
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 39
.....in. She closed her eyes again and felt how the soft palm of his hand and its warmth passed through her head. "Hello...." He said with a voice that showed a lot of care and concern in his voice. She moved her lips with the intention of telling him about herself... her head was hurting so much, but the palm of his hand on her neck stopped her mouth. Slowly the pain on the top of her neck goes through the skin of his hand and sends something to his body parts, he slips his hand slowly and relaxes, just as the message arrived from the clinic. He accepted it and came back, he put it on the bedside drawer and his eyes were still on her. She was crying.....she was crying softly, the crying that he heard was heavy on him, he stepped slowly and went out to the sitting room again. Within five minutes, this hidden prince walked into the room, carrying a tray, on which there were cops and a cup of tea and a tea flask. He quietly placed it on the bedside. He took one cup, mixed the tea a little and added honey according to his taste, because he doesn't use sugar at all. "You can get up...please God" He said with his voice that was cold and calm. The eye.....
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 39*
K'oqarin dagota yakeyi amma yanayin zafin da yaji jikinta yayi da rawan sanyin da yaji tana yi ya sanyashi saketa a hankali ya furta
"Subhanallah". Zafin kamar yayi yawa sosai,ya sanya hannunsa a hankali yana zame bargon data rufa dashi din gaba daya. Ta maida idanunta tana lumshewa,hawaye yana sauka ta gefan idonta dake rufe. Sanyi takeji.....sanyi takeji sosai,budetan da yayi ya zama kamar wani qara mata sanyin yayi.
Matsawa yayi inda ya ajiye wayarsa ya dauka yana budeta. Kai tsaye yayi kira zuwa ga clinic na hotel din.
"Ina buqatar wasu magunguna da allurai" Umarnin daya bayar kenan sannan ya ajiye wayar bayan ya bada number dakin.
Dawowa yayi ya tsugunna ta gaban gadon saman qafafunsa,ya daidaita kansa saitin nata,ya zube idanunsa a hankali kan baby face din nan nata da tayi ja,jan da zai nuna maka lallai zazzabin da takeji yakai wani mataki.
Hannunsa ya daga a nutse ya dora lallausan tafin hannunsa saman goshinta. Sake lumshen idanunta tayi tana jin yadda laushin tafin hannunsa da duminsa yake ratsa kan nata.
"Sannu....." Ya fadi da muryar dake nuna kulawa sosai da damuwa a cikin sautinsa.
Motsa labbanta tayi da niyyar gaya masa kanta.....kanta yana ciwo sosai,amma saukar tafin hannun nasa saman wuyanta ya kashe bakinta. A hankali zafin dake saman wuyan nata yake ratsa fatar hannunsa yana aike da wani abu zuwa sassan jikinsa,ya sake zame hannun nasa a hankali yana sauke ajiyar zuciya,daidai sanda saqon ya iso daga clinic din.
Karba yayi ya dawo,ya ajiye saman bedside drawer idanunshi still a kanta. Kuka take.....kuka take a hankali,kukan da yaji ya masa nauyi,ya taka a nutse ya sake fita zuwa sittingroom.
Cikin mintina biyar wannan hidden princes din ya tako zuwa cikin dakin,dauke da tray,wanda samansa cops ne da wani butan shayi me zubin tea flask.
A nutse ya ajiyeta a gefan bedside din. Cup daya ya dauka,ya hada tea din dan kadan ya zuba zuma daidai da irin taste dinsa,don baya amfani da sugar kwata kwata,sannan ya matsa gaban gadon,ya koma ya tsugunna gaban gadon yana sauke idanunsa a kanta.
"Zaki iya tashi......don Allah" Ya furta da muryar nan tasa dake da wani sanyi da nutsuwa. Idonta ta kulle sosai tana girgiza kanta alamun a'ah. Shuru ya gilma a tsakaninsu na sakanni.
"To na taimaka miki ki tashi?" Ya sake fadi yana kwantar da kanshi kamar me neman wata alfarma. Kai ta sake girgizawa.
"Pleeeeaaase" Ya sake fada yana hada hannayensa guri daya. Yadda ya danja kalmar ya sanya taji wani abu me sanyi yana narkewa tsakiyar sanyin da jikinta ke bala'in ji,sai tayi shuru ta kasa cewa komai,wannan ya bashi damar miqa mata tattausan tafin hannunsa dake da wani irin haske me kyau. Jirkitattun idanunta ta bude tana kallon tafin hannun nasa. Suna burgeta.....suna burgeta har batasan iyaka ba. Suna saukar mata wani irin yanayi duk sanda zai hadesu cikin nata.....amma a yanzun sai taji kunyar fara dora nata hannun saman nasa. Baya ga haka rigar jikinta......rigar jikinta tayi tsiraici da yawa,amma kuma batasan yadda zata gaya masa ba. Ba bra a jikinta,sannan saman rigar wani irin net aka shimfida red color daya manne da fatarta sosai ya haska gurin matuqa da gaske.
Bata gama daidaita tunanin ba taji an dagata cak,abinda ya sake razanata ya sanya kanta ya sara kadan jin yadda yake rabata da gadon da dukka hanuwansa kamar wanda ya dauki takarda.
Hannuwansan ta riqe sosai jikinta da bakinta suna rawa,ta rungumesu sosai cikin jikinta. Tanaso tace masa ya sauketa,tanaso tace masa ya barta ta lullube jikinta,tanason ta gaya masa ba wata riga me kauri bace a jikinta amma dukka tsoro ya hanata,ya qarasa gigitata gaba daya sanda taji yana ajiyeta saman kujera gayarta.
Daga sanda ta rungume singalalin hannunsa cikin jikinta,daga sannan yaji ta dasa masa wasu boyayyun halittu cikin jikinta ta aike masa da wani irin makami me qarfi daya soma raunata qarfinsa. Ya sani ba cikin saninta bane zata bashi access da gurin har haka......yayi kuma yaqi sosai da idanunsa akan kada ya kalli gurin. Ya samu nasara,don yana sauketa ya koma ya tattaro mata duvet din saman gadon,ya zagaya ta bayanta ya soma dora mata shi daga saman kafadunta yadda zata zama comfortable,saidai ina.....duk yadda yakai ga son kaucewa kallon gurin.......a sanda yake zagayowa gabanta yana qarasa rufe mata jikinta saida idanunsa suka sauka akai. Fatar gurin tayi wani haske sosai ta sanadin redlace din da aka qawata gaban rigar dashi. Kamar wancan ranar......suna tsaye kyam kamar wadanda suke gayyatarsa zuwa garesu. Wani abu ya fusgeshi har jikinsa yayi shaking kadan,ya cije lips dinsa yana qarasa lullubeta.
"Calm down......calm down haisam" Yake gayawa kansa da kansa can cikin kwanyarsa. Saidai duo da wannan qwarin gwiwar da yake bawa kansa hakan bai hana kowacce laka ta jikinsa zarewa ba.
Da wani irin laushi ya jawo wata kujerar zuwa inda take zaune. Ya zauna dab da ita,saidai kuma kusancin yayi mata yawa don tana iya jin gwiwarsa tana gogar tata a hankali a duk sanda ya motsa. Idanunsa ya lumshe gami da budesu duka a lokaci guda yana qoqarin controlling kansa. Ya dauka iya wancan wajenne kawai.....ya dauka sune kadai abinda keda qarfin karyashi da kuma raunata karsashi da kuzarinsa......sai gashi a yanzu ya gano wani abu na daban. Dogayen zara zaran yatsun hannunta.......sassalkan gashin kanta daya sauka har kusa da mazaunanta,ya kuma yi mata ado daga gaban goshinta har zuwa bayan kunnuwanta da gaban kunnen nata,yabar mata wani saje me kyau. A duk sanda zai kalli fuskarta da tayi wani fayau....da siraran labbanta da suka danyi dry kadan saboda zazzabin sai yaji wani abu yana tsarga masa.
"Take it" Ya fada cikin laushi yana miqa mata cup din tea din daya dauko. Wannan blue eyes din nata da sukayi laushi ta zuba masa,sun tara ruwan hawaye sosai. Ita din ba gwanar abinci bace ko lafiya lau ballantana yanzun da bata da lafiya. Idan tana lalura ruwa kawai take iya sha.....ba magani ba abinci. Tana iya tuna yadda hankalin mammina ke tashi a lokacin,tayita zarya a kanta har sai ta tilastata taci wani abun.
Kai ta girgiza masa alamun ba zata sha ba. Idanunsa ya zuba mata a hankali yana kafeta da kallonsa,wannan kallon dake iya tilasta maka yin abinda yakeso koda baka shiryawa hakan ba. Wani irin magnet yake fusgarta dashi,wani irin kashe mata sassan jiki dana zuciya idanunsa sukeyi.....bai sani bane?" Ta tambayi kanta tana qoqarin lumshe idanunta ko zata rage tasirinsu,saboda tana jin yadda wani bala'e'en sanyi yake sake ratsata.
"Karbi" Ya sake maimaitawa da sigar umarni. Hannunta ta miqa tana karba,yatsunta suka sauka saman nasa,ya lumshe idonsa a hankali yana budesu gami da zubesu akan yatsun nata da jan lalle ya yiwa wani irin kyau kamar dashi aka halicceta.
Dan qaramin bakinta yabi da kallo sanda tak sipping tea din a hankali,ya sake zare dubansa yana jin wani irin abu yana yamutsa masa
"Ya salam......haisam.....haisam" Ya kira kansa da kansa internally wai ko zaiji wani abu daban ya amsa kiran bashi ba.
Dan qaramin abu ya shimfida mata saman duvet din da take lullube dashi don kada ta batashi,saidai ko kurba biyar batayi ba ta sauke cup din tana langabe kai idanunta cikin nasa.
Bata tana ciwon da taci abinci haka ba,kuma ko a yanzun tasha yakai har hakanne saboda tsimammun idanunsa daya kafeta dasu.
"Ya isa" Lumshe idon ya sakeyi ya budesu duka a lokaci guda da wani irin calmness,ya motsa kyawawan labban nan nasa masu wani irin surkin red da pink.
"Ki sake qarawa" Ya fada a hankali kamar bayason yin maganar. Inda wani ne.....inda kuma zata iya zatace masa aah,amma kaifin idanunsa baze bari tace komai ba,ta langabar da kanta,ta sake kurba uku,wannan karon a shagwabe ta fadi.
"Ya isa" Saboda yadda taji kamar zai dawo. Dif yayi wani abu yana tsinkewa cikin kansa. Yadda tayi maganar da wata irin narkakkiyar shagwaba saita zama kamar tsokana a wajensa. Bai iya cewa komai ba,ya miqa hannu ta saka masa mug din ya maida saman tray din,sannan ya matsa baya yana jawo ledar da aka kawo daga pharmacy din.
*_Assalamu alaikum warahmatullah_*
*_Akwai pyjamas/home wear/lounge wear tsala tsala masu dadin zaman gida da bacci_*
*_Sabbi kar a mutunce cikin jakarsu,a affordable price_*
*NA IYAYE DA YARANSU*
*_kina kasuwancinsu?,Maza zoki gwada wadannan dana kawosu......quality dinsu ya girmi farashin_*
*_ki siga ki siyawa yara.....masu dadin sawa a zafinnan.....ga taushi ga ba nauyi_*
*_maza tuntubi huguma ta nan don ki ganewa idanunki_*
08187255862
Zazzagesu yayi saman gadon yana dubawa. Duk da azababbben sanyin da takeji hakan bai hanata qare masa kallo ba,idanunta can qasa kamar bashi take kalla ba. Komai nasa very calm,ba calmness me tattare da sanyin jiki ba.....aah calmness me cike da kuzari,saidai nutsuwa ta mamayi komai nasa. Tana jin wani tsoro yana mamayeta,tsoron yadda ya sanya take fara jin wani abu me qarfi cikin zuciyarta tattare dashi. Tsoron MEYE WANNAN? Da yake dasuwa a zuciyarta ba tare da shawara ko neman izini ba. Tsoron wani irin feeling.....strong feeling da bata taba jinsa tattare da kowa ba. Nutsuwar nan tasa me cike da izza shine abu na farko da yake sake daukan hankalinta.
Tsugunnawar daya koma yayi ya sakata janye idanunta cikin tsoron kada ya ganta,a daidai sannan idonta ya sauka akan allurar daya dauko yana farketa a ledar yana kuma ajiye cannula a gefe.
Hantar cikinta ta kada sosai,wani tsoro ya saukar mata a hankali.
"Allura" Ta fada a hankali tana jin tsoro yana sake shigarta. A tun tasowarta magani da allura suna cikin manyan abokan gabarta. Magani da allura suna cikin abubuwan da sam bata shiri dasu. Tana iya boye ciwo kawai don kada ace ga magani.....tana iyayin zamanta da ciwo kawai don kada ace za'ayi allura.
Tayi rau rau da idanunta sanda ya zauna a gabanta,idanunsa cikin nata,nata kuma yana kan allurar tana sake narke idanun nata,ruwan hawayenta suna sake daduwa. Ji takeyi kaman nata ya qare......har wani qarin sanyi takeji yana sake ratsata.
Duba daya yayi ma qwayar idanunta,Karo na farko da yaga raunin wannan princess din. Karon farko da yaga hawaye a idanunta har haka,karon farko da yaga lagonta akan zazzabi da allura.
Dogayen yatsunsa ya miqa mata,saita daga idanunta tana kafeshi da kallo a wani mugun tsorace. A wannan lokacin banda yayi da mugun gaske dariya ce tsaf zata kubce masa. Duk tsaurin ran mace da kafiyarta,qanqanin abu kaman allurar sai ya tsorata ya raunatata ya kuma nuna rashin qarfi da wayonta.
"Eheennn" Ya fada yana motsa mata yatsunsa alamun ita yake jira ta bada hannun yasa mata cannula. Noqewa tayi tana sake cukuikuyewa cikin duvet din kamar zata bace a cikinsa,sanyi kuma yana sake kadata.
"Please" Kawai ta fada da turanci duk da bata shirya magana da harshensa ba. Idanunsa ya kafe mata,sannan a hankali idanunsa suna lumshewa......wani irin kasala yana lullubeshi da kalan shagwabar da yake gani a yau dim tattare da ita. Ta narke gaba daya,kaman ba itace wannan princess din ba,.....me qarfin halin marin d'a namijin daya shiga gonarta duk girmansa da matsayinsa. Wadda ta kada 'yan maza goma sha hudu.....takejin komaima ta tsere masa tafi qarfinsa.
"Bakya ganin yanayinki?.....temperature naki is so high......zaki iya shiga level na convulsion fa?" Ya fada yana dage dukka girarsa biyun sama da wani sautin da koda kana cikin dakin ba lallai kaji magananshi.
Allurar da cannula din ta sake kalla sannan ta kalleshi.
"Kinaso na riqeki ne?" Saita girgiza kanta da sauri hawayen data maqale yana sauka daga idanunta
"Am.....amma ka cire wannan" Ta fada da rawar murya tana nuna cannula din. Idanunsa ya janye daga kanta,haka kawai yaji wani irin tausayinta yana ratsashi. Yaso yayi amfani da cannula din saboda allurar tafi saurin bin jininta ta sauke zazzabin,amma tunda haka ta zaba,sai yaji bari ya cire din.
*_Assalamu alaikum warahmatullah_*
*_Akwai pyjamas/home wear/lounge wear tsala tsala masu dadin zaman gida da bacci_*
*_Sabbi kar a mutunce cikin jakarsu,a affordable price_*
*NA IYAYE DA YARANSU*
*_kina kasuwancinsu?,Maza zoki gwada wadannan dana kawosu......quality dinsu ya girmi farashin_*
*_ki siga ki siyawa yara.....masu dadin sawa a zafinnan.....ga taushi ga ba nauyi_*
*_maza tuntubi huguma ta nan don ki ganewa idanunki_*
08187255862
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽