
Post
L U'U L U'U BOOK 3 PAGE HAUSA NOVEL PAGE 44
...... but first of all, that's not all..... we miss you like we've never done before, but I'll tell you the truth this time..... we're not here..... we welcome you as our guest..... can you be a little patient and finish watching this beautiful soul who managed to steal this heart that has failed to be opened to every woman?" The way she was treating him? Since she couldn't hide her cousins who were waiting for him? He didn't say anything to her. He was walking past her, all her eyes were on him. She was talking to him in a language she didn't understand The confirmation of her coming to a different world. He told her that now she is not in Agadez.
💎 *L U'U L U'U* *_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 44*
Sakin labulen yayi,a jikinsa yaji alamun shigowarta jirgin,sai ya miqe a nutse yana gyara thobe dinsa,sannan ya fara takawa zuwa dan qaramin kyakkyawan curtain din da shine kawai zai haba khansaaa ganinsu.
A tare suka daga labulen shi da ita,dukkaninsu fara'ar fuskarsu ta kasa boyuwa,musamman khansaaa da sai da jerarrun fararen haqoranta suka bayyana.
"Captain obbo" Ta fada tana kallonshi cikin dariyar dake nuna zallar qaunar juna dake tsakaninsu irin na 'yan uwantakar data samu kulawa daga iyaye,da soyayyar dake nuna zallar hadin kai.
"Malka khansaa(prince khansaaa)" Ya amsa mata cikin yanayi na sakewa da juna da kuma tsokana. Murmushi sosai tayi me hade da sauti
"Xiqqaa koo(my little one)" Ta amsa masa tana dubansa kai tsaye. Ya sani,tanason tsokana ne kawai,don tana cikin wadanda mamakinsu bai buya ba sanda akace musu yayi aure tun daga agadez.
"Na sameku lafiya?" Ya sake tambayarta yana dubanta.
"Alhamdulillah.....amma dai da farko duk ba wannan ba.....kasancewar munyi kewarka irin wadda bamu taba yi ba,amma zan gaya maka gaskiya a wannan karon.....bata taka muke ba.....baquwarmu muke marabta ba kai ba.....ko zaka iya dan yimin haquri na qarasa naga wannan kyakkyawan ruhin da yayi nasarar sace wannan zuciyar da aka gaza budawa kowacce mace ita?". Murmushi dole ya subuce masa,tun a nan?,a haka ma khansaaa mutuniyarsa ce sosai.....abokiyarsa....kuma ta wani fuskan yadda take treating nasa yasa yake mata kallon nanay ta biyu? Tun a nan ta gaza boye tsokanarta?,ina ga tarin cousins dinsa da suke jiransa da sauran abokai?.
Baice mata komai ba,yayi taku biyu baya ya matsa yana bata hanya.
Da murmushinta ta rabashi tana wucewa,dukkanin idanuwanta suna kan akhnan. Kanta yana qasa daga sanda taji baquwar muryar mace suna magana dashi da wani yare da bata ganewa. Ta lumshe idanunta,wannan yaren kawai ya isa ya bata tabbacin zuwanta wata duniya ta daban. Ya isa ya gaya mata a yanzun ita ba wancan akhnan din bace.....ba a agadez take ba....ba'a Niamey take ba,ta shigo wata duniya ne ta daban.
Mamakin saurin amintar da sultane da yayi,da har ya aminta ya dauketa ya damqa masa ita ba tare da sanin ainihin tartibin ina zaikaita ba?,wayeshi?,ina zai ajiyeta a rayuwarta ta gaba?.
"Keessummaa keenya” abinda khansaaa ta fada kenan da wannan 'yar gayun muryartata me dadin sauraro. Sautin kadai shine ya fusgi hankalin akhnan ta daga kanta bawai donta gane me take fadi ba.
A take idanunta ya sauka kan fuskar khansaaa.
" Subhanallah" Ta fada can qasan maqoshinta tana hadiye wani abu. Shige idanun nan nasa ne take dashi,banbancinsu nasa yana da wani irin shape da bata ganshi tattare da wannan ba,hakanan wadannan nata idanun an zizara musu kwalli daya sake qawata idanun.
Jar lafayar jikinta na nuna zallar iko,don duwatsun da aka shiryawa lafayan kadai magana suke da madaukakin sauti zuwa nuna ainihin tsada da darajar suturar jikinta.
Hannun khansaaa data miqo mata tana sake mata wani amintaccen murmushi tabi da kallo,wani tattausan hannu da aka zanawa kyakkyawan zanen jan lalle wanda adon flowers din sukasha banban dana yankin agadez nesa ba kusa ba.
"Afaan Ingiliffaan ishee waliin dubbadhu(ki gwada yi mata magana da English)" Yace da khansaaa data rusuna a gaban akhnan. Kai ta daga ta kalli haisam,ta saki murmushi tana maida dubanta ga fuskar akhnan,wadda sai yanzu taga fuskarta sosai saboda ta tsugunna ne ta gabanta.
"Maaaa shaaaaa Allahhhhhh......subhanallah.....captain?" Khansaaa ta fadi sanda idanunta ke saman fuskar akhnan idanunta suna nuna zallar daukan hankalinta da akhnan din tayi.
Basarwa yayi,don kafin tace komai yasan akan me zatayi magana,yanayinta ya karanta masa,sai ya fara takawa kawai yana ficewa daga gurin,abinda ya sanya khansaaa sakin dariya tana maido dubanta ga akhnan.
"Mijinki miskili ne.....yana da wahalan sha'ani wani lokacin,ina fata kin fahimci hakan?" Ta fada da harshen turanci tana kallon akhnan. Sai a sannan taji kaman an sassauta mata d'aurin da akayi mata,ta fahimci abinda Khansaaa tace,saidai kuma nauyin da takeji nata haka kawai ya sanya ta kasa maidawa,sai wani qaramin murmushi data saki tana sake karantar Khansaaa a fakaice. A jikinta takeji kamar JININ SARAUTA ce ita....wasu motsi nata yana mata kama da mutumin daya fito daga royal family.
"Ina miki jinjina......ina kuma sake sallama miki da yadda kika bude wannan zuciyar me tsananin kafiya....zuciyar data shekara talatin da biyar ba macen data dauko maqullinta daidai ballantana ta samu daman budeta" Ta sake fadi da wani yanayi na raha cikin muryarta. Murmushi akhnan tayi qoqarin maida matan,amma maganganunta suna sauka saman zuciyarta a hankali.
"Kowa so yake yaga wacce me sa'ar ce tayi wannan gagarumin aikin?" Khansaaa dake riqe da hannun akhnan tana jin kamar hannun rumaisa ko na Aanani ko noorah ne ta riqe ta fada tana qaramar dariya. Dariyar data sa ya akhnan sakin murmushi a nutse tana sake sadda kanta qasa,haka kawai takejin wani irin nauyin matar da ta kasa riqe sunanta da taji ya kira.
"Bazai taba bari ki fita a haka ba,koda al'ada batazo mana a haka ba,idan ban takuraki ba,ko zaki shiga dakincan ki canza kayan jikinki?,saboda zamu wuce palace learning residence kaman yadda yazo a al'ada" Yadda take maganan cikin kulawa da taushi ya sanya akhnan binta da kallo. Akwai sarauta sosai a yanayinta,amma akwai wani sauqin kai da martaba me yawa a kallonta da maganganunta,bata gane me take nufi ba illa dai batun canza kayan kawai.
"Akwai wanda za'a kira miki don ta taimaka?" Shuru ta danyi,kafin ta lumshe idanunta ta budesu a hankali sannan tace.
"Birra" Murmushi Khansaaa ta saki,karon farko da taji muryar data matuqar burgeta ba. Ta murmusa a nutse tana dannan wani madanni jikin wani lafiyayyen agogo dake daure a hannunta,sautin muryar akhnan na ratsata,laushi da wani irin aji dake tattare da ita.
"Birra" Kawai akhnan taji Khansaaa din ta fadi,cikin qasa da minti daya qofa ta bude birra ta shigo.
"Ki tayata ta shirya" Khansaaa ta fadi cikin yaren oromo. Ga mamakin akhnan sai taga birra ta gyada kai,a maimakon taga ta rude tana neman ma'anar abinda akace mata,sai taga ta dauki luggage din ta taka zuwa dakin
"A fito lafiya" Khansaaa ta fada cikin girmamawa da harshen English. Bata da wani zabi saita juya tana bin bayan birran.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Tunda taga dakin yanzunne shigarta ta farko. Tsoro takeji ta shiga bacci ya kamata ko wani abu makamancin haka wani abun ya faru da ita,shi yasa ta shanye dukka awannin a zaune cikin luxury sofas din.
Tasha mamakin irin suturar da taga birran na fitowa da ita daga cikin luggage din. Harkar sutura ce sana'arta....bangarenta ne. Duk wani fabric da zare yarn da dutse me tsada ta sanshi. Ta sake qarewa rigar kallo da kyau,sai taga tayi mata kama sak da sabuwar rigar da companyn Elie Saab sample din da ake saka ran zasu fiddashi shekarar 2030.
Batace komai ba,tana tsaye kawai birran ta shiryata tsaf,sannan ta nadeta cikin ni'imtaccen yadi na alfarma,wanda ya qarawa rigar kyau a jikinta.
Mirror ta ajiye mata yadda suka saba a kowacce shiga da zatayi a agadez,ta taka a hankali ta matsa gaban mirror din. Wata akhnan daban take gani ba irin wadda ta sani ba,wata akhnan ta daban ba princess of agadez ba. Wata akhnan daga wata qabila daban take gani,wata akhnan da kayan da take sanye dashi ya zame mata wani irin abu na daban daya fidda wata irin sigar kyau tata,duk kuwa da cewa ta lullube kowanne abu nata da zai iya zama al'aura. Haka kawai taji jikinta yana yin sanyi,hakan kenan yana nufin ta sauya qabila?,ta sauya qasa da al'umma gaba daya?.
"Zan iya shigowa?" Taji muryar Khansaaa daga bayan qofa.
"Eh" Ta amsa mata a sanyaye tana waiwayowa gaba daya.
"Fatabarakallahu ahsanul khaaliqeen" Ta fada murmushinta yana sake qaruwa. Hannunta ta miqawa akhnan tana fadin
"Duk kowa yana waje yana jiranki,lallai dole captain obbo ya buqaci a boye wannan kyan,mu kanmu kishinmu yake ballantana halal dinsa?" Ta fadi tana murmushi sosai. Murmusawa kadan tayi don kada tabar Khansaaa da fara'arta ita kadai,saidai can qasan ranta,can qasan zuciyarta tana jin wani shafi yana budewa na sanin sabbin halaye da dabi'unsa da bata sani ba a baya.
"Sunana Khansaa ko hasnaa.....duk wanda kikeso zaki iya kirana dashi.....nice yaya ta biyu ga captain sheikh,kuma aminiyarsa".
"Captain.....sheikh....obbo" Duka sunayensa ne?.
Zata iya cewa sunan sheikh dinne kawai ba baqon suna ba a wajenta,amma gaba daya sauran baqi ne a gurinta.
Ta daga kanta a hankali sanda suke dab da bakin qofa,sai idanunta suka sauka a kanshi. Yana tsaye fuskarsa na fidda wannan hasken,wannan kwarjinin da haibar shimfide saman fuskar tasa,saidai kuma mayen waya....mayen waya ne kaman yadda ta soma laqaba masa. Idanunsa suna kan wayar yana danne danne.
"Bismillah captain" Hasnaa'u ta fada tana miqawa haisam hannun akhnan. Sai a sannan ya daga fararen idanunsa ya saukesu a kanta.
"Ya hayyu ya qayyum.....ya zaljalalu wal ikram" Ya fada can qasan maqoshinsa adams apple dinsa yana motsawa sama da qasa.
Wata mace daban yake gani.....haihuwar qabilar oromo.. Wata matashiya yake gani daban ba khadeeja muhammad hammud ba cikin tufafin al'ada na sarautar jimma oromo. Sai yaji wani sanyi yana ratsa sannan jikinsa.....wani abu yana mamaye ilahirin jikinsa,ya dauke idanunsa a hankali yana duban gaban jirgin da mutanen da suke jiran saukowarsu.
"Su waye da waye a waje?" Ya tambayi Khansaaa da yaren oromo,da wani irin yanayi da kasala ke bibiye da sautinsa,kasalar da yanzu yanzu ta saukar masa.
"Daga nan yan uwa ne na kusa,daga can farfajiyar airport din kuma bazance ga adadi ba". Idanunsa ya lumshe a hankali saman fuskar Khansaaa sannan ya budesu. Da iya hakan kawai da yayi ta iya karantar yanayinsa,ta kuma iya gane me yake kaikawo cikin zuciyarsa.
"Kayi haquri captain.....iya na yau ne kawai,dukka masoyane dake daukin dawowarka" Ta amsa masa tana qunshe dariyarta. Shuru ya sakeyi baice komai ba,still cikin kwantar da kai tace.
"Ba wani abu daya bayyana,nayi amfani da sutura mafi suturcewa cikin kayan mu na al'ada" Ta fadi tana karyar da wuya. Tasan halinsa.....wani irin farin sani datayi imanin idan bata zama ta uku bayan moti da nanay ba bazata zama ta hudu ba.
Bai amsa ba still,saidai ya miqawa akhnan hannunsa,hannun da tabi da kallo a hankali ta aza nata cikin nasa.
Dukkaninsu kusan a tare kuma lokaci daya suka sauke wata boyayar ajiyar zuciya. Ba wanda yasan dan uwansa yayi amma Khansaaa ta lura hakan,ta saki siririn murmushi ta koma bayansu ta tsaya.
Ta jima tana burin ranar da zataga yadda haisam zai fada soyayya,wala'alla tsohon burinta ne yake dab da cika.
A hankali ya kalmashe siraran yatsunta cikin nasa da wani irin yanayi daya tilasta masa lumshe idanunsa,ya fara takawa sai itama ta fara takawa tare dashi suna nufar qofar fita daga jirgin.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875* *Safiya musa abdullahi* *Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261* *Safiya musa abdullahi* *NITA* *CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA* 09166221261
*SHAIDAR BIYA* 08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽