya ke kika jama kanki" Ta fada tana yamutsa fuska. A yadda taga falaak din a yamutse saboda abu qwaya daya tak ita saita bari ya faru da ita?.
"Duk fa wayon amarya sai ansha man ta.....kin manta?"
"Falaak.....ki kama kanki" Ta fada tana tsumewa
"Inacan tausayinki kamar zai hallakani,amma ke alfahari ma kike da abun?". Ta fada a qufule
"Dole nayi alfahari mana....nakai mutuncina gidan mijina,mijina na sunnah ne ya karbu budurcina abun alfahari ne yaa biftu,ina fata kema ya faru a kanki zakifi fahimta" Ta fada a ranta amma a fili sai tayi qasa da kanta tana cewa.
"Kiyi haquri na daina"
Knocking akayi aka turo ana shigowa,maleek ne,sai a sannan akhnan taga basarwar da yaketayi,sai yanzu ta fahimta
"Mugu" Ta fada qasan ranta tana jin haushinsa yana saukar mata. Wayarta ya ajiye mata a gefe yana cewa.
"Captain yace ki duba akwai saqo".
"Captain?" Ta maimaita tana daukan wayar,don sunan baqo ne a kunnuwanta,bata ma kuma gane wanene ba.
Procedures ne na yadda falaak zata samu relief a rubuce cikin wayar ya rubuta ya ajiye a notebook dinta. Kunya taji ta kamata sosai gauraye da haushi,har shima wai yasan meye ya faru ne?,kawa saita dan kai idanunta kansu maleek.
Yadda ya gwaggwafe gaban falaak din riqe da yatsunta yana murzawa,har ita dake gurin bata iyajin abinda yake gaya mata ya aza mata nauyi da yawa,kawai sai taji ba zata iya zama ba,ta miqe tsam,daidai sanda yake fadin.
"Tanti....ki zauna fita zanyi"
"No" Tace a taqaice kawai tana takawa gami da ficewa a dakin.
*_A G A D E Z_*
*_SULTANE PALACE_*
Zaune take a gabansa cikin nannauyar kwalliyar na dake cike da alfahari da kuma nuna isa,kwalliyar data qara adadin nauyinta don ta boye ramar data fara yi wadda ta bayyana kadan har a qasusuwan wuyanta.
Tun daga watannin baya,ranar da gobara ta tashi a gidan. Bacewar tamim.....bacewar yalwa,gobarar villa dama dauki daidai din da akewa hadimanta,har xuwa ranar qarshe da 'yan jarida suka dirar mata bata sake baccin kirki ba.
Kaman zatayi sanyi,kaman zatayi collapse,kaman zata saddaqar amma kuma zuciyarta ta gaya mata KI TASHI ZAITUNA!.
Wani irin salo take gani tattare da yaron da dawowarsa yafi haihuwarsa zame mata barazana a rayuwarta. AHMAD yaron data kowacce fuska baka isa ga qaryata jinin sultane bane a jikinsa.
Bai rayu dasu ba....bai rayu cikin masarautar ba......amma yasan kowanne nau'in salon sarautarsu.....lungu da saqo na cikin gidan.....adadin ma'aikata dama komai dake wanzuwa a cikin gidan. Batayi mamaki ba.....kasancewar ALSAAMIT tattare dashi zai iya zama mafi girman hatsari fiye da haka.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Wani irin takawa d'ai d'ai taga kaman morsa safiyya tanayi.....wani irin girma ta fuskanci kanta yanayi......abinda ya hanata bacci darare da yawa.....saidai kuma ta samu babban makama sanda ta soma lura da rade radin da kuma gani da tayi da idanunta SULTANE bashi da wani cikakken qwari da lafiya.
Murmushi tayi sanda ta lura da wannan
"Wataqila ina da sauran dama ne.....daman da zata zamemin ta qarshe" Ta kama damar da kyau kuwa,ta fara kusanta kanta da sultane matuqar kusantawa. Abinda ya bata mamaki yadda take samun cikakken dama da access da komai,saidai cikas kadan kadan da take samu daga ahmad din.
Yaron da idan hanya ta hadasu yake mata wani irin kallo,kallon data tabbatar idan har yana da dama.....idan har zai yuwu zai iya daukan wuqa ya kaita lahira.
"Ta yaro kyau take bata qarko..... Ka daina dariya wasa yayi kyau.....wannan zaqin mulkin......wannan darajar da wannan matsayin gaba daya na 'yan kwanaki zuwa watanni ne....zaka sake bacewa bacewar da har abada ba zaka dawo ba" Haka takan fadi cikin ranta,amma a fili saita bishi da murmushi.
Kamar yanzu da take zaune gaban sultane din,tana yanka masa fruit din tana bashi yana sha,tana kuma jansa da hira a nutse.
Tun daga nesa ta hangesu,morsa safiyya ce cikin wata irin shigar kamala dake bayyanar da darajarta da wani irin Kwarjini. Ahmad yana biye da ita a baya da wani kalan girmamawa tamkar yana fadawa duniya ITADIN MAKWAFIN MAHAIFIYATA CE.
Ta zuba musu idanu da gaske,har cikin tsakiyar zuciyarta tana jin wani irin zugi a duk sanda ta gansu a haka. Dawowarsa ta sake qarawa morsa safiyya wani irin girma da martaba da bata zata ba,saboda kowa kiranta yake UWAR YARIMA ME JIRAN GADO.
Duk kuwa da yadda taso sunan ya zamana nata ne.....ko ta hana tasirin sunan,amma ko daya a ciki bata samu nasara ba.
Akwai tarin mutane masu yawan gaske dake neman kusanci da Ahmed din,wanda kusancin yana da muhimmancin da dole kowa ya buqaci wannan gurbin a kusa dashi.
A zahiri saita saki fuskarta,tana maida dubanta ga sultane da bai lura da tahowarsu ba.
"Ga magaji nan zuwa shida mamarsa". Kansa ya daga zuwa sashen,yana duban Ahmad yana jin wani abu me girma yana motsawa cikin zuciyarsa. Baisan dame zai yiwa haisam sakayya ba....duk da har yanzu baisan yadda komai ya kasa ce ba har yanzu.
Murmushi kawai yake saki har suka iso,murmushin da mammina take jinsa kamar tsiruwar allura saman naman zuciyarta.
"Barka da hutawa" Morsa safiyya ta fada tana cire takalmanta a girmame tana qarasowa gabansa.
"Bakanki uwar yarima" Murmushi ya subuce mata tayi qas da kanta,yanayin da ya masa kama sosai da safeena.
"Da kanka me martaba?"
"Sunan ya dace da wadda aka bawa ai......ga maman gimbiya....ke kuma ta yarima ce" Ya fada yana nuna mammina data qaqalo murmushin dole. Idanu morsa safiyya ta daga ta kalli mammina,cikin sa'a ita ita take kalla,sai kawai safiyyan ta ajewa mamminan murmushi tana dauke kanta. A yanzun bataga komai tattare da mammina ba sai wata kwantacciyar damuwa,damuwar da duk dare saita tsaya saman abun sallah ta kaiwa Allah sunanta. Allah ya hanawa rayuwarta sukuni muddin da haqqin safeena saman wuyanta.
"Zamankin nan a gabana.....sai naga kaman safeena ce" Ya fada zuciyarsa tana masa nauyi.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽